← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 133 OF 175

Sashe 133

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Take Mommy ta bata amsa da fad’in “Yarjejeniya..! Bet Agreement Transaction.. Takarda ce da Abubakar Gamji ya sadaukar da illahirin dukiyarsa ga D’anuwansa Salman Gamji..” Ta murmusa kad’an kafin taci gaba da juya Document d’in tana fad’in “Salman yayi zaton wann takardan na hannun D’anuwansa Marwan ne, yayi zaton Marwan zai cinye dukiyar da D’anuwansa ya riga ya bar masa a rubuce ne.. A shahsanci irin na Salman da matarsa Shemau wai ni Hajara ce zasuyi amfani dani su karb’o wann document d’in daga hannun Marwan.” Tai murmushi irinta bosawa kafin taci gaba da fad’in “Basu San takardan na wajena ba tsawon shekarun nan.. Basusan Marwan baisan da existing d’in wann takardan ba.. Da ace Marwan yasan da wann takardan da babu abinda zai hanasa yarda cewa D’anuwansa Salman shi ya kashe Yayansu Abubakar.”

Hajiya Faty ta zaro ido waje tace “Toh ke ya akai takardan yazo hannunki..?”

Murmushi Mommy tai kafin tace “Kinga wann takardan shine kad’ai dalilin da yasa na amince Safeenah ta auri Mu’azzam, sabida na sani takardan na hannuna.. Da ace baya wajena sam bazan tab’a yarda tsinannen D’an Nuratu ya auri d’iyata ba balle har ya had’a shimfid’a da ita har ya bar mata guzirin jinin Nuratu cikin jikinta.!” Tana maganar tana sakin huci.

Hajiya Faty ta girgiza kai tace “Toh yanzu da kika cire cikin Safeenah ai kin kashe Magajin Mu’azzam..”

Cikin huci Mommy ke duban Hajiya Faty.. Bazan tab’a had’a iri da Nuratu ba.. Matar da na rayu da mijina da ruhinta cikin k’irjinsa.. Matar da na rayu gidan aurena da k’uncinta.. Ko Kinsan tun bayan da ya aure Nuratu duk daren Allah idan zaiyi kwanciyar aure dani sunanta yake ambata..!” Tana huci taci gaba da fad’in kaman yanda mijina yake ambaton sunanta duk dare akaina nima na tura mata Shed’ani da zai dinga kwanciya da ita duk dare.. Kuma wann Shed’anin bazai tab’a rabuwa da ita ba har abada.!”

Hajiya Faty ta had’iyi miyau da k’yar kafin tace “Amma naga Nuratu dai ha’asu aure akai da mijinki.. Ta yaya zai mata irin wann soyayyar bayan auren ma ko tarewa da ita baiyi ba..?”

A hasale Mommy tace “Shiyasa nai ma gidana lak’abi a wajenta da sunan GIDAN ARO... Gidana tamkar GIDAN ARO yake a wajen Nuratu.. Wllhi bazata tab’a kasancewa da mijina ba.. Kuma duk wanda ya zab’i ya tona mun asiri sai na gama dashi saina murk’ushe wuyansa.. Faty a lokacin da mijin Nuratu ya mutu naji da kunnuwa na irin sumbatun da Marwan ya dingayi, naji asalin labarinsu shida Nuratu da kuma D’anuwansa Abubakar.. Marwan bai tab’a son wata d’iya mace ba bayan Nuratu.. Marwan yana ma Nuratu irin soyayyar da banyi zaton ana ma wani D’anadam ba.. Marwan shi ya fara son Nuratu ba Abubakar ba.. Ki fad’a mun ta yaya bazan illata wann matar ba..? Ki fad’a mun ta yaya zan k’yale wann matar da ahalinta cikin zuri’ata..!”

Mommy taci gaba da hawaye tana jinjina kai “Saina gama da jinin Nuratu a doron k’asa.. Su kuma Marwan da Salman su jira suga tuggun da zan k’ulla masu.. Zan haddasa fitina a tsakanin ‘Yanuwan.. Fitinar da zaisa Mu’azzam yaga cewa ashe ni saliha ce ban aikata komai ba.. ‘Yanuwan mahaifinsa sune manyan ‘Yantadda domin kuwa antsakaninsu Mu’azzam zai nemo makashin mahaifinsa.!” Ta k’arashe tana mai fashewa da wani irin dariya mai gwab’i.
**

A tare Daddy da wasu Majinyatan lafiya suka shigo gidan, mata biyu sai namiji guda d’aya.

