Sashe 1
Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*GIDAN ARO*
*01*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
_Abuja, Nigeria_
National Police Headquarters.
_Criminal Investigation Department (CID)_
Cikin k’warewa da sanin makamar aikinta budurwar mai kimanin shekaru 29 taci gaba da kwararo bayanai tana mai nuni da Farin allo wanda hasken k’wan wutan projector ya haskesa, Ko ba’a fad’a maka ba zaka fahimci cewa cikin d’akin gudanar da binciken manya manyan laifuka suke musamman irin laifin da ya shafi kisan kai, fyad’e, Garkuwa da mutane da sauransu..
Hoton wani matashi ne na’urar Ta hasko, kwance yake a k’asa tamkar bai numfashi, ga dukkan alamu babu rai tattareda shi.. Ko ina na wajen a kewaye ne da Doguwar igiya mai launin ruwan d’orawa, jikin igiyan an rubuta _Restricted Area_ da manyan bak’ak’e...
Budurwar ta k’urama hoton idanu Wanda ya bayyana Babba gabansu kasancewar da na’uarar projector ake hasko hoton.. Ta matso sosai tana mai rage girman idanunta tana kallon hoton, a hankali take furta “Da hannun hagu ya rik’e bindigar, direction d’in da bindigar Ta kalla bai kamata harsashi ya samu k’irjinsa direct ba, ya kamata harsashin ya huda ribs d’insa kafin ya ratsa cikin k’irjinsa indai har da hannun da aka sami bindigar a ciki yayi harbin..”
Wani matashi mai kimanin shekaru 32 ya taso yana k’arasowa kusanta wanda shima d’aya ne daga cikin ‘yansanda masu gudanar da bincike da suke zaune a madaidaicin Zauren gudanar da binciken.. Hannayensa sakale cikin aljihun wandonsa, idanunsa naga hoton yake furta “Well done Agent Maleeka.. But wani hanzari ba gudu ba.. Baki tunanin idan mutumin nan ya kasance bahago zai iya karkata hannunsa har harsashin ta iso daidai tsakiyar k’irjinsa ta hudasa..?”
Karkatowa Maleeka tai tana duban wanda Yai maganar kafin ta d’an tab’e baki tace “Bani da tabbaci Inspector Assad.. Amma hakan nake tunani..”
Bata Kai aya ba wata murya ta katsesu da fad’in “Oh shut up.!”
Gaba d’aya suka juyo suna dubansa, kusan tun shigowarsu d’akin kansa a k’asa yana aikin murza zoben dake mak’ale yatsarsa guda wanda yin hakan kusan d’abi’arsa ce musamman idan yana nazarin bincike..
Ya d’ago kai yana dubansu, kallon da yake sanyata daburcewa ta rasa mai take ciki, tunaninta duk su sakwarkwace shi ya jefata dashi kafin yace “Tunani kikeyi.? Ko kuwa kin tabbatar..?”
Kasa furta komai tai sai yin k’asa da idanunta da tai
Hannayensa biyu sakale cikin aljihun wandon jeans d’insa, yana tsaye gabanta yana iya hango tsakiyan kanta sabida ratan tsawo dake tsakaninsu.. Cikin muryarsa da yake tsakanin kashe mata jiki lak’was wanda yake sanyata losing kanta gaba d’aya ya soma furta “We are investigating a murder here, in case you forgot.. There’s nothing like you thought, everything here must be known.. You must Know.. I want results and not assumptions.. Kin fahimta..” Ya k’arashe yana kwanto da fuskarsa kusan nata, idanunsa da suke matuk’ar furgitata dab kusan nata...
A hankali take jinjina kai cikin yanayi na d’an daburcewa “I..I’m sorry Inspector, Sir..”
“I don’t need your apology.. Just do your work correctly.. Or else, you’ll be kicked out of this team..!”
Yanda yake maganar cikin tsananin zafin rai zaka fahimci ransa a matuk’ar b’ace yake..
Mutumin dake tsaye gefen Maleeka ya d’an girgiza kai kad’an kafin yace “But..”
