Sashe 143
Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Asheer yaci gaba da fad’in “Jinjina kansa yai ya goge k’wallan da suka taru idanunsa sai yace na yafesu tuntuni, ban furta masu haka bane sabida su kuma gane kurensu a rayuwa.. Ku sani yarana Allah yana son masu afuwa da gafara kuma ku zamto haka kunji.. Zam maku wasilci da hak’uri da afuwa a duk yanda kuka tsinci kanku sann da biyayya ga mahaifiyarku.. Idan Kun samu daga Allah ne idan Kun rasa daga Allah ne.. Rayuwar duniya ba rayuwa ce Ta dindindin ba.. Rayuwa ce da wata rana dole za’a barta.. Duniya GIDAN ARO ne wanda watarana dole mu barta mu tafi gidan gaskiya.. Kuyi k’ok’ari ku inganta gidanku na gaskiya a wann rayuwar kunji yarana.. Ubangiji ya albarkace ku baki d’aya.. Sai Abba ya rungume mu nida Habeeb.. Bayan da muka gama shan raken Sai ya mik’ar damu tsaye ya rik’e hannayenmu a b’a garorinsa guda biyu.. Muna cikin tafiya mai mashin ya ratsa tsakaninmu ya buge Abba sann mai Mota ya kuma bin kansa..” Hawaye suka gangaro wa Asheer yana gogewa da hannun rigarsa.
Saurin rungumesa Sadiya tai tana jin kuka na zuwa mata had’ida wani irin Farin ciki da annashuwa.. Allah sarki Abba ashe ya jima da yafe masu har ya masu addu’an Allah ya zama gata a garesu.. Lallai Ta kuma yarda mahaifi Katanga ne gashi dukda baya dashi amma bai barsu haka ba, Dukda ya nuna b’acin ransa ashe can cikin ransa yana masu add’uan samun sauk’i.. Allah sarki Abbanta inama zata ganshi tai masa tsananin biyayya inama ana iya janyo lokaci baya.. Allah sarki, saidai idan lokaci ya tafi shikenan ya zama yarihi bazai kuma dawowa baya ba.. Babu abinda zata saka ma Abbanta dashi bayan add’ua samun rahamar Ubangiji.. Tana rok’on Allah ya huwace mata tai masa wani abin wanda ladan zai dinga samunsa har makwancinsa. A hankali Ta furta “Allah ya gafarta maka Abbana.!”
Asheer ya amsa da “Ameen Adda Sadiya.” Ta bud’e lumsassun idanun nata tana duban d’anuwanta, ta kuma janyosa jikinta tana sakar masa murmushi a hankali, ji Tai zuciyarta yayi wasai kaman an yaye mata wani damuwa na gidan Duniya.
Umma dake tsaye daga k’ofa taji tattaunawan yaran nata hawaye ne suka gangaro mata itama tana kuma tina mijinta, masoyinta da yai sadaukarwa da dama a gareta.
A haka Aunty Larai Ta tadda Umma tana matsan hawaye.
Aunty Larai ta d’an dubeta ta sai kuma ta hangi Sadiya da Asheer dake rungume da juna ta basa wayarta yana game, Aunty Larai Ta murmusa kad’an Ta kuma duban Umma tace “Gwanin ban sha’awa Allah shi masu albarka.”
Umma ta amsa da Ameen tana kuma goge hawayenta.
Ta k’arasa saman kujera ta zauna a hankali tana furta “Bayan duk tulin butulcin da nai masa a rayuwa ya zab’i ya yafe mun kafin ya bar duniya.” Hawaye sukaci gaba da kwaranyo mata yayinda Aunty Larai ta k’araso ta zauna cikin sanyin jiki.
Lokaci guda Umma taci gaba da fad’in “Bani da kowa a k’asar nan sai shi sai kuma yaran da muka haifa tare dashi..” Ta murmusa kad’an hawaye naci gaba da zubo mata “Ibrahim masoyina.. Wanda ya soni tin Ina k’ank’anuwan yarinya da bazan gaza shekaru 8 ba a rayuwa. Mutumin da ya mun sadaukarwa mai girma ya zamto gata da Katanga a gareni...” Ta saka hannunta ta goge hawayen da suka zubo mata kafin Ta dubi Aunty Larai wacce jikinta yai sanyi sosai.
