Sashe 128
Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya d’an b’ata lokaci kafin ya manna mata kiss a goshi yana dubanta, murmushi gauraye da hawaye saman fuskarsa yake furta “Mu’azzam ya girma ya zama babban mutum harda iyali, sann yana kan bincike dan gano makashin Ikram, bazai huta ba har Sai ya gano azzalumin da ya rabamu da Ikram.. And justice will be served..” Ya k’arashe yana jinjina kansa alamun tabbatarwa.
Hannunta ya kuma rik’owa cikin nasa ya sumbata kafin yace “Zan tafi gobe Noorie, but next time in sha Allah tare zamu tafi.. Akan k’afafunki.. Zaki koma gidanki da kika baro akan k’afafunki da yardar Ubangiji... Kaman yanda nai alk’awari ma D’anuwana.. Zan kula da bayansa.. Zan kular masa daku..!” Ya k’arashe hannunta cikin nasa yana murzasu a hankali, kyakkyawan murmushi saman fuskarsa mai gauraye da hawaye. A hankali ya gyara mata kwanciyarta kafin ya kuma sumbatar goshinta ya sa kai ya fice.
Yana ficewa hawaye suka gangaro daga lumsassun idanunta.
**
ABUJA...
Tinda Ta shigo gidan gaisuwa kawai sukai ta k’ule a d’aki tana aikin kuka.
A haka Aunty Larai ta shigo ta sameta, juyin duniya Aunty Larai tayi ta fad’i meke damunta meke faruwa tak’i fad’i sai kuka take.
Aunty Larai ta kuma lek’a waje ko zata hango motar Mu’azzam amma shiru bataga kowa ba.
Ta dawo d’akin ta dafa Sadiyar.
“Sadiya.. Wai meke faruwa ne..? Wani abu ne ya sami Mu’azzam d’in.. Kinzo kin kulle kanki a nan Kina kuka.. Idan Umma ta ganki haka ai sai ki d’aga mata hankali.”
Maimakon ta amsa mata sai kuka da kuma fashewa dashi mai d’an sauri wann karon.
Aunty Larai ta girgiza kai kafin ta dubi Ashiru da shigowarsa kenan d’akin tace “Kai Asheer d’auko min wayata a parlor, idan bazaki fad’i ba shi Mu’azzam d’in ai zai fad’i ai..”
Wani kuka Ta kuma fashewa dashi ta rik’o Aunty Larai tana girgiza kai take fad’in “A’a Aunty nidai kar ki kirasa dan Allah.. Kawai nayi kewarku ne shine nazo..” Ta k’arashe tana goge hawayenta..
Aunty Larai Ta dawo da baya ta zauna “Ina sauraronki.. Meke faruwa..?”
SameenaAleeyou📚
*GIDAN ARO*
*65*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Cikin kuka take sanar da Aunty Larai duk abinda ya faru.
Ga mamakinta murmushi taga Aunty Larai tayi kafin yaci gaba da fad’in “Ni na zaci ma wani babban abu ne, dama kan wann ne..? Yo banda abinki Sadiya ai uziri zakiyi wa mijinki, shifa d’ah dad’i ne dashi balle ace na fari.. Yo ni nan da Allah bai tab’a bani ba kinaga idan akace zan sami d’ah na kaina wane irin Murna da rawar k’afa ce bazanyi ba.. Hak’uri zakiyi Sadiya wann lokaci ne na hak’uri dole kiga abubuwa daban daban da kuma sabbin yanayi da chanji.. Rayuwar auren kenan..”
Sadiya Ta kuma fashewa da kuka tana fad’in “Aunty fah bai sanar dani komai ba, ni bansan ko ya maida Safeenah ba, kuma bansan ciki ne da ita ba.. Kuma ni rejecting wayata da yai tayi shine ya dameni, sann da ya dawo bai ce min komai ba bai kulani ba, haka ma da ya tashi ficewa da safe bansan fitarsa ba har saida Safeenah tazota Ta k’ulla min wann sharrin.. Wllhi Aunty ni babu abinda nai mata amma da yazo Sai yabi bayan Safeenah ya saurareta yak’i ya saurara daga b’angare na saima cewa da yai na shige gida..” Kuka sosai ya kuma taso mata sanda take fad’in “Akan idona ya d’auketa ya sakata cikin mota.. Aunty wllhi K’arya take mun.. Sharri tamin.. Ni babu abinda na mata.. Patrick ma shaidana ne..” Ta k’arashe cikin kuka.