Katsesa yai da fad’in “What do you mean but.?.. You know me quite well Assad, you know I hate incompetence.. And I easily get irritated by people like her around.”
Assad ya d’an shafi kansa dan yasan Wanene abokin nasa da kuma yanayin da yake ciki “MU’AZZAM.. will you please calm down.. I was only asking you to go easy on her..”
“Oh really..! Da gaske Assad.. Am I really being too strict?.. Let me remind you idan ka mance.. Mutuwar k’anwata muke bincike a nan Assad.. K’anwata was found dead tareda wannan d’an ta’addan.. And you’re asking me to go easy on her... My sister Assad.. My only Sister.. An kasheta in a cold blooded murder.. Someone murdered her Assad.. Sannan na kasa aiwatar da komai domin wad’anda suka kasheta su biya abinda suka aikata.. Tell me, a haka ne kake ce min na natsu.. A haka ne kake ce min I should calm down and go easy on her Assad.!” Ya k’arashe cikin tsananin d’aga murya gashin jikinsa na kuma mimmik’ewa
D’akin yai shiru sai hucin fitar numfashin Mu’azzam kakeji.. Cikin rarrabewar kalma yake ci gaba da furta “If she’s not competent enough to work with this team, the door is widely open..”
Cikin zafin nama Assad ya katse sa da fad’in “But the man who killed your sister is dead too.. He committed suicide after he killed your sister Mu’azzam..!”
Ya k’arasa jikin k’aton allon ya shiga nunawa yana fad’in “Look.. Look here, look at the suspect, ya kashe kanshi bayan ya kasheta.. Bindiga d’aya yayi amfani dashi.. Ga finger prints d’insa a jikin bindigar an samu.. Duk iyaka binciken da za’ayi anyi Mu’azzam but still babu wani abinda yake canzawa.. Until now we couldn’t figure anything out sabida bamuda wani dalili Ko hujja...Amsa d’aya muke samu a k’arshe shine mutumin nan kashe kansa yayi bayan ya kashe Ikram.. Sannan inaga ya kamata mu saki mutumin nan dake tsare cikin interrogation, babu amfanin detaining d’insa a nan..”
Wani irin duba yake ma Assad da idanunsa da suka gama rinewa zuwa ja, lokaci guda yake jinjina kai kafin ya mik’a hannu saman Table dake gefensa ya d’auko k’aramar bindiga piston.. Cikin tsananin huci yake furta “I’ll proof to y’all that that man didn’t kill himself.. Someone killed him..” Yai maganar yana pointing Assad da bindigar zuciyarsa na kuma tafarfasa..
Maleeka kame baki tai idanu a warwaje take duban Assad da Mu’azzam..
“Sir.. What are you doing.. Please don’t..” Maleeka tai maganar cikeda tsoro..
Ko kallo bata ishi Mu’azzam ba balle ya amsata.. Pointing bindigar yai daidai saitin k’irjin Assad, yana kallonsa yana huci kaman mai shirin d’ana harsashi..
Lokaci guda ya karkato da bindigar saitin ya juyo da Ita saitin nasa k’irjin, bindigar tana rik’e ne cikin left hand d’insa kasancewarsa left handed, shid’in bahago ne.. Bai daina sakin huci ba yana rik’e da bindigar idanunsa tar akan fuskar Assad.
Maleeka Ta kuma zaro idanu waje ganin Mu’azzam yayi pointing kansa da bindiga, cikin tsananin daburcewa take girgiza kai tana k’ok’arin rintse idanunta, dan gani take kaman d’ana ma kansa harsashi yake da niyya
D’aya mutumin dake zaune saman kujeransa wanda shine cikon na hud’unsu a cikin d’akin wanda ya d’an fisu gaba d’aya a haife dan shi zai kusan shekaru 39 sai sannan ya taso ya k’araso yanda suke a tsartsaye..
