Sashe 284
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
aje da ita, in sha Allah babu abinda zai faru sai alkhairi, we will go with her" Ammi sai da taji wani rass jin kalman da Abba ya fada wai Uwar Mayraah, sunan da ita ke ta bearing for 22 years now, a hankali Ammi ta sauke idonta tace "Toh shikenan" Abba yace "Hope duk sun gama shiryawa?" Kallonta Abba ya dinga yi jin bata ce komai ba, kuma bata ma san yayi mata magana ba, Abba yayi kasa da murya yace "To meye kuma damuwar? Gaya min menene kuma" Ta ɗan yi yake, sai kuma a hankali tace "And yallabai, sai jiya cikin dare abubuwan da suka faru suka dinga dawo min zuciyata, yallabai gaban wan Musharraf din nan fa aka yi duk wannan maganar? Wallahi da abun nan ya fado min cikin dare kasa bacci nayi, bai kamata ayi komai a gabansa ba, mun yi babban kuskure, kuma wannan kamar kara tona ma kanmu da ita Mayraan asiri muka yi, shi ma ai ba haka ake ba, family issue ne wannan da sai ya fita ya bamu waje, amma yana zaune duk ta bada wannan mummunan labarin shi ma yana ji" Abba ya sauke ajiyar zuciya yace "Maheer da Usman sun min wannan maganar tun jiya, but ya muka iya? tunda kika ga tayi duk maganan nan a gabansa kinsan ta yarda da shi ne sosai and suna da kusanci da kyakkyawan alaka da shi, kin ga bayan da muka hau sama zuwa dakin ita wannan matar ai bata fara magana ba sai da tace nurse din ta fita, so she trust him definitely" Ammi ta bata rai tace "Duk da haka dai, yayan fa tsohon saurayin Mayraan ne, yanzu idan ya kwashi duk wannan labarin mara dadin fada ya je ya gaya masu fa? Ni dai wallahi hankalina yayi mugun tashi da abun nan ya fado min cikin dare" Abba yace "In ma yaje ya gaya masu ba abu bane da zai dame mu, it's left for them, don ba mu da wani business da su har a tashi duniya, don su ne musabbabin rugujewan farin cikin Mayraah" A sanyaye Ammi tace "Haka ne Yallabai, lokaci na wucewa kuma airport da nisa daga nan" Abba yace "Ki duba ko sun gama shiryawa" Kofa Ammi ta nufa ta fita daga dakin. Usman ne zai yi driving din na su zuwa airport, Mayraah dake sanye da hijab har kasa tana kallon Maheer tace "Yaya to wa zai dawo da motar" Maheer ya bude mata back seat kafin su Ammi da Abba su karaso yace "Zai bar motar a airport" Mayraah tace "Amma dai biya ake ko?" Yayi murmushi yace "What did u expect" Murmushin tayi ita ma ta shiga motar, Usman dai yana zaune driver seat, Maheer ya zaga ya bude ma Abba front seat don yasan can zai ce zai zauna, karfe takwas da few minutes suka bar gidan heading to the airport. Ko da suka isa airport suka tarar Ceo har ta iso tare da Aaria sai nurse dinta duk suna zaune a lounge, Ceo ta mike tsaye suka gaisa da Abba da Ammi, sannan ta amsa gaisuwar su Maheer, Aaria dai sai kallon Mayraah take, Mayraah ta sukunyar da kanta, bayan ta gaida Ceo ta karasa gunta tana tafiya a hankali, zaunawa tayi tana kallonta ta gaisheta cikin sanyin murya, Aaria bata fasa kallonta ba kuma ta kasa amsa gaisuwar da take mata, Mayraah ta sunkuyar da kanta zuciyarta na bugawa, bayan few seconds Aaria ta sauke idonta kasa, nan da nan hawaye ya fara sauko mata, Ceo ta koma gefenta ta zauna ta jawota jikinta speaking calmly tace "Common My love, where is the promise u made to me" Aaria ta daura kanta saman shoulder din yayarta hawaye na sauka idonta, ita dai Mayraah bata iya ta dago kanta ba, Ammi dai sai kallonsu take, ashe kyan Mayraah ba komai bane a inda kyan uwarta yake, cause her mother is really beautiful, babu wanda zai bata shekarunta ko kuma yace ta haifi kamar Mayraah, A haka suka yi boarding jirgi, shi dai Maheer yayi mamakin da bai ga MD ba don ya zata da shi za su je kadunan, but daga shi har Usman a ransu sun ga hakan ya fi. Karfe tara da rabi suka sauka