Sashe 163
Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Gaba d’aya suka jiyo suna dubansa murmushi dama fuskokinsu lokaci guda Mu’azzam ya k’arasa tsakiyan ‘Yanuwan mahaifin nasa ya rungumesu hawaye guda d’aya na gangaro masa. Idan ka gansu a yananyin dole su baka tausayi.
Uncle Salman ya kuma rik’on gafaran Mu’azzam kan irin abubuwan da yaita yi masa a baya.
Ana haka Assad ya k’araso yana d’an sadda kai, ya gaida Daddy da Uncle Salman kafin suka nufi cikin gidan suna tattaunawa yanda suka bar Mu’azzam da Assad nan waje suma suna nasu tattaunawar.
Assad ya furzar da huci kad’an yace “Bazai yuwu ai releasing Musaddiq yau ba, dole Sai ya kai gobe.. Tare da Barr Ameer muke amma bamu k’araso nan tare ba..”
Mu’azzam ya jinjina kai a hankali kafin yana mai furta ”Thank you Assad.. Na gode da kokari.”
Murmusawa kawai Assad yai ba tareda yace komai ba, yasan idan shine a position d’in Mu’azzam zai masa abinda yafi wanda shi yake masa a yanzu.
Nan sukaci gaba da tattaunawa suna jinjina ta’addancin Hajara da yanda tai incriminating yaranta har guda biyu cikin case d’in.
Mu’azzam ya jinjina kai yace “Safeenah was telling the truth.. Iyakacin gaskiyarta ta fad’i gameda case d’in haka ma Musaddiq.. Amfani dasu kawai Mommy tai ta buga wasanta..”
Assad ya jinjina kai yana mai ci gaba da furta “Kasan na kasa yarda Umman Sadiya da Mamy are sisters.. Allah mai iko.. Allah buwayi gagara misali..” Ya d’anyi fasali kafin yaci gaba da fad’in “Wait.. Tsaya.. Munje muna binciken mutuwar Ikram... Kwatsam muka tadda Sadiya wacce Mommy ta tura Sagir ya nemi aurenta.. Abokina ya aureta da sunan auren mission domin ya cimma burinsa na gano makashin ‘yaruwarsa.. Soyayya mai tsabta ya shiga tsakani.. Tafiya yayi tafiya gaskiya yana bayyana kwatsam Sai ya fahimci cewa matarsa ‘yaruwarsa ce d’iyar ’yaruwar mahaifiyarsa da suka rabu Shekaru da dama.. Kai wann al’amari gwanin dad’i yake.”
Mu’azzam ya murmusa kad’an ba tareda yace komai ba. Assad naci gaba da da jinjina lamarin. Can ya sinkayo muryar Mu’azzam d’in yana fad’in “The mysterious word BAT is still the key to everything... Kuma shine source na faruwan komai.. Mahaifina ya rubuta kalmar a jikin yarjejeniya sabida Black African Team dake rubuce jikin coin d’in... Amma sai yai amfani da nasa tunanin yace da Uncle Salman kalmar yana nufin Bet Agreement Transaction ne..” Ya d’an murmusa kad’an kafin yaci gaba da fad’in “Who would’ve ever thought wann BAT d’in da muketa nema takarda ne da Mommy Ta ari Sunansa ta yafa.”
Assad ya d’an girgiza kai kad’an shima yana nazari da tunanin abubuwan da suka ci karo dasu tun farà case d’in.
“It’s over now.. Everything has come to an end.. Babu abinda zamuce sai Alhamdulillah.. Jaja yana rufe, Danger ma yana rufe sann Mommy ma za’a tsareta... The game is finally over.. And the mission has been accomplished.!” Mu’azzam ya k’arashe yana duban wani b’angaren daban.
Assad ya daidaita tsayuwarsa yana duban Mu’azzam d’in, lokaci guda ya k’ame had’ida sara masa “Congratulations Chief Inspector Mu’azzam Gamji.. Bazan iya jira ka amshi k’arin girma da d’inbin lambobin yabo da suke jiranka ba sakamakon kaiwa k’arahen case d’in nan da kai.”
