Sashe 168
Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin zuban hawaye mutumin ya k’araso gareta lokaci guda yakai hannayensa dake rawa yana shafa fuskarta wanda tuni itama d’in hawaye sun soma fitowa daga cikin dara daran fararen k’wayan idanunta zuwa fuskarta mai d’an duhu wanda bai cika haske ba.
Fuskar matarsa Hauwa da kamanninta yake hangowa tattareda yarinyar.. Cikin rawar murya irinta mai kuka yake furta “Kece.. Kece Jidda ta.. Ta rabani dake tsawon shekaru.. Ta rabani da gudan jinina..!” Lokaci guda ya rungumeta yana kuka sosai yana furta shine mahaifinta.
Ai nan Ajidde ma taji kukanta na k’aruwa tama rasa gane meke faruwa.
Mu’azzam ya girgiza kai a hankali yana duban wann kayan al’ajabin. Ko 24hr basuyi ba da suka gano cewa Sadiya ‘yaruwar mahaifiyarsace sai ga wani batu ma wani Ajidde ‘Yaruwaruwar Mahaifinsa ne.. Ikon Allah.. Yaci gaba da girgiza kansa kad’a yana furtawa a hankali “Unbelievable..!This is crazy..” Ahali dai sai dad’a bunk’asa yake cikin k’ank’anin lokaci kuma da mutanen da tuni sun sansu saidai basu San cewa sud’in ahali bane.
Mamaki ya cika Mommy jin Wai wann yarinyar d’iyar mai maganin wacce Shemau ta sanar da ita Musaddiq soyayya yake da ita Wai d’iyar D’anuwansu Marwan ne da aka fice da cikinsa.. Eh lallai ikon Allah.. Ita duk bama wann ba babban damuwarta shine shegiyar yarinyar ashe itace ta b’ata mata shiri take amso Ayoyin Allah wa Nuratu tana watsar da maganin Kyallu. Wann yarinya itace babbar ‘Yariskar da ta cuceta ta Karya mata shiri.. A a tamanin Mommy tai tsalle ta cakumo Ajidde tana fad’in “Shegiya matsiyaciyar yarinya ashe kece makarin.. Ashe kece kika Karya mun shiri..! Alhunguma.. Wllhi idan Ina numfashi Musaddiq bazai aureki ba.. Yau sai na kasheki..!” Baban Ajidde yana janye d’iyarsa yayinda Daddy yaita maza yana janye Mommy lokaci guda yake sanar da Mu’azzam maza ya kira Sergeant d’in nan ta fice da Mommy. Mu’azzam ya jinjina kai kafin ya kirawo sergeants mata guda biyun suka shigo suna janye Mommy..
Mommy kururuwa take tana fad’in babu yanda zata tafi.. Ta dubi Daddy tace “Marwan ni ce fah Hajara Matarka.. Da aurenka fah akaina har yanzu baka furta mun kalmar saki ba nasan kana sona Marwan sharrin Nuratu ne.”
Daddy yace “Bayan duk abubuwan da kika aikata har jira kike na furta miki kalmar saki Hajara.? Ai idan kunada sauran tunani ke da kanki yaci ace min sanar da kanki Ke sakakkiya.. Bari dai na maimaita miki Hajara ni Marwan Gamji babu sauran aure tsakaninmu na sakeki Hajara.!” Haba nan fah Mommy ta kuma sakin wani azababben k’ara tana kururwa. Sai tsalle take tana k’ok’arin zillewa daga hannun sergente Tina kaman wata birin wasa. Haka nan aka janye Mommy aka fice da ita.
Sauk’in abin Kiki tana can sashen Inne tareda Sadiya dama Mu’azzam yace Tai keeping Kikin Company tin sanda za’a tafi da Safeenah mental facility. Hakan yasa abin bai faru Kan idon yarinyar ba.
Inne ta janyo Ajidde jikinta tana hawaye, lokaci guda take furta “Allah sarki shiyasa mana tin sanda Ajidde ta soma zuwa gidan naji nastuwa tattare da ita dukda shiririta irin nata, kowa bai amince da maganinta ba Sai ni na amince da Ita da maganinta ashe gida Ajidde ta dawo..” Ta d’ago tana duban Baban Ajidde lokaci guda take furta “Ka yafeni D’an nan.. Ka yafe ni mai sunan watan albarka.”
