Sashe 240
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Jikin Mayraah yayi sanyi ta daga kai tana kallonta a hankali tace "Ma yaushe zaki zo Nigeria?" Ceo ta mata murmushi tace "Sai bayan wata biyu in sha Allah" MD dai na tsaye sai kallonsu yake, Mayraah tace "To Allah ya kai mu, thank you so much Ma, i appreciate" Ceo tace "You are welcome" Daga haka ta daga ma MD hannu, ta shiga motarta ta bar airport din, Mayraah ta bi motarta da ido babu ko kiftawa, lokaci daya ta juya taga MD har yayi shigewarsa cikin airport din ya bar ta wajen a tsaye, Business class Ceo ta sa MD yayi masu booking, but because he wants to rest kasancewar he wasn't too fine a conference ranan kawai sai ya biya masu ticket din first class. Sune farkon boarding plane din, Mayraah bata taɓa shiga first class ba iyakarta business class, wajen karfe takwas da rabi jirginsu ya tashi, ya kira flight attendants telling them he is taking nothing don bai ma son a zo a tambayesa, bayan Flight attendants din ta bar wajen, after few minutes Mayraah ta juya ta kallesa taga ya kwanta ya lullebe da duvet, two hours into the flight Mayraah tayi bacci. Bayan awa daya ta farka, ta mike zaune tana kallonsa, har sannan a kwance yake idonsa a lumshe sae karamin towel dake forehead dinsa, ta mike tana tafiya a hankali ta nufi inda yake, bude ido yayi da sauri jin motsi kusa da shi, ta ɗan koma baya kamar munafuka tace "Are you okay?" Flight attendant ce ta iso wajen with pain reliever, Mayraah ta bi ta da ido har ta basa maganin sannan ta zuba masa ruwa a daya daga cikin glass cups da aka ajiye masa da goran ruwa uku, bai amshi glass cup din ba ya dau bottle water instead ya kurbi ruwan ya sha maganin, bayan Flight attendants din ta ajiye glass cup din hannunta ta kalli Mayraah don tana son sake masa labulen wajen for his privacy, kafin tace komai Mayraah tace "We are together" Flight attendants din ta mata murmushi tace "Okay Ma" juyawa tayi ta bar wajen, Mayraah ta kai hannu kan karamin towel din forehead dinsa taji a jike yake da ruwa, cire towel din tayi don har a sannan he is running temperature, ta tafi toilet ta kara jika towel din sannan ta dawo, ta duka kusa da shi zata daura a goshinsa ya fixge towel din yace "Don't worry, je ki ci gaba da baccin ki" Ta wani hade rai tace "But i am a nurse" Daga sama har kasa ya kalleta yace "Nurse with no license and working experience, pls go back to ur seat Madam and sleep" Kwace towel din tayi tace "I don't mind what ever u will say, but i am sticking to the ethical obligations of a Nurse to a patient" Daga haka ta fara goge masa forehead dinsa that is hot with the towel din, kallonta kawai yake, sai kuma ta cire duvet din jikinsa tace "You are running temperature so there is no point in covering ur body with a Duvet" Ko minti goma ba ayi ba ya sake komawa bacci. Kafin su isa Nigeria he felt much better saboda painkillers da ya sha a jirgin, karfe biyu da rabi na dare suka sauka airport din Abuja. Bayan ta dauko akwatinta ta kalli inda yake zaune ya jingina da kujera idonsa a lumshe, shi dama bai taho da komai ba, ta karasa wajen da yake zaune tace "Zan kira yayana ya daukeni, u can leave me here" Ya bude ido da sauri yana kallonta yace "Karya kike ba yayanki bane" Tace "To naji ba yayana bane" Ya mata wani shegen kallo ya mike ya fara tafiya, he is just acting he is fine whereas he is sick, ta bi bayansa suka fito haraban Airport din, taxi suka shiga.... Bayan sun fita daga airport din yace "Ni zan gaya masa address din gidanku da kika yi shiru?" Tace "To ai naga kasan gidan tunda ka taɓa bin Dr Khalil" Juyawa yayi ya kalleta da sauri, ta maida hankalinta kan driver tana gaya masa address din gidan da zai kai ta, MD yace "Shi Khalil din ne yace maki ni na bi sa?" Without looking at him tace "Ai ba sai ya gaya min ba i saw it with my eyes" Bai sake tanka ta ba cause ba shi da strength din hakan, 10 mintues into the journey ya fara bacci, ta ɗan juya ta kallesa, da zata matsa ta koma edge din kujeran kuma dai kawai ta basa access to her shoulder, har suka isa gida yana bacci, Mayraah ta juya ta kallesa, after few seconds calmly tace "I am home" A hankali ya bude ido, sai kuma ya gyara zamansa da sauri, ta ɗan kyabe baki ta bude motar tace "Sai da safe" Daga haka ta sauka ya bi ta da kallo, drivern taxi din ya sauka ya dauko mata akwatinta a booth, bayan ta amsa ta kalli MD dake kallonta, sauke ido tayi ta daga masa hannu sannan ta juya da sauri ta nufi gate din gidan ya bi ta da kallo, Kwankwasa gate din tayi taji security na tambayarta waye, bayan ta basa amsa ya bude gate din ta shiga cikin gidan ya kulle gate din, sai a sannan MD ya sa taxi driver din ya ja motar suka bar unguwan. Mayraah ta zauna saman kujeran dake compound ta ciro wayarta tayi dialing number Maheer, sai da ya kusa katsewa ya daga a hankali yace "Mimi" Ta wara ido tace "Sorry i woke u up" Yace "Ya aka yi? Hope ba ciwon cikin bane?" Tana murmushi tace "Aa ba shi bane, ai tun ranan da aka min allura bai kara ciwo ba, yaya na dawo" Maheer ya mike zaune yace "Da gaske?" Tace "Eh" Yace "Yaushe?" Tace "Just now" Yace "In taho airport inyi picking dinki ne?" Tayi dariya tace "Eh ka taho" Yace "Right away" Daga haka ya katse wayar, mayar da wayar tayi cikin handbag dinta, ta daura handbag din kan akwatin sannan ta karasa chalet da sauri ta tsaya bakin stairs yanda bazai ganta ba har sai ya sauka kasa, bayan kusan minti bakwai sai gashi ya fito sanye da jallabiya, yana sauka stairs din tayi er kara saitin fuskarsa, ya juya da sauri yana kallonta da mamaki, ta kyalkyale da dariya tace "Wallahi nasan ka ji tsoro Yaya" Tun da Haseenah taji ya bude kofar dakinsa dama ta farka daga baccin da take a nata dakin, sai ta fito parlor, bai bi ta kanta ba as usual, tana ganin ya fita compound ta taho window tana leka waje, kawai kuma sai taji muryar Mayraah, Maheer dake kallon Mayraah daga sama har kasa yace "Wa yayi dropping din ki?" Mayraah na murmushi tace "MD dinmu, taxi muka shiga a airport din" Yace "Har kin kara haske daga zuwa Uk, are you sure we are not relocating there?" Tayi dariya tace "Wani haske? Bayan sanyi ake a can sosai, har fa mura sai da nayi, ni dai bana son kasar saboda sanyi" Yana murmushi yace "To ina akwatin?" Ta nuna masa inda ta bar akwatin tace "Yaya i bring you so many chocolates irin wanda kake so" Yace "Really" Tace "Wallahi" Gun akwatin ya nufa ta bi bayansa, Haseenah dake jikin window tana jin duk abinda suke cewa ta bi su da ido.