← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 175

Sashe 12

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A haka Umma Ke janyota har suka fito k’afar gidan, shid’in Ta soma hangowa mutumin da suka bangaji juna shida ita d’azu, fitowarta yai daidai da lokacinda yake zare glasses d’in daga idanunsa... Sai wannan lokacin ta sami damar ganin fuskarsa complete, saidai fad’uwar gaban data tsinci kanta ciki har ya d’ara wanda tayi a baya domin kuwa a halin yanzu ya cire glasses da suka rufe masa idanu a lokacin da suka bangaji juna, fuskarsa ya kuma bayyana had’ida k’wayan idanunsa..

Tsoron jami’an tsaron da take ya ninku.. Har Mu’azzam ya soma takowa gabanta bata Sani ba.. Dan shima sarai ya genate yarinyar nan ce data bangajesa ta kuma gudu, sannan itace ta jefesa da ledar ultra pad yanzu a nan..

“Ke.!” Ya fad’i yana mai kuma tsimewa idanunsa tarau akanta..

Ta d’ago a zabure tana dubansa..

“Kinsan wannan..?” Ya tambaya yana nuna mata hoton Sagir..

A daburce ta shiga jinjina kai tana fad’in “Umma Sagir ne.. Umma wllhi Sagir ne.. Taho ki gani.. Na fad’a miki zai dawo gareni..”

“Ke.!!” Ya daka mata tsawa sosai wann karon wanda ba Sadiya kawai ba harta Assad da Umma saida suka razana, Mu’azzam yaci gaba da takowa gaban Sadiya yana furta “Gawan kike jira..?!”

Daga Sadiya har Umma mutuwar tsaye sukai suna duban Mu’azzam dake ci gaba da takowa gaban Sadiya cikin tsananin k’unan rai ya d’ago hoton yana nuna mata yake furta “Well wanann D’anta’addan ya mutu..! He’s found dead.. He’s gone..! Ya mutu, shid’in gawa ne.! Bazai kuma dawowa cikin rayuwarki ba.. Now you’re going to tell me everything you know about him..!”

Sadiya dake dafe da k’irjinta tana jin maganganun D’ansandan sama sama, kalman ya mutu an tsinci gawarsa kawai take nanatawa cikin dodon kunnuwanta..

“Umma.! Umma.. Sa...Sagirrr..!” Luuu sai fad’owa tai jikin mahaifiyarta..

SameenaAleeyou📚

*GIDAN ARO*

*07*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Cikin tsananin tashin hankali Umma Ke jijjigata “Sadiya..! Sadiya.! Sadiya dan Allah Ki tashi, kar ki tafi ki barni.. Sadiya ki tashi dan Allah..”
Assad ya k’araso yana mata fifita da takardan dake hannunsa...

Kaman daga sama sai ji sukai an watsama Sadiya ruwa a saman fuskarta.. Suka d’ago idanu suna duban Mu’azzam dake tsaye saman kansu rik’eda bottle water. Dama tinda Sadiya ta sume ya nufi yanda suka aje motarsu ya d’auko ruwan gora a cikin motar..

Wani irin dogon numfashi Sadiya Ta saki tana mai k’ok’arin bud’e idanunta..
Daidai lokacin Mu’azzam ya d’an duk’a kad’an saitin fuskarta.. Aiko tana bud’e idanunta tai tozali dashi duk’e gabanta ya tsareta da wannan idanun nasa masu furgitarwa, fuskarsa sam babu alamun walwala..

Rungumeta Umma tai tana fad’in “Alhamdulillah.. Sadiya kar ki tafi ki barni kinji.. Ked’in nake so d’iyata.. A halin yanzu ban damu ki auri mai kud’i ko Talaka ba, idan dai zamu kasance tare...”
Wani irin kuka Sadiya ta fashe dashi had’ida fad’awa jikin Umma sanda ta tuna abinda D’ansandan nan yace Wai Sagir ya mutu gawarsa aka tsinta..

“The drama is over.. Tashi ki fad’a mana komai da kika sani akansa..” Mu’azzam ya fad’i yana mai mik’ewa tsaye had’ida zira hannayensa cikin aljihun wandonsa..

Umma ta taimakawa Sadiya suka mik’e a tare
“Rankaidad’e wllhi bamu San mutumin nan ba kaman yanda na fad’a maka, yaudara rum yai ya gudu ya bar d’iyata tana jira.. Wllhi bamu San daga yanda yake ba..”

