← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 175

Sashe 54

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaba d’aya gidan anyi carko carko babu mai iya zuwa kan Safeenah sabida buge buge da take ta famanyi.

Kuka take tana fad’in “Mommy wllhi sai na kasheta.. Whoever she is Sai nayi ajalinta.. Mommy mace ya d’auka yakai gidan aurena yana cin amanata da ita..? Mommy wllhi yau ko wacece ita sai tayi datasanin zuwanta duniya.. Sai ta tsinewa uwar data haifota duniya har ta d’aura ido kan mijina..!”

.. Ala dole Musaddiq ya rik’e Safeenah daketa faman buge buge tana hauka tana fad’in sai ta kashe Karuwar da Mu’azzam ya kai mata gida tin kafin ta tare.. Dan ma daga bacci yake hayaniyar ya tadashi.

Fad’i yake “Ke Feenah get your act together ki daina wa mutane wannan haukan..!”

Safeenah Ta fincike tana mai ci gaba da fad’in “Na rantse da Allah Mommy ko wacece ita sai tayi danasani.. Idan kuma ba haka ba wllhi Sunana ba Safeenah Gamji ba..!”

Mommy fad’i take ba ita kad’ai zaki kar ba harda shi babban minafikin Mu’azzam.. Bayan duk abinda na masa shida uwarsa a rayuwa babban butulcin da zai saka mana dashi kenan.. Bari Daddyn naku ya shigo yau sai muga bayan waye zai bi..!”

Cikin tsananin b’acin rai Musaddiq da aka barsa shi kad’ai tsakiyan mata ya daka masu tsawa gaba d’aya “That’s enough Mommy..! Bai kamata wad’ann yaran suzo Su fad’i magana ku d’auka ba Sai abi komai sannu a hankali a jira Mu’azzam yazo ba wai ku taru kuyita hauka ba..”

Katsesa Mommy tai cikin tsananin fushi “Kamin shiru kaima babban minafikin ne waya sani ko kana sane ma da abinda yake baka tab’a sanar da kowa ba.. Meema da Kiki ba k’Arya zasu masa ba.. Bak’in azzalumi maci amana.. Ni ko a labarai ban tab’a jin irin wannan cin amanar ba ka d’auki Karuwa ka tare da ita a cikin gidan matarka wacce ko tarewa batai ba.. Da kayan d’akin Safeenah ya tare da Karuwa sabida shi ya cika babban tantiri babu mai saka sa babu mai hanasa.”

Meema dake lab’e gefe tai tsulum tace “Mommy wllhi wllhi na rantse da Allah rungume da mace muka kamasa cikin gidan kuma harda police ya saka a gate babu mai shiga. Da muka tambayi Police d’in dake gate d’in ma ce mana yai Wai Oga yana Busy baiso a damesa..”

Musaddiq ya nufota a kufule ya kasheta da wani wawan mari “Ke waye sa’anki a nan zan b’abb’allaki na karerayaki naga k’arshen rashin kunyarki..”

Meema ta saki ihu tana kame fuskarta..

Mommy ta finciko Musaddiq tana fad’in “Kar ka sake dukar mun yarinya.. Gaskiya take fad’i.. Idan ma babu mai yarda da zancen Meema ai Kiki bazatayi k’arya ba tinda kowa ya mata shaida a gidan nan.. Kai kake rufa masa asiri waya sani ma ko tare kukeyi..”

Da tsananin mamaki kurum Musaddiq yake duban Mommy wacce Ta rufe idanu gaba d’aya ta yanda take shiga ba ta nan take fita ba.

Aunty Shemau tace “Toh Wai ni uban mi ake jira da baza’a tafi gidan Safeenar ba a fidda yarinyar ko a mik’ata ma hukumar ‘yansanda.”

Mommy tace “Kin mance shi shafeffe da mai d’in gadaransa kenan shi ga D’ansanda.. Maras mutunci butulu..! Wllhi yau ko Headquarters za’a d’aga sai anbi mun hakkin d’iyata.’”

Daidai nan Daddy ya shigo ana tsaka da hatsaniyar.

Safeenah ta nufi Daddy tana kuka cikin yanayin tausayi tana kuma d’ingile k’afarta mai ciwo yanda za’aji tausayinta sosai “Daddy mutuwa zanyi.. Zan mutu Daddy Mu’azzam ya cuceni yaci amanata Daddy.. Daddy karuwai yake kaiwa Gidana shiyasa yak’i na tare..”

