← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 175

Sashe 99

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya saka duka hannayensa biyu yana mai kuma manneta cikin jikinsa had’ida lumshe nasa idanun shima. Dik wani zafin kan da ya kwaso daga wajen Musaddiq sai yaji ya yaye.. Ya nema ya rasa, sai wani sanyi da annashuwa dake ratsa duk wani mahudar gashi na jikinsa. Yanayi da zaice bai tab’a tsammanin zai riske sa a rayuwarsa ta duniya ba. Tabbas yana da damuwoyinsa da kuma abubuwan da yake ya cimma na rayuwa, amma zai iya cewa shigowar Sadiya cikin rayuwarsa ya sanyashi ji kaman ya cimma wani buri na rayuwa. Sannan ta cike wani gurbi da ya jima da gib’i cikin k’irjinsa. Bai tab’a koda hasasho kansa cikin irin wann rayuwar nan kusa ba ko ba don k’alubale da matsalolin rayuwa da yake fuskanta ba.. A’a kawai dan soyayya ba abar shi bace.. Kuma baida lokacinta. Hasalima kullum fad’ansu da Assad kenan.. Sai yana ji kaman rayuwa ta basa dama ne yai experiencing abinda ya jima yana k’aryatata yana kuma gudunta Wato soyayya.. na wani d’an k’ank’anin lokaci k’ayyadadde.. Yanaji kaman rayuwar bazatayi k’argo a haka ba domin kuwa Ita duniya ba komai bace face GIDAN ARO. Bai yarda akwai Farin ciki mai d’aurewa a GIDAN ARO ba kaman dai yanda nasa ahalin basu sami irin wann Farin cikin ba.

Sun d’an d’auki lokaci a haka kafin ya ware idanunsa yana duban b’angaren dining area.

“Have you eaten..?” Ya tambaya tana nan mak’ale cikin jikinsa.

A hankali ta girgiza masa kai alamun a’a.

“Oya tashi muje kici abinci you know you are a patient..” Ya k’arashe yana mik’ar da ita tsaye a hankali kaman mai tsoron kar Ta subce cikin hannunsa.

“Can you walk..? Or should I carry you to the dining table..?” Ya tambaya still yana tallafe da ita.

Marairaice fuska tai tace “Kai Inspector zan iya fah..”

Ya d’an ja hancinta kad’an kafin yace “Alright just because you insist.. Ba wai dan inaso na barki kiyi tafiya da k’afarki ba..”

“Come here zan tsaya daga bayanki dan kar ki fad’i..” Ya k’arashe yana kamota ya rik’eta a haka suka nufi dining table d’in kaman mai koya mata tafiya.

A haka har suka isa sukai kalaci mai cikeda Farin ciki. Haka yinin ranan riritata ya dingayi kaman wata jaririya d’anyar goyo, itakam abin har mamaki yake bata dan bata tab’a zaton ko a mafarki ita dashi zasu kasance haka ba.. Bata tab’a zaton he can be as sweet as yanda yake tarairayata haka ba. Abu ne da a baya ko mafarki tai yanayi zata bud’e ido tace bazai faru ba.. Allah kenan mai gudanar da al’amari yanda yaso ba tareda shawarin kowa ba.

A b’angaren Shemau kuwa waya Safeenah tai mata tana tambayarta abinda ke faruwa Fufore.

Shemau taci gaba da fad’in “Meye ma bai faru ba Safeenah.. Ai komai ya faru..”

Safeenah ta dafe k’irjinta tana fad’in “Aunty na shiga uku komai fah kikace..?”

Shemau ta yab’e baki tace “Yo komai kai.. Duk wanda yake cikin gidan gonar nan a kunnensa komai ya faru jiya da dare.. Yau na shiga da sassafe domin na tabbatar da aukuwan hakan.. Yanzu haka maganar da nake miki yini Mu’azzam yai zubur yana tarairayar yarinyar nan. Keda kin gansa yau kinga sabon ango sharr har wani annuri goshinsa yake..”

K’ara Safeenah ta saki tana fad’in “Na shiga uku na mutu na lalace..!” Ta kuma kurma wani ihun tana jifa da wayar.

Shemau tai k’wafa tace “Bakiyi ihu ba ma sai kin ganta da tumbi d’ol.” Tana ida fad’in haka ta kuma k’wafa tana mai shigewa d’aki yanda ta tadda mijin nata kaman jiran shigowarta yake.