Da mamaki Mu’azzam ke dubansa kafin ya girgiza kai yace “Meye haka kakeyi.. Kai komai sai ka saka shiririta. Koda yake idan baka saka ba ai baka cika Assad ba.” Ya k’arashe yana mai d’an girgiza kai kad’an.
Assad ya dara kad’an yana fad’in “Ni zan wuce, sai munyi magana..”
Ya mik’o masa hannu sukai masabaha Mu’azzam na fad’in “Ai gwara dai ka tafi kam kafin kai wani shirmen.”
Assad ya kuma murmusawa yana fad’in “Da Allah ka isar min da gaisuwa wajen Mamy kafin na k’araso.”
Da kai kawai Mu’azzam ya amsa masa kafin ya wuce.
Mu’azzam ya nufo cikin gidan yanda ya hangi Inne tsaye jikin window tana dubansa, shima d’in dubanta yake amma fuskarsa a matuk’ar tsume, tasan bazai wuce kan labarin da ta bayar na gameda abinda ta aikata ba. Tana gani Mu’azzam ya d’auke kansa yai shigewarsa. Jikin Inne duk Sai ya kuma mutuwa. Har ga Allah batasan da wasu idanu zata dubi ahalinta ba. Gaba d’ayansu nauyinsu takeji dan gani take kaman itace ummulhaba’isin shiga dik wani tashin hankalinsu.
A parlorn Mu’azzam ya tarar dasu Daddy sunyi carko carko suna duban Mommy dake kwance wajen fuskarta duk ya dauje kaman an d’auraye da ruwan rini. Shigowarsa ma ya shigo ne ya tattare Mommy su wuce headquarters amma Sai ya tarar magana ma da k’yar take tana rok’on Aunty Nuratu tai mata rai kar a rufeta a kurkuku..
Mu’azzam ya danna mata wani kallo kafin yace “Ce miki akai baa jinya a can.. Ana tuhumanki da laifuka bila adadi dan haka you are under arrest.”
Mommy Ta soma rarrafawa Ta kamo k’afar Aunty Nuratu dake tsaye gefen Daddy “Nuratu ki ceceni.. Naci albarkacin yarana kar ki bari a kamani.. Ki ceceni Nuratu.. Na san kina zuciya mai kyau Nuratu.. Kimin rai kiji tausayina..!” Ta k’arashe tana jijjiga k’afafun Aunty Nuratu cikin kuka.
Daddy ya katseta da fad’in “Ya isa haka Hajara. Ke kanki Kinsan ko Mu’azzam bai kasance Jami’in tsaro ba dole hukuma Su kameki kuma Su hukuntaki ki daina wann wasan kwaikwayon naki haka..”
Ganin Mommy kwance k’asa tana jijjiga k’afafunta tana kuka duk sai yasa zuciyarta ya kuma yin rauni.
Mu’azzam ya kula da raunin mahaifiyarsa da tausayinta, cikin sauri ya katse Mommy da fad’in “Ki daina wann maganar dan kinsan ba mai yuwa bane.. You must face the law sabida court case ne akanki.”
Cikin kuka Mommy ke kuma duk’awa gaban Aunty Nuratu tana fad’in “Shin Maiyasa ni bazaa yafe mun ba idan za’a yafewa Inne.. Idan Inne taci albarkacin ahali nima naci albarkacin nawa yaran.. Dan Allah Marwan ka saka baki Ko dan yaranmu.”
Da tsananin mamaki Mu’azzam ke duban Mommy jin ta yanda ta b’ullo. Ba don mahaifiyarsa ba yayi imani da Allah baida lokacin tsayawa sauraron sunbatun Mommy.
Daddy ya katseta da fad’in “Kar ki kuskura kiyi wann batun Hajara, dole ki fuskanci hukuma kuma dole ki biya abinda kika aikata.”
