Sashe 166
Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta k’arashe tana mai duban Sadiyar “Toh mijinki na nemanki, ya kira wayarki bata shiga nace a gida ma kika barota.. Tashi kije, ki d’ibi kayanki ma ki tafi dasu dan mukam bacci zamuyi nasan Inne ma ta riga ta kwanta.”
Da mamaki Sadiya Ke dubanta kaman zatai kuka “Haba Aunty dan Allah ce masa kikai idona biyu..”
“Toh k’arya kike so na masa.” Ta bata amasa tana mai kwab’e mayafinta.
Ta kuma turo baki gaba tana buga k’afa kad’an, ba don taso ba Ta mik’e kaman zatai kuka.
Aunty Larai ta k’arada “Kayan naki fah ko na biyoki dashi ne.”
“A’a dan Allah ni dai zan dawo Aunty.. Kinji dan Allah..”
“Toh shikenan yanzu dai jeki.. Idan kuma kin makara saida safe.. Gashi can zaune waje yana jiranki..”
Ba dan taso ba ta zira hijab d’inta ta fice.. Can Ta hangesa zaune k’afarsa d’aya bisa d’aya waya manne kunnensa. Ta k’araso da sallama saman bakinta, har lokacin waya yake. Ya amsa a hankali yana mai nuna mata gefensa alamun Ta k’araso ta zauna. Saida ta d’an waiga gefe da gefe kafin ta k’araso tai yanda yace d’in.. Har lokacin waya yake.
Ji tai ya sakalo hannunsa ta baya saman kafad’unta daga nan yanda suke zaune saman ‘yar doguwar kujerar.
Ita dai duban hannun nasa kurum tai tana girgiza kai kad’an shidai babu ruwansa wai ko kunya baiji ne.? Ta tambayi kanta tana k’ok’arin matsawa amma sai taji hannun nasa saman kafad’arta, babu yanda ta iya haka nan ta zauna tana sauraren wayar nasa da ba fahimta take ba dan aikinsa ya shafa.
Daga yanda Safeenah take zaune a d’akinta tana aikin kula da Dantsanarta nan ta hangesu zaune a haka sabida labulayen d’akin nata dake janye. Hawaye masu zafi taji suna ciko idanunta. Lokaci guda Ta soma girgiza kai, a fili take furta “No way.. He’s mine.. Mu’azzam is mine..” Ta d’ago Dantsanan tana nuna masa Mu’azzam “See, kaga Dad d’inka koh.. Don’t worry champ, Dad d’inka zai dawo garemu.. I promise you this.” Ta k’arashe tana mai mik’ewa tsaye ta nufi k’ofa.. Saidai tana bud’e k’ofar taga Daddy alamun zai shigo.
Yanda ya tsareta da idanu ya sanyata sadda nata idanun kuka na k’ok’arin zuwa mata “Daddy please don’t stop me.. Please let me take back what was stolen from me.. Dan Allah Daddy kar ka hanani.. Mu’azzam is mine.. He is mine Daddy..”
Jiki a matuk’ar sanyaye Daddy ya rungumota gefen jikinsa, lokaci guda suka dawo da baya suka zauna saman gadon. Har lokacin kuka Safeenah take mai tab’a zuciya. Ta kuma d’ago kanta tana duban su Mu’azzam da Sadiya. Daddy ya kai dubansa ga yanda take kallo.
A hankali kanta kwance jikin mahaifinta take furta “Maiyasa bazai soni irin yanda yake sonta ba Daddy.. Maiyasa ya kasa fahimtan irin son da nake masa..? Look at them Daddy.. full of life.. and love. While ni gani nan left with nothing.. Daddy no one loves me right..?” Ta k’arashe cikin tsnanin rawar murya.
Saurin girgiza mata kai yai yace “We all love you Safeenah.. So much, kawai kink’i ki fahimci hakan ne..”
“But Mu’azzam doesn’t love me Daddy..” ta bashi amsa kai tsaye. Lokaci guda kuma taci gaba da jinjina kai tana hawaye “You know Daddy, I always thought of myself as a very strong woman.. Zan iya samun duk abinda nake so a lokacin da naga dama.. and that I can get through whatever comes in my way.. But then I was wrong.. That’s not how it works right Daddy..?” Ta k’arashe murmushi da hawaye saman fuskarta.
