← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 153 OF 175

Sashe 153

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mommy ta k’arashe tana mai cire d’ankwalinta tai jifa dashi.. Ta shiga tsalle tana ihu mai firgitarwa.. Lokaci guda kuma Ta zube a wajen tana kame k’irjinta tana fad’in “Wayyo na shiga uku k’irjina..! Wayyo mutuwa zanyi..! Wayyo ku kaini asibiti.. Wayyo k’irjina Wayyo cikina wayyo bayana. Wayyo k’ashin hak’wara na.. Ku kaini asibiti kar na mutu maku a nan.!”

Kaman daga sama suka sinkayo muryar Mu’azzam yana fad’in “Ba da sauri ba Mommy..!”

Gaba d’aya suka juyo suna duban Mu’azzam dake ci gaba da takowa cikin gidan, ga bakinsa da kamun jini da ciwo.. Hannunsa rik’eda envelope doguwa.

Mommy ta shiga girgiza kai tana fad’in “Wllhi mutuwa zanyi Mu’azzam.. Wayyo cikina Wayyo kaina.. K’irjina.. Zan mutu.. Ku kaini asibiti.!”

Ta k’arashe tana mai mik’ewa tsaye tana k’ok’arin kwab’e tufafin jikinta alamun hauka.

Kamo rigarta tai tana fad’in “Zan cire fah..!Wallahi zan cire..! Ku k’yaleni na fice ko na cire. Zan cire..! Zan cire..!”

Mu’azzam kaw tsaye yai gabanta cikin tsananin dakewa ya tsareta da idanu ko gizau baiba duk k’ok’ari da Mommy take tana fad’in zata cire tufafinta idan basu barta Ta fice ba.

“Go ahead..! Ki cire mana.. The hospital is right here in front of you.. Ni ne nan asibitinki Hajara.. Naci karo da Yantaddan da suka sha gabanki a taurin kai da hauka.. Ki cire kayan mu gani idan zai hanaki biyan duk abubuwan da kika aikata.!”

Mommy Ta shiga rarrabe idanu tana girgiza kai.. Lokaci guda kuma ta saki shewa tana tsalle tana tafi taka wak’ar zan cire..

“Zan cire.. Zan cire. Zan cire zan cire zan cire..”
Ta nufi gate a guje zata fice nan suka hango ana hangame gate d’in ga zuk’ek’iyar mota tana shigowa..

Gaba d’ayansu suka d’ago kai suna duban motar. Dikda motar Ta fice a yayi amma bazasu tab’a mance irin motar ba da kyaunta a wancan lokacin.

Hajara ma tsaye tai Cak da haukar k’aryarta tana duban motar. Saida motar Ta ida parking kafin suka fahimci motar.. Ba motar kowa bane face motar mahaifin Mu’azzam, Wato Alhaji Abubakar Gamji.

Cikin tsananin Shock gaba d’ayansu suke bin motar da kallo..

“Fa.. Faff..Fa.. Fatalwaaaa..!” Hajara ta furta haka tana nuna motar

SameenaAleeyou📚

*GIDAN ARO*

*76*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

A hankali take duk’awa tana kuma duban coins d’in dake aje saman kujera hawaye na ciko idanunta lokaci guda hotunan abubuwan da suka faru dasu na gifta k’wayan idanunta.. ‘Yaruwarta Yayarta take hangowa da lokacin da Ta rasata... Takai hannunta dake tsananin rawa a hankali tana shafa coins d’in. Hawaye d’aya na bin d’aya suna gangaro mata.. Ta d’aukesu cikin hannunta tana kuma juyasu hawaye basu daina gangaro mata ba.

Tana nan zaune wajen Aunty Larai ta fito daga kitchen ta nufo parlorn, nan ta hangi Umma duk’e wajen tana hawaye. Aunty Larai ta k’araso da sauri tana tambayarta lafiya meke faruwa.

Coins d’in Umma ta d’ago ta shiga nuna mata hawaye d’aya na bin d’aya “Wann sisin kobon shine alama da aka d’aura mana.. Shine alaman da na jima ina ajiye dashi tsahon shekarun nan domin na dinga tuna ‘Yaruwata dashi.. Larai nasan nawa guda d’aya ne toh daga ina wann ya fito.. Ya akai na sake samun irin alaman.? Ya akai sisin kobon suka zamto guda biyu.?” Ta k’arashe cikeda kad’uwa tana nunawa Aunty Larai.

