Sashe 170
Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mu’azzam da Assad dake tsaye gefe nan suka hango Jaja za’a shige dashi cikin doguwar motar. K’arasowa sukai gaban Chief muguwar murmushi saman fuskar Mu’azzam “Chief Jaja..” Ya ambaci sunansa yana murmushi kafin yaci gaba da fad’in “I told you so.. Kafin kaga bayana ni kuma zan kawo k’arshen ta‘Addancinka da rashawanka.. Na fad’a maka Kafin ka gama dani sai na tunb’ukeka daga NPF.. Na fad’a maka I’d get to the core of this case.. And look, I’ve kept my promise..” Ya kuma murmusawa yana jinina kai kafin yaci gaba da fad’in “Here we are now.. Zaka tafi gidan Yari kuma zaka k’arashe sauran banzan rayuwarka a can.. Kaji dad’in bak’in rayuwar dake jiranka a prison, Chief..” Ya k’arashe yana kuma sakin masa murmushi harda bubbuga kafad’an Chief kad’an irin yanda Chief Ke masa a lokutan baya. Lokaci guda ya tsume yace “Take him away..” Aka tasa k’eyan Chief aka wuce dashi sai huci yake yana aikawa Mu’azzam mugun kallo. Mu’azzam kaw ya bisa da kallon nan gani nan bari.
Su Mommy da Danger ma akazo za’a shige dasu.
Mu’azzam ya tare Danger, sukai tsaye su biyun suna duban juna, hannayen Danger rufe cikin handcuffs sai wani sakin mummunan murmushin nan nasa yake da gefen baki wanda yasan sosai yake bawa Mu’azzam haushi. Saidai wann karon Mu’azzam bai basa wann satisfaction d’in ba, hasalima shima murmushin yake, lokaci guda yake furta “I remember you once told me that you’re like a cockroach, you don’t die easily.. Just like a cockroach..” Ya gyara tsayuwarsa kafin yaci gaba da fad’in “Sai kuma gashi k’arshen Kyankyason nan yazo.. Zaka tafi yanda ya dace da Kyankyasai irinka and you’ll spend the rest of your miserable life there.” Ya k’arashe yana jinjina kai a hankali murmushin saman fuskarsa.
Danger ya kuma murmusawa yana jinjina kai shima “If I were you Officer.. I wouldn’t be so sure..”
“Take him away..” Mu’azzam ya fad’i yana tsimewa. Lokaci guda aka tasa k’eyar Danger.
Shari’a Ta k’are kowa ya amshi sakamonsa. Su Daddy ma suka d’unguma suka nufi gida. Washe gari Uncle Salman hardasu Inne da Uncle Ramadan Baban Ajidde harma dasu Ajidden suka d’aya zuwa Adamawa by flight. Kiki da Musaddiq ma sun bisu Fuforen dan tafiyan ya d’anyi taking mind d’insu off abubuwan da suka faru. Meema kuma ta koma school. Gidan Daddy ya rage saura Daddy ne kawai da Noor d’insa. Allah sarki Daddy daga k’arshe dai Allah ya k’addari shi da Noor d’insa zasu kasance tare bayan sadaukarwar da yaima D’anuwansa da kuma riskanta da jinya yai for 15 long years. Ganin abin ya dinga yi kaman dai a mafarki.. Shi kansa bai zaci zai iya ajiye tsufa da kunya ya nuna mata irin k’aunar da yake mata ba.. Haka ya d’ibe kusan sati bai fita ko company sai fitan na dole ya kama.. Tuni sun tsara yanda Kasuwancin ahalin zaici gaba da gudana ciki harda Ramadan mahaifin Ajidde wanda shima Keda kaso cikin kasuwancin Ahalin dukda cewa yana tab’a kasuwancinsa a can Kaduna. Abu mafi mahimmanci shine had’in kan ahali ba tarin dukiya da abin duniya ba. Sun kuma tabbatar da hakan bayan ahalinsu ya dunk’ule waje guda.
