← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 175

Sashe 52

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsareta yai da idanu yana dubanta, kafin ya murmusa kad’an yace “And what makes you think zan barki ki tafi..?
Ya d’an jnjina kai yana dubanta lokaci guda ya had’e rai yaci gaba da furta “Bayan juran duka tsaurin idonki na ‘Yan tasha da kika saba. Mu’azzam Gamji cooks for the very first time in his life.. He feeds a low life like you with his hand.. Bayan mahaifiyarsa bai tab’a ciyar da wata mace da hannayensa ba.. Kina tunanin mission mai sauk’i kikeyi da zai jure ya miki Duka wad’ann abubuwan..?”

Ya jinjina kai kafin yaci gaba da fad’in “Nayi duka wad’ann ne don na tabbata kin tsaya cikin k’oshin lafiya har dai na ida mission d’ina... Idan kina mafarkin zan barki ki tafi ba tareda nayi accomplishing mission d’ina ba you’re so mistaken.. You are staying right here until the mission is finally accomplished..!” Yana ida fad’in haka ya fice ya janyo k’ofar.

Girgiza kai take tana furta “No please.. Dan Allah kayi hak’uri..!”

Ta k’araso a guje tana tura k’ofar amma ta kasa.. Kuka Ta soma tana rok’onsa ya bud’e mata Ta fice amma a banza.. Ta nufo balcony a guje tana k’ok’arin tura k’ofar amma saidai shima a rufe ta jisa..
Cikin sanyin jiki ta dawo da baya Ta zube nan saman gadon tana kuka mai tab’a zuciya.. Tinawa da tai ko sallar azahar da la’asar da tuni an soma kiraye kiraye batai ba ya sanyata Saurin mik’ewa ta nufi bathroom d’in da zummar d’auro alwala tana hawaye.
Nan tazo ta tada sallah ta soma kai kukanta ga Sarkin da Babu kamansa.

**

Kasancewar isowar yamma lis sukai yasa Aunty Shema basu nufi gidan Safeenar da niyyan gyare gyare da kakkab’e k’ura ba. Dan dama tace da zaran Sun iso a yau d’in zasu d’iba ma’aikata aje a share gidan a gyara tas. Mommy ma tace su bari kawai gobe idan Allah yakai rai da safe sai suje su gyara gidan idan yaso zuwa yamma sai akai Safeenah. Hakan kaw akai basu je gidan a ranan ba saima bada hankali da ‘yan gyare gyare da ake ma Safeenar wanda Aunty Shema’u tai tsayin daka tana fad’in sai Safeenah ta rikita angonta. Safeenah kaw jin hakan sosai yai mata dad’i.. Mommy ma taji dad’in hakan sanin irin abubuwan da d’iyarta tai kafin aure idan mijinta ya tunk’areta a haka sunada babban matsala. (Su Mommy kenan, sun mance ba’ayi ma Allah wayo.. Maganin bari dai shine kar a fara.. Allah ka tsaremu daga fad’awa aikin danasani.. Ameen)

Safeenah Amarya Dikda ciwon dake k’afarta dan da crutches ma take tafiyar hakan bai hanata zumud’in shirye shiryen tafiya gidan mijin nata ba. Meema Ta dubeta tace “Waini Addah Feenah ina Ya Mu’azzam ne.. Tinda muka dawo ko ganin k’yallin motarsa banyi ba balle nayi tunanin ganinsa cikin gidan nan..? Toh kodai baisan kin dawo bane.?”

Safeenah ta murmusa tana kuma kurb’an tsimin da Aunty Shemau Ta tilasta mata shanyesa tas a daren tace “I want to surprise him.. Kema Kinsan yanayin aikinsa k’ila sai dare ki gansa ya dawo.. I’ll wait for him in his room saidai kawai ya shigo ya ganni.” Ta wani k’arashe tana girgiza k’afarta mai lafiyar.

Meema Ta tab’e baki kad’an tace “Toh amma idan kika taresa a d’akinsa ya b’ata miki shirin da akai na tafiya gidanki fah.. Ko so kike komai ya faru a nan gidan tin ba’aje gidan naki ba..?”

