← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 175

Sashe 11

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin sauri ya shiga furta “Baba muna buk’atan muga Sabeera yanzun nan..”
Shikam Mu’azzam tuni ma ya koma k’ofar gidan yana kuma bugawa..

Baba Maigadi da Assad suka dawo a tare, Baba na fad’in “Barin maka iso Yallab’ai ai inaga bata fita ba dan makarantarsu suna yajin aiki...

Koda Baba ya shiga ya sanar da Alhaji Isyaku ga mutumin da suke nema sosai ran Alhaji Isyaku ya b’aci, ya tasa Maman Sabeera da fad’a Ta yanda yake shiga bata nan yake fita ba “Na fad’a miki bana son alak’ar yarinyar nan da k’awayen banza.. Har yaushe Sabeera take kawo samari zance cikin gidan nan banida labari.. Kullum ina ja miki kunne bakiji.. Ga irinta nan kinga abinda taurin kunnenki ya janyo mana.. Toh wllhi Nidai kinji na rantse idan aka rufeta bazanyi belinta ba, Keda kike d’aure mata gindi take tarayya da ko wasu irin mutane sai kije kiyi belinta.. Aikin banza Ina Sabeeran take yanzu..?”

Maman data rapka tagumi cikeda tashin hankali take fad’in “Taje sayan Katin waya a bakin layi.. Amma yanzu zata dawo.. Oh ni Rahina na shiga uku.. Alhaji kar ka bari su tafi da Sabeera wllhi d’iyarmu yarinyar kirki ce..”

Tsaki ya buga yana fad’in “Ai Kinga irin abunda kullum nake fad’a miki, idan kukayi wasa daga rana mai kaman ta yau makaranta ma Ta daina zuwa.. Rahina sanin kanki ne Gudun kar d’iyata ta lalace yasa nak’i kaita wani wajen tayi karatu nace saidai tayi a nan, ko hostel ban amince ta zauna ba na ajiye mota da driver nace kullum a dinga kaita, toh tinda a nan d’inma ban tsira ba cireta zanyi Ta gama karatun..”

Cikin damuwa Maman Sabeera Ke fad’in “Alhaji kar kace haka, lalacewa ba daga nan take ba, Ko a d’aki kake rufe d’iyarka idan taso lalacewa sai ta lalace, tsananin tak’ura bashike tsare mana yaranmu ba, a’a ayi addu’a kuma a saka idon.. Nawa aka tak’ura masu kuma suka lalace d’in kaidai kawai addu’a shi zamuke masu.. Balle ma nasan Sabeera batayi komai ba..”

“Ke ni ki rufe mun baki, ki shige muje ki bama ‘yansanda bayanin yanda d’iyarki taje..” Ya k’arashe yana mai sab’a babbar rigarsa kafin yai ficewarsa..
Maman Sabeera ta biyo bayansa tana kiranta inaa ko sauraronta baiba..

A b’angaren Sadiya kuwa tana isowa gida ta tadda k’aninta kwance jikin Ummansu, da k’yar Umman ta shawo kan Tabawa da fad’in satin da za’a shiga tayi alk’awari dik yanda kud’ad’enta suka shiga suka fita zata nemomata Su, da wannan yarjejeniya Tabawa ta saki Habeebu bata tafi dashi ba..

Sabeera dake tsaye gefe rik’eda k’aramar bak’ar leda a hannunta, recharge ne na waya saiko sai sanitary pad da ta sayowa Sadiyar, ta cire recharge card d’in ta mik’awa Sadiya ledar sanitary pad d’in tana fad’in “K’awata barin k’arasa gida kafin a soma nemata, Baba na gida bai fice ba.. Nasan Sai ya tambayi Ina nake kafin ya fita..”

Sadiya dai tinda ta k’araso sai lek’e lek’e take a lungun, kaman mai jiran zuwan wani..

Sabeera ta d’an juya tana waige waige da mamaki tana duban mai ya d’auke hankalin Sadiyar..

“Wai lek’e lek’en me kike ne tintinin, Hajiya Tabawa dai ta tafi ba dawowa zatayi ba, dan Allah ki kwantar da hankalinki..”

Itadai Sadiya bata ce mata komai ba, dan tinda taci karo da wannan mutumin k’irjinta bai daina bugawa ba, sannan gabanta bai daina yankewa ba..