Umma taci gaba da jinjina kai tana fad’in “Zan sanar dake labarina Larai.. Domin kuwa ked’in kin zamto ‘Yaruwa a gareni.. ‘Yaruwar da na rasa a lokacin da na shigo k’asar nan.. ‘Yaruwar da Ta ceci rayuwana ta zab’i ita d’in ta halak’a..!” Kuka ya kuma kufce mata yayinda Aunty Larai tai mata k’uri tana jin hawaye na k’ok’arin ciko nata idanun itama.
_WAIWAYE_
Umma taci gaba da fad’in “Mu ‘Yan asalin k’asar Eritrea ne a wani gari mai suna Mazgon, mahaifanmu sunada rufin asiri babu laifi.. Mu biyu rak suka haifa a duniya daga ‘Yaruwata mai suna Halimatu sai ni mai suna Aisha.. Asalin sunana kenan domin kuwa a k’asar nan ne aka saka mun suna Uwani. Nida Yayata Haleematu mun taso cikin gata da soyayyan iyayemu, babu abinda muka nema muka rasa.. Komai iyayenmu na mana daidai gwargwado.. Tsakanina da Yayata akwai banbancin shekaru 7 a tsakaninmu a lokacin Yayata tana kimanin shekaru 15 a duniya ni kuma a lokacin inada kimanin shekaru 8 a duniya wani iftila’i na annoban cuta ya shigo garinmu.. A cikin wann outbreak na annoban muka rasa duka iyayenmu sann mutane da dama Sun rasa rayukansu a garinmu musamman wad’anda suka d’an manyanta.. Zan iya ce miki kusan kaso hud’u bisa goma na al’umman garinmu sun rasa rayukansu a wann Annobar. Muka zamto bamuda kowa sai tsirarun dangi Wanda da yawa ma Sun mutu.. Daga ni sai Yayata.. Rayuwa ta juye mana, bamusan yaya zamuyi ba bamu San mai zamuyi ba, ita kanta Yayata bata wuce a kula da ita ba amma sai d’awainiya na kula dani da kanta ya hau kanta.. Ana haka jinya ya kamani dan dama tun haihuwata inada yawan laulayi.. Da jinya yakamani sai Yayata ta dinga saida komai namu tana mun jinya, a haka har muka kusan rasa duk wani k’adara da mahaifanmu suka bar mana amma Allah bai nufa zan sami lafiya ba.. Haka Yayata takan sakani gaba tana hawaye tana fad’in kar na karaya in sha Allah zan sami lafiya.. A haka akace sai ta kaini asibiti a babban birnin tarayyar k’asarmu Wato Asmara.. Bamuda hanyar tafiya sai ta sayar da gidanmu dan shine ya mana saura.. Ta d’aukeni muka tafi Capital d’inmu Asmara. Toh a can asibtin akace sai an min aiki na samu lafiya.. Yayata Ta basu kud’in gidanmu da muka saida saidai wann kud’ad’en bazasu isa amun aiki ba.. Hankalin Yayata yakai mak’ura wajen tashi, ina asibiti tana fafutukan nemo kud’ad’en da za’a mun aiki na samu lafiya.. Wasu sukan yi yunk’urin nemanta da lalata dan kawai zasu taimaka dukda k’arancin shekarunta da shike taimako dan Allah yayi wuya a duniya.. Allah ya tsare Yayata bata saida mutuncinta ma kowa ba har wani mutumi yace zai taimaka mana, zai biya kud’ad’en amma idan na warke zamu masa aikatau dani da Yayata a gidansa, zai d’aukemu muje muyiwa matarsa aikatau.. Yayata ta amince da buk’atan mutumin cewa zamu masa aikatau duk tulin aikin kuwa idan dai har zai biya kud’ad’en da za’a mun jinya. Bayan da aka mun aiki cikin ikon Allah na samu lafiya.. Sai wann mutumin ya taho da buk’atarsa bayan da aka sallamemu a asibiti.. Bamuda wajen zuwa ma tinda gidanmu dake garinmu ma mun saida.. Hakan yasa dole mu amince mubi wann mutumin da ya taimaka mana.. koda mukaje gidansa abin mamaki Sai muka tadda ‘Yammata da dama ire irenmu