Sadiya da fitowarta kenan tai tsaye tana duban Umma rik’eda coins.. Sai ta k’araso da sauri tana duban coins d’in..

Ta shiga nuna coins d’in yatsarta tana fad’in “Umma dama wann shine alamar da aka d’aura maku a jelar gashinku keda ‘Yaruwarki..?”

Umma tai saurin jinjina kai “Wann alama irinshi aka d’aura mana dama duk wata budurwa dake cikin jirgin.”

Sadiya ta tina a hannun Mu’azzam jiya taga yanata juyasu. Ta d’an girgiza kai kad’an tana ci gaba da nuna coins d’in.

Muryar Umma ne ya katse mata tunaninta “Ya akai naga guda biyu..?”

Ta kuma dubansu tana murmushi kafin taci gaba da fad’in “Yaruwata.. ‘Yaruwata tana raye k’ilan.. Bata mutu ba..!” Hawaye sukaci gaba da gangaro mata tana hawaye. Lokaci kuma tai tsaye tace “Amma.. Ya akai suka zama guda biyu..? Waye ya ajiyesu a nan..?”

Sadiya Ta girgiza kai tana duban mahaifiyar tata sai kuma tace “Umma.. Wann ai hannun Mu’azzam na gansu jiya.. Shi ya mance a nan.” Ta fad’i tana duban Umma dan ita tama mance cewa bata so Umman ta d’ago nan gidan Mu’azzam d’in ya kwana.

Umma ta shiga girgiza kai tana duban Sadiya “Mu’azzam..! Mu’azzam fah kika ce.. Shi yazo da wad’ann..?”

Sadiya ta jinjina kanta a hankali “Hannunsa na gansu.”

Cikin sauri Umma ta mik’e tana fad’in “Ina Mu’azzam d’in.. Inaso na tambayesa ina ya samu wann alama.. Watak’ila ‘Yaruwata bata mutu ba.. Watak’ila Ta rayu... Watak’ila..” Yanda take maganar tana hawaye tana murmushi dole ta baka tausayi.

Sadiya ta kamo hannayenta tana k’ok’arin calming d’inta “Umma kince irin wann alamar aka d’aura ma sauran ‘yanmatan.. Umma shekarun da yawa mai zai faru idan wann alama ba na ‘Yaruwarki bane.”

Umma tai shiru tana hawaye tana tina sanda bomb ya tashi da jirgin, sai kuma ta soma girgiza kai tana fad’in “Ina so nasan yanda ya samu wad’ann shaidar ne.. Inaso naji mai ya faru da jirgin bayan bomb d’in ya tashi shin akwai wad’anda suka rayu ne kokuwa..? Sadiya Ina so naga Mu’azzam yanzu yanzu.. Dan Allah ku kaini yanda yake..” Ta k’arashe tana duban Sadiyar da Aunty Larai cikeda zak’uwa.

Sadiya da Aunty Larai suka dubi juna.
Sadiya zatai magana Umma ta soma girgiza kai tana fad’in “Bazan zauna a nan ba Sai naga Mu’azzam ya sanar dani yanda ya sami wann silallan.. Bazan zauna ba Sadiya sai na gansa.. Dan Allah ku kaini yanda zan sami Mu’azzam..” Ta k’arashe duk a dame.

Sadiya data tina cewa Mu’azzam a daren jiya ya sanar da ita yana fuskantar k’alubale da ahalinsa sai ta rasa mai zatace wa Umma, Aunty Larai ta dubi Sadiyar tace ta kira Mu’azzam a waya. Babu musu ta jinjina kai ta tafi d’auko wayarta. Saidai dik kiran da take bai d’aga ba. Umma tace a kira Assad.. Shi kuma wayarsa bata shiga.. Tuni sukaga Umma ta nufi d’aki ta d’auko mayafi tana fad’in wajen aikinsa zata tafi ta dubasa.. Aunty Larai da Sadiya sukai saurin nufota suna fad’in ta dakata har a samesa a waya. Inaa ko saurarensu Umma batayi tuni ta saka kai ta fice hakan yasa dole suma suka nufota, sauk’in abin su Asheer suna makaranta hakan yasa duk suka fice gana d’aya dan Umma dai ta dage sai taga Mu’azzam a wann ranan.