Suka murmusa gaba d’aya harda Baban Ajidde
“Na yafe ki tuntuni Hajiya..”
Inne tai karaf tace “Kirani kaman yanda ‘Yanuwanka ke kirana Inne..”
Ya kuma murmusawa yace “Toh Inne..”
Ajidde na hawaye take duban mahaifinta, Ta girgiza kai tana fad’in “Maiyasa ka barni hannun Azzalumar matar nan wanda taita azabtar dani Ta d’orani a turba maras kyau.. Turban sata da rufa ido harda bokanci..”
Ya kuma janyota yana share mata hawayenta “Komai yazo k’arshe Jidda kuma Kyallu bazata sake cutar da kowa ba da izinin Allah.. Rufa idonta da bokancinta ya k’are domin kuwa tana hannun hukuma an kamata.. Allah ya kawar mana da masu d’abi’a irin na Kyallu dan suna nan cikin Al’umma suna fakewa da sunan suna bada magani suna kashe mutane da bokancinsu da rufa idonsu.. Allah ya dad’a wayar da kan Al’umma su fahimci cewa masu magani irinsu Kyallu basu isa su warka da kai ba ko su cire maka cuta.. Allah shi yake yi, shi yake d’aura cuta yake kuma yayewa a lokacin da yaso.”
Gaba d’aya suka amsa da Ameen Daddy yace Ai sai suyi addu’a su kuma gode wa Ubangiji da wann baiwa da yaiwa ahalinsu.. Cikin k’ank’anin lokaci ahalin ya kuma bunk’asa ya dunk’ule waje guda.
Akai addu’o’i had’ida Godiya wa Ubangiji.
Alhaji Ramadan mahaifin Ajidde yace zai tafi da d’iyarsa, nan su Daddy suka rok’esa da ya hak’ura ya d’an k’ara lokaci kafin yakai Ajidde taga Iayayen mahaifiyarta.. Sann Ahalinsa gaba d’aya suna nan shima ya kamata a tafi Fufore tare dashi yaga gida da dangi.. Haka dai sukaita dannarsa har ya hak’ura zai k’ara kwanaki. Abu dai sai san Barka.
A b’angaren Mu’azzam kaw bai ita sanar da Musaddiq komai da bakinsa ba sai Daddy ne ya sanar dashi komai a tsanake. Allah sarki Zo kaga tashin hankali wajen Musaddiq sanda yaji muggan abubuwan da mahaifiyarsa ta aikata. Haka ya dinga kuka yana fad’in bazai tab’a yafe wa Mommy ba.
Kafin ya baro headquarters d’in saida ya nemi ganin Mommy.. Mommy tana kuka take fad’in kar ya yarda dasu sharri sukai mata..
Kuka Musaddiq ma yake yana girgiza kai yana duban mahaifiyar tasa cikin wane irin yanayi “You are not human Mommy.. How could you..?” Yaci gaba da hawaye yana furta “You made me believe that I raped Ikram.. You made me believe that I was a criminal.. How could you Mommy.. Ta yaya zaki aikata laifuka irin haka.. Ta yaya kike bacci da dare Mommy.. Ta yaya kike rayuwa cikin ahalin da kika zalunta irin haka.. Mommy bansan da mai zan dangantaki ba.. Amma ki sani zan rok’ar miki gafara sabida ke mahaifiyata ce.. But hakan ba wai yana nufin zan tab’a yafe miki abinda kika aikatawa Ikram bane.. Zan tafi kuma bazaki sake ganina ba.. Bazan sake ziyartarki ba.. Allah ya yafe miki Mommy..!” Daga haka yasa kai ya fice yana hawaye.
Mommy tana kiransa tana rok’onsa ya dawo inaa ko tsayawa baiyi ba. Sai kukansa dake k’arewa.
**
Tinda ya dawo gidan ya rufe kansa a d’aki baison ganin kowa kuma bai son magana ma kowa. Juyin duniya anyi Musaddiq yak’i kula kowa yak’i cin abinci sai kuka yake a d’aki.
Aunty Nuratu ta umarci Ajidde da ta kai masa abincin wann karon, jikin Ajidden ma duk a sanyaye take knocking a k’ofar d’akin nasa.. Kaman bazai bud’e ba amma Sai ya sinkayo muryarta cikin yanayi mai kama da kuka itama d’in take fad’in “Idan bazaka bud’e ba shikenan.. Bazan tak’uraka ba.. Amma ka sani nima zan tafi nabi mahaifina kuma bazaka sake ganina ba..”
