← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 175

Sashe 104

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Tasha poison ne Wai zata kashe kanta shine Mommy ta tsinceta a d’aki tana aman kumfa.” Cewar Kiki.

Yai shiru yana jinjina maganar kafin yace “Wani asibiti take.?”

Meema Ta fad’a masa asibitin.

JInjina kansa yai kafin ya basu hanya suka shige.

Kai tsaye shima hanyar asibitin ya d’auka.

Tare tare suka iso asibitin dasu Meema. Daidai lokacin motar Daddy ma ta shigo asibitin.

A fujajan Daddy ya nufi cikin asibitin bayan su Kiki sun Shige, hankulansu duk a tashe.

A natse ya fito daga nasa motar ya nufi cikin asibitin yanda ya hangosu carko carko k’ofar Emergency.

Mommy tana hangosa ta nufosa tana fad’in uban mai ya kawosa bayan shine silan shiga tashin hankalin da d’iyarta ke ciki. Ta rufe idanu ko tunanin asibiti ne batayi Ta yanda take shiga bata nan take fita ba saidai Mu’azzam ya fice daga asibitin.

Da k’yar Mommy ta daina borin da take saida Daddy ya kusan fice mata a giya.

Mommy na hawaye take duban Mu’azzam lokaci guda take dubansa tana fad’in “Idan na rasa Safeenah bazan tab’a yafe maka ba..” Tana kuka take ci gaba da fad’in “Bayan duk abinda nai ma mahaifiyarka a rayuwa abinda zaka saka min dashi kenan Mu’azzam.. I spent half of my marriage life ina d’awaniya da jinyar mahaifiyarka.. Wllhi nayi imani da Allah idan na rasa Safeenah bazan tab’a yafe maka ba..” Ta k’arashe cikin kuka.

Daidai lokacin Dr ya k’araso yana fad’in Safeenah tayi regaining consciousness..

Gaba d’aya suka bi bayan Likitan idan ka d’auke Kiki da Meema wanda dama basa tsaye wajen.

Suna K’arasowa k’ofa Mommy tace atafau Mu’azzam bazai shiga ba. Bai forcing ba, ya dubi Daddy yaima Safeenah fatan samun lafiya kafin ya fice daga asibitin.

Suna shiga cikin d’akin da kuka Safeenah Ta fara masu tana ambato her Halal.

Mommy takaici kaman ta shak’o Safeenah dake saman gado tana kuka tana fad’in Ina her Halal yake.

Daddy ya k’arasa ya rungume kan Safeenah dake zaune saman gado cikin jikinsa. Lallashinta ya dinga yana k’ok’arin calming nata kafin ya zauna gefenta.

Cikin kuka Safeenah ke ci gaba da fad’in “Daddy I love him.. I can’t live without my Halal..”

Mommy dake gefe tsawa ta darara mata da fad’in “Kika sake ambato wani my Halal a nan sai na halarta ma tafin hanuna fuskarki.. Sai na shata miki mari Safeenah. Shashasha kawai wacce bata San yanda ke mata ciwo ba.”

Safeenah Ta kuma fashewa da kuka yayinda Daddy ya aikawa Mommy mugun kallo “Fita ki bamu waje Hajara.” Ya fad’I yana duban Mommyn.

Cika kurum Mommy take tana fuci kafin tai k’wafa tasa kai fuu ta fice.

A k’ofa Ta had’u da Dr rik’eda file d’in Safeenar.. Ta dubesa tace “Yaya..?”

Likita yace “Report d’in Safeenah ne..”

Mommy Ta nuna masa hanya tace “Muje ka sanar dani ni ce nan mahaifiyarta.”

Dr ya d’an dubeta sai yace “Mijinta fah.?”

Mommy tace “Sun rabu basa tare. Zaka iya sanar dani komai..”

Ya d’an jinjina kansa kad’an kafin ya nuna mata hanya yana fad’in “After you.”

Mommy tasa kai Dr ya take mata baya.

A cikin d’aki kaw yanda Safeenah ke kwance Daddy yaci gaba da mata nasiha da fad’in “What were you thinking Safeenah.. Shin Kinsan matsayin wanda duk ya kashe kansa a addini.. Kafuri fah ya mutu Safeenah.. Shij kinaso ki mutu kafura..? Mai zai sa ki hallak’a kanki kan soyayya. Kwanakin baya kin tasamma halak’a matar Mu’azzam yanzu kuma kina yunk’urin halak’a kanki.. Kan wani dalili Safeenah..!”