Sosai taso bawa Aunty Larai dariya Wai Patrick ma shaidarta ne, Aunty Larai ta murmusa kad’an tace “Kai Sadiya k’uruciya dai har yanzu na d’awainiya dake.. Koda shike d’iyar tawa bata rufa ashirin ba har yanzu shatara take.”
Cikin rawar Murya Sadiya Ke fad’in”Aunty bayansa kike bi bayan kinji duk abinda yamun..?”
Aunty Larai ta girgiza kai tace “A’a Sadiya ba bayansa nake bi ba.. Ni na isa a b’ata ran d’iyata kuma nabi bayansa..” Ta d’an daidaita zamanta kafin taci gaba da fad’in “Sadiya shi zaman aure ibadah ne.. Kuma zama ne na hak’uri.. Zama ne na Zo mu zauna Zo mu sab’a.. Yau da gobe Sai Allah. Dik auren da kikaga yayi k’argo Toh ki sani hak’uri ne ya kaisu ga cin nasara... Kuma Ina so ki sani dan Kin sami d’an little misunderstanding kar kike d’iban jiki ki taho gida.. Ba komai ake d’iban jiki a nufi gida ba, wani abun tsakaninku zakuyi sorting out matsalarku kuyi fixing komai ba Sai kun k’ara da third party ba, just the two of you.. Kuyi abinku a d’aki ku binne babu wanda yaji.. Har kullum idan kikace komai sai kin kai k’ara toh fah ke da kanki kin bud’e ma aurenki gib’i ne.. Matsala tsakanin ma’aurata idan ba yafi k’arfinki bane karki kuskura ki kai gaba kinji koh.. Wani dama ba Farin ciki yake da zaman lafiyar da kuke keda mijinki ba, akwai ‘yan jira auren ya lalace suyi Farin ciki da hakan. Duniya ce mai tarin mutane na kirki da akasin hakan..Wani k’iris yake jira yaji akanki dan dama ba k’aunar ci gabanki yake ba koda a fuska yana nuna maki k’auna..” Ta d’anyi fasali kafin taci gaba da fad’in “Rayuwar aure haka ta gada Sadiya, yau dad’i gobe akasin haka.. Iyayenmu duk haka sukai hak’uri suka jure har ta kaisu ga cin nasara..Sann Kowa fah da irin battle d’in da take fuskanta gidan aurenta, babu auren da za’ace anyisa ya tafi smoothly hundred percent babu matsala babu shi, wata zaki samu matsalarta Uwar mijin ce, wata dangin miji.. Wata abokiyar zamanta, wata da ‘ya’yan cikinta ma za’a jarabceta wata kaw shi kansa mijin shine nata k’alubalen.. Saidai na wani yafi na wani, mai imani shine Allah yake jarabtarsa.. Shiyasa kansa auren kansa ibada ne.. Bautar Allah kike. Kinga kaw dik abinda akace ibadah ne dole sai an jure anyi hak’uri.. Zakiga auren soyayya akai amma abinda za’a fara maku nasiha dashi shine hak’uri.. Ayi hak’uri, zakice yana sona Ina sonsa yo wane hak’uri? Sanin abinda ke cikin zaman auren yasa ake cewa sai anyi hak’uri.. Ayi hak’urin zama da juna. D’an Adam ajizi ne, tara yake bai cika goma ba, idan ya gaza miki Ta wann b’angaren Sai ki duba b’angaren da bai gaza ba, shima haka a b’angaren mijin, idan matarka ta gaza maka ta wani b’angaren sai ka duba b’angaren da bata gaza ba.. Mu ‘yanadam ne kuma masu kuskure, kiyi hak’uri kiyiwa mijinki uzuri kinji koh..”
A hankali take jinjina kai tana hawaye.
Aunty Larai tace “Yauwa yayi kyau, toh yanzu salin alin ki tashi ki koma d’akinki banso ma Umma tasan anyi wann..”
Girgiza kai ta soma tana kuma fashewa da wani kukan “Aunty naji duk abinda kikace kuma zanyi amfani dasu in sha Allah.. Amma Aunty ni banzan iya komawa gidan yanzu ba, banson zuwa gidan.. I just need space.. Dan Allah ki barni a nan..”