Musaddiq yai shiru kaman bazai amsa ba Sai kuma ya mik’e ya k’araso ya bud’e mata.
Kallo guda yai mata ya koma cikin d’akin saman abin sallah dake shimfid’e wajen ya kuma zama. Da alama sallar yai..
Ta k’arasa ta ajiye masa abincin har lokacin baice komai ba.
Taisayinsu gaba d’aya ya kullub’eta. A hankali Ta goge hawayen da suka zubo mata kafin ta soma fad’in “Dukanmu abubuwa da zuciya bazata iya d’auka ba sun faru damu.. Dukkanmu Muna cikin lokaci ne na gwaji.. Amma kasan menene..? Allah baya tab’a d’aura ma zuciya abinda bazata iya d’auka ba.. Shin kana tunani kai d’aya ne aka jarabceka.. Shin kai ka mance ka girma gaban iyayenka guda biyu..! Shin ka mance ka taso cikin soyayyan ‘Yanuwan da iyayenka harma da Kakarka..? Shin kasan rad’ad’in ka taso cikin babu sai ka neman ma kanka..? Shin an tab’a d’aureka a turke ka kwana d’aki guda da dabba..? Baka San wann ba.. Baka San zafin kai tashin uk’uba gaban matar da babu dangi iya balle na Baba tsakaninku ba.. Baka San rad’ad’in ka taso gaban matar da babu Allah cikin zuciyarta sai shirka da bokanci da rufa ido.. Kasan cewa ni haka na taso.. Hannun wann azzalumar matar wanda taso d’aurani a turba maras kyau.. Na kwashe shekaru Ina ma Inna Kyallu Bauta da burin daidai da rana guda zata saka mun albarka.. Amma bata tab’a ba sabida ba Ita ta haifeni ba sann sana’ar da ta d’aurani akai ba mai albarkan bane.. Shin duk kai kasan zafin abubuwan da na lissafo maka..? Baka sansu ba.. Sai yanzu da kaji abubuwan da mahaifiyarka ta aikata Wanda duk ta b’oye maka su ba don komai ba sai dan soyyayar da take maka koda ace ta kasance mai laifi.. Ta zabi ta b’oye maka duk abubuwan da take aikatawa sabida ka kasance cikin Farin ciki.. Ni a nawa b’angaren ba haka bane.. Kuma ba wai Ina fad’a maka bane dan nuna rashin godiya da jarabawan da Ubangijina yaso jarabtana dashi.. A’a ina fad’a maka ne domin ka fahimci rayuwa da yanda kowa take zuwa masa da k’alubale daban daban.”
Ta soma Murmusawa hawaye naci gaba da gangaro mata “Daga k’arshe Allah ya cika Ahalinka da alkhairi koda ace babu Mommy.. Sai ka dubi wani rahamar da yai maka ka godewa Allah..”
Tinda ta soma magana hawaye ke gangaro masa. Yarinyar da ya d’auka shashasa mai sakasa dariya da nishad’i yau gashi kalamanta sun zamto masu taushi da tausasa zuciyarsa had’i da basa natsuwa na musamman. Lokaci guda yanajin tausayin rayuwarta da abubuwan da Ta fuskanta a matsayinta na d’iya mace na kuma dabaibaye zuciyarsa.
Muryarta ya sinkayo wann karon a yanayin da Ta saba masa magana “Kaga wllhi ko kaci abincin nan ko na bud’e tagar nan na rabza ma wancan Dansanda mai tsaron gate d’in kwanon a kansa harda abincin ciki.. Kuma kasan tsaf zan aika..” Ta k’arashe tana k’ok’arin mik’ewa had’ida d’aukan bowl d’in da pepper soup d’in Ke ciki..
“My Goodness..!What is she doing..?” Musaddiq ya furta a hankali yana mai k’ok’arin mik’ewa.
Tuni Ajidde ta soma bud’e glass.. Ai a d’ari ya rik’o bowl d’in yana fad’in “Ke Crazy dove have you gone mad.. Mai kike yi..?”
“Ah Toh ka tsaya kasha kallo kaikam.. Kuma kasan Allah yanda yasha malu d’in nan tau zata sauk’a a k’eyarsa.. A d’ari zai arce ina gaya maka..” Tana fad’i tana dariya.