airport din garin kaduna, motoci uku na airport din suna jiransu, nan da nan mood din Ammi ya canza bayan taga MD ya sauka daga cikin daya daga motocin, daga Maheer har Usman ma basu ji dadin ganinsa ba, a haka suka karasa har gun motocin, bayan duk ya gaishesu Ceo tace "Ya me jikin? Is she better?" Yayi murmushi yace "He is better Ma'am" Tace "To Allah ya basa lafiya" Cikin ladabi yace "Ameen, ni zan dau taxi in koma gida, idan kun gama za ku taho airport sai ki min waya Ma....." Sosai hankalin Ammi ya kwanta jin abinda MD yace, duk da dai aikin gama ya gama don me ya rage da bai sani ba kuma, Ceo tace "Where are you headed now?" Yace "Malali..." Ceo tace "Ohk to ba damuwa, zan kira ka if we are done" Bayan sun iso unguwar Malali, su Abba suka ga motarsu Ceo dake gaban nasu sun yi parking a gefen hanya, hakan yasa nasu drivern ma yayi parking, sauka drivern motarsu Ceo yayi ya nufi gun wasu matasa dake tsaye bakin hanya, daga yanda suke communicating zaka fahimci tambayarsu direction din gidan da za su yake su kuma suna masa kwatancen, bai jima tsaye yana magana da su ba ya koma ya shiga mota, Wani hadadden layi suka shiga bayan sun kara tafiyar wasu mintuna, nan ma sai da drivern su Ceo ya sauka yayi tambaya aka sake basa direction, tun da suka baro Abuja sai yanzu Mayraah ta dinga jin zuciyarta na bugawa sosai, kwantar da kanta tayi jikin Ammi da ta rungumeta ta lumshe ido, dai dai gate din wani gida me girman gaske wanda aka yi ma gini irin na zamani suka ga driver din su Ceo yayi parking bayan sun wuce wasu yan sanda kafin su shigo unguwan, motarsu Mayraah ma yayi parking a bayan nasu Ceo, sai da Ceo ta sauko tare da Aaria da nurse dinta sannan Abba ma suka sauka, da kyar Mayraah ta iya saukowa daga motar Ammi na rike da hannunta, her heart is just beating so fast, bayan motocin su akwai wasu tsadaddun motoci biyu a kofar gidan ko wanne kuma da soja daya tsaye jikin motar, Ceo ta nufi babban gate din gidan su Abba na biye da ita a baya, Securities din na kallonsu babu yabo babu fallasa da turanci suka shiga tambayarsu wa suke nema kuma daga ina suke taho, wasu dattawan maza biyu ne cikin shiga ta alfarma suka bude gate din gidan suka fito, security daya ya kulle gate din, gaisawa suka yi da Abba da su Ceo a mutunce, har Abba ya gane daya daga cikinsu don he is a wealthy business man that is well known, kallon securities din bakin gate din daya daga dattawan yayi cikin harshen turanci yake masa magana a ɗan fusace yace "Duk wanda za ku ga ya zo a wannan lokacin to zuwa yayi ya duba mai gidan, so ku barsu su shiga ba sai kun tsaya dogon surutu ba" Da ladabi securities din suka ce "Yes sir" bude masu gate din suka yi duk suka shiga ciki, Ceo dake rike da hannun Aaria tana kallon daya daga securities din tace "Ina ne direction din shiga entrance na gidan?" Nuna mata yayi da ladabi, tana kallon Nurse din dake tare da su ta nuna mata wani waje da aka yi a compound din domin shan iska tace "Farida zaki iya jiranmu a can" Da ladabi Faridar tace "Toh Ma" Daga haka ta tafi can ta zauna, parlor na farko su Ceo suka shiga wanda babu kowa a ciki, hakan yasa ta karasa har second parlor din kanta tsaye su Abba na biye da ita a baya, shi dai Maheer har mamakin courage da confidence dinta yake kuma da alama sam bata da tsoro, Ammi dai gabanta sai faduwa yake kar mai gidan ya masu tijara ko ya koresu, suna shiga second parlor din wata mata da bazata wuce 43 ba ta fito daga wani bangare, tsaye tayi tana kallonsu at the same time tana masu sannu da zuwa, lokaci daya ta buda ido sosai bayan sun hada ido da Aaria, da sauri ta karasa har inda suke tsaye da mamaki tace "Maryam??" Ammi da tayi stiff a inda ta tsaya sai kallon matar take bata ko kiftawa....