“Da wa kika gama waya.?” Ya tambaya yana dubanta.

“Banda shahshashar d’iyar D’anuwanka Safeenah.. Wai waya tayo tana tambayata mai Mu’azzam ke ciki.. Kasan ita akan Mu’azzam Sai ta iya halak’a.. Na k’unsa mata bak’in ciki kaman yanda uwarta ta k’unsa mana ta kasa mana amfani ta samo mana documents d’in nan..”

Shiru Uncle Salman yai kaman mai nazari kafin ya murmusa ya kad’a ‘yar yatsarsa “Ahaan..! I have an idea..”

Shemau Ta dubesa da mamaki kafin ta girgiza kai tace “Ban fahimceka ba mai kake nufi..?”

Gyara zama yai yana duban Shemau kafin yace “Idan uwar bata mana amfani ba ‘yar zata mana..!”

Ta kuma girgiza kai cikeda mamaki kafin tace “Hajara bata mana amfani ba sai Safeenah da kowa ya mata shaidan shashanci..”

Uncle Salman yai wata muguwar murmushi kafin yace “Ki bar mace akan kishi duk dolancinta.. Tabbas Safeenah zata mana amfani fiyeda mahaifiyarta.. Tsaya kiji..”

Shemau ta gyara zama sosai tana dubansa.

SameenaAleeyou📚

*GIDAN ARO*

*50*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

“Dama muka samu Shemau da Zamuyi amfani da ita, Kinga na farko Safeenah d’iyar Marwan ce. Kuma ni nasan D’anuwana kaf cikin ‘ya’yansa babu wacce yake matuk’ar so babu wacce ta shiga zuciyarsa irin Safeenah.. Soyayyar da yake ma Safeenah yasa ya aura mata Mu’azzam dan haka itace key d’in mu idan munaso Documents d’in nan su dawo hannunmu.. Sannan bugu da k’ari Marwan ya jima yana preparing Safeenah dan itace zata gajesa a kasuwanci ba wann mahaukacin D’an nasa ba wanda baisan ina ya saka gaba ba... Saidai dukda shirya Safeenah da ya jima yana yi shashasha ce batada wayo.. Amma kuma mu yanzu zata mana amfani dan ita Keda access da Company.. Kuma tana matuk’ar son Mu’azzam wanda zata iya aikata komai domin Ta mallakesa.”

Aunty Shemau ta d’anyi jim kafin ta girgiza kai tace “Mai kake so ayi yanzu..?”

Ya murmusa kad’an kafin yace “Zata samo miki wann takardun daga wajen Mahaifinta ke kuma zaki mata alk’awarin mallaka mata Mu’azzam..”

Da mamaki take dubansa kafin ta girgiza kai tace “Ka kuwa ji abinda kace.. Ta ina nakeda ikon mallaka mata Mu’azzam..?”

“Wani sa’in kina abu kaman marar basira Shemau.. Shin baki samu yarda da amincewar mahaifiyarta ba a lokacin da kika zab’i zaki taimaka mata Nuratu ta bar gidanta..?”

Shemau ta jinjina kai a hankali..

Ya kuma murmusawa kafin yace “Everything in life has a price. Zaki san yanda zakiyi ki raba wann yarinyar da Mu’azzam domin ya koma ga Safeenah... Ke kuma sai ta nemo miki wad’ann documents d’in in exchange.”

Shiru Aunty Shemau tai kafin tace “Wann aiki ne mai matuk’ar wahala.. Farin cikin Mu’azzam kake cewa mu tarwatsa fah.. Sann mai zance ma Safeenah yanda bazata zargi D’an uwan mahaifinta ba.. Ina nufin kai kenan..”

“I don’t give a damn idan zata zargeni muddin wad’ann takardun zasu dawo hannu na.. Kina magana kaman baki San mai duniya ke ciki ba.. Idan ta tona mana asiri kaman ta tona ma kanta ne tinda dole Mu’azzam zai San tareda ita aka had’u aka cutar da matarsa.. In fact mu sai mu jefata a ramin ma ta rufza ciki ita da mahaifiyarta da ta cutar da tasa Uwar.. Kinga Safeenah ta halak’a matarsa Hajara ta halak’a uwarsa shikenan mun zame kanmu cikin sauk’i... Just trust me Shemau wann shine kad’ai hanyar da zamu bi mu mallaki takardun nan..”

