Sashe 155
Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mommy Ta shiga rarrabe idanu tana girgiza kai.. Lokaci guda kuma ta saki shewa tana tsalle tana tafi taka wak’ar zan cire..
“Zan cire.. Zan cire. Zan cire zan cire zan cire..”
Ta nufi gate a guje zata fice nan suka hango ana hangame gate d’in ga zuk’ek’iyar mota tana shigowa..
Gaba d’ayansu suka d’ago kai suna duban motar. Dikda motar Ta fice a yayi amma bazasu tab’a mance irin motar ba da kyaunta a wancan lokacin.
Hajara ma tsaye tai Cak da haukar k’aryarta tana duban motar. Saida motar Ta ida parking kafin suka fahimci motar.. Ba motar kowa bane face motar mahaifin Mu’azzam, Wato Alhaji Abubakar Gamji.
Cikin tsananin Shock gaba d’ayansu suke bin motar da kallo..
“Fa.. Faff..Fa.. Fatalwaaaa..!” Hajara ta furta haka tana nuna motar
SameenaAleeyou📚
*GIDAN ARO*
*77*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Mamaki bai gama cikasu ba saida sukaga mutanen dake fitowa daga cikin motar.
Mama Hindu itace a gidan gaba, daga bayan motan kuma, b’angare guda Ajidde ce.. D’aya b’angaren basu iya tantance matar ba sabida mayafi da ya rufe mata fuska.
Ta yanda Mommy ke tsaye ta side d’in matar ke zaune cikin motar, hakan na nufin a gaban Mommy akai parking motar.
Mommy Ta saki baki da hanci kai babu ko d’ankwali sabida haukar k’arya da Ta tasamma yi. Nan ta hangi matar ta sakalo k’afarta guda tana sauk’owa daga motar.
Jiri ya kusan d’iban Hajara ya kaita k’asa.
Yayinda matar tai tsaye fuskarta na lullub’e cikin farar lafaya da Ta rufa kan nata dashi.
Saida aka d’ibi dak’ik’ai a haka kowa na jira yaga wacece wann matar k’iraje sai bugu suke.. A hankali Ta fiddo hannunta wanda yasha k’unshi gwanin ban sha’awa, ga awarwaro masu kyau da d’aukan idanu, ta soma janye mayafin da ya rufe mata fuska sannu a hankali har fuskar nata ya bayyana.
Hajara ta saki wani irin k’ara tana mai zubewa wajen yayinda Daddy yai mutuwar tsaye yana dubanta.. Mu’azzam kam kasa jure ma tsayuwa yai Sai k’ok’arin soma takowa da yake yana nufo mahaifiyarsa, zuciyarsa naci gaba da bugawa a hankali, so yake ya tabbata gaskiya ne ba gizo take masa ba..
Har lokacin Daddy ya kasa motsawa sai dubanta da yake cikin wane irin yanayi yana ganin abin kaman d’aya ne daga cikin mafarkan da ya saba.. Wai Noor ce yake gani tsaye gabansa kuma tana takawa. Take yaji wani irin kuka gauraye da rauni ya kufce masa. Dubanta yake hawaye na gangarowa daga cikin idanunsa, wann hasken fuskar nata da ya soma gani sanda ya tsinceta a cikin jirgin ruwa shine yake kuma hangowa a halin yanzu.. Shekaru sunja amma shi gani yake Noor d’insa bata canza ba, itace dai wancan Noor d’in da ya tsinceta ya kuma ambaceta da *Haske*.... Kuka yaci k’arfin Daddy dake binta da kallo daga sama zuwa k’asa tayi shiga tsaf cikin tufafi irin na Larabawan k’asar Sudan..
Mu’azzam dake takowa da k’yar yana jin kaman bazai iya jan k’afafunsa ba.. Tsananin Shock d’in da ya tsinci kansa ciki baki Bazai iya fad’i ba.
