← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 136 OF 175

Sashe 136

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Musaddiq yaci gaba da girgiza kai “But why can’t I remember all the details..? Na kasa tuna yanda abin ya kasance..” Ya d’ago yana duban Mommy kafin yaci gaba da jinjina kai yana furta “All I can remember shine ta kirani, munyi waya, sann tace dani na taho na sameta, sann tana magana ne like she wanted to tell me something.. A hanyatane na dawowa daga friend’s party bayan naje dan na mance k’uncin da Daddy ya sakani ciki dikda cewa nayi alk’awari ma Ikram no parties no girls no drugs dama duk wani abu da nake a baya maras kyau..” Ya d’an nusa kafin yaci gaba da fad’in “I... I couldn’t speak clearly because I was drunk... Sai tace mun ga location d’in da take mu had’u a wajen..Ban amsata ba sabida bana so Ta gane wani abu from my voice tinda na mata alk’awari na daina.. She texted the address bayan mun gama wayan.. Sai nacewa mai taxi ya ajeni close to wann location d’in.. Naji mamakin mai takeyi a wann wajen..

Sanda ta ganni ina tangad’i kaman zan kifa k’asa rik’eni Tai tana fad’i cikin muryarta ‘Musaddiq mai nake gani.. Are you high.. Mai ka aikata..? Didn’t you promise me ka daina..? Mai kuma nake gani yanzu Musaddiq..?’ Hawaye suka ci gaba da gangaro masa kafin yaci gaba da furta “Dariya nake irinta bugaggu.. Tana k’ok’arin mik’ar dani tsaye Ina k’ok’arin janyota jikina.. Dariya nake Ina janyota Ina fad’in You said it yourself na daina.. But Daddy didn’t believe na daina.. Daddy yace bazai bani aurenki ba wai ban cancanceki ba.. Daddy hates me you know.. Dikda na canza baya ganin hakan.. Mu’azzam ne kawai yake iya gani.. Mu’azzam ne kawai D’ansa a k’wayan idanunsa shiyasa ya aura masa Safeenah, and ni kuma yace bazai tab’a bani aurenki ba, na fad’a masa you are mine, ni kad’aina ked’in tawa ce Ikram kuma zan tabbatar masa da haka..!” Kuka ya sanyasa yin fasali kafin yaci gaba da fad’in “Sai ta fara tureni tana k’ok’arin k’wace kanta daga wajena ganin irin yanda nake janyota jikina ina fad’in ita tawa ce.. Cikin siririyar muryarta take fad’in ‘No Musaddiq what are you doing... Please don’t do this.. Don’t Musaddiq..’ Naci gaba da janyota Ina fad’in ita tawace.. anyi auren Safeenah da Mu’azzam, Daddy yace bazai tab’a bani ke ba har abada, kin San ya fad’i haka..? Wai bazai bada d’iyarsa ga mahaukaci irina ba... Mu’azzam will forever be his favorite.. He does everything Mu’azzam wants.. Naci gaba da janyota jikina tana tureni...!” Yaci gaba da girgiza kai yana hawaye.. Ban sake sanin mai ya faru ba, Sai tsintar kaina nai a gida Ina bacci..! And Washe gari na tadda labarin Ikram ta mutu..!” Kuka mai k’arfi ya kufce masa.

Mommy taci gaba da hawaye tana fad’in “I saved you from going to jail that day.. Na ceceka sabida ni mahaifiyarka ce.. Bazan bari ka tafi jail ba..!”

Katseta yai da fad’in”But who killed Ikram Mommy..? Waye ya harbeta.. Mai takeyi a wann location d’in..? Ya akai kika taddani a can..?”

Mommy tace “Ban sani ba, bansan wa ya kasheta ba.. Iyakacin abinda na sani shine I saved you that day, and you should be thankful Mahaifuyarka was there for you.. ‘Yantaddan da suka sace Ikram sun kasheta ne bayan ka mata Fyad’e Musaddiq..”

Dafe fuskarsa yai da duka hannayensa biyu yana kuka sosai yana ci gaba da fad’in bazai tab’a yafe ma kansa ba.