Uncle Salman ya shirya tafiya Rugarsu Shemau dan ya dawo da ita domin kaw Musaddiq ya fad’i duk abinda ya faru, yanda ya lalata shirin Shemau da Safeenah da suka so k’ullawa Sadiya sharri, shi kuma ya lalata shirin nasu k’aik’ayi ya koma kan mashek’iya. Bayan da Musaddiq ya warware komai Uncle Salman ya nufi ruga. Yanda ya sami rakiyar Danuwansa Ramadan. Allah sarki idan kaga Shemau dole ta baka tausayi, ta kod’e ta rame tayi duhu.. Sai dogon wuya kawai kake hangowa da k’walk’walan idanu. Dik ta fice a hayyacinta Dikda cewa wann karon Baffan nata da matarsa basu bata wahala amma saidai Sabo da rayuwar jin dad’i da tai da rashinsa na d’an kwanaki duk shi ya jigatata ya fiddata hayyacinta. Sanda sukaje ma ta dawo kenan daga tasan nonon saniya.. Tana hango Uncle Salman sai kuka.. Shid’inma yaji kaman kukan Ke zuwa masa.
Bayan sun keb’e su biyun Shemau na kuka take sanar dashi cewa bata aikata laifin da yake zarginta ba.. Taci gaba da share hawaye tana fad’in “Wllhi ba halina bane.. Amma haakki ne ya bibiye ni.. Kuma kaikayi ne ya koma kan mashek’iya.. Kuma na d’auki darasi irin wanda ban d’auka ba a baya..”
Shima kaman zai hawaye yake furta “Na sani Shemau, nasan baki aikata ba.. Musaddiq ya sanar dani gaskiyan komai.. Kuma idan akwai wanda yafi kowa laifi a nan toh kuwa ko shakka babu ni ne domin kuwa ni na umarceki da kiyi komai domin mu mallaki important document da D’anuwana ya bari wanda Hajara tai wasa dani dake.. Allah ya ganar damu baki d’aya yasa masu irin wann d’abi’a na son zuciya da son mallakan duniya ko ta hakink’aka suma su hankalta.”
Shemau ta Jinjina mai tana hawaye, tana satan kallonsa yanda yake dubanta yana sakin murmushi.
“Inasu Husna da ‘Yanbiyu..?” Ta tambayi yaransu.
Murmushi ya kumayi yace “Suna gida suna jiran dawowar Mamansu.. Nasan zaki sake bani dama a karo na biyu na nuna miki irin k’aunar da nake miki Shema ta..”
Rufe fuskarta tai da tafukan hannayenta tana murmushi cikeda jin dad’i.. Uncle Salman ya sanar dasu Baffah cewa ya maida matarsa Shemau kuma yazo ne ya d’auketa su tafi.. Su Baffah sukai Farin ciki Uncle Salman ya cikasu da abin arziki da burin zai sama masu gida Suma su fito gari.
**
Rayuwa Ta soma daidaita masu, sai son Barka da fatan alkhairi daga duka b’angarorin.
Yau Daddy yai kiran Mu’azzam parlornsa, Mu’azzam ya zauna daga can gefen k’afan Daddy. Lokaci guda Daddy yai gyaran murya ya soma fad’in “Mu’azzam akan maganar Foundation d’in nan ne..”
Mu’azzam ya jinjina kansa kad’an, Daddy yaci gaba da fad’in “Lokacin da na d’aukeka na kaika wann foundation d’in na sanar da kai cewa nayi investing inheritance d’inku a can.. Maganar gaskiya ba haka bane.. Domin Shari’a bai amince ka d’auki gadon mutum ka aiwatar da wani abu dashi ba tareda yarda da amincewarsa ba koda wann abun ya kasance abu mai kyau ne kuwa.. Nayi haka ne a lokacin domin Salman ya daina bin diddigin Ina Dukiyarku yake.. Wann foundation d’in wasiyace da mahaifinmu ya bari yace ko bayan ransa a cikin abinda ya bari a masa haka dan ya zamto sadaqatul jariyya a gareshi. Shares d’inku yana nan harma da Uncle d’inku Ramadan da muka san dashi yanzu.. Kasonku yana nan, mahaifiyarka ta sadaukar da nata dukiyar ma gidan marayu amma naka yana nan a asusun sirri da na Jima da bud’e maku.”
