← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 147 OF 175

Sashe 147

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ameer ya bita da kallo murmushi saman fuskarsa, lokaci guda ya bud’e murya yace “I love you my chubby.”

Takaici ya cika Meema ko juyowa bataiba balle ta amsa shi.

**

Suna tsaye k’ofan Headquarters d’in nasu suna tattauna yanda zasu b’ullowa lamarin Jaja da Danger suka hango wasu police guda biyu cikin wad’anda suke tsaron gidan Daddy sun nufosu, ga Musaddiq tafe daga tsakiyansu.

Mu’azzam da Assad sukai tsaye suna dubansu har suka k’araso yanda suke.

‘Yansandan suka sarawa Mu’azzam wanda ke ta binsu da kallon mamaki. Kafin Mu’azzam d’in yace wani abu Musaddiq da kansa ke duk’e k’asa yai saurin d’agowa ya dubi Mu’azzam yace “I.. I am here to turn myself in.. I am here... to confess.!”

Ba Mu’azzam kawai ba harta Assad saida k’irjinsa ya bada wani irin sauti Dummm.!

SameenaAleeyou📚

*GIDAN ARO*

*74*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Ya girgiza kansa kad’an yana duban Musaddiq d’in da kansa ke kife yana hawaye “Musaddiq lafiya kake..? Meke damunka..? Mai kake nufi da cewa zaka mik’a kanka..?” A tare yake jero masa tambayoyin yana jin kaman bugun zuciyarsa na yunk’urin tsayawa.

Musaddiq yaci gaba da girgiza kai yana hawaye “Bazan iya kallonka cikin ido ba Mu’azzam... Bazan iya ba.!” Ya d’ago yana kuma girgiza kai yana hawaye. Bindigar dake mak’ale jikin belt d’in Assad ya zaro yana mik’awa Mu’azzam d’in yayinda suka kuma karaya gaba d’ayansu.

“Shoot me right in the head.. Ka harbeni, rayuwata batada sauran amfani.. Please ka harbeni Mu’azzam..!” Ya k’arashe yana mai duk’awa gaban Mu’azzam d’in da ya koma tamkar mutum mutumi yana duban Musaddiq.

Assad yai saurin matsowa yana ‘yan waige waige lokaci guda yake fad’in “Mai kake aikatawa Musaddiq.. Ka kuwa san Ina ne nan.. Police Headquarters ne fah.. Idan wasan kwaikwayo kakeyi toh ya kamata ka daina kafin wani ya ganka..”

Cikin d’aga murya yake duban Assad yana fad’in “Ba wasan kawaikwayo bane.. Gaskiyar kenan wann.. Ni Musaddiq Gamji ba komai bane face D’antadda.. A Criminal.. A rapist.. D’antadda mafi muni..!”

Zuciyoyinsu sukaci gaba da bugawa da sauri da sauri wann karon.

Assad ya girgiza kai yana duban Musaddiq d’in cikin wane irin yanayi kafin yace “Rape..! Who did you rape.. Wacece ka mata fyad’e Musaddiq.?!”

Musaddiq ya tsaya da kukan da yake Cak yana duban Mu’azzam da ke tsaye kansa tamkar mutum mutumi, kai kace statue ne aka dasa Sa a wajen. A hankali ya soma jinjina kai yana duban Mu’azzam kafin ya soma furta “I was the one who raped her.. I.. I raped Ikram..!” Ya k’arashe wasu hawayen suna gangaro masa.

Mu’azzam da yaji maganan kaman daga can nesa kaman echo ne ke d’ibo masa sautin, kaman daga wata duniya daban yake jin kalaman.. Idanunsa akan Musaddiq wanda shi d’inma Mu’azzam d’in yake duba.

Assad yai tsaye cak cikin tsananin shock yana duban Musaddiq d’in wanda yake furta cewa shi yayima Ikram Fyad’e..
Saida suka kwashe dak’ik’ai dukansu suna tsaye kaman gumakka kafin Assad ya iya motsa bakinsa yace “What..! What did you just say..!”

Musaddiq yaci gaba da jinjina kai yana hawaye “Kaji daidai.. Ni ne nan naika Ikram fyad’e kuma nazo nan ne domin na biya laifin da na aikata.. Please arrest me..!” Ya k’arashe wani kukan na kufce masa.