“Safeenah..?” Daddy ya kira sunanta da mamaki kafin ya k’arada “ Mai kike fad’i haka.. Mai Kike fad’i kenan.. Lafiyarki.?” Daddy yace cikin d’an tsawatarwa.

Mommy tai karaf tace “Abinda kaji gaskiya ne.. D’an D’anuwanka D’an matarka azzalumi ne kuma maha’inci ne.. Gidan Safeenah da ko tarewa cikinsa batai ba yake d’iban karuwai yana kaiwa ba dole yace kar a kai masa Safeenah ba tinda yanada wad’anda zaike kaiwa.. Wllhi wllhi sai anbi ma d’iyata hakkinta.. Wllhi idan ta kama mu makasa a kotu ne zamu tafi.. K’aryar Kakin Dansanda yake..!”

“Ina Mu’azzam d’in..?” Daddy yace yana duban Safeenah.

“Yana can tare da ita Daddy.. Tare suka kwana a gidan Daddy kuma wllhi tare suke kwana.. Nasan wannan Police Woman d’in ce dama budurwarsa ce..”

Meema da zafin marin da aka mata ko d’aukuwa baiba ta kuma bud’e baki tace “Wllhi wannan watace daban ba police woman d’in bace..” Ta k’arashe maganar tana ci gaba da kukan marinta..

Musaddiq ya kuma yiwa kanta yana fad’in idan bata daina saka baki ana magana ba Sai ya karyata.

“Toh sannu makaryi sai ka karyata mu gani..!” Mommy ta katsesa da fad’in haka.

Musaddiq ya dubi Meema yace “Ke bar nan kafin na takaki..!”

Mommy Ta janyota tana fad’in “Babu yanda zataje ko kotu akaje akwai shaida kuma Meema ce shaida ehe..! Bazai yuwu na nik’a gari na tafi har Dubai naima Safeenah sayyan kayan d’aki wata ‘yar iska can Ta rigata kwana saman gadonta ba ehe..!”

Daddy ya girgiza kai yana duban Musaddiq “Kira mun D’anuwanka a waya..” Daddy yace yana duban Musaddiq d’in.

“Alright Daddy.” Musaddiq ya amsa kafin ya soma dialing layin Mu’azzam yana aikawa mutanen dake parlorn mugun kallo idan ka cire Daddy.

Aunty Shemau ta kamo Safeenah da k’yar ta zaunarta saman kujera tana fad’in ta zauna ta huta duba da yanayin ciwon dake k’afarta.

Ana haka Mu’azzam ya shigo yana takunsa cikin nastuwa kaman babu abindake faruwa.
Duk suka zuba masa idanu suna dubansa.

Wani zabura Safeenah tai tana mai kuma fashewa da wani irin kuka.

SameenaAleeyou📚

*GIDAN ARO*

*30*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Musaddiq ya girgiza kai kurum kafin ya fice daga parlorn gaba d’aya. Meema dake Ta faman sosa fuskarta yanda Musaddiq ya mareta satan kallan Mu’azzam tai Ai kaw nan taga kaman jefo mata razannan kallon nan nasa babu shiri ta nemi hanyar ficewa daga parlorn itama. Gani take kaman daga kanta zai fara tinda ita ta kawo rahoton. Batama San ko kallon yanda take baiba balle yasan tana parlorn. Tsaban tsoro ne da imagination d’inta suka nuna mata hakan.

Safeenah Sai kokawan k’wacewa daga rik’on da Aunty Shemau tai mata take “Daddy Mommy kuce ya fice bana son ganinsa.. I don’t want to see him.!”

“Ki rufe wa mutane baki ki natsu ki daina haukar nan..!” Daddy ya katseta da fad’in haka.

Lokaci guda Mu’azzam d’in ke k’ok’arin gaida Daddy kafin ya juyo yana duban Mommy “Mommy Ina kwana..”

Mommy baki sake take dubansa bayan d’aga masu hankali da yai har yanda guts d’in dubansu yace masu ina kwana.

“Da ban kwana ba ai bazaka ganni ba mugu kawai azzalumi macuci maci amana.. Kaji kunya Mu’azzam Bayan duk abinda naiwa mahaifiyarka a rayuwa, na d’auketa ‘yaruwa na kwashe shekaru ina mata jinya abinda zaka saka mun dashi kenan.. Ka rasa mai zakaiwa d’iyata sai ka dinga d’auko Karuwai kana kaiwa Gidan aurenta gidan da ko tarewa cikinsa batai ba.. Wllhi kaji kunya Mu’azzam.. Tirr.!”