“Ta yaya zaku d’auki ‘yarku ku bada aurenta ga mutumin da baku sani ba..? Shin dama irin haka na faruwa..?” Assad yace yana mai tsare Umma da idanu..

Mu’azzam kam har wanann lokacin idanunsa na kan Sadiya, yanai mata wani irin duba.. Maganganun Alhaji Isyaku Baban Sabeera na Yawo a dodon kunnuwarsa cewa yarinyar Ballagaza ce mai bibiyan maza dan neman abin duniya..
Baima sauraron tambayoyin da Assad Kema mahaifiyar Sadiya dan Sadiyar kam har lokacin rawa kawai jikinta yake Ta kasa katsb’us sai kuka da take har lokacin. Tana cikin tsananin shock har wannan lokacin.

Cikin tambayoyin da Assad yayima Umma ya fahimci cewa su kansu basu san tak’amaimen wani abu gameda Sagir ba, son abun duniya ne da ya rufe masu idanu ya sanyasu amincewa da Sagir har ta kaiga suna yunk’urin aura masa d’iyarsu..

Ya d’an girgiza kai yana duban yanda Uwa da d’iyar suka rungume juna suna hawaye.. Yaji tausayinsu dan tausayi amma something was amiss a cikin labarin, something wasn’t clicking, the math wasn’t mathing.. shi bai tab’a jin yanda akayi aure haka ba..
“Hajiya baku San kowa nashi ba kuka amince zaku basa auren d’iyarku..?” Assad ya kuma fad’i yana dubanta..

D’an jim Umma tai dan bata fatan wani abu ya jefata cikin fitinan da Sagir yake ciki.. Uban bashin da Tabawa Ke binsu ma kad’ai ya ishesu.. Hakan yasa ta girgiza kai alamun a’a..

“Kina nufin bai turo magabata ba haka kurum kuka amince zaku d’auki d’iyarku ku basa..?” Assad ya kuma jefo mata tambayar..

Umma ta daburce ta shiga girgiza kai tana neman kalaman da zata had’o saman harshenta..

Sai sannan Mu’azzam ya k’araso gaban Sadiya da kanta Ke kifi cikin jikin mahaifiyarta tana aikin kuka

Cikin kuka Umma Ke fad’in “Rankaidad’e dan Allah kuyi hak’uri d’iyata Ta dawo cikin hayyacinta.. Dan Allah enough with the questions for now..”

Kafin yakaiga magana wayarsa Ta soma ruri, Chief Inspector Officer ne Ke kiransa daga ofishinsu can headquarters..

Ya matsa gefe yana amsa wayan.. Neman gaggawa da Chief Ke masu yasa ya k’araso yanda suke..

Ya d’an fuzar da fuci kafin ya dubi Umma yace “Ku tsammacemu ko wani lokaci daga yanzu..” Daga haka Assad yai yace suje...

Suna tafe Assad Ke fad’in “Maybe they’re telling the truth.. Maybe basusan komai akansa ba.. Kwad’ayin abin hannunsa ya rufe masu ido har sukayi tunanin basa auren d’iyarsu ba tareda sunyi bincike sunsan shid’in waye ba..”

“And you believe them.? Well idan ma haka d’in ne ita yarinyar dole tasan wani abu, dole tasan yanda ta had’u dashi.. I believe through wannan yarinyar zamu samu wani abu..”

Assad yai shiru yana nazari “You’re right.. Zatai linking d’inmu to gaskiyar al’amarin..”

**
Su Mu’azzam suna tafiya Umma ta janyo Sadiya suka shige gida harda saka ma gidan sakata..
Ita kanta Sadiyar sai sannan ta warware ta shiga rabe raben idanu tana fad’in “Umma yanzu ya zamuyi idan ‘yansandan nan suka sake dawowa.. Mai zamu ce masu..?”

Umma ta yarfe gumin dake kwance saman goshinta tace “Gwara mu barsu akan cewa bamu San komai ba kafin muje mu saka kanmu a UKU.. Allah kad’ai Yasan Sagir d’in nan wane irin gasunk’umin D’anta’addan ne..”

Umma ta nusa tace “Ni Anya bazamu bar garin nan ba, bazamuyi hijira ba kuwa.. Tashin hankalin tayi yawa, bamu gama da Tabawa ba yanzu ga wani ya kunno Kai..”