sai wasu dattab’an mata wanda suke kula da ‘Yanmatan da kuma basu abinci.. Abin ya d’aure mana kai sabida tulin ‘Yanmatan da muka tadda a gidan.. Wad’ann dattab’an sune suka sanar damu cewa mu saki jikinmu wahala ya yanke mana.. Suka bamu tufafi wanda zamu saka naga sai duban Yayata suke suna maganganu k’asa k’asa suna cewa nida Yayata munada tsananin kyau sann za’a sami Kasuwa akanmu.. Tin daga nan hankalinmu bai nastu ba.. Musamamn Yayata data fahimci wann mutumin ba mutumin kirki bane kaman yanda mukai zato dan wad’ann dattab’an matan ma bana tunanin matansa ne.. A haka muna zaune cikin tsoro da d’ar d’ar wani rana aka Zo aka kwashi wasu daga cikinmu muna muka mu duka ‘Yanmatan dan mun kula wann mutumin cutar damu zaiyi.. Wad’ann Dattab’an matan su suke mana tsawa cewa muyi shiru ko Su jibgemu.. Haka Yayata take janyoni jiki tana lallashi gashi ban jima da mik’ewa daga rashin lafiya ba. A haka muka rage saura mu kad’an a gidan an kwashi ‘Yanmatan sahu sahu ana tafiya dasu yanda bamu sani ba, sann muma munsan watarana za’a Zo a tafi damu tinda an kwashe da dama an tafi dasu akan idanunmu.. Mukai yunk’urin guduwa nida Yayata amma sai wasu k’artan maza suka kamamu.. Mutumin yace tinda guduwa zamuyi ya kamata a tafi damu kafin mu masa asara.. Washe gari akazo da Mota aka d’aukemu aka kaimu tashan jirgin ruwa.. Haka aka sakamu a wann jirgin ruwan nida Yayata da wasu ‘Yanmatan.. Mun shafe kusan sati muna Yawo saman teku muka yada zango a wasu k’asashe har kusan uku da bamu San ko wasu k’asashe bane dan an b’oye mu ne can wani d’aki a k’ark’ashin jirgin ruwan.. Duk k’asar da muka tsaya sai muga an shigo da wasu ‘Yanmatan ma’ana dai wasu daga cikin k’asashen Africa muke zagayawa ana kwasan ‘Yanmatan. Dik k’asar da muka tsaya idan aka shigo da ‘Yanmatan sai a d’aura mata alama na wani coin a jelar kitsonta kaman yanda muma suka d’aura mana nida Yayata sann sun d’aura ma ko wacce daga cikinmu wann alama na coin a bakin kitsonta wanda nake da tabbacin shaida sukai mana.. Tsoro bai sakemu ba Yayata tana rungume dani.. Dik rana biredi guda ake bawa ko waccenmu a cikin wann jirgin ruwan shine abincin da zamuci.. Wasu lokuta haka Yayata take hana cikinta Ta bani nata kason.. A haka muka tsinci tattaunawan wasu ma’aikatan jirgin ruwan ana cinikinmu kaman wasu bayi.. Nan mukaji cewa K’asar turai zasu fice damu ‘Yanmatan da suka d’an data daga cikinmu zasu yi amfani dasu su dinga kawo masu kud’i dan mazan turawa suna son matayen Africa sann K’anana irina kenan zasu saida wasu b’angare na jikkunansu akan kud’i mai yawa.. Wasu zasu saida k’odansu dama duk wani organ mai amfani na jikin D’anadam.. Hankalin Yayana ya tashi musamman da Ta fahimci cewa nima naji tattaunawan mutanen.. Na soma kuka Ina fad’in zasu kashemu.. Ta rungumeni tana kuka tana fad’in Allah bazai nasu nasara akanmu ba da izinin Allah.. Tace dani nai shiru kar na nuna naji tattaunawar su da sannu Allah zai kub’utar damu.. Aiko bamu ida wann tunanin ba muka soma sinkayo harbin bindiga ashe Jami’an tsaro ne suke bibiyan wann jirgin ruwan.. A haka suka soma bud’emu suna son transferring namu zuwa wani jirgin suna fad’in ga jami’an tsaro..