Mu’azzam ya murmusa kad’an kafin yace “Daddy nima gaskiya Bana buk’ata Alhamdulillah.. amma inaso idan zai kai a gina gidan marayu ko makaranta da masallatai ko tone boreholes wa mahaifina da mahaifin matata Allah ya kai masu ladan makwancinsu.”
Daddy ya murmusa kad’an yace “Allah sarki.. Allah ya saka a mizani ya maka albarka ya kuma albarkaci rayuwarka da ta iyalanka.”
Ya amsa da Ameen Daddy daidai lokacin Mamy Ta k’araso rik’eda tea d’in Daddy tana fad’in “What are you up to father and son..? Tattaunawar D’a da mahaifi..?” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta tana aje ma Daddy shayinsa.
Suka murmusa gaba d’aya Daddy na fad’in “kaman dai yanda Kikace tattaunawa ne na d’a da mahaifi..” Duk suka dan dara kafin Daddy ya soma sanar da ita yanda sukai da Mu’azzam. Farin ciki tai da batun itama had’ida saka masa albarka.
Mu’azzam ya gaisheta yana k’ok’arin mik’ewa alamun zai tafi.
Daddy yace “Har zaka tafi..? Bazaka zauna musha shayin ba..?”
Ya d’an sosa kai yana girgiza kai “A’a Daddy na gode..”
Mamy tace “Kyalesa kar ya cika cikinsa yaje ya amsa query wajen d’iyata..” Suka d’an murmusa gaba d’aya kafin Mu’azzam yai masu sallama ya fice.
Nan Daddy Ke sanar da Mamy batun da D’anuwansa Ramadan yai masa na fad’awa soyayyar ‘Yaruwarta Aisha da Ramadan din yai.
Sosai Mamy taji dad’in batun itakam hakan yayi mata.. Daddy harda Zolayarta da cewa itace babbar Ya uwa dole a nemi izininta.
Ta d’an rausayar da idanu kafin tace “Na amince amma da sharad’in bazasu d’auke min d’iyata Ajidde ba tinda gashi ta fara zuwa makaranta a nan.. Kuma tana gamawa za’a saka aurenta da D’a na Musaddiq.”
Kaman daga sama suka sinkayo muryar Musaddiq yana fad’in “Mamy please Ta k’arasa a gidana jss3 fa suka sakata a nan a haka ma saida mai da gaske.. Kawai nima tinda zan tafi UK d’in sai mu tafi tai a can please Mamy... Zanke mata extra lesson..” Ya k’arashe yana wani had’e hannaye alamun rok’o.
Daddy ya tsime yana fad’in “Waye zai baka d’iya ka tafi har uwa duniya da ita baa ga kamun ludayinka ba..” Daidai lokacin ya k’ara wayarsa dake faman ruri a kunne.
Musaddiq kaman zai kuka yake duban Aunty Nuratu , yana sadda murya yake fad’in “Mamy please say something.. Wllhi I’m all grown up fah..”
Itama cikin sigan rad’a tace dashi “Kasha kuruminka we have each other’s back ai..”
Daddy da ida wayarsa kenan yaci gaba da shafa wayarsa ba tareda ya dubesu ba yace “Duk ina sauraronku..”
Mamy ta murmusa tace “Toh Rankaidade a duba lamarinmu dai.. Mun girma kuma zamu iya rik’e d’iyarka in sha Allah.. We promise..”
Murmusawa Daddy Musaddiq kaw zuciyarsa sai bugawa yake yana duban Daddy yana jiran amsar Sa.
A hankali ya jinjina kai yace “Shikenan idan kun tabbata zaku iya..”
Musaddiq harda tsallen murna. Yana furta “Yess.!” Daddy ya katse da fad’in “Ba yanzu ba Sai next year in sha Allah.. Ka fara gaba, wata shekara idan ka dawo hutu sai ku tafi gaba d’aya.. That’s idan naga hankalinka.” Cikeda tsarewa Daddy Ke maganar.
Musaddiq badai haka yaso ba dan murna ta d’an koma ciki.. Toh amma ya ya iya indai za’a basa Farin cikinsa Crazy Dove d’nsa.
Mamy tace yasha kuruminsa nan da next year kaman gobe ne a wajen mai duka.
Musaddiq yai masu sallama bayan Mamy ta taushesa iyayen suka ci gaba da hiransu.