D’an murmusawa kad’an Sabeera tai tana fad’in “K’awata badai tsoro ba.. Kinga bara na k’arasa gida, sai munyi magana..”

Juyawan da zatai ta hango ta hango Babanta da mamanta harma da wasu mutane guda biyu Sun karyo kwanan gidan Babanta sai masifa yake..

Ba Sabeera data kusan sakin fitsari a jikinta ba, harta Sadiya saida taji ‘yanhanjinta sun juya musamman data hango wannan mutumin da suka bangaji juna shida Ita...

Sabeera tai saurin rik’o hannun Sadiya tana fad’in “Na shiga uku Sady wllhi Baba ne... Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.. Shikenan yau kasheni kawai zaiyi wllhi..”
Sadiya kam Ta kasa katab’us sai duban mutumin nan da suka bangaji juna take d’azu, zuciyarta taci gaba da bugawa idanunta akansa.. Har wannan lokacin idanunsa na rufe cikin bak’in glasses.

Baban Sabeera dake gaba yana sab’a babbar riga yana nunasu da yatsa yake fad’in “Yauwa Inspector, ka gansu can, gasu can.. Dama na fad’a maku a nan za’a sami Sabeera.. Tana tareda wannan annobar.. Yarinyar ta riga ta zame mana masifa a unguwar nan, banda tara maza bata komai.. Duk ta lalata tarbiyan yaran layin nan..” Ya kuma sab’ babbar rigar yana jefo dak’uwa ma Sabeera tin daga nesan yana fad’in “Zakici gidanku ne yau..!”

Sabeera Ta kuma rikicewa tana kuma b’oyewa bayan Sadiya daidai sanda suka k’araso k’ofar gidan.. Har lokacin Baban Sabeera bai daina bala’i ba mamar Sabeera na kwab’arsa hankalinta duk a tashe itama amma kaman cewa yake Ta k’ara...

Sadiya tsoro Sabeera tsoro, Sabeera na tsoron Babanta Sadiya kuma gani take Baban Sabeera ‘yansanda ya d’auko mata zai sa a rufeta a police station tinda ya mata iyaka da d’iyarsa tak’iji.. Aiko suna k’arasowa ta finciki hannunta daga rik’on da Sabeera tai mata, tuni tai jifa da ledar sanitary pad dake rik’e hannunta wanda Sabeera ta sayo mata a shago... Aiko ledar nan bai sauk’a ko Ina sai Fuskar Mu’azzam, tim kakeji ya samesa a fuska sai da glasses d’insa ya gauce.. Ya saka hannu a hankali ya zare shades d’in yana mai sauk’e idanunsa k’asa dan ganin abinda ta jefesa dashi.. A hankali ya duk’a ya d’auka yana juyawa, bai ce ma kowa k’ala ba Sai d’age suit pocket d’insa da yai ya saka ciki.. Ya gyara zaman suit d’insa had’ida maida glasses d’insa kafin ya k’arasa k’ofar gidan ba tareda yabi takan su Sabeera da Babanta dake k’ok’arin janyota tana b’oyewa bayan mahaifiyarta Assad na k’ok’arin janye Baban Sabeeran.

Hayaniyar da Umma ta jiyo daga waje ya sanyata fitowa bayan taga shigewar Sadiya d’aki a guje Ta maida k’ofa ta rufe..
Kana ganin yanda Umman Sadiya ta fito a birkice zaka fahimci suna cikin tsananin tashin hankali ne, dan ba’a jimaba Tabawa ta tafi da yarjejeniyar sati mai zuwa za’a mata kashin kud’ad’en mutane ‘yan group d’inta na online business d’inta..

Umma tana fitowa Baban Sabeera ya soma nunata yana fad’in “Yallab’ai gata nan, wannan itace mahaifiyarta.. Duk wani barikanci da tara maza Ita take koya mata, wannan mata mak’otaka da irinsu masifa ne.. Ka ganta nan..”

Mu’azzam ne ya katsesa da fad’in “Kana iya Barin mu muyi aikinmu Alhaji..”

Baban Sabeera ya jinjina kai yace “Amma nima Yallab’ai zan iya shigar dasu k’ara sabida Auren d’iyarsu da suka saka a k’ofar gidana ba tareda sanina ba.. Ina zaman zamana ‘Yansanda suka kawo min sammaci..”

