Sashe 148
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
window yana kallonsu bai ce komai ba, Haseenah kuwa sai kururuwa take tana juye juye saman gado tana cewa wayyo Allah zata mutu, Aunty Fauziyya da Aunty Farida suka fice daga ward din Murja da kawar Aunty Farida suka bi bayansu, dama mijin Aunty Fauziyya babban dan sanda ne amma yana Abuja kuma daga kanon aka maida shi Abujan, tana fita ta kirasa a waya tana huci tace "Abban Ikram wallahi mun zo asibitin abun ba na wasa bane, ya wuce yanda muke tunani Abban Ikram, yarinyar tayi raga raga da kanta da kyar raunin bai taɓa kwakwalwarta ba zancen da nake maka yanzu haka, kuma abun takaicin har zuwa yanzu da muka zo asibitin babu shegen da ya kira mu ba balle su gaya mana abinda ke faruwa wato so suke su rufe case din mu kuma an cuce er mu an illata ta, ka kira division din da kace kawai muje yanzu a hada mu da yan sanda a bamu mota ai nasan gidan su yarinyar, wallahi ko ta gudu sai mun tafi da uwarta ta fito da ita" Haka nan duk suka shiga motar Aunty Fauziyya suka nufi police station, motar yan sanda guda aka basu, Aunty Fauziyya tayi ma motar yan sandan jagora har gidan Hajja a tata motar.... Mama Ladi na tsakar gida tana alwala tayi maza tayi sallah ta tafi gidan Ammi, Hajja kuwa na kitchen tana ta kokarin hada girki ta koma asibiti ko don saboda Maheer, yan sanda kusan biyar suka shigo tsakar gidan Su Aunty Fauziyya da Aunty Farida na biye da su a baya, Tsabar gigicewa sai da Mama Ladi tayi zaman dirshan a kasa tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una" Aunty Farida na huci tace "Ina Badiyyar take?" Bakin Mama Ladi na rawa tace "Wallahi ni me aikin gidan ce, ga kakarta can a kitchen bazata rasa sanin inda take ba, ni ban san komai ba" Yan sanda suka nufi cikin gidan su Aunty Fauziyya na biye da su, Hajja ta saki murfin tukunyar hannunta bayan taga yan sanda tsaye kanta a kofar kitchen, tambayar da aka jefa ma Mama Ladi a waje shi aka kara jefa ma Hajja wato ina Badiyyah, Jikin Hajja na ɓari tace "Wallahi wallahi Badiyyah bata dawo gidan nan ba" Wani ɗan sanda yace "Amma ai kin san abinda ta aikata?" Hajja ta fashe da kuka tace "A gabana aka yi komai ranka shi dade, amma don girman Allah ku yi mata hakuri ku yafe mata wallahi marainiya ce yarinyar ba uwa ba uba, bata taɓa haka ba tunda take" Cikin daga murya Aunty Farida tace "Iyyeee wato marainiya, ita Haseenar uba gareta aka ce maki? To wallahi sai an dau mataki a kanta bata illata banza ba" Wani ɗan sanda na kallon Hajja yace "Kinga wannan kalman da kika yi Hajiya ya nuna cewar kin san inda yarinyar take ko kuma kina goyon bayan duk abinda take yi, don haka ki fito mu tafi station idan kika yi providing mana yarinyar sai a sake ki, kuma kina sake buda baki a nan za mu yi using din shi against you" Kuka sosai Hajja take jikinta na rawa tana cewa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, nace maku bata dawo gidan nan ba ku shiga duk inda za ku shiga a gidan nan ku duba ta, wallahi bata dawo ba, ku rufa min asiri tunda nake ban taɓa zuwa Caji opis ba" A fusace Aunty Fauziyya ta kalli yan sanda tace "Don Allah mu tafi tana bata mana lokaci officer, ta fa san inda yarinyar take sarai da hadin bakinta yarinyar ta gudu tunda tace ai tana wajen abun ya faru, don haka in mun je station din sai ta fadi inda yarinyar take sai a saketa" Haka nan Hajja ta saka Hijabi tana kuka yan sandan suka tisa keyarta zuwa tsakar gida, Mama Ladi dai sai wanke kayan da ta ga an jiƙa a cikin baho take ita a dole