← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 142 OF 175

Sashe 142

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yusuf ya murmusa kad’an kafin yace “You’ll always be the same Mu’azzam Gamji.. And I have faith in you.. Nasan zaka kamasu kuma zaka kawo k’arshen ta’addamcinsu.”

Wann karon Mik’ewa tsaye Mu’azzam yai hannayensa dafe da table d’in yake furta “Did you call us here to be telling us stories.. Are you fucking with us now..!” Ya k’arashe yana mai cakumo Yusuf d’in.

Assad yai k’ok’arin k’watan Yusuf yana fad’i wa Mu’azzam subi komai a sannu har Su sami abinda suke so.

Yusuf ya murmusa kad’an yace “Banga laifinka ba.. Komai kamun kayi daidai kuma na cancanci hakan.. Kuje location d’in da zan sanar daku inada tabbacin zaku iske Danger harma da Jaja a wann location d’in.. Zaku kama Jaja redhanded domin kuwa yau rana ce da suke had’uwa a wann location d’in suna gudanar da cocaine business d’insu.”

“Cocaine business.?” Assad ya nanata.

Yusuf ya jinjina kai yace “K’warai kuwa, Danger ba k’aramin D’anta’adda bane sann bai dogara fa wann shagon nasa na saida karan sigari ba. Hasalima yayi shagon ne dan ya b’adda kama.. Amma Danger gasunk’imin D’antadda ne wanda yake hark’an cocaine da drugs. Ya samu d’aurin gindi ne daga wajen manyan ‘Yansanda Irinsu Chief Jaja domin kuwa tare suke gudanar da alk’allarsu.. Nima Jaja ne yai introducing d’ina zuwaga ta’addancinsu.. Kuma bani kad’ai ba a different departments sunada masu yi masu aiki a cikin NPF domin su samu sauk’in gudanar da ayyukan ta’addancinsu na saida k’waya da hodar ibilis harma da sauran ta’addanci da suka shafi garkuwa da mutane da sauransu. Zan baku sunayen duk wanda nasan suna aiki k’ark’ashin Jaja..”

Mu’azzam ya jinjina kai kafin yace “Yayi.. Bamu location d’in..”

Yusuf ya sanar dasu location d’in Assad na jotting down.

Suna gama tattare bayanan Yusuf suka Sa kai zasu fice sai kuma Mu’azzam ya dawo da baya yace “And about BAT..? What do you know about BAT..?”

Yusuf ya girgiza kai yace “Suna kiransa da BAT.. Boss At the Top.. Amma babu wanda ya tab’a ganin BAT cikinmu yaran da muke aiki ma Jaja da kuma Danger.. Iyakacin abinda na sani kenan kuma Iyakacin abinda zan ita sanar daku kenan.”
Assad ya jinjina kai yace “Mun gode Yusuf, wann information da ka bamu ba k’aramin taimakon mu zai ba.”

Yusuf ya jinjina kai yace “Ina fata nai abu mai kyau daga k’arshe koda zasu hallak’ani.. This is the least I can do bayan cin aman k’asa da kuma abokai na da nayi.. Akwai ire irensu Jaja da dama a cikin Police Force wanda zanyi fatan asirinsu yaci gaba da tonuwa.. Allah ya kawo mana k’arshen ta’addanci ya kuma cire mana gurb’atattu daga cikinmu.”

Assad ya amsa da Ameen yana mai sakar masa murmushi kafin sukai sallama yabi bayan Mu’azzam da tuni ya fice.

Basu nemi backup ba Su kad’ai suka nufi location d’in Mu’azzam na zabga gudu saman kwalta Fatansa ya capke Jaja da kuma Danger once and for all.

Daga nesa sukai parking suka shirya harsashi cikin bindigoginsu, Assad yana duban Mu’azzam dake yin komai da zuci da zuci, ya d’an dafa hannunsa yace “Lets call for backup.”

