Sashe 138
Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Sannu da zuwa, Uncle.” Mu’azzam ya fad’i a tak’aice gudun kar Inne ta d’ago wani abu. Uncle Salman ya amsa masa kaman ko yaushe fuska ba yabo.
Mu’azzam na rik’e da hannun Inne guda suka nufi cikin gidan tana fad’in “Yo mi wad’annan masu zanzaron suke k’ofar gidan.. Gida ya koma saikace Barikin ‘Yansanda “Inji komai lafiya a gidan.. Ina Baban naku Marwan yake..?” A jere take kan jefowa Mu’azzam tanbayoyi kafin ya amsa guda Ta jefo masa wani. Nan suka had’u da Musaddiq a hanyar shiga cikin gidan.
Shi kaw Uncle Salman yana biye dasu ne kawai amma jikinsa ya basa wani babban Al’amari na faruwa tinda yaga irin duban da Mu’azzam yai masa.
Mommy kaw daga window take lek’ensu, zuciyarta ya tsananta tsinkewa Ganin harda Inne Uncle Salman ya taho.. Wato dai Mu’azzam ya shirya ma wann ranan. Ya rantse Sai ya tsige gaskiya.. Aiko wann gaskiya da yake k’ok’arin tsagewa ba komai zai haifar masa ba face tarwatsewarsa da rushewar ahalinsa. Ta murmusa kad’an tana jinjina kai kafin Ta furta a fili “Yayi kyau.. Da kyau Mu’azzam Gamji, da alama dai abinda zaka tono shi zai ajalin wann jarabebbiyar tsohuwar Wato Kakarka Inne..” Ta kuma murmusawa kafin Ta isa jikin wardrobe d’inta sai waige waige take. A hankali ta bud’e ta tura hannunta ta ciro wani k’aramin akwati ta, ta k’arasa ta danna ma d’akin nata makulli kafin ta dawo saman gado ta zauna, bud’e akwatin tai wani hoto ya bayyana, hoton wani mutumi ne matashi. Ta ciro hoton tana murmushi “Bansan meye alak’arka da ahalin Gamji ba, amma saidai na tsinci wann hoto naka ne a cikin Takardan yarjejeniyar BAT.. Yarjejeniyar da Abubakar Gamji ya rubuta.. Na shafe tsawon shekaru Ina ajiye da hotonka, nayi k’udirin sai na nemo ko Wanene kai.. Na kuma cika k’udirana na samoka, sann na kawar da kai dan mai yuwa kaima kanada alak’a da Ahalin Gamji ne.. Kaine mahaifin Yarinyar da Mu’azzam ya aura wacce na tura Sagir domin ya nemi aurenta, aka samu akasi Mu’azzam ya zamto mijin yarinyar.. Ban tsara haka ba, watak’ila da Mu’azzam bai auri yarinyar ba da yanzu baka mutu ba.. Ka mutu bansan mecece alak’arka da Abubakar Gamji ba da har ya saka hotonka cikin takardan Yarjejeniyar.. A ina ya sanka..? A ina ya samo hotonka..? Toh kodai kaima kanada Gadon mahaifinsu ne.? Kodai kaima D’an ahalinsu ne..? Ya akai Abubakar Gamji ya samu hotonka..? Toh amma kai d’in ba daga yankinsu ka fito ba.. Bakada wata alak’a na jini tsakaninka da Gamji family a iyaka binciken da nayi..!” Ta d’anyi fasali kafin ta mik’e tsaye still tana rik’e da hoton, lokaci guda taci gaba da furta “Menene alak’arka da ahalin Gamji..?” Take zuciyarta ta bata amsa da fad’in ‘Sanin alak’arsa da ahalin baida wani amfani a halin yanzu tinda ya riga ya mutu an kawar da nasa babin idan ma nada alak’a da dukiyar ne bazai tab’a cimmata ba tinda ya mutu kuma ga dukkan alamun bayan mahaifin Mu’azzam ke kad’ai ce kika San mutumin nada alak’a da ahalin..’ Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali kafin ta juya bayan hoton Wanda aka rubuta haruffan BAT a bayan hoton..
“Shin Yarjejeniyar nada alak’a da kai ne..?!” Ta tambayi kanta a fili kafin ta sauk’e ajiyan zuciya ta maida hoton cikin akwatin ta rufe.
