← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 165 OF 175

Sashe 165

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Umma sai dubanta take tana murmushi tana tuno lokacin da suke yara yanda Aunty Nuratun Ke kula da Ita kaman dai yanda yanzu take kula da Kiki. Umma Ta bud’e murya tace “Baki canza ba Yaya.. Har yanzu Kina nan da zuciyarki mai kyau, Kina saka Farin cikin kowa a sama da Naki.. Sai na tuna a lokutan baya yanda kikaita d’awainiya dani.. Tin mahaifan mu suna da rai Kina kula dani sann ko bayan da basu nan baki fasa duk abinda kikeyi ba sai ma k’arawa da kikai.. Mu’azzam takes after you.. Bayan babu Ibrahim shi yaci gaba da kula damu..”

Aunty Nuratu ta k’araso tana murmushi kafin ta kamo hannayen ‘Yaruwar nata cikin nata “Haka ya kamata mu kula da junanmu, wann shine cikan zumunci..” Ta d’anyi fasali kafin taci gaba da fad’in “Shin Kinsan Sadiya ta kula dani a lokacin da nake kwance a can Fufore.. Bansan dalili ba amma inajin nastuwa had’ida k’wanciyan hankali tattare da ita na d’an lokacin da mukai tare.. Ashe kusancinki ne nakeji a tareda ita.. Babu wanda ya kaini farin ciki da d’iyar ‘Yaruwata kuma mai sunana Ta zamto matar Mu’azzam.. Allah ya albarkacesu da Zuri’a d’ayyiba wanda mu dasu da al’umma baki d’aya zasu amfana dasu.”

Umma ta kuma murmusawa kafin tace “Ameen Yaya..” Ta gyara mayafinta tana k’ok’arin mik’ewa.

“Wai da gaske tafiya zakiyi Aysha.. Shin bazaki zauna a nan ba.. Su Asheer da Habeeb sai a kawo su nan duk ku zauna a nan gaba d’aya.”

Umma ta murmusa kad’an tace “Bari dai al’amara su gama daidaita Yaya.. Da sannu zakiga Habeeb da Asheer, nima ba don naso zan tafi na barki ba..” Ta d’anyi fasali kafin taci gaba da fad’in “Kinga ga yanda yanayin gidan yake ciki komai a rikice.. Abubuwa suna kan faruwa, ya kamata mu baku sarari har Allah ya daidaita al’amran ahalin..”

Aunty Nuratu ta murmusa kad’an kafin tace “Haka ne, kuma kawo Asheer da Habeeb a wann hatsaniyar da ake ciki bazai ma yaran dad’i ba duba da yanayin da ake ciki a gidan, ko Ina jami’an tsaro ga Hajara bamusan makomarta ba har yanzu dan babu alamun nadama tattareda ita. Allah dai ya iyar mana ya kawo mana k’arshen tashin hankalin nan.”

Umma Ta amsa da Ameen Yaya. Daidai nan Aunty Larai tai sallama a k’ofa.. Mamy ta bata izinin shigowa.. Nan take sanar dasu Adnan na jiransu.

Umma ta dubeta tace “Sadiya fah.?”

“Bacci take can b’angaren Inne.. Inne tace a barta kar a tada ita.”

Umma ta girgiza kai kad’an tace “Oh shikenan tanata yawo tsakani, daga gidanta ta tafi can yanzu kuma ta taho nan..”

Aunty Nuratu ta katseta da fad’in “Nan da can da gidan nata duk d’aya ne.. A k’yalemun d’iyata dan dama ko zarafin gaisuwa bamu samu ba balle muyi hiran yaushe rabo.. Kudai kuje abinku ku bar mana ita a nan..”

Umma ta d’an girgiza kai kad’an tana furta “Shikenan Dama d’iyarki ce kunfi kusa.” Suka d’an murmusa gaba d’aya kafin suka nufo waje suna kuma sallama da juna kaman kar Su rabu.
**

Tsaye yai k’ofan store d’in da Mommy Ke kulle yana sauraron surutanta.

“Dan Allah kuyi hak’uri.. Wayyo hannu na.. Wayyo Kaina..! Wayyo bayana.. Kar ku tab’ani.. Wayyo.!” Ta kuma sakin wani ihun.

