← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 175

Sashe 32

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta jinjina masa kai a hankali kafin tai masa sallama. Yana nan tsaye yana dubanta tana tafiya tana cilla Jakarta. Murmushi saman fuskarsa. Lokaci guda itama take juyowa tana sakar masa murmushi, har saida Musaddiq yaga shigewarta kafin ya nufi masallacin dake nan cikin Gidan Gonar da zummar gabatar da nasa sallar dan already sun sallame.

**

A can cikin gida kaw Inne ce ta tsaresu tanai masu d’add’aya dan babu wanda yasan da zuwansu sai ganinsu akai kaman sauk’an aradu dikda cewa Meema tace da sanin Mommy da Daddy suka zo.

Inne tai k’wafa tana mai kuma furta “Idan da sanin iyayenku kuka taho ke Safeenah mijinki yasan kina tafe ne.. Ko kuma saran da kuka d’auko kenan, shi yazo ke kin biyosa.. Zai shigo ne ya sameni, dukkanku Ina dai dai daku nikam..”

Meema ta mik’e tana fad’in “Nidai na gaji d’aki nake son zuwa na huta.. And I’m starving already.. Hindu..! Hindu.. An gyara mana d’akin..”

Inne da Ta saki baki tana duban Meema dak’uwa tai mata tana fad’in “Kinci gidanku.. Baza’a gyara maku d’akin ba, idan baku da hannaye kuna iya kwanciya a haka.” Ta dubi Hindu da k’arasowarta kenan tana fad’in “Ummilo tana can tana gyarawa..”
Lokaci guda Inne tace kije kice mata ta bar d’akin mata ne, zasu gyara da kansu..”

Baki sake Meema ke dubanta kaman zata kurma ihu “Haba Inne Haba Inne.. Dan Allah fah we just arrived here, and I’m pretty tired wllhi Ko hanuna ban iya d’agawa.. Please mana Inne, I can’t do any house chores wllhi..”

“Ni kike ce ma kin gaji baki iya ba idan ban tashi na jefaki cikin turmi na dakaki ba, sangartacciyar banza a rasa da wa za’a mun takwara sai ke.. Matsa min a nan kafin na tashi na daddakeki.. Kuna mata kuce komai sai an maku saikace ba gidan wani zaku ba.. Ba dai kunzo nan ba, toh har girki sai kunyi ni bazan lamunci goyon sangarci da iyayenku sukai maku ba.. Kun sanni sarai ba a nan zakuyi iya shegenku ba..”

Meema ta shige tana bud’e murya kaman mai kuka “Wayyo Wayyo na shiga uku.. Wllhi this is all your fault Adda Feenah.. I shouldn’t have followed you here.. Wayyo Allah na..” Haka Meema ta dingayi kaman wacce ake bugunta, ta shige tana tafiya tana jefa k’afafu tana fad’in dik Safeena ce ta jawo mata.

Ana haka Musaddiq yai sallama ya shigo.

Kallo d’aya yaima Inne ya fahimci a d’ane take yau ko ba’ace ba su Safeenah suka kunnata.. Ya nufo parlorn yanda Inne ke zaune tana girgiza k’afafu.

Musaddiq da ya hango Safeenah zaune da bak’in fuska tana yatsina fuska dariya ya soma yana fad’in “OMG! Who do we have here.. Hey yaushe kikazo..? And what’s that on face..?” Ya k’arashe yana kuma k’unshe dariyarsa.

Harara Feenah ta watsa masa “Kaga babu ruwanka dani.. Mind your own business..”

Musaddiq ya kame bakinsa yana fad’in “Allah baki hak’uri Dodanniya..”

“What..? Mai kace.. What did you just call me..?”

“Abinda kunnenki yaji..” Ya bata amsa kai tsaye.

“Inne Kinga kice ya fita hark’ata..” Safeenah tace tana kuma turo baki.

“Ke rufewa mutane baki ank’i ace d’in..” Sakaryar banza.