**
A b’angaren Mu’azzam yana isowa gidan Hajiya Faty ya fahimci wani abu baya tafiya daidai, babu kowa a gate, babu securities sann ga k’ofar gidan a bud’e. Take ya ciro intercom dake aljihunsa ya nemi backup.. Lokaci guda kuma ya ciro bindigarsa ya zama cikin shiri ya soma sand’a ya nufi cikin gidan. D’akin masu gadin ya soma dubawa yanda ya tadda an d’auresu an rufe masu bakuna.. Yai masu alama da hannu dake nunida suyi shiru.. Suka shiga jinjina masa kai a galabaice.

Mu’azzam ya kwancesu ba tareda ya tsaya sauraron bayanansu ba dan yasan hakan bazai wuce aikin Danger ba.

Yana isa cikin gidan ya dinga bud’e k’ofofin a hankali yanda ya tadda ma’aikatan gidan mata suma an rufe su a wani store a d’aure masu bakuna sai kuka suke. Yana bud’esu kenan ya soma sinkayo muryar Hajiya Faty tana fad’in “Dan Allah kar ka kashe ni.. ko nawa kakeso ka fad’a zan baka.”

“Shut up rufe wa mutane baki.!” Danger ya daka mata tsawa da fad’in haka kafin yaci gaba da nunata da bindiga yana fad’in “The document.. Ina yake..?”

Hajiya Faty jiki na rawa take fad’in “Wane document Kenan... Dan Allah ka mun rai wllhi ni bansan komai ba.”

Danger ya kuma harzuk’a yana nunata da bindiga “BAT.. Takardan BAT.. Ina yake..?”

Hajiya Faty ta kuma girgiza kai kaman batasan komai ba dan Ta d’au alwashin hannun Mu’azzam zata mik’a wann takardan, saidai rauni irin na mace ga bindiga da yake nuna mata yasa Ta bud’e wardrobe jiki na rawa ta zaro document d’in. Daidai lokacin Mu’azzam ya daki k’ofar d’akin ya shigo... Danger kaw jin an bud’e k’ofa ya sanyashi janyo Hajiya Faty ya danna mata bindigar akai yana fad’in kodai Mu’azzam ya koma da baya ko ya fasa mata kai da harsashi.

Mu’azzam ya d’aga hannunsa alamun surrender yana fad’in “It is over for you Danger.. Just surrender now..!”

Danger na murmushi da gefen bakinsa still Hajiya Faty tana cikin hannunsa yayi pointing d’inta da bindiga yake fad’in “Bazan tab’a baka wann satisfaction d’in ba Inspector.. Bazan tab’a tsayuwa ka kamani ba.. Never..”

Mu’azzam dake aika masa mugun kallo yunk’urowa yai zai k’araso yanda yake.. Take Danger ya kuma danna bakin bindigar akan Hajiya Faty yana fad’in “If you take one more step believe me I won’t hesitate to blow her head..” Lokaci guda ya amshe document d’in ya soma jada baya yana rik’eda Hajiya Faty daketa kuka tana fad’in kar ya kasheta, taga mutuwa muraran.

Mu’azzam yai mata alama da ido sanda zasu hauro saman rug cewa tai tuntub’e da carpet d’in.

Hajiya Faty zufa duk ya wanketa aiko ta fahimci abinda Mu’azzam ke nufi dukda tsoro da ya cikata.. Suna k’arasowa saman rug tai tuntub’e ta nufi k’asa.. Shiko Danger tuni ya saki harbi wa Mu’azzam yana mai arcewa a guje, saidai Mu’azzam ya kaucewa harsashin bata samesa ba.. A wani irin speed yabi bayan Danger a guje dake rik’eda document d’in yana kiran sunansa.. Danger yai tsalle daga saman balcony ya fad’o k’asa.. Mu’azzam ma ya kama k’arfen balcony din yai tsallen yana chasing d’insa.
Chapter 153 · 0% Book details