Cikin kuka take fad’in “Daddy tambayata kake kan wani dalili bayan kasan dalilin son Mu’azzam ne.. Ni dai Daddy gwara na mutu kan na rasasa..”

Daddy ya girgiza kai yace “Mu’azzam doesn’t love you Safeenah. Learn to accept this.”

Safeenah Ta kuma girgiza kai tana hawaye “My Halal loves me Daddy.. He loves me.. I know he does.. Kawai dai wancan muguwar ce ta rabamu.. Daddy you need to help me please.. Dan Allah ka masa magana Daddy.. Yana jin maganar ka.. Dan Allah Daddy kace ya maidani..” Ta k’arashe tana mai kuma fashewa da kuka.

Daddy ya lumshe idanunsa a hankali yana mai tura hularsa baya kad’an. Harga Allah ya soma gajiya da halin Safeenah akan Mu’azzam. Ya kula tana ma Mu’azzam son da bazata iya yakicesa cikin zuciyarta ba. Daga wnn sai wancan.

A can office d’in Dr kuwa da tsananin mamaki Mommy ke dubansa, ta d’an girgiza kai tace “Kace she’s 4 weeks pregnant.?”

Dr ya jinjina kai yace “Gwaji ne na jini wanda ko cikin Kwana guda ne jikinta zai nuna.

Mommy tai shiru tana jinjina kai tana tuna tarewar Safeenah gidan Mu’azzam wata guda kenan harda kwanaki. Muryar Dr ta sinkayo yana ci gaba da fad’in “Luckily cikin bai fice ba amma yana iya zuwa da tangard’a sai a kula da ita sosai kar irin abinda ya faru da ita yanzu ya kuma faruwa.. Dan komai ka iya faruwa.”

Mommy Jiki babu kuzari ta jinjina kai tace “Za’a kula da ita Dr. Kuma haka bazai sake faruwa ba.. Amma Likita inaso maganar nan ya tsaya tsakaninmu kar kowa yaji harda ita Safeenar duba da yanayin halinda take ciki.. Nafi so na sanar da Ita a naste.”

Dr ya jinjina kai yace babu komai dik yanda tace. Lokaci guda ya mik’awa Mommy result d’in. Ta cukukuye ta tura cikin jaka kafin ta fice daga Office d’in tana sakin huci tana muzurai.

Cikin zuciyarta take fad’in “Lokacin ramuwa yayi Mu’azzam zaka d’and’ani k’unci wanda baka d’and’ana a baya ba. Idan sunana Hajara sai na sauk’e maka wann d’anyen kan naka.. Sai na nuna maka kai k’aramin maras kunya ne.” Ta kuma yin k’wafa kafin tasa kai ta shige.

**

A can Fufore kuwa tun bayan tafiyar Mu’azzam Ta dawo d’akin Mamy da kwana. Tare tare suke gudanar da komai itada Mama Hindu da Ajidde..

Yau ma ruwan addu’a data kawo Malama ta bata zamzam ce tace ta Bawa makusancinta ya karanta mata ayatul Shifaa a ciki a bata Ta sha.. Saidai babu Mu’azzam wanda yake d’anta sann babu Daddy da yake mijinta. Sadiya ta amsa tace zata karanta mata Ta bata tasha tinda damuwar shine a karanto ayoyin da yak’inin Allah ya bata lafiya.

Nan kuwa ta karanto ta tofa mata ta bata tasha saura ta shafe mata a fuskarta.

A ranar da dare suna kwance suna bacci taji kaman gadon Aunty Nuratu na motsi. Ta mik’e a hankali daga saman katifar da take kwance.. Kaman wasa motsin na kuma yawa matar da ko hannunta bata iya motsawa.

