← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 175

Sashe 97

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tabbas wann mission d’in yasha banban da ko wanne, kaman yanda yace he’d be gentle bashi ya hanata jin jiki hannunsa ba.. Inspector bai farga da aika aikan da yai cikin mission d’in nasa ba saida ya maida stubborn head d’insa cikakkiyar mace. Kuka da raki kam yashasa wann daren. Haka ya dinga aikin lallama da lallashi kaman ya d’auketa ya goyata bayansa haka yakeji. Duk wani gyara da Aunty Larai tai mata saida Inspector ya b’ata wann gyaran. Hamdala kurum yake cikin zuciyarsa yana kuma godewa Ubangijinsa da wann baiwa da yai masa na mallaka masa mace kaman Sadiya da yai. Soyayyarta da k’aunarta sun kuma ninkuwa cikin zuciyarsa. Wani irin k’imanta ne mai girma had’ida daraja suka k’aru a idanunsa. Tabbas yasha kunya a wnn dare dan zaton da yai mata ba haka take ba. Cikakkiyar budurwa ce wacce ya zamto mutum na farko da ya soma saninta d’iya mace. Tausayinta gauraye da k’aunarta na kuma mamaye masa zuciya.

Da kansa ya kaita bathroom har lokacin bata daina masa kuka ba. Ganin Wai so yake ya mata wankan ya sanyata sakin wani sabon kuka tana fad’in “Ni ka fice mun.. Kuma na fasa mission d’in... Kuma zan koma wajen Inne bazan sake dawowa wajenka ba har mu tafi..”

Ga tausayinta yanaji ga dariya, lallashinta ya kumayi yace “Ayi mun afuwa kar ki gudu wajen Inne.. Kinga ficewata ma..” Ya fice yana kuma k’unshe dariyarsa.

Yana ficewa kuka ta kuma saki cikin zuciyarta tana fad’in dik Aunty Larai ne Ta cuceta, ga Inspector ya tasamma kasheta cikin mission.

Da kansa ya kuma gyara masu shimfid’ar tasu ya cire ya canza wani.

Tai lamo tana baccin galabaita.

Bayan ya ida nafilfili zaune yai gaban gadon yana dubanta cikeda tausayawa had’ida k’aunarta, kai da ganin yanda ta tak’ure kasan baccin wahala take.

Ya matso kusanta ya kamo yatsun hannayenta cikin nasa yana tuna munanan kalaman da ya dinga jifanta dasu a baya. Sumbatan yatsun hannun nata yai yana mai lumshe idanu “Thank you for making me the most happiest Man on earth.. Na gode miki da kika adana mun kanki har zuwa wannan lokaci.. Na gode da kika martaba mun kanki.. Na gode da baki watsar min da kanki ba... Dikda irin shaidar da mutane suka miki Kinyi k’ok’ari kin killace min kanki.. Believe me, I’ll love and respect you til my last breath..” Ya d’anyi fasali had’ida manna hannun nata gefen fuskarsa. Lokaci guda yaci gaba da furta “I .. I’m sorry.. I’m sorry for judging you.. It was truly wrong for me to do what I did.. I’m genuinely sorry for my actions.. Please forgive me.” ya k’arashe siririyar hawaye na gangaro masa daga idanu guda. Lokaci guda ya d’aura kansa saman hannun nata, tana jin d’umin hawayensa cikin tafin hannunta, hawaye suka gangaro mata itama. Cikin zuciyarta take furta “Baka mun komai ba Sai Alkhairi Inspector.. Kai d’in alkhairi ne a gareni.” Tana jin sanda ya taso ya kwanta saman gadon ya sanyata cikin jikinsa ya rik’eta sosai kaman zai bud’e k’irjinsa ya sakata ciki. Bacci mai dad’i had’ida shauk’i yai gaba da su. Da niyyan Allah ya tadasu asuba.

**
Washe gari kasa fitowa tai sabida kunyarsa da ya dabaibayeta. Idan ta tina abubuwan da yaita mata a daren jiyan sai taga kaman dai ba Mr Inspector bane da ta sani. Wani irin mutum ne da b’angarensa guda Keda zafi d’aya b’angaren kuma Keda matuk’ar taushi. Ta lumshe idanunta a hankali tana jin k’aunarsa na bin b’argo da jijiyoyin jikinta.