Mommy ta kuma fashewa da kuka tana fad’in “Kuji tausayina.. Nima uwan ce kaman yanda Inne take uwa a cikin ahalin nan..”
“Ki mana shiru ki daina danganta laifinki da kuskuren Inne..!” Daddy ya katseta.
Nan ya kuma fashewa da kuka tana fad’in “Sabida ni banida gata shiyasa bazaa min rangwame kaman yanda akaima Inne ba.. Ai laifi baifi laifi ba, laifi iri guda muka aikata mun salwantar da rayuka.. Idan kuma za’a kamani Tabbas za’a kama Inne.. Kai Mu’azzam ai kai jami’in tsaro ne kasan ba k’aramin laifi kakarka ta aikata ba harda jariri ta salwantar. Idan har ka cika jami’in tsaro adali kana danna mun handcuff itama ka danna mata kaga sai a saka mu cell d’aya da Inne, tana gadon sama Ina na k’asa, idan kuma ba haka ba dukanku azzalumai ne masu son kai..!”
Idanun Mu’azzam suka kad’a sukai ja yana duban Mommy da tsananin mamakin k’arfin hali irin nata. Wato rashin kunyar Mommy yakai yanda yakai.
Daidai lokacin Kiki ta shigo taga mahaifiyarta duk’e tana kamo k’afafun Aunty Nuratu tana fad’in Ai mata rai.
A guje Kiki ta k’araso tana kuka ta rungume Mommy tana fad’in “Mommy mai ya sameki.. Mommy Addah Feenah zataji sauk’i bazaki tafi ki barmu ba right.” Kiki da batada masaniya kan laifukan da mahaifiyarta ta aikata ta fad’I haka.
Mommy Ta rungumeta tana kuka, yayinda Kiki Ta d’ago tana duban Daddy “Daddy Mommy can’t leave us right.. Please Daddy.. Adda Feenah needs Mommy now..!”
Gaba d’aya sai tausayin yarinyar ya rufesu. Aunty Nuratu ta k’araso tana k’ok’arin janye Kiki.. Mommy ta rik’e d’iyarta tsam tana fad’in “Kiki kar ki barni kulleni zasuyi a prison.. Kiki stay with your Mom kinji..”
Cikin tsananin b’acin rai Daddy ya katse Ta da fad’in “Ya isheki haka Hajara.. Kar ki maida mutane mahaukata.!” Ya janyo Kiki yana fad’in “Muje Karimatu.. Zo mu tafi.”
Kiki tana waigowa take fad’in “Daddy Ya Mu’azzam zai kulle Mommy.. Daddy la basa hak’uri.. Daddy please Mommy can’t go to jail sabida abinda taiwa Adda Feenah.. Dan Allah ka bawa Ya Mu’azzam hak’uri.”
Daddy yana fitar da Kiki Mommy taci gaba da magiya tana rok’on Aunty Nuratu.
Mu’azzam zai magana Aunty Nuratu ta dakatar dashi da fad’in “Ya isa haka Mu’azzam.”
Da tsananin mamaki yake duban mahaifiyarsa, lokaci guda yake girgiza kai yana fad’in “Mamy please don’t.. Matar nan fah ‘Yartadda ce, gasunk’umar ‘Yartadda wacce authority ke nemanta.. Mamy case d’in nan tin daga sama ne ba wai a hannuna bane kawai.. Hukuma nemanta suke itada D’anuwanta Muttaqa.. Mamy please kar ki ce zaki dakatar dani.”
Dubansa mahaifiyar tasa tai tausayinsa duk ya cikata.. Lokaci guda ta janyo hannunsa suka fice. Sai juyowa yake yana aikawa Mommy mugun kallo.. Har lokacin duk’e wajen take tana hawaye.
Zaune sukai a waiting kansa na k’asa yana furzar fuci a hankali, yana jinjina K’arfin hali irin na Mommy, waima cewa take idan za’a tafi da Ita sai an tafi da Inne.