Knocking da taji a k’ofarta ne ya sanyata saurin saita kanta, Ta marairaice fuska tai kalan tausayi kafin Ta k’arasa tabud’e k’ofar.
Kiki ce mai knocking d’in, Mommy Ta dubeta kad’an kafin ta sakar mata murmushi. Kiki ta isa ta rungume mahaifiyar tata cikeda tausayawa.
“Mommy haka zakiyita zama a d’aki ke kad’ai, Mommy abinda ya faru ya riga ya faru, dama tun can Allah ya k’addara cikin Addah Safeenah ba mai zama bane.. Mommy ki daina kulle kanki a d’aki Kina kuka musamman yanzu da Inne tazo zata fahimci wani abu.”
Mommy Ta murmusa kad’an kafin ta shafi kan Kiki tace “Karima kunyarku nakeji gaba d’aya, abinda nai ma Safeenah ban kyauta ba yanzu gashi Safeenah tana asibitin mahaukata dik ta dalilin abinda nai mata..” Wani kukan ya kuma kufce mata.
Kiki ta fad’a jikin Mommy suna kukan tare. Da k’yar kukan Mommy ya tsagaita har saida Kiki taita lallashinta tana bata baki.
Kiki ta goge fuskarta tace “Inne tazo tana sashenta, idan bazaki iya zuwa gaisheta ke kad’anki ba muje ni zan rakaki Mommy.”
Mommy ta dubi Kiki ta murmusa tana mai kuma goge hawayenta kafin tace “Ba komai Kiki, zan iya zuwa.. Amma saidai bansan da wane ido zan dubi Kakarku ba, gani nake kaman zata fahimci na cire cikin Safeenah.. Kuma idan ta tambayi Ina Safeenah take mai zance mata..?”
Kiki tai sauri tace “Ce mata zakiyi tana gidanta da Ya Mu’azzam..”
Mommy ta murmusa kad’an kafin tace “Idan Mu’azzam yace bai maidata ba fah..?”
Kiki ta d’anyi shiru sai kuma ta girgiza kai tace “Mommy nasan Ya Mu’azzam idan har yaji kince Safeenah na can gidansa bazai musa ba, bazai ce komai ma Inne ba.. Mommy ba kece kika haifi Ya Mu’azzam ba amma na tabbata shid’in uwa ya d’aukeki ke kisan da haka..”
Mommy ta jinjina kai a hanakali kafin tace “Shiyasa nake jin ciwon abinda nai masa, sharrin zuciya batada kyau.. Wllhi ina nadaman cire cikin Safeenah da nai akan idanun Mu’azzam dik sabida burin fansar abinda ya aikata min.. Allah sarki gashi da yake yaron kirki ne bai makani a kotu ba balle ya kulleni..”
Kiki ta jinjina kai tace “Shiyasa nace miki har yanzu kallon uwa yake miki Mommy, da ace ya daina ganin girmanki da tuni ya kulleki a cell.. Yanzu ma ko kince Addah Feenah ta koma gidansa ne bazai ce komai ba nasan bazai so Inne tasan ya abinda ya samu cikin Addah Safeenah ba balle har Ta fahimci asibitin mahaukata aka kaita.”
Mommy ta jinjina kai tace “Haka ne Karima.. Muje ko Allah shi miki albarka.”
Kiki ta murmusa kafin ta d’an rungume hannun Mommy guda b’angaren jikinta kafin suka nufi sashen Inne da aka gina mata a cikin gidan.
Suna isowa suka tadda kaf d’insu suna Parlorn, Daddy Uncle Salman Mu’azzam harma da Musaddiq. Inne na zaune daga tsakiya saman kujerarta da akasarin lokuta take zama bisa.
Duba d’aya zakaiwa Mommy ka fahimci jikinta a matuk’ar sanyaye yake. Ta saci duban Daddy da Mu’azzam taga irin kallon da suke aikata mata musamman Daddy. Amma abinka da gogaggiya sai tai k’ok’arin saita kanta kaman dai babu abinda ke wakana.. Nan ta shiga gaida Inne tana mata sannu da zuwa cikeda ladabi kaman dai yanda ta saba harda cewa batasan tana tafe ba da an girka mata abincin da tafi so.
Inne tace “Yanzu ma bai b’aci ba Hajara Kinsan ni bana son abincin nan naku wanda banda ganye babu komai.. Mutum yaita tura ganye zallarsa a cikinsa saikace tsutsa, Yo ganye ya wuce zogale ai ba ganye bane..”