“Ma..Mam..Mamy.. Mamy.. It is you.. You.. You can walk again..!” Ya fad’i cikin tsananin rawar murya mai rarrabewa lokaci guda ya rungume mahaifiyarsa yana mai fashewa da wane irin kuka, kuka mai ban tausayi.. Kukan da ya jima tare cikin k’irjinsa.. Kukan da ya jima yana son ya fidda.. Kukan da ya tara for over 15years.. Yanda kasan k’aramin yaro haka ya rungume mahaifiyarsa yana kuka sosai kuka mai sauti wanda ya sanyaya jikin duk wani mahaluk’i dake wajen.
Itama d’in rungumesa tai sosai tana kuka saidai nata kukan maras sauti ne ba kaman na Mu’azzam da ya kasance mai sauti ba wanda kowa ke iya sauraro.
Ta tallafo fuskar Mu’azzam da har lokacin akwai alamun jini, Ta kai dubanta ga kafad’arsa yanda shima akwai alamun ciwo.. A hankali ta saka yatsarta tana goge jinin dake fita daga gefen bakinsa hawaye saman fuskarta, ba tare da ta furta komai ba take tallafe da fuskarsa tana ci gaba da goge masa hawayen fuskarsa da ya had’e da jini.
Ya tallafi fuskarta shima yana dubanta hawaye naci gaba da gangaro masu Su duka biyun.
“Mamy.....” ya kuma furtawa cikin tsananin rawar murya yana dubanta.. Sake rungumar mahaifiyarsa yai wani kukan na kuma kufce masa. Abun ne tamkar ba a zahiri ba tamkar dai a mafarki.
Daddy da kansa ke kife, a hankali ya d’ago hawaye na gangaro masa yana duban Mu’azzam da mahaifiyarsa gwanin ban tausai.
Kowa a wajen dubansu yake cikeda tausayawa hawaye na gangaro masu. Harta Uncle Salman dake tsaye gefe shima saida yai hawaye.
Mama Hindu dake tsaye gefen Mamyn hawaye ne itama ke gangaro mata cikeda shauk’i... Kai harta Ajidde da tak’i jinin Kofur Zalimu saida taji hawaye na gangaro mata.. Dik son kallo irin na Ajidde balle ma ta tsinci kanta a gida irin wanda bata tab’a gani ba a zahiri kayan tausayin da taci karo dashi bai barta Ta tsaya kalle kalle ba.
Allahu Akbar! Allah abin godiya, buwayarsa gagara misali. Yau ga Nuratu tsaye kan k’afafunta cikin gidan da akai mata lak’abi da GIDAN ARO.
Farkawan da Mommy zatai sai ganinta tai kwance saman carpet a tsakiyar parlorn Daddy.. Ta soma d’ago kai tana duban mutanen dake zagaye da parlorn d’aya bayan d’aya.
Fuskar Daddy Ta soma gani kafin ta dubi na Mu’azzam, ta dubi na Inne dake zaune daga can angle d’in, sann ta dubi Uncle Salman... Lokaci guda kuma Ta sauk’e dubanta kan Nuratu dake zaune gefen mijinta Mu’azzam na zaune daga k’asa gefen k’afar mahaifiyar tasa. Irin duban da Mommy taga yana mata yasa hanjin cikinta murd’awa.
Mommy na zaune wajen sai ta soma k’ok’arin fashewa da kuka tana girgiza kai ganin yanda kowa ya zuba mata idanu alamun farkawarta ake jira. Tabbas yau rana ce na tonan asiri. Allah ka rabamu da jin kunya duniya da lahira. Ameen.
Mommy ta aza hannayenta aka Ta soma kururuwa tana fad’in ta shiga uku. Sai kuma ta mik’e zataci gaba da hauka. Tana fad’in “Ba haya..! Ba haya zanyi.. Ku barni na fice kar na zuba a nan..!”
Saidai ko gizau babu wanda ya motsa sai dubanta da suke.
Wann karon Nuratu ce ta taso ta matso kusan Mommy daketa tsalle tana kame cikin Ta tana ihun ba haya. Ta saka hannayenta duka biyu ta rik’o hannayen Mommy dasu.