Harara Ta aikawa Meema kafin tace “Na sake miki da yawa Meema.. Yaushe har muka fara irin wannan tad’in dake..?”

Meema tace “Ahap na yaushe kuma Adda Feenah.. Ai bakida aminiyar da ta wuceni dan haka dole nasan komai..” Ta k’arashe tana kashe mata ido guda.

Suka tintsire da dariya a tare Safeenah na fad’in “Of course my sister is my sidekick.. Zanyi missing shishiginki da gulmarki Meema.. Daga gobe I won’t be living here anymore..! Come here give your sister a hug..” Ta k’arashe tana turo baki gaba kaman zatai kuka.

Cikin sauri Meema ma ta k’arasa ta rungumeta tana fad’in “I’ll miss you too Addah Feenah.. And this your Savage Husband shi zai ke hanani zuwa gidanki.”

Safeenah ta dara kad’an tace “And I love him just like that.”

“I know..!” Meema tace tana d’an tab’e baki.

Lokaci guda Ta k’arada “And I hope he doesn’t surprise you instead..!”

Daidai lokacin glass cup d’in dake hannun Safeenah ya fad’I k’asa ya tarwatse tsimin dake ciki ya zube. Jin abinda Meema ke fad’i mata.

Meema ta zaro ido waje tana kame baki “Oh no.! This is a sign Addah Feenah... It’s a bad omen..! Something terrible is going to happen..!” Tai maganar tana kuma firfito da idanu waje cikin k’ok’arin razana Safeenar.

Jifa mata pillow Safeenah tai tana fad’in “Shame on you Meema.. Fice min a d’aki I need positive vibes..” Ta k’arashe tana k’ok’arin kwad’a mata Sandar crutches d’in nata..

Meema ta fice tana dariya lokaci guda take furta “I’ll miss you Addah Feenah.. I love you..”

Daga nan yanda Feenah ke zaune take fad’i da k’arfi itama “And I hate you little sis.. Ki turo wata cikin maids d’in nan Ta gyara nan..”
**

Har safiya Safeenah bataga Mu’azzam a gidan ba.. Mamaki ya cikata, nan Ta yanke shawarin tambayar Mommy dan ko jiya da daren Ta kirasa yafi abinda yafi amma bai d’aga ba.. Ta fara tinanin ko wani abu ne ya faru dashi sanin irin had’arin dake tattareda aikinsa.

Saidai tana k’ok’arin shiga d’akin Mommy Ta soma sinkayo tattaunawar Mommyn da Aunty Shemau.

Cak Safeenah Ta tsaya tana jin Wai tinda Mu’azzam ya dawo bai kwana a gidan.. Idan ba sharholiyarsa yake waje ba mai zaike hanasa kwanan gida matarsa bata gari.. Sau d’aya ma suka had’u da Mommyn.

Zuciyarta ne yai wani irin yankewa amma sai ta bawa kanta k’warin gwiwa da cewa aikinsa aikin Al’umma ne zai iya kasancewa a ko Ina any moment. Mijinta bazai tab’a cutar da ita ba.. Mata basu gabansa, sannan shima baida lokacinsu.. Bazata saka ma zuciyarta wannan damuwar ba musamman yanzu da ta samu Mu’azzam yake nuna damuwarsa akanta.

Da wannan tinanin ta juyo ba tareda ta shige d’akin Mommy ba. Saidai gaba d’aya jikinta a mace ne.. B’angare mafi girma cikin zuciyarta yafi karkata ga zancen da taji Mommy nayi.. Take taji zuciyarta na son amincewa Mu’azzam ha’intarta yake. Da gaske sharholiyarsa yake a nan.. Toh amma tambayar da su waye yake sharholiyar tasa..? Take taji zuciyarta na bata amsa da matan banza mana.. Ji tai kaman sandar taimak ma tafiyar nata ya gaza d’auakrta.

Tana tafe kaman mutum mutumi K’annenta Meema da Kiki dake haurowa saman suka hangota, Kiki sanye da sch uniform d’inta da safiyace da alama makaranta zata.. Meema kuma sanye da tracksuit da alama morning exercise ta fito.