Musaddiq ya k’unshe dariyarsa yana k’ok’arin k’arasowa kusan Inne dan yanzu har wani shiri ne na musamman ya shiga tsakanin Musaddiq da Innen tinda ya fara watsar da rayuwarsa ta baya.

“Gidado na Zo ka shige abinka kaji fita sha’aninta..” Inne tace tana duban Musaddiq d’in.

“Toh Inne na..” Ya fad’i yana gwalo ma Safeenah had’ida kashe mata idanu.

K’wafa Safeenah tai ba tareda tace komai ba dan harga Allah alla alla take Masoyinta Mu’azzam ya shigo Ta gansa.
Aiko bata ida tinanin ba ta hangosa yana tafe ya nufo k’ofar parlorn, yana sanye cikin k’anan kaya dark blue polo shirt da faded pants. Idanunsa na kan wayar salularsa dake hannunsa, hasken k’wan wutan manya manyan wutan lank’arki da suka k’awata gaban gidan sun haske masa fuska tarau, gani tai kaman ma zuwansa nan ya k’ara haske da kyau ne babu damuwar CID akansa babu komai.. Ta saki murmushi a hankali dan tama mance da abinda ke fuskarta. Idanunta akansa tana sakin murmushi har yai sallama ya shigo parlorn.
, idanunta naga masoyinta wanda shima ita yake duba cikeda mamakin bak’in dake fuskarta dan sam bai fahimci wacece ke zaune wajen ba har saida ta bud’e murya tace “My Halal.!”

“Safeenah.!” Ya furta a hankali yana mai kuma shigowa parlorn mamaki fal fuskarsa, har lokacin idanunsa na kanta. Bama mamakin bak’in fuskar nata yake ba, mamaki yake yaushe Safeenah tazo.

Inne ce takatsesu da fad’in “Yauwa k’araso dama kai nake jira.. Kazo ka sanar dani idan kai ka bata lasisin Ta dinga gantali saman kwalta da sararin samaniya Ita ba tsuntsuwa ba, tana a matsayin Amarya wacce ko tarewa batai ba.. Ai Iyayen naku ma basuda hankali da suka zuba maku idanu haka.. Toh ni bazan lamunci wannan asaranci ba.. Kafin Dangi su fara k’anan magana tinda shi Marwan ya zuba maku idanu kuyi yanda kuke so da rayuwarku ni zan masu abinda suka kasa.. Zaku tare a nan. Idan yaso a miki sabon jere a nan..Tinda abin naku ya zama haka sai a gyara maku d’aya b’angaren ki tare a nan.” Ta k’arashe tana duban Safeenah da ta saki baki tana jin Innen Wai zasu tare a nan.

Safeenah zatai magana Inne tace “Rufe mun baki.. Ba shawarinki nake nema ba.. Bazaku bar mun abun fad’i a dangi ba.. Na riga na gama magana.” Ta k’arashe tana mai mik’ewa da zummar barin parlorn.
Sai kuma ta juyo ta dubi Safeenah tace “Ke kuma Ki tashi kije ki wanke wann bak’ar fuskar taki kafin Ki razani mijin naki da ita..”

Sai sannan Safeenah ta tina da bak’in dake fuskarta, tai saurin Kai hannu zata tab’a sai kuma ta kasa ta shiga muryar kuka tana fad’in “Oh my gosh.. Eww.. I can’t touch it, It stinks.. My Halal please help me get rid of it.. Wllhi I can’t touch it..” Yanda take da fuska da hannu Kai kace kashi aka watsa mata.

“Meye a fuskarki..?” Ya tambaya yana dubanta.

“I don’t know.. Wllhi wata mahaukaciya ce ta watsa min.. Inne tace wai magani take bawa Mamy.. My Halal wllhi Mahaukaciya ce ka koreta.. I don’t trust her around Mamy..” Ta k’arashe tana kuma yatsina fuska da hannu.

“Biyoni..” Ya fad’i yana mik’ewa tsaye. Babu musu Safeenah ta biyo bayansa..

D’akinsa suka shige ya maida k’ofan ya rufe. Ya nuna mata hanyar bathroom “Shige muje..”