Ya isa jikin board d’in yana nuna hannun mutumin yanda ya rik’e bindigar ya d’ana ma kansa harshashi cikin hoton, kafin ya kaikaito yana duban Mu’azzam dake rik’e da bindiga yayi pointing kansa daidai yanda wannan mutumin yayi.. A hankali ya saki murmushi yana ma jinjina kafin tunani da jajircewa a aiki irin na Mu’azzam.. Rik’e bindigar da yayi so yake ya masu proving cewa mutumin nan baiyi committing suicide ba kaman yanda ya bayyana masu cikin hoton.. Wani ne ya kashesa sannan ya saka bindigar cikin hannunsa dan idan ba haka ba babu yanda za’ayi ya harbi kansa a wannan position d’in...
Tafe hannunsa mutumin ya shigayi yana furta “Impressive.. Bravo Officer MA Gamji..” Yai maganar yana mai tafe hannayensa lokaci guda yake duban Mu’azzam..
Assad ya kai dubansa ga hoton yana yanda mutumin ya rik’e bindigar sannan yakai dubansa ga Mu’azzam, ko shakka babu wannan rik’on bindigar saka masa akayi sannan ya tabbata bashi ya harbi kansa ba..
Jinina Kai Assad yai murmushi saman fuskarsa yake duban aminin nasa.. Lokaci guda ya k’araso gabansa kafin ya d’aga hannu yana sara masa alamun jinjina.
Officer Maleeka ma wani irin murmushi ne taji ya kufce mata cikeda jin dad’i dan har Ta fara tunanin idan basu samu komai out of this case ba watsi za’ayi da binciken and bazata samu lokacin da take so Ta samu dan Ta kasance da Mu’azzam ba.. Sabida son kasancewa taredashi ne yasa tayi yanda tayi akayi assigning nata to case d’in...
A hankali mutumin ya zare bindigar daga hannun Mu’azzam yana mai furta “Weldon Mu’azzam har na fara tunanin idan bamu samu komai ba anything can happen.. Za’a iya rufe case d’in...”
Sai sannan Mu’azzam ya dubesa ya sara masa kafin yace “Believe me Yusuf babu wanda ya isa ya rufe case d’in nan until I get to the bottom of everything.. Is a promise, Alk’awari ne da na d’aukarwa mahaifiyata dake cikin tsananin jinya wacce batasan d’iyarta Ta mutu ba.. Wacce duk randa ta farka daga wannan jinya nata zata farka ne ta tadda babu d’iyarta.. Babu Ikram..” Ya k’arashe wane irin gumi na karyo masa tin daga cikin sumarsa har zuwa karan hancinsa da ya dace da kyakkyawan fuskarsa...
Lokaci guda yaci gaba da furta “Yanzu da duk muka fahimci abu guda nida ku.. I’m goin to make that imbecile talk..!” Daga haka cikin sauri ya juya ya fice daga cikin d’akin..
Assad yabi bayansa yana kiran sunansa inaa Ko zarafin tsayawa bai samu ba balle ya amsa sa..
Yana isowa ya bud’e k’ofan interrogation d’in ya shige ciki saidai yana shigewa ya maida k’ofar ya danna mata lock yanda Assad Bazai iya shigowa ba...
Girgiza kai kurum Assad yayi dan yasan waye abokin nasa idan ransa ya b’aci..
Wani mutumi ne zaune saman kujera nan cikin interrogation d’in, Mu’azzam ya d’ibi lokaci yana dubansa cikin tsananin tsimewa..
Murmushi ne saman fuskar mutumin, yana murmushin yana shafa hab’arsa, cikin muryarsa da yafi kama da ta ‘yantadda yake furta “Officer MA Gamji, you’re not going to get anything from me.. zaifi kyau idan ka sakeni nayi tafiyata dan idan ba haka ba zan iya shigar da k’ara an ajiyeni a police station babu dalili..”
Cikin takunsa irinta cikakkun mazaje da suka sha training suka k’oshi ya soma takowa, hannayensa dafe da belt d’in wandonsa.. Saida ya k’araso har gaban mutumin kafin ya zauna a kujera mai fuskantar mutumin.. Zoben dake hannunsa ya cire ya wainata saman table d’in da ya raba tsakaninsu da mutumin, saida yayi hakan kusan sau uku k’afarsa d’aya bisa d’aya kaman bazai ce komai ba, har lokacin idanunsa naga zobensa da yake faman wainata saman table..