Assad da ya kasa daidaita bugun zuciyarsa duban Mu’azzam yai da har lokacin tsaye yake wajen kaman gunki, ya kuma duban Musaddiq dake duk’e gaban Mu’azzam d’in yana hawaye yana ci gaba da furta “I don’t deserve your forgiveness Mu’azzam.. Ban cancanci komai ba face uk’uba.. I don’t even deserve life.. Just end my miserable life Mu’azzam... Ka harbeni ka hukuntani..!” Ya k’arashe yana janyo hannun Mu’azzam guda maras ciwo yana fad’in ya harbesa yana kuka sosai duk’e a gabansa.

Har lokacin koda ‘yar yatsarsa Mu’azzam ya kasa motsawa. Yana nan tsaye wajen Musaddiq naci gaba da jijjiga hannunsa yana fad’in ya harbesa.

Assad yai k’ok’arin janye Musaddiq, ya kuma dubansa kafin ya furzar da fuci kad’an yana mai kauda kai gefe sabida girman zancen da Musaddiq d’in yazo dashi “Are you aware of what you’re saying.. Ka kuwa San mai kake fad’i Musaddiq.. This is a very serious crime.!”

Musaddiq ya jinjina kai yana duban Assad d’in “Na sani Officer.. Kuma nayi confessing cewa na aikata laifin.. Na aikata.. Yes ni D’antadda ne.. Put me behind bars.!” Ya k’arashe yana mai ware idanunsa tar kan fuskar Assad.

Jinjina kai Assad ya kumayi yana furzar da fuci had’ida Shafa kansa da tafukan hannayensa biyu “Zamu shiga da kai zamu d’auki statement d’inka.” Yana ida fad’in haka ya kamo hannun Musaddiq d’in guda suka nufi building d’in nasu.

Har lokacin Mu’azzam tsaye yake Cak wajen, yanda dai kasan an ajiye statue ko motsawa baya iyayi.
Har Assad ya shige da Musaddiq Mu’azzam bai farga ba, bai san meke wakana ba, yanaji kaman mafarki ne kaman kuma zahiri ne.. Yana ji kaman shidai an canza masa tasa duniyar ne.. Yana ganin abubuwan kaman ba a zahiri suke faruwa ba.

Har Assad ya shiga ya d’auki bayanan Musaddiq Mu’azzam na nan tsaye wajen.

Assad ya tsaya daga can nesa yana duban Mu’azzam d’in. Ji yake shi kansa zuciyarsa ta gaza d’aukan abubuwan dake faruwa da Mu’azzam d’in, Toh inaga Mu’azzam d’in wanda abubuwan ke faruwa akansa da ahalinsa.. Ta gama tabbata case d’in mutuwan Ikram da suketa bincike akai ashe criminal d’in na cikin ahalin Mu’azzam d’in ne.. Kai wann tashin hankali da yawa yake.. Wann masifa da yawa yake.. Tabbas mutum baya zab’en ahalinsa amma shi tinda yake bai tab’a cin karo da ahali irin wann ba.. Kenan Mu’azzam kewaye yake da mak’iya wanda sukai masa kisan mummuk’e a tsaye.. Sun saresa da mashi mai tsananin guba sann Sun watsa masa k’ayan gafiya mai tsananin dafi... Bai tab’a jin tausayin wani d’an adam ya rufesa a ranan irin yanda yaji tausayin Mu’azzam ba.

Ya k’araso a hankali ya tsaya gefen Mu’azzam d’in, sukai tsaye wajen babu mai cewa komai. Assad ya d’an shafi fuskarsa da tafukan hannayensa had’ida furzar da fuci kad’an “Mun d’auki statement d’insa he’ll be detained here.. Nasan you can’t question him right now, so banma yi inviting d’insa to interrogation room ba.”

Magana kurum yake amma da alama wanda yake ma maganar baya sauraron sa.

Assad ya d’an kuma tamke idanunsa kad’an cikin zuciyarsa yana furta ‘Why am I even telling him all this..? Ya Allah give him strength to overcome all this trials’

“Ka gane muje na kaika gida..” Assad ya fad’i yana juyowa yanda ya bar Mu’azzam d’in a tsaye. Saidai to his surprise babu Mu’azzam a wajen. Sai Sautin tashin motar Mu’azzam d’in da yaji, kan yai wani aune Mu’azzam yaja motar ya bar wajen dikda cewa hannunsa guda akwai ciwo.. Assad yai k’ok’arin bin bayansa amma bai cimmasa ba. Yai tsaye wajen hannayensa dafe saman k’ugunsa.. Girgiza kai kurum yake yana addu’a ma abokin nasa cikin zuciyarsa Allah Ubangiji ya basa ikon cin jarabawa. Baban damuwarsa ma shine Mu’azzam d’in ba k’oshin lafiya bane dashi ba, baisan ya sai driving a haka ba.