Ta d’ago tana dubansa da mamaki sai kuma ta shige sim sim.. Mu’azzam ya take mata baya.

Washbowl suka nufa yace ta saka fuskarta, tanaji ya d’auko sabulu yana wanke mata.

Yana ida wanke mata ta d’ago fuskarta tana duban mirror saidai to her surprise Mu’azzam ta hanga ta cikin mirror d’in yana rage tufafin jikinsa.. K’akk’arfan suffarsa da yasha training irin na Force ya bayyana. Ta zaro ido a tsorace had’ida juyowa tana dubansa, tana ganin ya soma nufota Ta soma k’ok’arin komawa da baya..
Fincikota yai ta fad’o jikinsa hakan yai daidai da tab’a makunnin shower dake kansu ai kuwa ruwa ya soma zubowa kansu. Tana jin hannunsa saman zip d’in rigarta yana k’ok’arin zugewa.. Har lokacin ta kasa janye idanunta daga duban fuskarsa da ruwa ya wanke tas Wanda sam babu walwala..

Zuciyar Safeenah yaci gaba da tsinkewa.. Cikin sauri kaman wacce aka zabura, tamkar wacce ta tina wani abu tai saurin rik’e hannun nasa ta hanasa tana mai girgiza masa kai ga idanunta da sukai rau rau.

Wani irin duba yake mata, lokaci guda ya kamo hab’arta had’ida d’ago kanta kad’an ruwan na zubo mata a fuska. Tsoro da tsananin firgici ya hango saman fuskar tata wanda dik a nasa tinanin tsoran kasancewa dashi take a matsayinta na budurwa sabuwar aure da bata tab’a sanin wani d’a namiji ba..

“Why.? Ba abinda kike so bane..? Ba abinda kike bibiyata sabida shi ba kenan.. Well na shirya baki yanzu a nan idan har zaki k’yaleni na gama binciken mutuwar ‘yaruwata da nake in peace ba tareda Kinyi causing mun distraction ba.. Fine zan baki sai ki daina bibiyata har na natsu na ida binciken da nake..”

Lokaci guda hawaye ya soma zarya saman fuskar Feenah.. Ta shiga girgiza kai hawaye na gangaro mata “No ni dai ba haka bane.. Dama dama kawai I was missing you ne.. That’s why I followed you here..” Tai maganar hawaye gauraye da ruwa saman fuskrta.

Ya tsareta da idanu yanda take shivering.. Janyota jikinsa ya kuma dikda tsananin rawa da jikin nata keyi, saitin kunnenta yake rad’a mata “Really..? Did you miss me that much..” Ya fad’i yana mata wasu salo irin nasa wanda tuni sun kashe mata jiki.. Lokaci guda yaci gaba da furta “Dama baki shirya ba kiketa bibiyata..?” Tai saurin girgiza masa kai tana hawaye.. Zatai magana ya rufe bakinta da nasa. K’arar wayarsa dake cikin aljihun wandonsa ya dawo da hankulansu.. Yai saurin zaro wayar yana duba mai kira, ba kowa bane face abokinsa kuma colleague d’insa Assad. Yai saurin kashe ruwan kafin ya shiga janyo Feenah yana fad’in “Zo ki fice..”

Ta dubesa da mamaki yanda yake fuzgota saikace ba shine ya nuna San kasancewa da Ita yanzu yanzu ba “Mu’azzam a haka zan fice.. Duba fah ka gani from head to toe a jik’e nake fah..”

Har saida suka k’araso k’ofa kafin ya turata ya janyo k’ofar ya rufe ba tareda yace mata komai ba.. Baki sake Feenah ke dubansa da tsananin mamaki.

Yana rufe k’ofar ya d’aga wayar Assad “Hey Officer, hope all is well with you..” Mu’azzam yace yana mai tsane jikinsa da towel.
Saida suka gaisa kafin Mu’azzam d’in ke tambayarsa “How are things at the CID.. Mai da mai kukai discovering so far..?”
Chapter 32 · 0% Book details