Tana jin shiga da fitan shi tai kaman mai bacci. Can taji yana waya taji kuma kaman ya fice daga parlorn. Da k’yar ta iya mik’ewa kaman zata kifa k’Asa tana jin jijiyoyin jikinta kaman an d’add’aure, ko ina ciwo yake a jikinta. K’afarta kuwa da k’yar take iya d’agawa. A haka da bin garu ta samu ta zame daga nasa d’akin ta nufi nata d’akin. Wanka ta kumayi ta shirya cikin wani red embellished mai kyaun da taushi, d’inkin riga da skirt da ya mugun amsarta. Ta kuma hayewa saman gado Ta kwanta sabida yanda take jin gaba d’aya jikinta kaman ba nata ba.

Sallama da taji a k’ofar parlor ya sanyata dole Ta k’ok’arta ta fito.

Aunty Shemau ce sai dubanta take tana karantarta musamman yanayin tafiyarta.

Sadiya duk sai taji kunya ya danaibayeta, tanata k’ok’arin b’oye yanayin nata amma tuni Shemau ta d’ago jirgin, ta zauna tana mata sannu.

Sadiya Ta k’ok’arta kaman zata duk’a k’asa Don gaida Shemau’un. Tuni Shemau ta kamota tana fad’in “A’a Haba Amarya ai durk’uso ba naki bane. Na yafe wllhi.” Ta k’arashe tana mai zaunar da Sadiyar saman sofa a hankali.

Shemau ta zauna gefenta tana sakin murmushi yayinda Sadiya ta sadda kai kad’an ta gaisheta.

Gyara zama sosai Shemau tai tana ‘yan waige waige.

SameenaAleeyou📚

*GIDA ARO*

*49*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

A d’aki ya tadda Musaddiq d’in yana shirin fita. Fuska babu walwala yake dubansa “Can we talk now..?” Ya tambaya yana duban Musaddiq.

A d’an karkarce Musaddiq d’in ke dubansa lokaci guda yana manna batten d’in hannun long sleeve d’insa “Say what you want say quickly.. As you can see fita zanyi..”

Da tsananin mamaki Mu’azzam ke dubansa. Sosai Musaddiq ya canza abubuwan da baya yinsu a baya.

“Really Musaddiq.? What has gotten into you.. what exactly is wrong with you..?” Ya fad’i yana duban Musaddiq din.

Karkartowa yai sosai yana dubansa “I should be the one asking you that question.. What exactly is wrong with you.. Why can’t you mind your own business and leave me alone, Mr Officer.!” Ya fad’i kai tsaye.

“Musaddiq ni kakema magana haka..?”

Murmusawa Musaddiq yai kafin yace “I forgot you are Mu’azzam Gamji.. Wanda ba’a fad’a masa magana.. Wanda yake yin abinda duk yaga dama ba tareda kowa ya taka masa Burki ba..”

“Enough Musaddiq..! You know that’s not true..” Ya dakatar dashi da fad’in haka cikin kakkausar murya.

Musaddiq ya matso kusansa yana murmusawa kafin yace “Gaskiyar kenan.. You are their favorite.. Kana yin duk abinda kaga dama a lokacin da kaga dama ba tareda Sun taka maka birki ba sabida suna tsoron b’acin ranka..” Ya d’an jinjina kai kafin yaci gaba da fad’in “What..? K’arya nayi.. Ba haka bane..?” Ya d’anyi fasali yana duban Mu’azzam d’in wanda ke kan dubansa.

Lokaci guda yaci gaba da fad’in “Ko kuma matar da na zab’o ne batayi ma Mu’azzam Gamji ba yake so ya sauya mun tinda shi a koda yaushe abinda yake ra’ayi shi yake so mutane su bi.. Well idan wann ne ka saka ma ranka na auri Ajidde an gama, and from now I’ll make decisions on my own.. Bana buk’atan tunanin kowa especially kai..”