Daddy na danne hawayensa yake jinjina mata kai.
Safeenah taci gaba da girgiza kai tana hawaye “I can’t take this anymore Daddy.. I’m not that strong.. I can’t Daddy..!” Kuka yaci k’arfinta.
Lokaci guda yake furta “You are strong Safeenah... Just try to get better.. Nasan kinada zuciya mai kyau.. And you’ll see komai zai wuce.. Kuma zaki sami lafiya da izinin Allah.”
Safeenah na hawaye ta rik’o hannayen Daddy cikin nata “I’ll get better in sha Allah Daddy.. I promise you.. Ka kirasu su tafi dani.. And please visit me often kaji Daddy..”
Ya jinjina mata kai hankali yana share mata hawayenta “I’ll visit you every day.. I promise..” Ya fad’i hawaye na gangaro masa.
Cikin rawar murya take furta “I love you so much Daddy.”
“And I love you too my princess.”
Safeenah ta kuma kwantar da kanta b’angaren jikinsa kad’an hawaye na kuma gangaro mata.
Daddy bai bar d’akin ba saida ya tabbata Safeenah Ta samu bacci Dikda cewa daga k’arshe abubuwa marassa kan gado taita fad’i wanda zai tabbatar maka cewa kwanyarta ya sami matsala. Haka tai kwance rungume da Dantsanarta gwanin tausayi.
Yana isa b’angarensa ya ci karo da Mommy cikin d’akinsa ta kasa ta tsare sai huci take.
Da mamaki yake dubanta yana girgiza kai “Mai kikeyi a nan..?”
“Aw tambayata ma kake.. Ka kulleni cikin store dan ka samu daman watayawa kaci amanata da Nuratu koh.. Toh baka isa ba Marwan.. Wllhi bazan tab’a barinku cikin kwanciyar hankali ba..!” Ta k’arashe tana huci.
“Zo ki fice mun a d’aki.” Ya fad’i yana nuna mata k’ofa.
“Bazan fita ba Sai naga shigowar Nuratu.. Idan kun cika marassa kunya kuyi komai akan idanuna..” Ta fad’i tana kuma jijjiga.
Ya jinina kansa kad’an kafin yace “Kar ki damu bazata shigo ba, kinsan dalili..? Tana can tana kula da k’aramar ‘Yarki Karima wacce kika tasamma haukatata da haukarki kaman dai yanda kika haukata Safeenah kika tura Musaddiq ya d’auki laifinki.. Kinji dad’i Hajara kin tarwatsa min yara.. Amma kar ki damu da sannu zaki biya duk abubuwan da kika aikata..”
Yana ida fad’in haka ya nufi bathroom ya barta nan tsaye sai jijjiga take tana huci. Aiko Daddy na shigewa ta soma ganin wani halitta ya nufota a guje yana fad’in shine mijinta. Mommy ta shiga ihu tana fad’in kar yazo kusanta..
A haka Daddy ya fito ya taddata sai ihu take tana tsalle tana fad’in “Mijin Nuratu ne kai.. Kaje ka sameta.. Wayyo na shiga uku.. Marwan ka ceceni zai kasheni..!” Ta k’arashe tana mai silalewa wajen tamkar sumammiya.
**
Washe gari Sadiya a d’akin Mu’azzam ta tsinci kanta bayan ya tashe ta tai sallar Asuba, sai lokacin take tuna wayon da yai mata daren jiya yace tai masa rakiya ya kwanta shima zai rakata, Ashe dai bacci yayi gaba da ita a nan, ta kuma duban tufafin dake jikinta rigarsa ne da ya tsaya daidai cinyarta. Ta girgiza kai kad’an tana dafe fuskarta.
Ya fito daga closet sanye da jallabiya yana dubanta “Good morning Beautiful.” Ya fad’i yana dubanta harda kashe mata ido guda ganin yanda ta tsaresa da duban tuhuma.
Kaman zatai kuka take furta “Na shiga uku.! What have you done Inspector..? Allah fah yana ganinka..”
Sosai taso basa dariya yanda tai maganar amma Sai ya gimtse had’ida tab’e baki kad’an yana mai girgiza kai “What did I do..?”