Shemau tai shiru kaman mai nazari sai kuma ta jinjina kai tace “ Wai shin yaya wann Document d’in yake.. Ya kamanninsa yake..?!”

Mik’ewa yai tsaye yana mai rungume hannayensa ta baya, saida ya bata baya kafin yace “Takarda ce doguwa cikin envelope mai ruwan k’asa.. Jikin takardan an rubuta wasu harrufa daga sama *BAT*.”. Lokaci guda ya juyo yana duban Shemau kafin yace “Ina so ta samo mun wann takardan mai d’auke da wad’ann harrufan.. Inaso Safeenah Ta samo mun BAT..!”

Sauk’e ajiyan zuciya Shemau tai kafin ta jinjina kafin tace “Mai harrufan BAT ke nufi..? Kana nufin Jemage.?”

Juyowa yai yana dubanta sai kuma ya saki murmushi yace “Kalmar BAT ba Jemage yake nufi ba, yanada ma’anarsa mai zaman kansa, kawai ki saka Safeenah ta nemo mana yanda mahaifinta ya adana BAT.. Ni kad’ai nasan mai haruffan BAT ke nufi dan ko Marwan baisan mai haruffan BAT ke nufi ba. .. Saidai watak’ila yanada masaniyar had’arin dake tattareda BAT idan har ya shiga hannu na, shiyasa ya mishi ajiya mai nisa ta yanda bazan cimmasa ba.. Amma yayi kuskure dan idan har ina numfashi sai na mallaki takardan BAT.”

Sauk’e ajiyan zuciya Shemau tai kafin tace “Don Allah ka fayyace mun mai BAT yake nufi..?” Ta fad’i a d’an dame.

Juyowa yai yana dubanta, murmushi saman fuskarsa, hannayensa hard’e ta baya.

Lokaci guda yake furta “B for Bet, A for Agreement, T for Transaction..” Ya k’arashe yana sakin murmushi.

Cikin rashin fahimta Aunty Shemau tace “Bet Agreement Transaction..” Ta girgiza kai kad’an kafin tace “Mai hakan yake nufi..?”

Ya kuma murmusawa kafin yace “Bet yana nufin rantsuwar da Yayanmu Abubakar yai cewa baya buk’atar komai na daga inheritance d’in da mahaifinmu ya bari. Agreement yana nufin yarjejeniyar da mukayi nida shi cewa idan ina son nasa shares d’in zan iya had’awa da nawa kason duka na cinye. Transaction yana nufin transferring Assets d’insa kaf da yayi daga nasa sunan zuwa nawa sunan..!”

Ya kuma karkatowa yana duban Shemau kafin yace “Shemau I badly need that document.. Kafin BAT ya isa hannun Mu’azzam hannuna ya kamata ya fara isowa.. You must help me find BAT..!” Ya k’arashe cikeda zak’uwa.

Sauk’e ajiyan zuciya Shemau tai kafin tace “Shikenan zan saka Safeenah ta nemo mana takarda mai d’auke da kalmar BAT.. Toh amma idan ta tambaya na menene mai zance mata..?”

“Bazata tambayeki ba muddin zata sami abinda take so Wato Mu’azzam..” Ya bata amsa kai tsaye yana dubanta.

Lokaci guda yaci gaba da furta “Aiki zaki bata Ta nemo miki BAT idan har tana so ki taimaketa Mijinta Mu’azzam ya koma gareta..!” Yana ida fad’in haka ya zauna a mazauninsa.

Shemau tai masa K’uri tana dubansa. Tunani fal zuciyarta, Anya mijinta bai zauce kan son abin duniya ba.? Bata gama warware qullin da suka had’awa mahaifiyar Mu’azzam ba itada Mommy yanzu gashi Uncle Salman ya kuma ingizata Ta k’ulla wa matar Mu’azzam d’in itada Safeenah.. Ga mahaifiyarsa ga matarsa Anya basu d’ebo da zafi ba..? Tinanin da ta dinga yi kenan har Uncle Salman d’in ya fice yana amsa waya. A hankali ta furta kalman BAT tana mai mik’ewa tsaye.

**
Chapter 99 · 0% Book details