Assad ya d’anyi gyaran murya ya dubi Sabeera dake mak’ale jikin Mamanta tana hawaye yace “Ki daina tsoro kinji, tambayarki kawai zamuyi..”

Sabeera tai saurin jinjina kai still tana hawaye..

Sketch d’in ya warware ya nuna mata yace “Kinsan wannan mutumin..?”

Tai K’uri tana kallo, ta kuma d’ago kai ta dubi Assad kafin Ta dubi Umma dake tsaye gefe tayi zuru zuru..

Duban yanda Sabeera take kallo Assad yayi kafin yace “Saurayin k’awarki ce da take zuwa gidanku dashi zance. Am I right..?”

Ta jinjina masa kai a hankali kafin tace “K’warai Sagir ne..”

Jin Ta ambaci Sagir yasa Umma matsowa tana duban sketch d’in..
Umma ta shiga tafe hannaye tana salallami tana fad’in “Wannan Bawan Allah shi ya jefa mu a ukun da muke ciki.. Rankaidade dan Allah ina zamu samu Sagir yazo ya sanar damu abinda d’iyarmu tai masa ya mata wannan wulak’anci da cin kashi..”

Assad ya jinjina kai yace “Bisa ga dukkan alamu kece mahaifiyar yarinyar da Sagir zai aura..?”

Tai saurin jinjina masa kai tana jin hawaye na zuwa mata..

Jinjina kai Assad ma yai kafin ya dubi Alhaji Isyaku da iyalansa yace “Alhaji mun gode K’warai kuna iya tafiya daga nan..”

Alhaji Iskayaku yace “Alhamdulillahi.! Muna iya tafiya koh..?”

Wannan karon Mu’azzam ne yai magana “Kuna iya tafiya, amma kaman yanda muka fad’a maka idan Ta kuma kamawa mu nemeku zamu nemeku, muna kuma fatan ku sake bamu goyon baya da had’in kai..”

Alhaji Iskayu ya jinjina kai yace “In sha Allahu Inspector.. Mun barku lafiya..” Ya k’arashe yana mai duban Sabeera
“Ke kuma shige mu tafi..” Tana matsan hawaye ta shige Assad ya d’anyi kaman zaibi bayansu ganin yanda mahaifin nata ke k’ok’arin janyota, d’an girgiza kai kurum yai ya dawo da baya yanda Mu’azzam ya tsare Umma da tambayoyi..

Mu’azzam yaci gaba da fad’in “Ina mahaifin ‘yarki yake..?”

Umma Ta girgiza kai tace “Ya fita tin safe..”

Ya jinjina kai a hankali kafin yace “Toh zamu gayyaci d’iyarki zuwa ofishinmu domin gudanar da bincike had’ida amsa mana wasu tambayoyi..”

Umma ta shiga salati tana fad’in “Na shiga uku ni Uwani.. Sadiya wane irin mutumi kika kwaso mana..Tinda nake ni ban tab’a zuwa police station ba.. Rankaidad’e wllhi bamu San mutumin nan ba, kuma kaman yanda na fad’a maka ba’ayi auren ba ya gudu.. Muma nan nemansa muke..”

“Zaki iya shiga ki fito mana da d’iyarki domin ta amsa mana wasu tambayoyi..” Ya fad’i babu walwala tamkar ba hawaye yake hangowa fuskar Uwani ba...
Jiki a sanyaye Umma ta shiga kiran Sadiya..

Har lokacin Sadiya tana kulle a d’aki, tana jin shigowar Umma tace “Umma Sun tafi ne..?”

Umma tace “Ki fito magana sukazo dashi akan Sagir..”

Ai Babu shiri Sadiya ta bud’e k’ofa ta fito tana fad’in “Umma mai ya sami Sagir.. An gansa ne.? Ina yake.. Ya dawo daga US d’in koh.. Ai dama ni na sani Sagir yana sona bazai tab’a watsa mana k’asa a ido ba.. Saidai ‘yan bak’in ciki su mutu.. Tabawa kuma harda abinda yafi kud’inta za’a biyata.. Event kuma Eagle square ma ya mana kad’an..”

Fizgota da Uwani tai ne ya sanyata had’iye sauran zancen nata.. Ta shiga janyota tana fad’in “Shige muje kafin Babanki ya dawo ya tadda ‘yansanda k’ofar gidansa..”
Chapter 11 · 0% Book details