Mu’azzam yana bud’e k’ofar ya hango Mommy tsugune tana rok’on a k’yaleta. Amma da shike gogaggiya ce tana ganinsa sai ta d’auke kai gefe tana sakin huci.

“Fito” ya Fad’i daga nan yanda yake tsaye.

“Mahaukaciya ce ni da zan fito ka sunkuceni ka tafi dani ofishinku.. Tsaf nasan a Rashin mutuncinka zaka aika Mu’azzam.”

Jinjina kansa yai kad’an kafin ya soma k’ok’arin janyo k’ofar.. Da sauri ta rik’e k’ofar ta fito tana fad’in “Nuratu ce tamin turen makarai dan su hanani zaman Gidan nan.. Kuma wllhi bazan fice daga gidan nan ba.. Zama daram babu uban da ya isa ya fitar dani.. Yo ko Marwan wllhi bai isa ya fiddani ba balle Nuratu.”

“Idan basu fitar dake ba dama ni zan fitar dake.” Ya bata amsa daga nan yanda yake tsaye.

Ta murmusa kad’an tana dubansa tsegege “Zaka fitar damu dai.. Dan kana kamani zaka kama kakarka.. Yo ai itace mai laifi.. Nikam burin Marwan da Nuratu na cika zasu samu daman kasancewa k’ark’ashin inuwa guda bayan amanarsu da mahaifinka yaci.. Mai za’ai da ahali irin wann wanda banda ‘yantadda da maciya amana babu komai cikinsu.. Kakarka criminal Babanka betrayal wanda yaci amana D’anuwansa.!”

“Ya isheki.. Ya isheki haka..!” Ya dakatar da ita cikin tsnanin fuci. Lokaci guda yaci gaba da nunata da ‘yar yatsa “Don’t you dare mention my Dad..! Kar ki sake.!”

Mommy ta rakasa da harara yanda yasa kai ya fice cikin sauri. Dogon tsuka taja kafin ta nufi saman Daddy tana fad’in “Na rantse da Allah Marwan baka isa kaci amanata da Nuratu ba.. Ina nan na kasa na tsare.. D’akinka ma zan shige na jira shigowarku ayi komai akan idona. Maciya amanan banza.!” Ta k’arashe tana mai tura k’ofar d’akin Daddy.
*

Mu’azzam na ficewa ya k’arasa saman kujerun shak’atawa dake a haraban gidan, yai zaune yana tunanin maganganun Mommy, Babansa maci amana ne yaci amanan D’anuwansa.. Ya saka tafukan hannayensa duka biyu yana mai shafe fuskarsa dasu. Daddy shine asalin masoyin mahaifiyarsa amma sai Dad d’insa ya aureta.. Shin da gaske Dad d’insa maci amana ne..?

Bai kaiga samo amsar ba yaji hannun mutum saman kafad’arsa.

D’agowa yai yana duban Daddy dake tsaye saman kansa. Bai iya furta komai ba Sai sadda kansa k’asa da yai.

Daddy ya zauna gefensa kad’an yana mai d’aga kai sama had’ida duban hasken Farin wata da ya fito tarau. Suka b’ata lokaci a haka kafin Daddy ya soma fad’in “Shin kasan ko wani namiji ana halittan matansa ne daga ribs d’insa.?”

Mu’azzam ya d’ago ya dubi Daddy da mamaki dan gani yake kaman Daddy ya fahimci tunanin mai yake.

Daddy ya jinjina kai kafin yaci gaba da fad’in “Wani zaka samu an d’ibi halittan mata da dama daga ribs d’insa kuma duk Sai ya auri wad’ann Matan.. Kaman yanda itama wata macen zaka samu an d’ibi halittarta daga hak’ark’arin maza da dama kuma duk sai ta auri wad’ann mazan sabida ita d’in matarsu ce..” Ya d’anyi fasali kafin yaci gaba da fad’in “Naji abinda Hajara ta Fad’a maka.. Amma inaso ka sani mahaifinka was never a betrayal.. Baici amanata ba.. Allah ya hukunta sai ya auri Nuratu, ya kuma sanya rabo a tsakaninsu.. A rubuce ne dole Sai sunyi aure kuma dole Sai an haifeku.. Watak’ila da Allah bai k’addari zata aureni ba Sai kaga na iya mutuwa dan kawai Ta auri D’anuwana sabida rabo dake tsakaninsu.. Amma haka Allah ya hukunta.. Ya riga da ya k’addari akwai aure tsakaninmu gaba d’aya.. Babu wanda ya isa ya canza wann abu da Allah ya riga ya hukunta tuntuni.. A lokacin da muka rasa mahaifinka ban tab’a kawowa rashin mahaifinka zaisa na auri mahaifiyarka ba, amma yanda zaka gane bamu Ke gudanar da al’amaranmu ba bayan da mahaifinka ya rasu sai Inne ta had’a aurenmu da mahaifiyarka alhali Inne bata san farkon labarin ba sabida mahaifiyarka batada kowa sai mu...Wann zai nuna maka Allah shi Ke gudanar da Al’amranmu ba mu ba. Sann ya hukunta faruwar hakan tuntuni.. Kar ka bari maganganun Hajara suyi tasiri a cikin zuciyarka.. Your Dad was a good person.. Sadaukarwan da zan mishi shima zai iya min irinshi koma fiye dashi.. That’s how much we loved each other ni da D’anuwana..”

