← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 175

Sashe 86

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ajidde tai shiru tana duban Malama bata sanar da ita abinda Musaddiq yai mata ba Sai ta soma sanar da ita abinda taga Kyallu tayi.

Malama Ta nusa kad’an tace “Da yawan irin wad’ann bokayen sun ari sunayen masu magani na gargajiya suna fakewa suna yin bokancinsu Ajidde.. Tabbas akwai masu magani na gaskiya na gargajiya wanda ubangiji ya huwace masu ilimin sanin magunguna.. Sannan akwai Malamai masu magani da ayoyin Ubangiji bisa tsari da shari’a.. Sannan akwai wad’anda suke fakewa suke bokanci suna yanka dabbobi bada sunan Allah ba suna bawa mushirikan Aljanu jini.. Sai kiji ana cewa a kawo bak’in jaki za’ayi magani, a’a a kawo faran tinkiya za’ayi magani.. Irin wad’ann masu maganin Ajidde duk sun b’adda kama suna shiga cikin na gari suna bokanci da tsafi.. Suna shirka ma Ubangiji da sunan magani.. Akwai majinyata da ciwo zaik’i ci yak’i cinyewa.. Aita kawo masa sunayen masu magani gari wa gari.. Idan ba’ayi sa’a ba har a fad’a hannun irin wad’ann masu maganin wad’anda bokaye ne masu shirka ma Ubangiji ba wai maganin sukeyi ba wasu ma kawai sai su had’a ‘yanuwa gaba suce wane ne yai maka jifa alhali k’arya ce kawai bokanci ne da tsafi... Abu na farko da majinyaci zai saka a ransa shine jinyar nan Bautan Ubangiji yake.. Kuma jarabawa ce da Allah ya jarabcesa da ita domin yaga zaiyi hak’uri yaci jarabawa kokuwa zai kauce wa rahamarsa.. Duk zafin jinya zunubi ake kankare wa majinyaci.. Sannan suma masu jinyar wann majinyacin jarabawa ce da Allah ya jarabcesu da ita kuma duk d’awainiyar da sukai wa mai jinya lada suke samu wanda Allah shi zai biyasu wanan ladan na hak’uri da kuma d’awainiyarsu.. Hadisi yazo ingantacce Manzon Allah (S.A.W) yace babu wata cuta da Allah ya sauk’ar saida ya sauk’ar mata da maganinta. Ko wata iri ce kuwa... Neman magani ba haramun bane kuma godiyan Ubangiji shine ka saka dukiyanka ka nemi lafiya da Ita, amma saidai kar garin neman magani ka kai kanka ga halak’a.. Kar kaje wajen boka domin ya baka lafiya.. Babu mai warkarwa sai Allah.. Shi yake saka cuta kuma shi yake yayewa.. Idan yaso ko baka sha komai ba Sai ya baka lafiya dan shine mai bayarwan. Idan baiso ka sami lafiya ba ko zaka zaga duniyar nan Sai k’a k’arashi neman maganinka baka samu ba.. Tauhidi itace abu na farko da majinyaci yake buk’ata Ajidde.. Ita ce magani na farko da majinyaci zai sha.. Ya saka a ransa Allah shine mai yi kuma shine mai hanawa.. Idan ya tsira da tauhidinsa ko da Ubangiji ya k’addari wann jinya ba na tashi bane sai yayi fatan ya d’auki ransa yana mai imani ba yana mai kauce ma Ubangijinsa ba.. Sau tari zakiga anje wajen irin wad’ann masu maganin anyi bori anyi yanka ma aljanu sannan an halak’a daga k’arshe ba’a samu biyan buk’atan ba dan basu sukeyi ba Allah shine mai yi.. Ba’a samu biyan buk’ata ba Sannan an mutu ana kauce wa Ubangiji.. Allah ya shiryemu gaba d’aya ya kuma datar damu.. Ya ba ma marassa lafiyanmu lafiya, ya tsare mana imanin mu da tauhidinmu.. Ya d’auki rayuwarmu yana mai farin ciki damu..”