“Mommy I don’t know what you’re talking about.. Ni ban kai wata Karuwa ko ina ba..” Ya fad’i cikin dakewar Murya.

Baki sake Su Mommy dasu Safeenah suke dubansa. Wai bai kai Karuwa ko ina ba.. Tsaban shi tacecce ne maimakon ya bada hak’uri ya amshi laifinsa denying ma yake hankalinsa kwance.

A hasale Mommy ta mik’e tana fad’in “Kai bari kaji na fad’a maka ba tsoronka fa ake ba.. Ka bar ganin kana dik abinda kaga dama ana d’auke ido..”

“Hajara ya isa haka..!” Daddy ya katseta cikin tsananin b’acin rai..

Da mamaki take duban Daddy kafin ta ci gaba da jinjina kai tana fad’in “Dama na sani bayansa zaka bi.. Ya cutar da d’iyarmu ya Zalinceta amma kana bin bayansa..!”

“Nace kimin shiru Hajara.. Ta yanda kika b’ullo bata nan za’a gyara al’amarin ba..!”

Safeenah dake kuka Ta bud’e murya tace “Daddy are you really taking his side..? Daddy karuwa fah Karuwa ya kai mun gida tun kafin na tare..!”

Wannan karon Mu’azzam ne ya mik’e a zuciye yana nuna Safeenah da yatsa “Don’t you ever call her Karuwa again..!”

Mommy ta soma salati tana tafe hannaye tana duban Daddy “Ka gani ko.. Ka gani da idonka.. Ya nuna mana shi tabattacene.. Goyon bayan Karuwa yake akan matarsa.”

Ya juyo ya dubi Mommy “Mommy ita ba Karuwa bace..”

“Idan ba Karuwa bace to mecece..?”

Kafin Mommy takai aya ya bata amsa da fad’in “She’s my wife..! Matata ce kaman yanda Safeenah take matata..!”

Yanzu kam gaba d’aya mutane parlorn in a shock suke dubansa kaman wanda aka danna masu pause aka hanasu motsi.

Daddy ya girgiza kai wannan karon “Mu’azzam matarka fah kace..?”

Ya jinjina kai a hankali yana mai sadda kai gaban Daddy.

Daddy yace “But.. But how’s is this possible... Wane irin matarka kuma..?”

Mu’azzam yace “Daddy I’ll explain everything..”

Mommy ta shiga tafe hannaye tana fad’in “La’ilaha’illahu na shiga uku ni Hajara..! Mu’azzam ta nan ka b’ullo kuma.. Na shiga uku wata irin mata Mu’azzam..!”

K’aran da Safeenah ta saki tana mai zubewa wajen yai daidai da soma kiran wayar Mu’azzam da akai.

Gaba d’aya su Daddy Mommy harma da Aunty Shemau sukai kan Safeenah suna jijjigata suna ambato sunanta.

Assad ne mai kiran nasa, ganin yak’i daina kira yasan dole abu ne mai mahimmanci..

Ya d’aga wayar yana sauraron Assad daga d’aya b’angaren

“Mu’azzam you need to come right away.. Ka baro duk abinda kake kazo.. Mun samu abinda zai fayyace mana wanene Sagir..!”

Ai Assad bai kai aya ba Mu’azzam yace “Alright.. I’m on my way there..!”

Ya dubi Daddy yace “Daddy I need to go now.. I’ll explain everything later..”

Shi kansa Daddy yau d’in bai iya amsa Mu’azzam ba sai zuba masa idanu da yai..

Safeenah wacce dama sumar k’arya tai jin zai fice bai ko bi takanta ba ta mik’e tana furta “Mommy Kun gani wajen Karuwar zai koma ya k’yaleni a nan bai damu ko mutuwa nai ba.. Daddy you need to stop him.. Wllhi wajenta zai koma..!”

Ko tsayuwa sauraronsu bai ba ya fice cikin sauri.

Safeenah ta saka hannayenta biyu aka tana k’walla wane irin birkitaccen k’ara.

Mommy taci gaba da bala’i tana fad’in wllhi sai Sun tafi Kotu da Mu’azzam.. Yau d’in nan ba sai gobe ba zasu rubuta masa sammaci.
Chapter 54 · 0% Book details