← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 175

Sashe 68

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta jima tana duban hoton su itada Mu’azzam na ranan aurensu dake lik’e a hanyar matakalan. Lokaci guda Safeenah ta isa jikin hoton tana sakin murmushi tana shafa hoton a hankali musamman b’angaren Mu’azzam. Sunyi kyau har sun gaji, sannan sun dace da junansu.. Ta kuma sakin murmushi har lokacin shafa hoton take “Hakan ya nuna tabbacin ni ce a zuciyarka My Halal.. Da ace wancan ‘yariskar tanada matsayi na tabbata da baka aje hoton nan a nan ba.. I’m the Queen of your heart Mu’azzam.. And I won’t allow any woman ta sace mun wannan matsayin a wajenka.. I’ll do whatever it takes to make sure banyi sharing d’inka tareda wata ba.. You are mine.. Alone..!” Tana ida fad’in haka ta nufi nata d’akin tana k’are ma d’akin kallo.. Kaman babu wanda ya zauna ciki, komai tas tas harda hotonta gefen bedside Mu’azzam ya aje. Ta kuma sakin murmushi tana duban hoton saidai hango kaya jere cikin wardrobe da tai ne ya sanya zuciyarta tsinkewa.. Ta isa ta bud’e ta shiga firfito da kayayyakin tana watsi dasu wasu tana kekketa su da hannayenta musamman da taga dik dangin English wears ne..
“I curse you.. I curse you.!! I curse you..!!” Haka ta dinga fad’i tana keta kayyakin tana watsi dasu. Taci gaba da sakin huci kafin ta nufi bathroom d’in tana k’are masa kallo.. Harda kayan wanka dasu shampoo.. A fili ta furta “Shegiya Karuwa.. Idona idonki sai na kasheki..!” Ta tattaro kayan wankan danginsu shower jell dasu Shampoo ta dinga matsesu tana zubar dasu cikin toilet seat saida ta zubar dasu kaf tai flushing d’insu tana sakin huci kafin ta fito ta nufi ta nufi nasa d’akin. Haka kurum taji gabanta yayi wani irin yankewa sanda ta hangi saman gadon.. Muasamman data lura saman gadon is kind rough alamun an kwanta ba’a gyara ba.. Take wani tunanin ya soma d’arsuwa zuciyar Safeenah.. Tai saurin rintse idanunta tana bud’e hannayenta take furta “Enough Feenah.. Nothing happened, kawai dai ya kwanta ne ya tashi bai gyara gadon ba.. And that’s all.. Yanzu sai ki gyara masa and play a perfect wife role..” Ta d’an rausayar da idanunta kafin ta haye saman gadon tana mai tattaro pillows d’in..

K’amshin da hancinta ya jiyo mata cikin pillows d’in shi tasa zuciyarta kusan bugawa, dan k’amshin shower jell da Shampoo d’in da ta gama juyowa cikin toilet taji.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.. Tare fah suke Kwana kenan.. D’akin mijinta wanda ko tarewa basuyi ba.. Gashi ya tare da wata Karuwa tana can baki sake.. Take taji kuzarin jikinta sun tafi gaba d’aya.. Ta koma ta silale tana jin wane irin kuka gauraye da k’unci na taso mata.. Haka ta dinga kuka tana fatali da kayayyakin dake cikin d’akin.. Saida tai mai isarta kafin Ta danni kanta da fad’in “Feenah kuka bai ganki ba.. You need to be strong if you want to get your husband back.. Think Feenah..!” Ta soma kame kanta tana tinanin abinyi tinda dai yanzu babu Meema mai bata shawari. Murmushi ta saki still hawaye na gangaro mata sanda ta tuna abinda zatai. Nan kuma ta hango takarda yashe a k’asa.. Ta rarrafa ta d’auki takardan tana juyawa, rubutun da ta gani jiki shi ya bala’in kashe mata jiki ya kuma haifar mata da bugawan zuciya. Na farko na Mu’azzam ne yana umartan Sadiyar da tai wankan tsarki dukda babu abinda ya faru.. Sai note d’in da Sadiyar ta bar masa a k’asa na cewa bazata tab’a yafe masa ba kan abinda yai niyyan mata sannan mission d’in ya k’are..