“Drive safe Inspector.!” Ya furta a hankali yana mai girgiza kansa kad’an. Agogon dake d’aure hannunsa ya duba yaga har uku na rana ta gauta.. Ya dawo da baya yana kuma furzar da huci a hankali. Nan ya hangi wata Mota na nufosa. Yai still yana duban motar Dan kaman yaso ya gane motar.

Barr Ameer ne ya fito cikin motan ya nufo Assad d’in, sukai masabaha da juna Assad na fad’in “Barr kaine tafe..? How may I help you.?” Ya k’arashe maganar suna d’an takawa a jere. Yayinda suka k’arasa saman wasu kujeru suka zauna.

Barr Ameer bai b’oye ma Assad komai na gameda abinda ya kawosa ba. Assad ya amshi recordings d’in yana sauraro wanda Maleeka ke fad’in asirin Jaja da cewa shi yake kare makashin Ikram sann shida Danger suna aiki ne hand in hand.

Assad ya sauk’e ajiyan zuciya bayan ya gama saurara kafin ya dubi Ameer yace “Maiyasa sai yanzu ka bayyana wann.. Shin ko kasan da ace ka bayyana wann recordings d’in da wuri watak’ila da Maleeka bata rasa ranta ba sann watak’ila da yanzu an kama Danger an kawo k’arshen case d’in nan..”

Ameer yai shiru yana girgiza kai dan shi baima San Maleeka Ta mutu ba sai wann lokacin sabida tin bayan da ya tabbata bazai samu daman kare Safeenah a kotu ba ya yanke duk wata alak’a da Maleeka dama sabida Safeenah ne suka k’ulla alak’ar.

“Kana nufin kace mun sun kashe Maleeka..?” Ameer ya tambaya cikin tsananin Shock.

Assad ya jinjina masa kai a hankali kafin ya sanar dashi duk yanda abin ya kasance.

Cikin wane irin yanayi Ameer ke girgiza kai cikeda tausayin Maleeka, lokaci guda yake furta “‘Yar sanda ce mai k’wazo saidai dama a irin a hanyar data d’auko komai ka iya faruwa da ita.. Allah sarki Maleeka Allah ya yafe mata yasa k’arshen wahalan kenan.”

Assad ya d’an nusa kafin ya amsa da Ameen. Lokaci guda yake ci gaba da furta “Komai rubutacce ne tun kafin ayimu, Allah ya nufa hakan sai ya faru.. Koda ka bayyana recordings d’in da wuri koda baka bayyana ba Allah ya k’addari faruwan hakan tuntuni..”

Ameer ya jinjina kai a hankali yana mai furta “Wann gaskiya ne.. Allah ya yafemu gaba d’aya..”

Assad ya amsa da Ameen kafin ya k’arada “Dikda haka bai b’aci ba, wann recordings d’in concrete evidence ne da yake nuna cewa Jaja yana aiki da Danger sann shi ya bada umarni aka kashe Maleeka.. Sosai wann recording d’in zai incriminating Jaja. He has no other option than to expose Danger and their accomplices.”
Ya mik’o wa Ameer hannu sukai masabaha yana fad’in “Thank you so much Barr.. Thank you for choosing to do the right thing.”

Ameer ya jinjina kai yace “A koda yaushe mu abokan aiki ne.. Ku binciko gaskiya mu kuma mubi bayan gaskiya a kotu..”

Suka murmusa a tare gabaki d’aya kafin Ameer ya dubi Assad yace “Mu’azzam fah..? Ina tsananin buk’atar na gansa na nemi yafiyarsa na kuma sanar dashi yanada full support d’ina akan ko menene..”

Assad yai murmushi wanda da gani na k’arfin hali ne kafin yace “Kar ka damu zaku had’u ne idan al’amra suka daidaita.. Mun gode sosai da wann gudumawa da ka bayar.”
Chapter 147 · 0% Book details