Mommy Ta tsaresa da idanu kaman mai tausayinsa, nan taci gaba da fad’in “Bazan tona maka asiri a wajen Mu’azzam ba, zanci gaba da rufe sirrinka..”

Musaddiq na hawaye yake dubanta “I can’t live with this anymore Mommy.. I can’t.. I need to turn myself in.. I need to pay for my crime koda hakan yana nufin zan rasa Mu’azzam..”

Mommy ta kamo hannayesa tana zaro ido “Koda hakan yana nufin zaka hallak’a Mu’azzam da abinda zaka Fad’a masa.. Mu’azzam mutuwa zai idan yaji abinda ka aikata Musaddiq.. Mu’azzam ya yarda da kai ya aminta da kai, ya d’aukeka D’anuwa idan yaji abinda ka aikata ma K’anwarsa zuciyarsa zata buga kaga hakkin mutuwan Mu’azzam zai kuma rataya a wuyanka bayan na Ikram na wuyanka already.”

Matse kunnuwansa yai da k’arfi yana girgiza kai yana hawaye.

Rik’o hannayensa Mommy tai tana fad’in “Kana jina you’ll help me escape Musaddiq.. And you’ll keep quite, you won’t say a word to Mu’azzam.. Idan ba haka zaka lalata rayuwan Mu’azzam ne harda naka..!” Ta k’arashe tana dubansa sosai..

Banda hawaye Musaddiq baya komai.

A can waje kaw wajen su Daddy babu mai iya cewa komai daga Daddy har Mu’azzam d’in. Sai sautin kukan Daddy dake fita a hankali.

Kan Mu’azzam na kife yake fad’i da Daddy “Zaka kira D’anuwanka Daddy.. Zai taho nan ya amsa mun tambayoyi na..”

Daddy ya dubi Mu’azzam yace “Ka yarda Salman zai iya kashe mahaifinka..?”

Murmushi mai ciwo Mu’azzam yai kafin yace “I don’t know what to believe or who to believe anymore.. Iyakacin abinda na sani shine zaka kira Uncle Salman zai taho nan.. Mommy zata maimaita abinda Shemau ta fad’a mata.. Uncle Salman zai sanar damu komai gameda wann takardan yarjejeniyar wanda yace yana wajenka. Babu wanda zai fice daga cikin gidan nan Daddy, idan hakan na nufin zai d’auke mu tsawon kwanaki da yini ne har Uncle Salman ya iso nan..!”

Yana maganar yana jinjina kai alamun tabbatar da kalamansa. Lokaci guda ya ciro wayarsa ya shiga dialing layin DIG.

DIG na d’agawa Mu’azzam ya gaisar dashi cikeda girmamawa kafin ya d’an matsa gefe suna wayan.

Yana ida wayan ya dawo yanda Daddy ke zaune saman kujera kansa a kife.

Mu’azzam ya d’anyi gyaran murya kafin ya soma fad’in “I don’t know if I’m doing the right thing Daddy.. But I just hope ba kare Uncle Salman kake ba bayan kasan wani abu.”

Daddy ya lumshe idanunsa yana jin zuciyarsa na masa zafi. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un kawai zuciyarsa ke nanatawa, maike shirin faruwa da ahalinsu..? Ahalin da yai alk’awarin karewa da rayuwarsa.. Ya jinjina kansa kad’an yana duban Mu’azzam d’in “Ni kaina Ina son sanin Maiyasa Salman yace takardan na hannu na alhali bansan anyi haka ba.. Bansan da maganar wata yarjejeniya ba.. Zan kira Salman ya taho nan Sai a warware komai..” Ya mik’e tsaye ya d’an dafa Mu’azzam d’in kafin yace “Dik abinda zai faru Mu’azzam ka sani ina k’aunarka.. Kuma kaid’in D’a na ne koda bani na haifeka ba..”

Shiru Mu’azzam yai yana dubansa strangely ba tareda yace komai ba daidai lokacin suka hango Mommy da Musaddiq sun nufosu.. Daddy ya yunk’ura yana fad’in “Bazata shige mun cikin gida ba.. Batada muhalli a gidana.. A nan d’akin waje zata zauna har al’amara su daidaita.!”