Safeenah ta gyara zama sosai tana nazarin rubutun, idan taso fahimtar wani abu kenan zaman mission wann ‘yariskar tai a gidanta..? Toh kodai da gaske ba zaman auratayya sukeda Mu’azzam ba..? Kardai auren yarjejeniya ne shiyasa yace wa Daddy zaiyi bayani..? Toh amma wane irin mission kenan..? Ta kuma tambayar kanta.. Toh koma dai menene mission d’in ta tabbata kusantar yarinyar yasoyi kenan.. Mu’azzam d’in da tai masa shaida babu ruwansa da mata ashe hauka take gashi har zai ma wata da k’arfi ita tana can tana bibiyarsa ko kallo bata ishesa ba.. Zuciyar Safeenah yaci gaba da harbawa cikin sauri.. Babu abinda ya tsaya mata kaman cewa da Mu’azzam yai cikin note d’in ‘Thank you for taking care of me last night’. Safeenah ta shiga keta takardan tana kuka tana birgima a wajen.

**

Suna isa gidansu Sadiya suka tadda kaman Kufai, babu kowa sannan babu alamun kowa wajen, Mu’azzam yai tsaye yana tina farkon zuwansa layin wanda bincike ya kawosa, ya tuna had’uwarsu Ta farko a lokacin da suka bangaji juna, ya tuna jifarsa da ultra pad da tai, ya tuna randa ya aureta ya kuma sunkuceta ya tafi da ita.. Haka ya dinga tina every bit na abubuwan da suka faru tun bayan had’uwarsa da ita.. Saman dakalin k’ofar gidan ya zauna yana mai d’aura hab’arsa saman hannayensa da ya had’e waje guda.

Assad da k’arasowarsa kenan bayan yabi layi layi yana tambaya ko sunga Sadiya amma babu wanda yace yaga Sady Pretty sannan Mahaifiyarta ma da ‘yanuwanta har yau basu san yanda suke ba, babu wanda ya kuma ganinsu a unguwar.

Assad ya k’araso kusan Mu’azzam d’in yana mai girgiza kai “Mu’azzam negative..! Babu wanda ya ganta, da alama batazo nan ba.. Sannan k’awarta Sabeera sun bar gari..” Ya k’arashe cikin sanyin murya.

D’agowa Mu’azzam yai ya dubesa kafin ya jinjina kai a hankali ya mik’e yana kuma duban gidan.. Inama ya ganta a gabansa, inama ya ganta tana fitowa daga cikin gidan.. Ya kuma fuzar da fuci kad’an kafin yace “I’m not leaving this place har Sai na ganta.. Nan kawai zatai tunanin zuwa. I’m hundred percent positive.. So you go Assad.. Ni zan tsaya a nan..”

Assad ya d’an girgiza kai kad’an yana mai zama gefen Mu’azzam d’in nan saman dakalin.

Wayar Mu’azzam ne ya soma ruri, ya ciro daga aljihunsa yana duba mai kiran, ba kowa bane face Safeenah.. Bai d’aga ba sai maida wayar da yai cikin aljihu. Bata fasa kira ba.

Assad ya dubesa yace “Bazaka d’aga ba.. It might be something serious..”

Gajeren tsaki yai yace “Assad, don’t you think I have a lot on my plate already. Banida lokacin haukar Safeenah..”

“She’s still your wife Mu’azzam.. She’s your responsibility.. Ya kamata ka d’aga kaji meke faruwa.”

Ya d’an fuzar da fuci kad’an kafin ya d’aga kiran.

Kukan Safeenah ya soma jiyowa tana fad’in Tasan komai duk kalan cin amanarta da yai shida wancan ‘yariskar da sunan mission.

Ya lumshe idanunsa kad’an kafin yace “Look Feenah.. I don’t have time for your stupid tantrums.!”