mai aikin gidan har aka fito da Hajja aka yi kofar gida da ita tana rusa kuka tana salati, gaba daya yan anguwa aka fito ganin motar yan sanda a kofar gidan Hajja sai ga kuma Hajja an fito da ita tana kuka wiwi an saka a motar yan sanda an tafi da ita, makociyar Hajja Maman Bala ta dau waya jiki na rawa ta kira Ammi ta sanar mata ga yan sanda sun zo da katuwar mota an saka Hajja a ciki an tafi da ita..... Ba karamin gigicewa Ammi tayi ba bayan Maman Bala ta kirata, ta fita ward din da sauri don Maheer yaje office din likita yana kiransa, A hanya suka hadu, ganin yanda Ammi ta rude Maheer yace "Ammi lafiya?" Ammi ta fashe da kuka tace "Yanzu Maman Bala makociyar Hajja ta kirani wai yan sanda sun zo sun tafi da Hajja Maheer" Sake baki Maheer yayi yana kallon Ammi with shock, ya kasa cewa komai, Tuni Ammi ta nufi reception tana kuka sosai, Maheer ya bi ta da sauri yace "To ina za ki Ammi" Ammi tace "Police station din zan tafi mana Maheer, su yanzu don basu da mutunci da tsufan Hajja za su tafi da ita station?" Maheer ya kama hannunta yace "To ai bamu san wani station din bane Ammi, ki kwantar da hankalin ki mu fara sanin wani station ne tukun" Ammi ta kasa ci gaba da tsayuwa ta zauna kujeran dake reception din tana kuka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, wannan wani irin fitina ne, wace irin yarinya ce Badiyyah? Meye wannan ta ja mana fisabilillahi?" Maheer that was so confuse ya ciro wayarsa yana tunanin wanda zai kira. Hajiya Amina na zaune parlor wajen karfe biyu Abba ya shigo da sallama, mikewa tayi bayan ta amsa tana kallonsa tace "Ka sameta a wayan Yallabai?" Abba yace "Ban sameta ba, wai tun yaushe ke kika lura bata gidan?" Hajiya Amina tace "Dazu wajen karfe goma na safe na shiga dakin ban ganta ciki ba duk tunanina ko tana bandaki ne, sai na koma na kwanta kawai, sai yanzu da aka yi azahar na tashi na sake komawa dakin inji ko ta ci abinci still ban ganta a ciki ba, shine na duba bathroom naga it's empty...." Da mamaki Abba yace "Kuma bata ce maki zata makaranta ba yau?" Hajiya Amina ta girgiza kai tace "Gaskiya bata ce ba Alhaji, kaga jiya da zata tafi makarantar ai ta gaya min, Kuma ina parlor da safe Mama ta fita balle ince tare suka tafi" Call logs Abba ya shiga na wayarsa ya ga ko zai iya gane number da Musharraf ya kirasa da shi jiya, yayi tracing calls dinsa har zuwa yesterday evening trying to recognize Musharraf's Number before calling, dai dai nan kiran Maheer ya shigo wayarsa, Abba da kamar bazai daga ba sai dai kuma ya daga, Hajiya Amina ta juya ta bar parlon ta koma sama, a takaice Abba ya amsa gaisuwan da Maheer ke masa, nan Maheer yayi kasa da murya ya sanar ma Abba duk abinda yake faruwa, Abba yayi shiru with surprise, can dai yace "Police station? To kai kana ina duk wannan abun ya faru? Sannan ina Badiyyar take har suka tafiya da Hajjar?" Maheer yace "Basu ganta bane ai Abba, shi yasa" Abba ya sauke wani ajiyar zuciya yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, yanzu wani station din aka tafi da ita Hajjan?" Maheer yace "Ban san division din ba, makota suka kira yanzu suke sanar mana" Abba yace "To bari dai ina zuwa...." Yana katse wayar yana kokarin kiran number wani abokinsa ɗan sanda sai ga Hajiya Amina ta sauko da wata farar takarda a hannunta da ta gani a dakin Mayraah tana kallon Abba babu ko kiftawa, Abba na kallon takardan yace "Na meye wannan?" Bata iya ta ce masa komai ba bata kuma fasa kallonsa ba, Abba ya karasa ya amshi takardan ya warware yana duba na menene....