Sukai carko carko suna dubanta.

Meema tai saurin zare earpiece d’in dake mak’ale kunnenta Ta k’araso Ta dafata tana fad’in “Addah Feenah lafiya..?”

SameenaAleeyou📚

*GIDAN ARO*

*29*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Feenah Ta dubi Meema data tsareta da idanu, sai kuma ta girgiza kai tace “I don’t know.. Ban Sani ba Meema.. I.. I’m feeling restless. Ina son sanin wani hali Mu’azzam ke ciki.”

Meema ta d’an rausayar da idanu tace “Idan dan wannan ne kar ki wani dami kanki, Kinsan halinsa ya iya bada mamaki yanzu zaki iya ganinsa a cikin gidan nan kaman babu wani abinda ya faru.. Com’on chill, ki daina damuwa Ya Mu’azzam fah ba yaro bane balle ace za’a saka masa ido dan bai dawo gida ba.. Magidanci dashi mutum da gidansa, na tabbata yana can gidan naku Kinsan ba’a sona zuba kaya a gida sannan a barshi haka nan babu kowa.. Balle ma kin sansa kinsan halinsa, Kinsan yada yake abubuwansa ba tareda ya saka kowa ciki ba ko ya fad’a ma wani.. Bari ma yanzu zamuje da Aunty Shemau wanka kawai zanyi zamu kai wasu kayayyakin.. And you’ll see zamu tadda Ya Mu’azzam can yana jiran isowarki..” Ta k’arashe cikin k’ok’arin kwantar da hankalin ‘yaruwar tata.

Feenah ta murmusa tana Ware idanu “Ok akwai wasu frames da zan baki a tafi dasu please..”

“Tau amaryar Yaya..” Meema tace tana kashe mata idanu.

Sauri sauri Meema ta wuce tai wanka tana fad’ima Kiki ta jirata su had’a hanya tinda lesson ne take zuwa ba latti zatai ba.

Hakan kuwa akai, breakfast ma sama sama Meema taci sai shirya sauran kayayyanki da za’a tafima Safeenah dasu take.

Aunty Shemau tace ta fara gaba tabi Kiki tinda Mu’azzam na gidan ba sai an tsaya neman key ba. Ita zata Zo da wasu kayan daga baya, yanzun akwai wani shirin da zataima Safeenah ne na musamman shisa.

Gidan Amarya mai Farin jini kowa San zuwa yake ko yaya ne. Kiki ta dubi Aunty Shemau tace “Aunty nima zuwa Zanyi..”

Aunty Shemau tace “Toh makarantar fah..?”

“Aunty dan Allah zanje ai bazanyi latti ba, lesson ne kawai kuma sai 10am ma a fara, idan yaso daga can na wuce.”
Kiki tace tana turo baki gaba.

Aunty Shemau tace “Toh shikenan sai ku tafi da Spices d’in nan..” Tai maganar tana mik’owa Kiki basket na spices da za’a Kai gidan Safeenar. Kiki ta saki baki tana duban tulin spices d’in.. Ta saci kallon Safeenah dake zaune parlo k’afafu mike tana shafa wayarta. Kwantar da murya tai tana kare bakinta kad’an alamun bataso Safeenah Ta jita “Chabd’in.! Aunty ma waye za’a kai spices d’in nan.. Toh wllhi saidai su gaji suyi K’warai dan dai Addah Feenah ba girki take ba..”
Muryar Safeenah suka sinkayo tana fad’in “I heard what you said Baby sis.. And yes Cooking is not my thing, Allah yasa akwai eateries a garin zamu saya..”

Kiki ta dubi Aunty Shemau tana tab’e baki alamun kinji dai da kunnenki..

Aunty Shemau tace “Shige maza kuje k’yaleni da Addarku zamuyi magana.”

Kiki ta d’au books d’inta da hannu guda d’aya hannun basket d’in spices d’in ne.
Nan suka fice driver ya tuk’asu.

**

A can gidan Mu’azzam kaw shirinsa ya ida cikin suit d’insa ruwan toka dan yau yake reporting back to work bayan dakatar dashi da akai na d’an lokaci.
Chapter 52 · 0% Book details