Katsesa tai da fad’in “Bakada lokaci na amma kanada lokacin shirya mission a bayan ido na hardai ka tasamma raping d’in ‘yar mutane. Ko kunya bakaji ba kana da mata kaman Safeenah Gamji amma kaje kana k’ok’arin aikata fyad’e wa k’aramar yarinya.. Kodai shima cikin mission d’in naka ne..?”

Assad kaw matsawa gefe yai yana amsa wayarsa wanda ya soma ruri.

Da Mamaki Mu’azzam yace “Mai kika ce Safeenah..?!”

“Kaji sarai abinda nace, Wllhi ko ka dawo gida ka kula dani ko na sanar da Daddy ga irin auren da kayi Kasan sarai Daddy bazai lamunci irin wannan auren ba musamman idan yaji cewa auren mission ne.. Sannan harda fyad’e ka tasamma yi a matsayinka na jami’in tsaro.”

Gyara zamansa yai kafin yace “First of all kar ki sake cewa na tasamma yin fyad’e wa matata ta sunna.. Secondly, don’t you dare threaten me Safeenah, for as far as I know, I didn’t do anything wrong.!”

Safeenah ta jinjina kai tace “I’m not threatening you, I’m only saying the fact.”

Mu’azzam ya fahimci cewa Safeenah Ta tsinci note d’in da suka bari ma juna ne shida Sadiya. Hakan yasa ya jinjina kai yace “Okay, well.. Go ahead and tell Daddy.. Kije ki fad’a ma duk wanda kikaga dama cewa ni Mu’azzam Gamji nayi auren mission sannan idan kinje fad’a kice na tasamma kusantar matata wacce nai mata mummunan fahimta daga farko.. And after na fahimci cewa she’s a total opposite of duk abinda nake zato kanta sai na fasa kusantarta dan ba a haka ta cancanci nazo mata ba, because she deserves nothing but the best.!” Daga haka katse kiran yai Safeenah na kuma fashewa da wane irin kuka wanda batayi irinsa a baya ba.

Daidai lokacin Assad ya k’araso yana fad’in “Shall we inform our team members ko zasu tayamu da search d’in..?”

Girgiza kai Mu’azzam yai yace “Ni a halin yanzu ban yarda da kowa ba Assad, especially mutanen da muke aiki dasu, bayan abubuwan da suka faru nasan ba zakaga laifina ba idan na zargi kowa.”

Assad ya d’an shafi kansa yace “Haka ne Mu’azzam, toh yanzu kana nufin ba komai zamu sanar dasu ba gameda case d’in..?”

Ya jinjina kai yace “Ko Yusuf ne bazamu sanar dashi komai ba for the mean time har Sai mun fahimci waye mai mana zagon k’asa..”

Assad ya jinjina kai yace “What do we do now..?”

Mu’azzam Baikai ga basa amsa ba wayarsa ta soma ruri.. Unknown number shine ya bayyana saman screen d’in. Ya dubi Assad ya kuma duban wayar dake ci gaba da ruri.. Lokaci guda ya d’aga wayar.

Daga d’aya b’angaren dariya aka fashe dashi kafin mutumin ya furta “Detective Gamji.. It’s been a long time.. Did you miss me..?” Sai aka kuma fashewa da dariya...

SameenaAleeyou📚

*GIDAN ARO*

*36*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

“Danger.!” Abinda Mu’azzam ya furta kenan yana jinjina kai a hankali.

Dariya ya kuma kecewa dashi kafin yace “Correct.. Ashe dai baka mance ni ba.. Koda yake ta yaya zaka mance Abokin shan shayinka..!”

“I’ll catch you.. Believe me I will..!” Mu’azzam yace yana sakin murmushi mai zafi.

Danger ya kuma k’yak’yata dariya kafin yace “If I were you ba wann maganar zanyi ba yanzu.. Zai fi kyau ka bada mahimmanci ga neman matarka da kake..!” Ya kuma fashewa da dariya kafin ya katse kiran.. Yana katse kiran ya karairaya SIM card d’in yai watsi da ita.

K’iris ya rage zuciyar Mu’azzam bata buga ba.. Mai Danger yake nufi.. Badai Sadiya tana hannunsa ba.. No no no. Baiso yayi tunani haka.
Chapter 68 · 0% Book details