A hankali Ajidde ta jinjina kai tana fad’in “Ameen Malama..”

Malama Hafsah ta mik’o mata ruwa addu’a da take bata sannan ta had’a mata da garin Habbatussauda tace wannan hayak’insa zaki mata a cikin d’akin da take kwana.. Yana koran shaid’anu.. Sannan yanada kyau mutum ya dinga hayak’in habbatussauda a cikin gidansa lokaci zuwa lokaci domin yana kore shaid’anu daga gida.”

Ajidde ta jinjina kai tace “Toh Malama Allah ya saka da alkhairi ni zan wuce..”

Malama ta jinjina kai tace “Allah ya nufemu da dacewa ya kuma bawa Nuratu lafiya..”

Ajidde ta amsa da Ameen kafin sukai sallama da Malama ta fice.

**

ABUJA

Yau kusan kwanaki uku kenan bata sanyasa a idanunta ba, tinda ya tafi ranan da dare bata kuma ganinsa ba, gashi harta waya ma bai mata ba.. Haka zatai ta kallon lambarsa taji kaman ta danna kira amma sai ta fasa dan batasan mai zata ce masa ba.. Kasancewar laraba tayi ya sanya take ta jin wani Farin ciki cikin zuciyarta dan tafiyarsu Alhamis ne kaman yanda yace. Harga Allah ba Farin cikin tafiyar take ba amma tasan tana Farin ciki ne sabida zata gansa.. Tai shiru tana tuhumar kanta Maiyasa take jin haka akansa..? A baya zata iya cewa bata tab’a jin irin hakan ga kowa ba harta kuwa Sagir da suka kusan aure.. Ko dan lokacin abin hannayensu take so ba Su d’in ba..? Toh Maiyasa yanzu da bata son abin hannun kowa take jin haka gameda Inspector..? Kar fah maganan Aunty Larai ya tabbata cewa son Inspector take.. Cikin sauri ta d’ago kai tana duban fuskarta cikin dressing mirror.. Ta kuma tambayar zuciyarta.. Sai kuma ta rintse idanunta cikeda tsoron ansar da Zuciyar nata ke bata.. Ta k’ura ma fuskarta idanu cikin mirror kafin tace “Are you messing with my heart now Mr Inspector..?” Cikin sauri ta lumshe idanunta tana jinginuwa jikin gini.

Aunty Larai dake lab’e bakin k’ofa tana dubanta murmushi saman fuskarta, a hankali tai knocking da yatsarta guda.

Sadiya tai saurin tattara natsuwarta tana kintsa kanta.

Aunty Larai ta shigo sallama saman bakinta, hannunta rik’eda had’in Kankana..

“Maza Zo ki shanye wann..” Ta fad’i tana zama gefen gado.

Sadiya ta d’anyi rau rau da idanu dan kusan kullum Aunty Larai da irin had’in da take bata.

Ta d’an dubeta kafin tace “Bari dai na miki bayanin menene a cikin wanann.. Kinga akwai Kankana K’wallo d’aya sannan sakwai sabuwar tsamiya k’wara hud’u sannan akwai tafarnuwa curi d’aya.. Ita Kankana tanada tasiri jikin ‘ya mace sannan tsamiya magani ce itama.. Tafarnuwa kuwa Antibacterial ne.. Duk wata cuta da ta shafi mara tana maganceta.. Yana da kyau bayan lokaci ki dinga yi ma kanki wannan had’in dan takan bada kariya daga cuta na sanyi da ya addabemu a gidajen aurenmu.. Sannan ita wann had’in ko wanda ke fama da cuta na sanyi zai iya had’awa ya dinga sha da izinin Allah za’a samu waraka. A had’asu waje guda a dafa a dinga sha safe da yamma.. Kinga ba wani abu mai cutarwa na baki ba maza d’auki ki shanye.”