A parlor suka tadda Safeenah tana canzawa D’antsananta Diaper. Daddy ya k’araso yana murmushi yake sanar da Safeenah tazo zasuje wani waje, zasuje yanda za’a kula da ita da little Inspector.

Safeenah ta d’ago tana duban Daddy sai kuma ta dubi malaman asibitin, ta kuma dawo da dubanta ga Daddy “Daddy seriously mental facility zaka kaini.. Daddy kana tunanin ni mahaukaciya ce.. Daddy ni fah ba mahaukaciya bace.. Daddy Mu’azzam muke jira yazo ya d’auke Mu..”

Daddy ya matso da niyyan rik’o hannunta..

Ta jada baya tana fad’in “No.. Don’t.. Kar ka kuskura.. How could you Daddy..? Ta ya zaka kaini gidan mahaukata bayan da hankalina.. Ni kawai Mu’azzam muke jira nida D’ah na.. Wllhi wllhi babu yanda zanje ba tareda Mu’azzam ba.. Duk wanda ya matso kusa dani kuma ko D’ah na zan caka masa wuk’a.. Mu’azzam ne kawai zaizo ya d’aukemu mu tafi gidanmu.”

Musaddiq ya d’anyi yunk’urin matsowa yana fad’in “Feenah listen to me please..”

“Don’t you dare..!” Ta fad’i tana nuna masa table knife dake aje gefenta. “Idan ka matso kusana ko D’a na zan caka maka wuk’ar nan.. Only my Halal is allow to come near us.” Ta k’arashe tana sakin huci.

Ana a haka Mu’azzam yai sallama.

Safeenah ta tafi a guje ta fad’a jikinsa “My Halal.. I’ve missed you.. Munyi kewarka nida D’anmu.. Dama nasan zaka Zo ka d’aukemu.. Kaga ga D’anmu nan.. Yanata so ya had’u da Dad d’insa.” Ta tafi a guje Ta d’auko D’antsanan “Come here little Champ, your Dad is finally here..” Ta mik’a sa wa Mu’azzam tana fad’in “Go to Daddy.. Oya say Hi to Daddy..” Tana maganar tana mik’awa Mu’azzam babyn robar murmushi saman fuskarta.

Mu’azzam jiki a matuk’ar sanyaye yake duban Safeenah kafin ya mik’a hannunsa da k’yar alamun zai amshi abinda take mik’a masa.

Safeenah take “Careful My Halal ka San jariri ne..”

A hankali Mu’azzam ya amshi D’antsanan ya rik’esa cikin hannunsa irin yanda ake rik’e D’anmutum har d’an jijjigasa yake.

Safeenah ta saki murmushi tana dubansu hawaye saman fuskarta “Na sani zama mahaifi zai dace dakai.. Just look at you know.. You look so cute holding our Baby..”

Murmushi Mu’azzam yai yana dubanta cikeda tsananin tausayi, ta k’araso ta kamo hannunsa “Zo ka zauna ka jirani I’ll park our stuff nida little Inspector.. Yanzu zan fito mu tafi gidanmu.”

Saurin rik’o hannunta yai yana girgiza mata kai “Don’t park anything Kiki zatayi.. Kawai kizo mu tafi yanzu..” Ya k’arashe cikin sigan lallama yana mai mik’ewa tsaye.

“Really..?” Ta fad’i tana dubansa.

Ya jinjina mata kai a hankali yayinda Kiki ta jinjina kai tace “Eh zan shirya maku kayanku Keda little Inspector Adda Feenah.. Just go with Ya Mu’azzam now.. I’ll park all your stuff, I promise.”

Jinina kai Safeenah tai sai kuma ta dawo da dubanta ga Mu’azzam “Let’s go my Halal.”

Ya jinjina mata kai kad’an yana sakin murmushi, ya dubi su Daddy ya d’an masu alama da ido. Gaba d’aya suka d’unguma suka bi bayansu harda ma’aikatan lafiyan.

Suna fitowa waje suka hangi wata mata tana nufosu...Gaba d’aya Cak suka tsaya suna dubanta..

SameenaAleeyou📚

*GIDAN ARO*

*68*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Ba kowa bace face Mommy, kanta a duk’e ta nufosu tana jan k’afafunta da k’yar kaman mai tsoron k’arasawa garesu.

