Sashe 173
Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daidai lokacin Danger da yai kwanto b’auna yana jiran k’arasowar Mu’azzam ya mik’e yana pointing Mu’azzam d’in da bindiga. Lokaci guda yana bushewa da muguwar dariya “Uuh..! Look who’s here.. Ashe dai zan samu damar congratulating d’inka Inspector..! Af na mance Chief Inspector..! You know, it will be a huge honor for me to kill in your uniform.. A wann rana mai mahimmanci a wajenka.. Yanzu dai na tabbata ka yarda ni d’in dai kaman Kyankyaso ne bana mutuwa cikin sauk’i.. Kuma wann Kyankyason zai gama da kai da harsashi guda.!” Yana maganar yana kuma fashewa da dariya cikeda izgilanci.
Mu’azzam huci kurum yake yana duban Danger da idanunsa da tuni sun gama kad’awa “Where... is... my wife.. you maniac..?” Abinda ya iya fad’i kenan yana fitar da huci a hankali.
Danger ya kwashe da dariya Hajara na tayasa “Ta isa barzahu na tabbata by now.. Da ita da abinda ke cikinta bazasu rayu ba bayan harsashin da na d’ana mata kaman dai yanda na d’ana wa k’anwarka sann na cire cikin Safeenah na kuma rufe mahaifinka a Cold room..!”
Wani irin duhu ne yaga ya gifta masa, take abubuwan da Mommy tai ma ahalinsa ya shiga zuwa masa d’aya bayan d’aya.. Ji yai baya tsoron harsashin dake cikin bindigar da Danger Ke nuna masa.. Yai kukan kura zai kamo Mommy Danger ya saki harsashi daidai nan Safeenah ta bangajesa harsashin ya hudata a cikinta..
Lokaci guda Safeenah ta silale tana dafe cikinta yanda Danger ya huda da harsashi jini na b’ulb’ulowa.
Wane irin k’ara Mommy Ta saki tana ambato sunan Safeenah.. Yayinda Mu’azzam ya duk’a yana ambato sunata.
Girgiza kai Safeenah take cikin tsananin jin jiki take furta “Go Mu’azzam.. Save your wife and child.. Ka canci farin ciki bayan duka abubuwan da Mommy tai maka da ahalinka. Just go..!” Ta k’arashe muryarta na fita da k’yar farar fuskarta ya koma jajazir haka nan k’wayar idanunta.
Danger da yaga aika aikan da yaima ‘yaruwarsa Hajara ya harbe mata d’iya Sai ya soma k’ok’arin aunewa a guje.. Mommy tabi bayansa a guje tana fad’in sai ta kashesa tinda ya kashe mata d’iya akan idanunta Bayan duk abubuwan arzikin da ta masa a rayuwa.
Suna isa saman kwalta am basu ankare da Babbar motar dake zuwa ba nan k’atuwar Trailer d’in Ta take kan Danger wanda har kana iya hango yanda k’ashin kansa ya diddige saman kwalta. Mommy kuma k’afafuwanta motar tabi kai tin daga cinyoyinta har zuwa k’asa.. Haka motar nan tai daga daga da k’asusuwan k’afafun Mommy saman kwalta.
Murmushi da hawaye saman fuskar Safeenah take duban nasa fuskan wanda shima hawaye ne Ke gangaro masa “Please forgive me Mu’azzam.. Forgive me for all the.. trouble.. I.. caused you... Kace ma Daddy ya yafe mun... Just go.. Your wife and your child need you... Just go Mu’azzam..!” Ta k’arashe tana lumshe ido.
Mu’azzam da hawayensa suka gaza daina gangarowa girgiza mata kai yake fad’in “No Safeenah.. Bazan barki a nan ba.. Just hang in there kinji.. Zaki samu lafiya kinji.. In sha Allah.. You will see zaki samu lafiya..”
Murmushi take hawaye na gangaro mata sanda ya sakata a mota “A ranata na k’arshe a duniya inaso naji wann kalma daga bakinka.. Even just this once.. Tell me you love me Mu’azzam.. Dan Allah ka fad’a mun wann kalmar naji daga bakinka.”
Sosai yake kuka yana dubanta “Kiyi shiru Safeenah zaki samu lafiya kinji..”
Ta kuma murmusawa tana girgiza kai “Just.. Tell me please..”