Aunty Larai ta murmusa kafin tace “Shikenan bazan tak’ura miki ba, barin barki ki d’an huce kad’an maza tashi ki shiga band’aki ki wanke fuskarki.. Ni bani son ganin damuwar nan saman fuskarki ne balle Umma ta d’ago wani abu.. Kinsan idan ta fahimci ba da sanin mijinki kika taho ba tsaf zata koraki ne.. Maza tashi ki wanke kizo kici abinci nasan da wahala idan kin saka abinci a cikinki..”
Ta jinjina kai da k’yar dan har lokacin kanta bai daina sara mata ba, Ta mik’e tana jin jiri na k’ok’arin kayarda ita.. Aiko kaman wasa tana ida mik’ewa Ta yanki jiki ta fad’o kan gadon..
Hankali tashe Aunty Larai ke jijjigata tana ambato sunanta.
Muryar Aunty Larai d’in da Umma Ta jiyo yasa ta nufo d’akin babu shiri rik’e da cazbahanta dan dama tinda ta ida sallar la’asar bata mik’e saman abin sallar nata ba.
“Subhanallahi.. Meke faruwa.. Ke Sadiya..?” Umma ta fad’i a d’an kid’ime tana jijjiga Sadiyar yayinda tuni Aunty Larai Ta fice d’ibo ruwa, Ta k’araso ta shiga shafawa fuskar Sadiyar Umma na mata fifita da bakin hijabinta.
Tana numfashi amma still idanunta a lumshe ga jikinta da ya sake gaba d’aya.
Umma na mata fifita take ambato sunanta tana fad’in “Ke Sadiya.. Kina jina.. Sadiya bud’e idanunki mana.. Sadiya..!” Hankalin Umma duk a tashe, ba komai take tunawa ba sai rashin mahaifin Sadiyar da sukai.. Gani take kaman zasu kuma rasa ahali ne..
Aunty Larai kam tuni Ta shiga neman layin Mu’azzam amma saidai bata samu, hakan yasa Ta yanke shawarin kiran Assad.. Nan ta sanar dashi maza maza ya taho ya kaisu asibiti.
Cikin mintoci da basu gaza talatin ba Assad ya k’araso, Umma da Aunty Larai suka tallafeta suka sakata cikin motar. Aunty Larai tace da Umma ta zauna gida wajensu Habeeb ita zata kula da Sadiya. Yaranma duk hankulansu a tashe.
Umma ta jinjina kai tana duban d’iyar tata cikeda tausayawa had’ida k’aunarta. Nan tai masu fatan sauk’a lafiya da addu’an samun sauk’i ga d’iyarta Sadiya.
**
Mu’azzam ya tsare Musaddiq d’in sosai da idanu kafin yace “Kana tunanin zamu iya samunta a wann gidan.?”
Jinjina kai kad’an Musaddiq yai yace “Gidan Amaryar Senator Abba Mijinyawa, na tabbata zamu iya samun Mommy a wann gidan dan Hajiya Faty aminiyarta ce.”
Jinjina kai Mu’azzam yai kafin yace “Muje.”
Babu musu Musaddiq ya zaga ya shige mazaunin mai zaman banza.
Koda suka iso gidan Musaddiq ne ya shige ciki yayinda Mu’azzam ke jiransa daga haraban gidan.
Musaddiq ya dubi Hajiya Faty k’awar Mommy wacce Kwanakin baya Mommy tazo gidanta sanda suka sami sab’ani da Daddy. Musaddiq ya gyara tsayuwarsa yace “Aunty zaifi kyau idan kika sanar dani gaskiya, nasan Mommy batada yanda zataje da ya wuce nan..”
Hajiya Faty Ta d’an sauk’ar da farin glasses na k’ara k’arfin gani dake manne saman idonta kafin tace “Musaddiq, kana so na sake maimaita maka ne.. Your Mom isn’t here.. Bata nan, kuma ni bansan yanda take ba..”
Musaddiq ya d’an shafi fuskarsa kad’an cikeda k’osawa “Aunty please.. Dan Allah ki fito da Mommy idan har kece kike b’oyeta.. Aunty Mommy fah ba mai laifi bace kawai, Mommy is dangerous.. Please idan tana tare dake ki fito da ita..”