Sashe 26
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mayraah na fita gida ta fara tunanin abincin da zata siya ma Musharraf, sannan a ina ma zata samu abincin har ta siya, tayi deciding ta fara fita daga area dinsu tukunna don ba lallai ta samu eatry da zata siya masa abinci me kyau a nan ba, after leaving the area ta samu wani babban eatry ta siya masa abincin with bottle water da drink sannan ta fito, tana fitowa wayarta dake jakarta ya fara vibrate, ta ciro wayan tana duba me kiranta taga Ya Maheer ne, ta ɗan yi jim, yanzu fa kilan tana dagawa idan ta gaya masa abinda ta gaya ma su Ammi sai ya iya cewa ta koma gida, sarai ta san halinsa, taki daga kiran har ya katse, zata mayar da wayar cikin jaka sai gashi ya sake kira, bayan ta ɗan yi nazarin abinda zata ce masa sai ta daga ta kai kunne tace "Yayana...." Yace "Ina kike haka nake jin noises din vehicle haka?" Mayraah ta ɗan buda ido tace "Gidansu Hamida zan je yaya..." Yace "Hamida? Zaki je ko zaki dawo?" Ta ɗan turo baki tace "Zan je dai" Yace "Are you serious?? Since morning baki je gidansu Hamida ba sai yanzu that everywhere is busy? Almost five o clock now" Mayraah ta marairaice tace "Yaya ba dadewa fa zan yi ba" Yace "I see, yanzu kina ina?" Ta ɗan kalli inda take, sai tayi saurin cewa "Nima dai ban sani ba ina cikin adaidaita sahu amma nasan mun kusa, ina amso reading material dina zan juyo, we are having test on Monday" Yace "Ohk, amma baki ga hadari ba?" Ta kalli sama tace "Ba sosai ba, abinda ya ma fara washewa" Yace "Toh Allah ya tsare" Tace "Ameen, Me zaka gaya min ka kirani?" Yace "Wanted telling u kiyi min stirred fried spagh....." Mayraah tayi murmushi tace "Ai dama nasan girki zaka ce in maka, baka taɓa kirana sai in kana son in ma girki, but don't worry yayana idan na dawo zan maka in sha Allah" Yace "Take care, and do not stay long" Tace "In sha Allah" Daga haka ya katse wayarsa, ta ɗan yi jigum kamar me nazari, to ma dai tukunna a ina ma za su hadu da Musharraf ya amshi abincin, ko tambayarsa ma fa bata yi ba ta fito daga gida, sannan bata ma san maganin da zata siyo masa ba tunda bai gaya mata ba, Tana kokarin dialing numbersa sai ga kiransa ya shigo wayarta ta daga ta kai kunne, yace "Where are you?" Tace "Yanzu na fito eatry, wani Drugs zan siya maka?" Nan ya gaya mata drugs da zata siyo tace "Toh, amma ta yaya za a kai maka abincin da maganin? Dispatch rider?" Musharraf yayi shiru jin abinda tace, jin shirun yayi yawa tace "Hello?" Yace "Dispatch ridern zaki ba abincin da zan ci?" Ta ɗan hade rai tace "To ya za mu yi, do u have the strength to drive ka fito ka amsa?" A takaice yace "I don't have" Tace "To ai ni ban san inda kake ba, and beside i can't say...." Ya katse ta yace "I will send u d address of my location" ta buda ido da mamaki tace "Sae na je har can kake nufi?" Shiru yayi, cike da damuwa tace "Am i suppose to come to ur location?" A hankali yace "Toh shikenan ki samu dispatch rider din ki basa magungunan kadai ya kawo min" tace "Abincin fa?" Yace "Bazan ci ba, it is not proper for a dispatcher to deliver my food" Tayi shirun few seconds, a ranta kuwa tunani take, how is it wrong for a dispatcher to deliver someone's food? a hankali tace "Let me get the drugs, sai ka turo min address din location din naka, ina isowa unguwan sai ka fito ka amsa" Yace "Alright tnx" Katse wayar tayi, ta nemi nearest pharmacy ta siya masa magungunan da ya gaya mata, tun kan ta fito pharmacy din address dinsa ya shigo wayarta, bayan ta fito ta samu adaidaita sahu ta gaya masa inda zata sannan ta shiga, nan kuma gabanta ya dinga faduwa, what if ta hadu da any of her family members or relatives? tunanin hakan yasa gabanta ya tsananta faduwa and she became so uncomfortable, sae kusan biyar da minti talatin da biyar suka isa layin, mai adaidaitan yace "Nan ne unguwar Hajiya" Mayraah dake ta bin unguwan that is so quiet da kallo tace "Pls kayi hakuri yanzu zan mika sakon nan sai ka maida ni, ban ga alamar zan samu adaidaita sahu a nan ba" Yace "To, amma kiyi sauri kinga yayyafi ake" tace "To Nagode" Da sauri ta shiga dialing number Musharraf, yana fara ring ya daga, tace "I am at the street, ka fito ka amsa pls, mai adaidaita sahu yana jirana kar mu bata masa lokaci kaga an fara yayyafi" Musharraf yace "Ki basa kudinsa, zan ajiye ki gida" Ta wani zaro ido tace "I don't understand? Kai da baka da lafiya, pls i am going