Sadiya tace “Umma mu tafi muje ina.. Bamuda wajen zuwa.. Kuma Tabawa bazata tab’a k’yalemu ba dik yanda muka je..Umma idan ma muka tafi bamusan wani irin fitina da tashin hankali zamu kuma fuskanta gaba garemu ba.. Sannan Umma ga Ashiru ga Habeeb yaya zamuyi dasu..? Sud’in fah yara ne Umma.. Tafiya dasu yana nufin jefa rayuwarsu cikin garari, and Umma bana fatan abinda zai b’ata rayuwan yaran nan.. Dik abinda nakeyi Umma inayi ne domin na inganta rayuwarsu.. Ina son mai kud’i ne domin su sami rayuwa mai inganci su kuma girma cikin gata.. I don’t want my little brothers to experience what I have been through in the past...Umma bana son ‘yanuwana su sha wahala irin wahalan da ni nasha a baya a lokacin muna cikin tsnanin talauci Abba kuma yana cikin tsananin jinya..” Ta kasa ci gaba da magana sabida rawa da muryarta keyi..
Umma tai saurin k’arasawa ta rungume d’iyarta su duka biyun suna hawaye..

Cikin zuban hawaye take furta “Sadiya I don’t want you to suffer the same fate da mahaifiyarki na auren Talaka Shiyasa na dage sai kin auri mai kud’i.. Amma bayan abubuwan da suke faruwa yanzu, na yarda mutum baya wuce k’addararsa.. K’addararka tamkar inuwarka ce duk yanda kaje sai ta bika.. Ki yafe min ‘yata.. Ina ji kaman ni na saka rayuwarki cikin wannan gararin..”

Sady ta kuma rungume mahaifiyarta su duka biyun suna kuka mai ban tausayi..

**

Da tsananin mamaki Mu’azzam ke duban Chief Inspector, ya kasa yarda da abinda yake ci.. D’an girgiza kai yai kafin yace “Chief you need to believe me mutumin nan ba Iyakacin gaskiya yake fad’i ba.. Sir, I’m positive shid’in yasan Sagir sosai.. And yes munje location d’in da ya bamu and we found something.. Mun sami yarinyar da Sagir was about to marry.. Sir idan ka amince mun we are so close to finding the truth.”

Girgiza kai Chief Inspector yai yana mai duban Mu’azzam d’in idanu a kannare yace “I can understand you’re desperate to get to the bottom of this case.. And According to your team report Officer Gamji, mutumin nan ya sanar dakai Iyakacin hiran da yaji daga tattaunawar shi Sagir d’in yake da budurwarsa.. And kaima ka fad’a da kanka kaje wannan location d’in ka tabbatar da hakan, harma ka samu yarinyar.. So tell me, wani hujja kakeda shi da zaisa kaci gaba da ajiye shi a nan..?”

Huci kurum Mu’azzam yake yana duban Chief Inspector wanda yayi imani biyansa akayi ya kare mai laifi..

A hankali yake takowa gaban Chief kafin yace “Sir, I know my job.. I know exactly what I’m doing.. I only need a little more time to prove to you that..”

Katsesa Chief yai da fad’in “All the decisions are taking by me Inspector Gamji..! Now I’m ordering you to process his release immediately...!”
Cikin tsananin daka tsawa Yai maganar..

Mu’azzam dake ci gaba da sakin huci ji yake kaman ya shak’o wuyan che of inspector ya matsesa Sai ya fad’a masa uban wa yake karewa.. Assad ya kula da hakan, a hankali ya soma k’ok’arin janyo Mu’azzam yana fad’i cikin rad’a “Control yourself, don’t do anything foolish..”

K’ok’arin saita kansa Mu’azzam yai kafin ya jinjina kai yace “Yes, Sir.. Permission to leave, Sir.”

Chief ya jinjina kai yace “Good.. Dismiss now..”

Sara masa Mu’azzam d’in yai kafin yasa kai ya fice daga office d’in zuciyarsa na masa wani irin zafi...Shi kad’ai Sai wani irin tsuma yake.. Yana isowa ofishinsu buga benci yai yana sakin huci.. Maleeka ne da wasu abokan aikinsu guda biyu.. Suna ganinsa a haka duk suka mimmik’e.
Chapter 12 · 0% Book details