Cikin zuban hawaye yake furta “I love you.. I love you so much Safeenah.. We all love you.. Please don’t leave us kinji..” Ya k’arashe hawaye na kuma gangaro masa.
Murmushi ta saki tana mai lumshe idanunta a hankali hawaye suka gangaro ta wutsiyar idanunta.
Sauri sauri yake tuk’in motar yana juyowa yana duban Safeenah yana kuma fad’i mata kalaman k’arfafa gwiwa. Saidai Ita Safeenar bata iya amsashi saima murmushi da take tana mai k’ok’arin ambato mahaliccinta a hankali. Hannayenta dafe da cikinta yanda harsashi ya huda jini na bin hannun nata.
Asibitin da Musaddiq ya kawo Sadiya nan Mu’azzam ya kawo Safeenah dan asibitin ne mafi kusa da yanda suke, rufin asirin Allah kuma asibiti ne na k’wararru dake cikeda manyan Likitoci.
Mu’azzam na k’arasowa aka kawo gadon tura marassa lafiya aka soma bawa Safeenah taimako na gaggawa. Musaddiq ya rikice yana k’ok’arin kamo hannun Safeenah da ake kan turata cikin sauri za’a nufi ER da ita.
Sosai Musaddiq ma yake kuka yana kamo hannun Safeenah wacce tuni idanunta sun rufe sai bakinta dake motsawa a hankali.
Mu’azzam da gaba d’aya blue kakinsa na yansanda ya b’aci da jinin Safeenah tare Dr guda yai yana fad’in “And my wife.. How’s my wife doing..?” Ganin Musaddiq a wajen ya tabbatar masa nan ya kawo Sadiya sabida Safeenah ta sanar dashi Musaddiq na tareda matarsa.
“Matarka da abin cikinta suna k’ark’ashin kulawa na musamman.” Abinda kawai ya iya fad’i kenan kafin wasu Dr’s guda uku suka k’araso suka janyesa suka nufi ER cikin sauri.
Mu’azzam yai k’ok’arin bin bayansu yana tambayarsu saidai bai sami zarafin cimmasu ba dan tuni sun shige wasu nurses na k’ok’arin dakatar dashi.
Shafe fuskarsa yai yana kuma tamke idanunsa lokaci guda yana jin k’afafunsa na barazanar gaza d’aukarsa.
Musaddiq ne yai k’arfin hali ya janyosa ya zaunar dashi. Daidai lokacin su Daddy da Mamy suka k’araso kowa hankalinsa a matuk’ar tashe.
Mu’azzam na ganinsu ya mik’e ya nufi mahaifiyarsa. Bai iya furta komai ba sai fad’awa jikinta da yai yana mai fashewa da wane irin kuka.
Mamy Ta tallafosa tana jin hawayen na zuwa mata itama.
“Kai hak’uri Mu’azzam. Kaita karanta Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un kaji..” Abinda take iya fad’i masa kenan cikin tsananin rawar murya itama.
Daddy kaw gefe suka matsa da Musaddiq yana sanar dashi abinda ke faruwa cikin tsananin damuwa dan shima Musaddiq d’in kana ganinsa zaka fahimci k’arfin hali ne kawai.
Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un kurum Daddy Ke iya nanatawa yana rok’on Allah ya kawo masu d’auki.
Can sukaga wasu nurses guda biyu sun fito cikin sauri Sun nufi wani d’akin Sun kuma dawowa gudu gudu.
Mu’azzam ya mik’e ya nufesu saidai kafin ya k’araso sun shigo k’ofar glass d’in da ya raba tsakani ya rufe.
Juyowa yai yana duban Daddy da ya take masa baya “Why aren’t they saying anything..? Ya kamata su sanar damu halinda suke ciki right Daddy..?” Yanda yake maganar zai tabbatar maka ba cikin hayyacinsa yake ba.
Daddy ya kamosa yana k’ok’arin kwantar masa da hankali. Daidai lokacin wasu Doctors guda biyu suka fito d’ayan na zame nose mask d’in dake bisa bakinsa da hancinsa.
Daga yanda yanayin Likitocin ya nuna suka fahimci akwai babban matsala.
“Dr where’s my wife..? Tinda nazo nan ban ganta ba.. Dan Allah ku barni na ganta.” Mu’azzam ya fad’i cikin tsananin d’imauta.