back together with the Tricycle" Yace "I will try and take you back Mayraah, bana son ruwan nan ya taba ki" Ta sauka daga cikin adaidaita sahun don she is not comfortable making call in front of the owner, A bit worried tace "Don girman Allah ka fito ka amshi abincin nan da magani in koma gida, wllh ce ma Ammi nayi zanje gidansu Hamida, da kyar fa ta bar ni, don Allah ni dai tsoro nake ji kar ayi finding out inda na je kayi hakuri ka zo ka amshi abincin in wuce gidanmu" Musharraf yace "Mayraah..." Kamar zata yi kuka tace "Ina ji" Yace "Ki sallami mai tricycle din nan nace, ba ni nace zan ajiye ki gida ba?" Tace "Am sorry I can't, kayi hakuri ka fito ka amshi abincinka in koma gida" Yace "Ohk" daga haka ya katse wayar, ta koma gun mai adaidaita sahun tana basa hakuri, tana ta tsaye jikin tricycle din duk da yayyafi da ake ba me yawa ba, sae ga Musharraf ya fito daga gate din dake opposite dinta, ita bata ma san nan ne gidan ba kawai sun tsaya ne ita da ɗan sahun, tun da ya fito take kallonsa, bata taɓa sanin he is this vast and broad ba sai yau, ko don bata yarda ta kallesa a school ne saboda kunya, bashi da haske a inda take, ma'ana tafi sa haske sosai amma kuma shi ba baƙi bane, duk hancinta kuwa ya fi ta, and he have got a very beautiful eyes with thick eyebrows that one can ever imagine, lips dinsa look so cute on his face, duk a cikin few seconds Mayraah ta kare masa kallon nan kafin tayi saurin dauke idonta, nan kuma taji gabanta na faduwa sosai, har ya karaso inda suke, da kyar tayi karfin halin cewa "Good evening sir, ga abincin da magani, i don't know if you will...." Kasa ci gaba tayi da mamaki ganin kudi yan dubu dubu da bata san nawa bane ya mika ma mai adaidaita sahun yace masa zai iya tafiya, Mai adaidaita sahu bai ko kalleta ba ya fara kokarin reverse da machine dinsa, Mayraah ta kasa cewa komai cause she became so confused and lost of words lokaci daya, da kyar ta kallesa tace "What is the meaning of this?" Yace "Ke baki da aiki sai yin musu da ni ko? ban taɓa ce maki abu kinyi direct ba sai kinyi musu, is that how u will be treating me after the marriage?" Kamar zata yi kuka tace "I told u i lied to my Mother about where i am going to, me yasa baza kayi considering dina ba sir, i did this because i was so worried about you" Shiru yayi yana kallonta, Lokaci daya hawaye ya cika idonta ita ma tana kallonsa, babu abinda ke kara karyar masa da zuciya sae hawayenta duk da Nikab din fuskarta he can see the tears in her eyes, yayi kasa da murya yace "I promise u in just 10 mins time zan maida ki gida Mayraah, i appreciate ur care and concern toward me, the rain is going to make u wet, mu shiga ciki in shirya sai in kai ki gida, kiyi hakuri" Tana goge hawayen idonta tace "I will wait outside, zan jira ka a nan" Yace "Bana son ki kara min musu, since ni nace zan kai ki gida, just do as i say" Yana fadin haka ya juya ya nufi gate din gidan da ya fito, hawaye ya dinga sauka idonta tana bin sa da kallo, nan da nan ta jika Nikab dinta, don ma babu kowa a Unguwan, bayan few seconds ta bi sa zuwa cikin gidan tana shiga gate din gidan ta zauna ɗan dakalin dake kofar dakin da aka yi ma Mai gadi, ya kulle gate din, ita dai sai kallonsa take gabanta na wani irin faduwa, dukawa yayi gabanta yana kallonta a hankali yace "Mayraah kinsan saboda ke na shiga wannan halin da nake ciki yanzu? Throughout yesterday night i couldn't sleep, ban taba shiga damuwa irin damuwar da na shiga daga jiya zuwa yau ba Mayraah, i am so disturbed" Kasa ci gaba yayi, yayi shiru yana kallonta, Maganganunsa suka dinga mata yawo a kai, ya shiga damuwa saboda ita kuma? As how? To me tayi masa? Dage Nikab din fuskarta tayi tana kallonsa for some seconds, can ta marairaice tace "Did i offend you in anyway? Ka gaya min don Allah ko wani laifin nayi maka, me yasa zaka shiga damuwa saboda ni?" Sunkuyar da kansa yayi bai ce mata komai ba, nan taji hankalinta ya kara tashi, cike da damuwa tace "Don girman Allah kayi hakuri ka gaya min sir, wllhi ban san me nayi ba, how did i offend you?" Nan da nan wasu sabbin hawayen suka ciko idonta, Yayi gathering courage, da kyar yace "Baki min komai ba Mayraah, baki taɓa min komai ba, asali ma u are the most nicest, Pious, gentle lady i have ever come across all my life, samun mace irinki sai an tona, i am always proud u accepted me after all the up and downs, ina alfahari da ranan da na fara