Sadiya ta mik’e tana karanto addu’o’i saman harshenta. Nan ta hangi kaman Mamy d’in ce ta mik’e zaune. Zuciyarta yai wani irin yankewa.. Ta soma lalumar haske zata kunna wutar d’akin.. Tana kunna wutan sai kuma taga tana nan kwance harta abun rufauwarta na nan kaman bata motsa ba. Tai k’ok’ari tai k’arfin hali ta matso kusanta ta karanto mata amanarrasulu da ayatul kursiy da kuma k’ul’au’zai.. Ta tofa mata kafin tai zaune gefenta tana dubanta dan gaba d’aya ji tai baccin ya tafi daga idanunta..

Washe gari da safe haka ta dinga mamakin abinda ya faru daren jiya wanda kaman mafarki ne tai haka take gani. Koda Ajidde tazo Sadiya ta sanar da ita abinda ya faru amma tafi tunanin watak’ila mafarki ne tai.

Ajidde ta jinjina kai tace “Ince baki sanar da kowa ba..?”

Sadiya ta gyad’a mata kai alamun eh.

Jinjina kai Ajidde tai tace “Yauwa Malama tace idan anga wani canji kar ayi Saurin fad’a wa mutane.. Yanzu yau in sha Allah zan sanar da ita abinda kika fad’a mun.. Allah yasa a dace matar nan ta sami lafiya.. Al’amarinta akwai ban tausayi.”

Sadiya ta karkato tana duban Aunty Nuratu. Sai kuma ta furta Ameen a hankali. Ta maidoda dubanta ga Ajidde dake saka tsakin habbaussauda cikin gaushi tace “Idan ana buk’atar wani abu ki fad’a mun kinji.. Ajidde ta murmusa tace “Kar ki damu zan sanar dake in sha Allah..”

Sadiya ta sakar mata murmushi tace “Barin duba Inne..”

Jinjina mata kai Ajidde tai tace “A dawo lafiya.”

Suka sakar ma juna murmushi kafin Sadiyar ta fice.
**

Bugu biyu a na uku Shemau ta d’aga dan Safeenah ce mai kiranta.

“Ina jnki Safeenah tin shekaran jiya nake neman layin ki.. Sai yau kika samu sararin kiran wayata.”

Safeenah Ta fuzar da fuci kad’an tana duban hannunta da aka saka mata drip tace “Aunty banida lafiya ne.. Ko Kinsan Jiya a asibiti na yini Ina shan drip..”

Aunty Shemau Ta zaro idanu tace “Mai ya faru..?”

Safeenah tace “Mommy bata baki labarin abinda Mu’azzam ya mun ba..? Aunty na tsani matar Mu’azzam zanyi komai Dan Ta fice daga rayuwarsa.”

Shemau ta jinjina kai tace “Wann sadaka yallar ai ba banza ta bar Mu’azzam ba.. Zan taimaka miki Safeenah.. Zata fice daga rayuwar Mu’azzam na miki alk’awari..”

Musaddiq yai tsaye Cak yana sauraron wayar Aunty Shemau da Safeenah.

SameenaAleeyou📚

*GIDAN ARO*

*52*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Shemau Ta numfasa tace “Kina jina, naji Inne na maganan za’a turo Driver ya d’auketa, kuma naji tana magana da Mama Hindu ko za’a sama mata yarinya ‘yar tayin zaman Mota cikin ‘yanuwa. Nasan duk tsiya cikin satin nan za’a turo direban..”

Safeenah ta katseta da fad’in “Aunty ai bazamu bari ta dawo ba.. Ni kawai ki taimakeni kar ta dawo Gidana Dan girman Allah Aunty Shema.. Ayi mai yuwa kar Ta kuma tako mun k’afa cikin gida Ta fita da fitar Ta kenan..” Ta k’arashe tana fito da idanu waje kai kace Shemaun na dubanta.

Shemau tai shiru tana nazari Ta tuna exactly abinda Mommy Ta fad’i mata kenan lokacin da za’a kawo Aunty Nuratu jinya cewa Ta fice kenan daga gidanta fita ta har abada. Ta nusa kad’an tace “Yanzu meye abinyi Safeenah..? Mai kike so ayi Kinsan dai tafiya ya zama dole babu fashi tinda har Inne ta amince da hakan..”

“Ni kawai kiyi duk abinda zakiyi dan kar ta dawo..”

Da Mamaki Shemau tace “Toh kasheta kike so ayi..?”
Chapter 104 · 0% Book details