Sadiya ta d’auka ta kafa kanta ta shanye. Duk a kwanakin had’e had’e iri daban daban masu inganta lafiya da matantakanta Aunty Larai ta dinga bata.. Wasu Ta mata bayani wasu kaw bata mata bayani saidai ta sanyata cinyewa ko shanyewa.. Ga gyaran fata na musamman da take mata ita har Ta fara tinanin kodai had’a baki Inspector sukai da Aunty Larai shisa ya dena zuwa gidan.. Taga har alhamis Yayi babu Inspector babu batun tafiyarsu.. Abin har dai ya soma damunta gashi Aunty Larai bata fasa mata abu guda da take mata ba.. Fatarta ya kuma murjewa har wani kyalli da shek’i yake.. Jikinta ya kuma cika dan tana iya jin hakan tattare da ita.. A tak’aice ita kanta tana jin kanta Ta kuma canzawa. Idan ka kalleta dole kaso sake kallanta.. Wasa wasa saida akai kusan sati Inspector baizo gidan ba.. Ba abin Ta tambaya ba bama zata iya ba.. Idan ta zauna haka zatai ta kallon lambar wayarsa tana tinani.. Wasu lokutan ta kwab’i kanta tace k’ila ma ya mance da ita.. K’ila ma ya d’auki d’aya matarsa sunyi tafiyar.. Wannan tunanin shi yafi d’aga mata hankali.. Kardai ya d’auki d’aya matar tasa sun tafi ne tinda yace bazai kuma tilasta mata komai ba.. Maganganun Aunty Larai suka shiga zuwa mata cewa namiji baya son taurin Kai da kafiyar masifa da kuma musu, wad’ann abin sosai suke rage darajan mace wajen mijinta.. Sannan Ta bawa mijinta dama ya zamto babban abokinta kuma abokin shawarinta.. Yanzu ita da Mr Inspector Wai har zasu zamto manyan abokai irin yanda Aunty Larai ke fad’i..? Ta kuma duban fuskarta a madubi kafin zancen Aunty Larai ya kuma zuwa mata cewa Great Mission d’inta shine rayuwar aure dake gabanta, dan aure ibadah ne kuma bautan Ubangiji ne. Duk abinda Ta gani cikin gidan aure ibadah take.. Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali kafin ta isa ta kwanta hoton fuskar mijinta cikin idanunta.

A ranan da yammaci Aunty Larai tazo da mai lalle Ta zana mata bak’i da ja hannu da k’afa.. Sosai k’unshi yai kyau ya amshi fatarta musamman da shike fatar tata ta d’auki gyara sosai.

Idan ka ganta kaman wata sabuwar Amarya ga wani k’amshi na musamman da take duk yanda Ta gifta..

Habeeb ya dubeta yace “Aunty Sadiya kunyi kyau sosai kaman ana bikinki..”

Gaba d’aya suka d’an dara Habeeb na kuma cikasu da sururtu. Kafin dare mai kitso tazo tai mata dan harta wanke kai da drying saida Aunty Larai tai mata.

Safiyar Washe gari litinin Aunty Larai ta sanyata ta shirya tsaf cikin wani embroidery atampa mai kyaun gaske ruwan cikin k’wai wanda ya tafi da kalan jikinta, d’inkin riga da skirt ne da ya masifan mata kyau cikin kayyakin da su Aunty Larai suka d’inka mata a nan cikin foundation d’in. Dama tin kwanakin baya Aunty Larai ta d’au measurement d’inta ashe Mu’azzam ne ya bama Aunty Larai tai mata d’inkuna masu kyau na zamani.. Sai gani kawai tai Aunty Larai dasu Farida ‘yanmata masu koyar da sana’ar d’inki a foundation d’in suna shigo da kayayyaki kama daga laces zuwa atmapopi hardai irinsu Dubai materials d’in nan.
Chapter 86 · 0% Book details