D’aya Dr d’in ya kalli d’ayan. Ganin irin duban da suke ma juna yasa Mu’azzam soma girgiza kai yana furta “No.. No please.. Ku sanar dani halinda suke ciki..” Yana maganar yana k’ok’arin nufan ER d’in.
D’ayan Likitan yai saurin rik’osa Sai ya soma fuzgewa cikin tsananin huci yana k’ok’arin shak’o wuyan likitan “Ina matata.. Ina matata nace..?!”
Daddy ya soma k’ok’arin janyesa “Mu’azzam mu saurari abinda likitocin zasu ce.. Kai hak’uri.”
Girgiza kai yake yana duban Daddy cikin wane irin yanayi mai ban tausai “Daddy Maiyasa basu cewa komai.. Maiyasa bazasu barni na ganta ba.”
A haka Daddy ya janye hannunsa jikin Mu’azzam d’in na kuma mutuwa lak’was.
Dr yai gyaran murya yace “The situation is very delicate.. I’m afraid we couldn’t remove the bullet from her body..” Ya d’an daidaita tsayuwarsa kafin yaci gaba da fad’in “But Fortunately, harsashin bai tab’a Jaririn dake cikinta ba. Amma We are not sure waye zamu fara cirewa cikin biyun. jaririn dake cikinta ne Ko harsashin da ya hudata.. Zamu iya rasa d’aya cikin biyun koma mu rasasu gaba d’aya.!” Abinda Likitan ya fad’i kenan cikin tsananin sanyin jiki.
Girgiza kai Mu’azzam yake yana jin duniyar na juya masa “No.. No please.. Dan Allah kuyi duk abinda zaku yi.. Just save my wife please.. Dan Allah ku ceci matata.. I can’t lose her.. I can’t lose her right Mamy..” Yai maganar yana duban mahaifiyarsa cikin wane irin yanayi mai ban tausayi.
Daddy ya shafe fuskarsa da tafukan hannayensa yana karanto innalillahi wa inna’ilaihi raji’un cikin zuciyarsa. Duban Dr yai kafin yace “Likita kuyi duk abinda zakuyi ku ceci Mahaifiyar da Jaririn.. Please Dr.. Just do whatever you can..”
Dr ya jinjina kansa a hankali kafin yace “Ban San mai zan sanar dakai ba Alhaji.. But all I can is.. Mu shirya ma aukuwan koma menene.. Let’s prepare for the worse.”
Ai bai kai aya ba Mu’azzam ya cakumosa “Incompetent! Are you telling us to prepare for the worse.? What kind of a Dr are you..?” Yaci gaba da jijjiga Dr yana fad’in “Zata sami lafiya.. Matata zata sami lafiya Kaji koh.. She’s going to get better.. And you will see.!”
Daddy yai saurin janyesa yana dannarsa.
Silalewa Mu’azzam yai wajen saman gwiwoyinsa yana jin wani abu mai zafi ya tsaya masa a k’irji.. Wayansu yake tunowa na k’arshe da yanda taita kallon fuskarsa har kaman bataso Ta janye idanunta. A hankali ya dafe fuskarsa da garu yana girgiza kai bai iya komai sai lumshe idanunsa da yai, yanajin hannun Mahaifiyarsa saman kafad’arsa tanata k’ok’arin kwantar masa da hankali had’ida karanto masa addu’an da zai dinga fad’i.
Ya d’ago gajiyayyun idanunsa yana duban mahaifiyarsa “Mamy sun hani ganin Sadiya tinda nazo nan.. I can’t lose her.. Right Mamy.?” Yanda yake maganar dole ya baka tausai. Cikin sauri mahaifiyarsa ta rungumosa jikinta tana jin kuka na zuwa mata itama “Bazamu rasasu ba duka kaji.. Sadiya da abinda Ke cikinta harmada Safeenah.. Allah zai tashesu kaji koh.. Kaita karanto Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.”
Daddy ya tare Likitan da fad’in “And Safeenah..? How’s my Daughter doing..?”
Duban Daddy Likitan yai Sai kuma ya sadda kai kad’an.
Daddy ya girgiza kai yace “Babu wani rufa rufa Dr, ka sanar dani situation d’in ‘yata please..”