Mu’azzam ya girgiza kai yace “Tukuna Assad.. Sai na damk’o wuyan Jaja da Danger cikin hannayena..!”

Yana ida fad’in haka yai tsalle ya diro daga cikin motar rik’eda bindigarsa ya soma kwanton b’auna ya nufi bulging d’in.. Assad ma ya nufi d’aya b’angaren yana sand’a.

Ta window suke lek’e yanda suka hango Jaja ya bud’e doguwar akwati na kud’i yana Washe baki ga Danger zaune gefensa yana busa hodar ibilis, wasu matasa da ko shakka babu yaransu ne sai aikin juye cocaine d’in suke cikin leda.

A hankali Mu’azzam ya furta “Danger.! Daga k’arshe mun sake had’uwa.!”

Yana maganar yana jinjina kai lokaci guda ya daki glass d’in window d’in da k’afafunsa suka tarwatse. Haba nan fa su Danger suka ciro bindigogi suka soma batakashi tsakaninsu dasu Mu’azzam.

Su Mu’azzam sukai nasaran harbe yaran Danger yayi a Danger da Chief Jaja suka soma k’ok’arin gudu. Chief Jaja na jan tunbinsa da k’yar yana gudu yana furta “I cant be seen here.. I can’t get caught.. I can’t go to jail..”

Mu’azzam yai tsalle ya haye garu yana furta “Jajaaa!”

Chief ya juyo ya kaima Mu’azzam harbi Mu’azzam ya kauce, yaci gaba da binsa a guje, Chief sai haki yake ya kasa gudu. Wani irin tsalle Mu’azzam yai ya naushi Fuskar Chief wanda saida ya kai Chief k’asa. A daidai lokacin kuma sautin siren na motocin ‘Yansanda ya karad’e wajen.

Mu’azzam yana huci yake duban Jaja, ya kuma kai masa naushi da k’afa, yana jinjina kai yake duban Chief dake duk’e k’asa kaman b’era “I told you so Chief Jaja.. Idan B’era na Yawo Mage tana Yawo wata rana zasu had’e.. You’ll rot in jail you miserable criminal.. B’eran banza.!” Ya k’arashe yana mai kuma kai masa naushi.

Daidai lokacin sauran ‘Yansanda suka k’araso Mu’azzam ya jefa masu Jaja yana fad’in “Cuff him..” Suka amsa cikeda jinjinawa suna masu sara masa.

Can ya hangi bayan Assad dake chasing Danger a guje.

Bazai so wann dama ta kufce masa ba wanda zai iya zama damarsa Ta k’amshe kenan idan yana so ya capke Danger.

A guje yabi bayansu suna gudu yana binsu, cikin wane irin sauti yake furta “Dangerrr..!”

Danger ya kuma waigowa yana kai masu harbi kwatsam harsashin ya samu Mu’azzam. Cak Assad ya tsaya ya daina bin bayan Danger ya juyo yana duban Abokinsa da harsashi ya hudasa.

SameenaAleeyou📚

*GIDAN ARO*

*72*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Mu’azzam ya dafe kafad’arsa yanda Danger ya huda da harsashi bai fasa k’ok’arin bin Danger ba yana fad’i da Assad cewa kar ya damu dashi abu mafi mahimmanci shine su kama Danger kuma a raye yake son Danger. Hakan yasa sukaci gaba da chasing Danger sauran ‘Yansandan na tayasu. Saidai ana haka Danger ya malmalo nakiya ya jefa masu wanda hakan ya tarwastasu suka watse sanda Nakiyar Ta fashe. A haka Danger ya samu ya escaping.

Wasu daga cikin ‘Yansandan suka sami rauni wasu kuma suka rasa rayukansu ma, Assad da Mu’azzam suna daga cikin Wanda nakiyar Danger ta raunanasu amma saidai Sun tsira da rayukansu cikin k’udirar Ubangiji.