Musaddiq ya tare gaban mahaifiyarsa yana fad’i cikin dakewar murya “Mommy bazata zauna waje tareda securities ba, zata shige cikin gidan, idan bataci darajan kasancewa matarka ba zataci darajan kasancewa mahaifiyar ‘ya’yanka.. Unless zaka nuna halinda ka saba ne cewa D’an D’anuwanka yafi Naka D’an soyuwa a gareka.. Which’s not new.”

Daddy ya yunk’ura yayo kan Musaddiq cikin b’acin rai. Mu’azzam yai saurin rik’o Daddy ya jinjina kai yace “Kai hak’uri Daddy ka barta Ta shige.. Fita ne dai babu mai yinsa sai an warware komai..!” Yana maganar yana duban Mommy yana jinjina kai alamun tabbatar da kalamansa.

Daddy ya jinina kai yana duban Musaddiq “Kaci darajan D’anuwanka..”

Musaddiq yai murmushin takaici yace “Kaman dai ko yaushe..Daddy.” Daga haka janyo hannun mahaifiyarsa yai suka nufi cikin gidan yana fad’in “Let’s go Mommy.”

Kiraye kirayen sallar magrib aka soma yayinda Mu’azzam da Daddy suka gudanar da alwalansu, dai dai lokacin Musaddiq ya fito shima ya gabatar da nasa alwalan Tun a cikin Gida, yasa kai zai fice. Mu’azzam ya dakatar dashi da fad’in “Babu mai ficewa sai an kammala bincike.. Zamuyi jam’i a nan gaba d’ayanmu..”

Da mamaki Musaddiq ke dubansa kafin ya daidaita tsayuwarsa yace “Barin fad’a maka wann Mu’azzam Gamji.. You should know, The world doesn’t revolve around you.. Kai baka isa kace zaka gindaya mana sharudd’a mu bi ba..!”

Gajeren murmushi Mu’azzam yai yana warware long sleeve d’insa da yai folding sanda zai alwala “K’warai na isa.. Kasan maiyasa..?” Ya k’arashe maganar yana nuna ID d’insa kan idon Musaddiq.. “Wann kad’ai ya isa na tabbatar maka ni na isa na hana kowa ficewa har Sai lokacin da na ida bincike na.” Ya ida maganar yana mai maida ID d’insa cikin aljihu.

Musaddiq ya kauda fuskarsa gefe kad’an yana mai furzar da fuci.

Musaddiq bai ida shan mamaki ba har saida motocin ‘Yansanda har biyu suka iso gidan sukai ma gidan zobe.

Mommy daga window na d’akinta ta hangi motocin, cikinta ya bada wani irin sauti “Na shiga uku ni Hajara mai zan gani.. ‘Yansanda D’aniskan yaron nan ya kawo suyi gadinmu..!” Hannunta guda dafe da k’irji.. Koda wasa bata zaci Mu’azzam zai tafi da nisa irin haka ba, bata zaci zai kawo ‘Yansanda gidan ba.. Ya zama dole tasan yanda zatai Ta samu hanyar guduwa.. Allah yana gani bazata bari Mu’azzam ya kaita gidan yari ba.. Dole tasan yanda zatai Ta fice.. Mabud’i guda d’aya takedashi shine Musaddiq.. Zatasan yanda zatai ta gudu dan wllhi bazata tafi gidan yari ba.

**

FUFORE

Daga bakin k’ofa Uncle Salman yai tsaye yana duban Aunty Nuratu dake kwance saman gado Mama Hindu na mata hayak’in habbatussauda. Take ya soma tuna Shemau da yanda suka k’ulla cewa ta shiga jikin Hajara ta samu yardarta har su cimma burinsu na amso wann Document d’in daga hannun D’anuwansa Marwan.. Zuciyarsa ta tuhumesa ‘Salman kana sane aka kawo matar nan ana mata jinya da maganin ‘yar 419 yanzu idan matar nan ta mutu a haka kana tunanin Allah bazai kama ka ba..?’
Chapter 136 · 0% Book details