“Ai ba haka mukai ba..” Ta kuma fad’i kaman zatai kuka.
Murmushi ya sakar mata harda kashe ido guda “Tashi kije kiyi sallah idan na dawo zamu k’arasa.” Bai jira cewarta ba ya fice yana kuma murmusawa.
Dafe kanta tai cikeda takaici, Mu’azzam ya gama da ita, yanzu batasan ta yanda zatai ta fice daga d’akinsa ba.. Shikenan za’ai Ta nemanta aga bata nan.. Itakam ta shiga uku.. Ba abin ta fice ba ta b’ace a hanya dan ba wai tasan kan gidan bane. Da wann tunanin ta mik’e ta nufi bathroom d’insa.
Tazo zata d’auki kayanta kenan da yai hanging a closet d’insa ta hango wani abu kaman ledar ultra pad. Ta k’arasa tana dubawa. Take ta shiga tina farkon had’uwarsu da yanda ta jefa masa a fuska. Murmushi ne ya kufce ma. Wato Ashe yana ajiye dashi.. Ta cigaba da juyawa tana murmushi har bataji shigowarsa ba.
A hankali ya k’araso ya rungumeta ta baya. Ya sumbaci gefen wuyanta kad’an yana furta “Kina mamaki na ajiye ne.?”
Ta d’an kaikaito tana dubansa. Lokaci guda yake jinjina kai murmushi bai bar saman fuskarsa ba “I couldn’t throw it away.. Kinsan Maiyasa..?”
Ta tsaresa da idanu ba tareda ta iya cewa komai ba.
Mu’azzam yaci gaba da fad’in “Ina adana duk memories d’in da suka danganceki tin daga randa muka had’u.. Duk abinda ya shafeki yanada mahimmanci a wajena Beautiful.” Ya k’arshe yana mai kwantar da kansa saman wuyanta.
K’ok’arin zame jikinta tai tana fad’in “Nifa sallah zanyi Inspector.. Dan Allah ka rakani hanya kafin gari ya waye.” Ta fad’i kaman zatai kuka.
“Alright yi sallah na miki rakiya kafin gari yai Haske tinda baki so a ganki.. Allah sa kar nai bacci..” Ya maganar yana mai hayewa saman gado had’ida kishingid’a. Sai kallonta yake kyakkyawan murmushi saman fuskarsa.
Ta fara k’ok’arin sakar masa kuka. Ya soma lallashinta yana fad’in “Yi hak’uri.. Yi sallan na rakaki..” Ya k’arashe yana k’unshe murmushinsa.
**
Washe gari da safe Daddy ya kira asibitin Safeenah suka tafi da ita. Mommy ma an shirya tafiya da Ita a safiyar, ga abubuwan da take tun a daren jiya mai kama da hauka. Idan kaga Mommy kaman ba Ita ba dik Ta koma abin tausayi.
Koda za’a tafi da Ita dogewa ta dingayi tana fad’in sai an tafi da Inne idan ba haka babu uban da ya isa yai arresting d’inta.
Inne kifa kanta tai tana hawaye ba tareda Ta iya duban ahalin nata ba. Suna a haka wayar Mu’azzam Ta soma ruri, daga gate ake kiransa.
“Ramadan Gamji..?” Ya nanata yana duban sauran mutanen dake parlorn.
“Alright give me a minute.” Ya fad’i yana mai kai dubansa ga Daddy.
Daddy ya tambayesa meke faruwa. Nan yake sanar dashi “Wai wani mutumi ne a waje yace yana son magana da kai.. Sunansa Ramadan Gamji.”
Gaba d’aya suka nanata sunan kafin Daddy ya jinjina kai yace “Ce masu ya shigo..”
Mu’azzam ya maida wayar kunnensa yace da security d’in ya shigo da mutumin.
Jim kad’an saiga security d’in wani mutumi mai cikeda kamala na biye dashi. Zuciyarsu sai tsinkewa yake sanda mutumin ke nufo parlorn.
Daga Daddy harma Uncle Salman da Inne mik’ewa sukai tsaye suna duban mutumin dake nufosu wanda ba fuskan kowa suke hangowa tattare dashi ba face mahaifinsu.
SameenaAleeyou📚
*GIDAN ARO*
*82*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*