Mommy sai murmusawa take kanta a duk’e tana fad’in “Babu komai Inne yanzu za’a shiga kitchen a girka miki naki..” Ta k’arashe maganar tana mai tambayar Inne “Ya kuka baro can gidan.. Ya Aunty Nuratu kuma da jiki..?”
Da tsananin mamaki Mu’azzam ke duban Mommy yana jinjina makirci irin nata, matar da ta turata a bata maganin ‘yanrufa ido shine yanzu take tambayar k’arfin jikinta. Bai ma iya sauraron amsar da Inne ta bawa Mommy ba banda kallon mamaki da yake binta dashi baya iya komai, baya fata Inne ta fahimci wani abu sabida kar hankalinta ya tashi, a dole yai k’ok’arin saita kansa. Muryar Inne ya sinkayo tana tambayar Mommy ina Safeenah taga kowa bata ganta ba.
Mommy ta d’ago ta dubi Daddy dake aika mata mugun kallo kafin ta d’an saci duban Mu’azzam wanda shima d’in da gani kasan k’ok’arin danne kansa kurum yake. Ta d’an gyara zaman mayafinta tana murmushi kafin tace “Ai Safeenah ta koma gidanta Inne.. Tana can d’akinta..”
Shaye da tsananin mamaki Mu’azzam ke duban Mommy yanzu kam. Wai Safeenah ta koma d’akinta.
Inne ta dubesa tace “Kai Modibbo haka akai ashe..?”
Mu’azzam ya rasa ta cewa, ya d’an jinjina kansa kad’an yana fad’in “Eh.. Haka ne Inne..” Ya k’arashe yana mai aikawa Mommy mugun kallo.
Inne tace “Yayi.. Yayi kyau, hakan ai yafi.. Mutuwar aure sai dole balle ma ace auren zumunci irin wann.. Allah ya kad’e fitina ya zaunar dasu lafiya ita da abokiyar zaman nata..”
Mommy har na murmushi take amsawa da “Ameen Inne..”
Mu’azzam kasa jure zaman parlorn yai dan sosai zuciyarsa ke masa zafi musamman idan ya dubi Mommy da Uncle Salman. Hakan yasa yai ficewarsa daga parlorn cikin sauri..
**
A b’angaren Safeenah kaw tana can Mental Facility yanda take samun kula daga k’wararrun likitoci.
Haka Safeenah tai kusan a daren da ya gabata tana bugun k’ofa tana fad’in Su k’yaleta ta fice ita ba mahaukaciya bace da hankalinta. Yanzu ma hakance ta kasance sai dukan k’ofa take tana fad’in suzo su fitar da ita zataje wajen mijinta da D’anta suna jiranta.
A haka Ta gaji Ta kwanta saman gadonta hawaye na gangaro mata. Wai ita Safeenah Gamji ce aka kawota asibtin mahaukata aka ajiyeta, kenan da gaske mahaukaciya suka d’auketa bacin ita da hankalinta kuma ta tabbata cikinta na nan bai fice ba, zata haifo D’anta kuma Mu’azzam zai mai da ita.. Har abada bazata tab’a barin Mu’azzam ma wata ba shid’in nata ne.. Haliliyarta ce ita kad’anta. Hawaye mai zafi ya gangaro daga cikin idanunta.
Tana jin alamun shigowar nurse cikin d’akinta tai likimo kaman dai bacci take.
Nurse d’in ta aje tray d’in magunguna da Ta shigo dashi ta shiga k’ok’arin had’a allurar da zatai ma Safeenah.
Safeenah ta kuma kannare idanunta kad’an tana duban Nurse d’in daketa k’ok’arin had’a ruwan allurar. Aiko tana ida had’a allurar ta nufo Safeenah zata mata allurar Safeenah tai kukan kura ta janyo k’arfen lank’aye drip dake gefenta ta rabza ma nurse d’in akai.. Nurse d’in tana fad’uwa Safeenah ta d’auki allurar ta danna mata.. Sauri sauri ta soma k’ok’arin sauya tufafin malamar jinyar da nata.
Tsaf Safeenah ta shirya cikin tufafin Malaman jinyar asibiti ta rufe fuskarta da mask, ta inayo nurse d’in da k’yar ta azata saman gadon bayan ta sauya tufafinsu, lokaci guda ta silale ta fita daga asibitin.