Ya murmusa kad’an yana duban Daddy kafin yace “Yau ake karanta mana hadisin nan da yake cewa imanin d’ayanku baya cika sai yaso ma D’anuwansa abinda yaso ma kansa.. Tabbas ka hak’ura ka bar ma D’anuwanka abinda kaso ma kanka.. Kayi sadaukarwa mai girma Daddy wanda ba kowa ne zai iya yi ba.. Ka cika D’anuwa na gari da kowa zai alfahari da irinka.”

D’an kifa kansa yai kad’an ba tareda yace komai ba, nan suka ga ana bud’e gate, Adnan ne ya dawo daga kai su Umma. Ya ida parking Aunty Larai ta bud’e ta fito, dan dole ta biyo Adnan suka dawo sabida Sadiya ta taho babu kaya babu komai Ta d’an d’ebo mata wasu kayayyakin.

Ta k’araso suka gaisa dasu Daddy da Mu’azzam kafin ta nufi b’angaren Inne.
Mu’azzam sai dubanta yake yana addu’an Allah yasa Sadiya bata tafi ba cikin zuciyarsa.

Daddy ya mik’e yana fad’in zai shiga wajen Uncle Salman zasu tattauna gameda yanda zasu tunk’are Inne dan tun bayan abinda ya faru basu fuskanci Mahaifiyar tasu ba. Mu’azzam ya jinjina masa kai yana fad’in “A fito lafiya Daddy.”

Gyara zamansa ya kumayi yana duban tapka tapkan k’wan wuta da k’anan k’wari keta shawaginsu jikin k’wan wutan. Kai da ganin kasan k’warin nan basuda wata matsala, ya murmusa kad’an yana mai jin dad’in kallon k’warin.
**

Sadiya da bata jima da farkawa a bacci ba zaune sukai parlor itada Ajidde tana sauraron shiriritar Ajidde dake d’ibe mata kewa. Rabin labarin tafiyarsu ya shafa da abubuwan da suka gani a hanya dan dai itakam bata tab’a tafiya haka ba. Mama Hindu na gefe tana gyangyad’i, saidai idan Ajidde tayi wani abin dariyar Ta dara kad’an.

A haka Aunty Larai ta taddasu. Sadiya ta turo baki tak’i kulata, Ita a dole fushi take Sun tafi sun barta itada Umma.

Ko takanta Aunty Larai batabi ba saima gaisawa da take dasu Mama Hindu da Ajidde. Kaman wad’anda suke jira kaw suka mik’e suka nufi kwanciya, dan Ajidden ma ta fara hamma alamun bacci gajiyan hanya bai ida sakinsu ba.

Har lokacin Sadiya bata daina ture turen baki ba.

Aunty Larai ta tab’e baki kad’an tace “Kinyi dai ki gama.. Gashi can yana zaune shi kad’ai waje k’wari na tayasa hira shi zakije ki tura ma wann bakin ba ni ba.” Aiko bata kai aya ba wayarta ya soma ruri.

“Da alama yaji zancen namu, gashi nan yana kira.” Aunty Larai tace tana mai d’aga wayar.

Sadiya tai kaman nata a wajen Dikda taji zancen nasu akanta ne.

“Gata nan ta tashi a baccin ma.. Aaah kar fah ka damu, mukam ai ‘yan Abuja style ne.. Gata nan tafe.”
Chapter 165 · 0% Book details