Mu’azzam yai zaune gefe ana treating wound d’insa, sai murza hannunsa yake a hankali yana duban waje guda, ba zafin ciwon yake ji ba zafin kufce masa da Danger ya sake yi yake ji.. Ya rasa Danger wane irin D’an adam ne sai gashi kaman za’a kamasa Sai ya samu ya kufce.. Bashida babban brin da ya wuce ya capke Danger a halin yanzu.

Assad ya k’araso goshinsa rufe da bandage yanda ya sami nasa raunin yana tambayar Mu’azzam jikinsa.

Mu’azzam ya furzar da huci kad’an yana fad’in “Ya sake kufce mana.. Assad shin yaushe zamu kama Danger ne.?”

Assad ya d’an furzar da huci kad’an yace “Sannu a hankali zamu kamasa, Gashi mun kama babban yaronsa Jaja inada tabbacin shima zai shigo hannunmu ne nan gaba kad’an da izinin Allah. Mu k’arasa Headquarters.”

Mu’azzam ya d’anyi still kafin ya shiga jinjina kai a hankali yana furta “Zan kama ka.. Zan baka wahala kaman yanda ka bani wahala.!” Yana ida fad’in haka ya mik’e suka nufi yanda sauran abokan aikin masu suke.

**

A b’angaren Sadiya kuwa zaune tai jigum tana jin gabanta na fad’uwa lokaci zuwa lokaci, ga tinanin mijinta da ya addabeta.. Yau kusan kwanaki uku kenan bata sanyasa a idanunta ba kuma bai kirata ba.. Anya wann rayuwa.. Ta yaya za’a ce mijinta ya shafe yini da kwana bai nemi sanin ya take ba.. Toh kodai wani abu ne ya samesa.? Tambayar da ya kuma haifar mata da fad’uwan gaba, Sai kuma zuciyarta ta bata amsa da fad’in da ace wani abu ne ya samesa da kinji dan kuwa da Assad ya fad’i hakan.. Toh Assad d’inma Ina suka ganshi.? Ta d’an lumshe idanunta a hankali tana addu’an Allah ya daidaita lamuranta.

Asheer dake zaune gefenta yana shan rake ya bud’i baki ya soma fad’in “Adda Sadiya Kinsan mai Abba yace ranan da muka fita tare har aka kad’esa..?”

Sadiya tai saurin bud’e lumsassun idanun nata tana duban D’anuwan nata dake shan rakensa hankali kwance. Tai saurin girgiza kai tana mai kuma duban Asheer d’in.

“A’a ban Sani ba.. Mai yace.?”

Asheer ya jinjina kai kad’an yace “Ya saya mana rake nida Habeeb bayan da muka fice daga gida.. Sai muka zauna gefen hanya muna shan raken.. Abba ya dafe kanmu yace Allah shi mana albarka.. Sai Habeeb yace masa harda Adda Sadiya.? Sai Abba ya dubi Habeeb yana murmushi sai kuma ya jinjina masa kai yace harda Addarku.. K’walla suka ciko idanun Abba ya goge.. Sai ya dafe kanmu nida Habeeb yace Iyalaina suna cikin jarabawa, banida shi Banida k’arfin sauk’e masu wann bashin dikda cewa su suka ciwo ma kawunansu.. Allah ka kawo masu mafita koda ban zamto wanda zai sauk’e masu wann bashin ba.. Allah kar bari iyalaina su tagayyara a bayana.. Allah ka zamto masu Katanga ka zama gatansu a doron k’asa...” Asheer yai aya yana duban Sadiya da hawayenta suka gaza tsagaitawa. Sai kuma yaci gaba da fad’in “Habeeb ya dubi Abba yace Abba ka yafewa Umma da Adda Sadiya.?” Ya kuma yin aya yana duban Sadiyar wanda kukanta ke k’aruwa.

Cikin muryar kuka take duban Asheer tana fad’in “Fad’a mun Asheer mai Abba yace..!”
Chapter 142 · 0% Book details