“And you will leave Ajidde alone, sabida ita d’in zata zamto matata nan gaba kad’an.. I don’t care idan kanada matsala da hakan..” Ya d’anyi fasali kafin yaci gaba da fad’in “Koda yake idan har ina d’an ahalin nan zan auri Ajidde wacce ba kowa ba, a wajenka na koyi hakan.. After all, idan har za’a janye ido kan auren Sirrin da kai dukda cewa babu wanda yasan dangin wacce ka auro da asalinta banga dalilin da zaisa a hanani auren Ajidde ba..”

Wann karon cikin tsananin k’unan rai yake duban Musaddiq d’in.. Lokaci guda ya d’ago yatsa yana nunasa cikeda gargad’i “Don’t you dare..! Don’t you dare talk about my wife.. Kar ka kuskura ka sake ambato matata.. Much less ka had’ata da wann mahaukaciyar..!” Yaci gaba da jinjina kai yana fad’in “It’s your life Musaddiq.. Do what you want to do with it.. I just hope you won’t have any regrets..!” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice ba tareda ya kuma bi takan Musaddiq d’in ba.

Mu’azzam yana ficewa Musaddiq ya zauna saman gado yana kame kansa had’ida tamke idanunsa. Ya jima yana zaune haka a wajen kafin ya mik’e ya nufi waje.

Yana fitowa ya hangota tana tahowa. Yai tsaye yana dubanta bugun zuciyarsa na k’aruwa. Cak itama ta tsaya sanda ta hangosa. Tinani kala daban daban cikin zuciyarta. Na farko k’watan ta da yai jiya wanda ba Don Allah ya ceceta ba da asirinta ya tonu domin kuwa Tabbas abinda Mu’azzam ya fad’i gaskiya ne amma Musaddiq ya ceceta gaban Inne.. Da ace an koreta a jiyan Tabbas da hallak’ata kurum Kyallu zatai. Tinani na biyu kaw b’oye mata kansa da yai wanda shi yafi komai tsayuwa a zuciyarta. A hankali ta kifa kanta tana mai k’ok’arin canza hanya.

Musaddiq yai saurin cimmata yana kiran sunanta yana fad’in ta tsaya suyi magana.

Cak taja Ta tsaya ba tareda ta juyo ta dubesa ba.

Ya k’araso gabanta yana dubanta. Suka d’ibi lokaci a haka kaman babu mai cewa komai cikinsu.

Can ya d’anyi gyaran murya yace “I know by now kin San ko ni wanene..”

Sai sann ta d’ago ta d’an dubesa, sai kuma ta kauda kanta gefe ba tareda tace komai ba.

Shafa kansa ya d’anyi dan yama rasa mai zai kuma fad’i mata.

“Kiyi hak’uri kan abinda ya faru jiya..” Abinda yaji bakinsa ya iya fad’i kenan.

Da mamaki ta kuma dubansa kafin ta girgiza kai tace “Maiyasa kake bani hak’uri kan laifin da baka aikata ba.? Maiyasa kake bani hak’uri kan laifin da gaskiya ne na aikata.. Da ni da kai munsan cewa D’anuwanka gaskiya ya fad’i akaina.. Ni b’arauniya ce kuma na tasamma masa sata, ba karo d’aya ba har sau biyu... Tabbas baiyi k’arya ba.. Ni da kai duk munsan haka.. Amma abinda ban fahimta ba shine Maiyasa kake kareni.. Bayan baka bani yarda da amincewarka ba..?”

Kauda kansa gefe yai kad’an yana fuzar da huci a hankali hannayensa saman kunkuminsa, lokaci guda ya juyo yana duban idanunta da tuni sun ciko da k’walla.

A hankali ya soma girgiza kai kafin yace “No that’s not true.. Ke ba b’arauniya bace.. Inna K’yallu ce ke umartanki da ki d’auki kayan mutane.. Amma ke d’in ba b’arauniya bace.. Kar ki sake kiran kanki da wann sunan domin ke mutuniyar kirki ce..?”

Katsesa tai da fad’in “Kaji abinda ka fad’i kuwa..? Mutumiyar kirki..? Ta ya kasan ni mutumiyar kirki ce idan har kana shakkun ka sanar dani asalinka da wanene kai..?” Ta k’arashe hawaye na gangaro mata.
Chapter 97 · 0% Book details