Aiko Safeenah na ganinta ta saki k’ara tana b’oye D’antsananta a bayanta tana fad’in “Kar ku barta Ta k’araso.. Kar ku barta tazo nan.. Zata kashe mun D’a.. Daddy ka koreta..” Ta isa gaban Mu’azzam a guje tana fad’in “You need to arrest her my Halal.. She’s a criminal.. ‘Yar ta’adda ce itad’in.. She killed our Baby.. Mu’azzam zata kashe mana little Inspector ka kamata kaji..” Ta k’arashe tana jijjiga Mu’azzam da tun shigowar Momy farfajiyan gidan yai tsaye Cak yana dubanta.

Mommy ganin Safeenah a haka ya sanyata d’aura hannu aka tana fad’in “Na shiga uku.. Safeenah mai ya sameki.. Wayyo Allah ni Hajara.. Safeenah mai nake gani haka..? Mai ya sameki Safeenah.?” Mommy Ta fashe da wane irin kuka. Ta yunk’ura ta nufo Safeenah Daddy ya saka mata tsawa da fad’in “Don’t you dare come near my daughter.. Kar ki kuskura Hajara.!”

Mommy Ta kuma fashewa da kuka tana d’aura hannaye aka.

Wani irin ihu da tsalle Safeenah keyi tana nuna Mommy tana fad’in sai an fitar da ita, take ma’aikatan lafiyan sukai dabaran rik’e Safeenah suka ciro allura cikin motarsu sukai ma Safeenah.. A hankali Safeenah ta silale idanunta suka lumshe.

Daddy ya dubesu yace su tafi da Safeenah zai taho ya dubata daga baya. Suka jinjina kai had’ida masu sallama.. Allah sarki ‘yanuwan suna ji suna ganin aka saka Safeenah a mota aka tafi da ita.. Ko wanne D’an adam farkonsa da k’arshen ya sani, farkonsa haihuwa k’arshensa mutuwa.. Saidai babu wanda yasan K’addarar da zata faru a tsakiyan rayuwarsa, Allah ka bamu jarabawar da zamu iya ci ka karemu da mummunan K’addara.

Cikin wane irin yanayi Daddy ke duban Mommy yana fad’in “Hajara kar ki kuskura.. Kar ki kuskura ki shigo mun gida.. Bakida muhalli a gidana.. Gidan yari shi kamanci azzaluma irinki..!”

Cikin kuka Mommy ke fad’in “Wllhi ba yin kaina bane sharrin zuciya ne.. Na shiga uku ni Hajara.. Marwan dan Allah kar ka bari a kulleni.”

Daddy ya jinjina kai yaci gaba da fad’in“Burinki ya cika Hajara.. Ga d’iyarki nan kin haukarta da ita, kin cire jinin Mu’azzam a cikinta, Kin maidata haka sabida son zuciya irin naki.. Hajara Anya ke ‘yar Adam ce..? Hajara wace irin uwa zata aikata abinda kika aikatawa Safeenah.?”

Kuka Mommy keyi tana girgiza kai “Dan Allah ku yafe ni wllhi sharrin zuciya ne da burin d’aukan fansa.. Fansar duk abubuwan da Mu’azzam yai mun.. Fansar k’untata mana da yai nida Safeenah.. Da ace nasan abinda na aikata zai koma kan Safeenah ne da ban aikata ba.. Dan Allah ku yafe ni.”

“Drop the act..!” Suka sinkayo muryar Mu’azzam daga bayansu na fad’in haka..

Mommy ta kaikaito da k’yar tana dubansa. Sosai ya tsareta da rikitattun idanun nan nasa masu firgita mai laifi.

Daddy ya dubi Kiki yace ta shige gida ya kuma duban Musaddiq zai sallamesa Mu’azzam yace “No Daddy.. Musaddiq zai tsaya a nan domin ya zama shaida akan abinda zan tambayi Mommy yanzu.”

Daddy ya dubi Musaddiq da mamaki sai kuma ya dubi Mu’azzam d’in, ga Mommy dake duk’e wajen tana hawaye.

Mu’azzam ya gyara tsayuwarsa, cikin wani irin murya mai tsananin gizo da dukan zuciya yake furta “You tell me the truth Mommy.. Maiyasa kika zab’i cutar da mahaifiyata..?!”

Zuciyar Daddy yai wani irin yankewa, ya dubi Mu’azzam sai kuma ya dubi Mommy..

Ya girgiza kansa kad’an yace “What’s going on here.?”

Mu’azzam ya kuma jefo wa Mommy tambaya “Ki amsa mun Mommy.. Meye mahaifiyata Ta miki kika zab’i ki salwantar da rayuwarta.!”
Chapter 133 · 0% Book details