Mommy ta Ware idanu tana duban Nuratu da yanda Ta rik’ota.
Murmushi saman fuskar Nuratu take furta “Baki tunanin yayi kusa Hajara.. Yaushe garin ya waye balle har daren yayi..?”
Cikin wane irin yanayi Mommy ke duban Nuratu dake murmushi tana rik’eda hannayenta.
Tai yunk’urin cire hannayenta daga cikin na Nuratu amma saidai bata sakar mata ba. Ta tsareta sosai da idanu “Ni ce fah Hajara.. Kishiyarki da kika kwashe shekaru ak’alla shabiyar Kina d’awainiya da ita.. Maiyasa zakiji tsorona..? Maiyasa zakiji gujeni..? Ki kwantar da hankalinki Abubakar ya tafi gidansa na Gaskiya ya bar GIDAN ARO kuma bazai tab’a dawowa ba.. Ya tafi yanda dani dake da koma wanene bamuda haufin wataran duk zamu tafi..”
Mommy ta girgiza kai cikeda daburcewa tana fad’in “Amm..Amma Maiyasa kika sanya fararen tufafi kika shigo motar sa.. Na tabbata Kinyi haka domin ki razaneni ki kuma fiddani daga gidana kaman yanda na fiddaki.” Ta fad’i cikin rawar murya irinta mai kuka.
Aunty Nuratu Ta murmusa kafin tace “Allah sarki.. Ashe har akwai abinda zai baki tsoro a wann duniyar Hajara.? Lallai wann abu ba k’aramin abu bane.!”
Mommy ta shiga girgiza girgiza kai tana hawaye “Bai kamata ki tashi ba Nuratu.. Boka yace tashinki na nufin kwanciyana ne.. Nuratu Maiyasa kika tashi bayan na mik’a ki ga masu magani na bogi, ‘Yan bori da rufa ido Wanda nakeda Tabbacin babu abinda maganinsu zai miki saidai ma ya k’ara miki kan uk’ubar da kike ciki.. Nuratu gidana da mijina sun haramceki Maiyasa kika dawo cikinsa.. Kin mance na fad’a miki gidana tamkar GIDAN ARO yake a wajenki zaki fice, kuma kin fice kaman yanda na miki alk’awari.. Amma ban miki alk’awarin zaki dawo cikin gidana ba Nuratu.!” Ta k’arashe tana girgiza kai hawaye d’aya na bin d’aya.
Aunty Nuratu ta murmusa tana duban Mommy wacce itama d’in ita take duba suna fuskantar juna “Kin mance cewa waraka baya hannunki Hajara.. Na Allah ne mai yin yanda yaso dabayinsa.. Dani dake da duk wani abin halitta a GIDAN ARO muke Hajara.. Duk daren dad’ewa zamu tafi gidan da kikaita k’ok’arin turani, amma saidai Watak’ila lokacin tafiyan nawa ne baiyi ba.. Hajara, tsawon shekaru goma shabiyar da kika kwashe da sunan Kina min abinda duk akewa majinyaci, ina sauraronki da duk sunbatunki akaina.. Sann na rok’i Allah da ya nuna min ranan da zaki bud’e bakinki ki fad’i duk abubuwan da ki aikata ma ahalina kafin na bar GIDAN ARO..” Ta d’an juyo ta dubi Daddy daketa dubanta, Sai kuma ta maidoda dubanta ga Mommy tace “Ba gidan mijina ba. Ina nufin duniya, wanda dani dake da koma waye zamu bari dik daren dad’ewa.”
Mommy Ta had’iyi miyau da k’yar tana mai rimtse idanu, tana jin wani abu kaman k’urji ya tokare mata mak’oshi.
_WAIWAYE_
Tin bayan da Marwan ya auri Hajara babu wata aba mai suna soyayya tsakaninsu, dama auren nasu ba wai yana so bane ya kasance sai dan babu yanda ya iya da tayin da abokin Babansa yai masa wanda shine Baban Hajara.