Sashe 76
Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daddy yai shiru yana mai duban wani b’angaren kafin ya jinjina kai yace “Shikenan babu damuwa.. Ai dani da Salman d’in duk d’aya ne.. Abinda yayi mahaifinka shi yayini ya kumayi Salman.. Bakai laifi ba dan ka baiwa Salman daman zama mahaifi a gareka.. Su waye ahalin matar ya kamata mu San dasu tinda an zama ahali a halin yanzu..”
Mu’azzam ya jinjina kai yace “Marainiya ce Daddy batada kowa sai mahaifiyarta da k’annenta guda biyu.. A halin yanzu mahaifiyar tata takaba take da zaran ta ida in sha Allah zanyi maku introducing nasu..”
Daddy ya sauk’e ajiyan zuciya kafin yace “Nasan bazakaje ahalin da ba decent ba Kai aure.. Babu damuwa Allah ya kaimu lokacin.”
Mu’azzam ya murmusa yace “Ameen Daddy.. Ni zan wuce Daddy akwai yanda nake son zuwa..”
Daddy yace “Tashi kaje abinka Allah shi maka albarka ya had’e maka kan iyalanka ya kuma azurtaku da Zuri’a wanda Al’umma zasuyi alfahari dasu kaman yanda muke alfahari dakai..”
Murmushi kurum Mu’azzam yake kansa a k’asa yana amsa ma Daddy da Ameen kafin ya fice.
Wayar Musaddiq ya kira yace something urgent ya taso masa su bar fitan sai wani lokaci.
Musaddiq yace babu komai hakan shima yafi masa dan gaba d’aya ko kuzarin fita baidashi.
**
Meema na tsaye Lambun gidan ta hangi ficewar motar Mu’azzam.. Tai tsaye tana tinanin abin yi bayan juya mata baya da ‘yaruwarta tai harda zargin da tai mata akan mijinta.. Meema ta jinjina kai tana fad’in “Safeenah ‘yaruwata ce.. Kuma wanda ya tura wa Ya Mu’azzam sak’on nan a bayyane take so yake ya raba Addah Feenah da mijinta.. I need to clear my name a wajen Addah Feenah.. Nasan tana buk’atata da shawarwari.. Saidai wannan karon shawari na k’warai zan bawa ‘yaruwata bayan na wanke sunana a wajenta.. Tabbas ishara Allah ya nuna mun da masu halayyan irin nawa wanda su a kullum basuda buri saidai suji abinda mutane ke tattaunawa su k’ara.. A koda yaushe yafi kyau mutum ka zamto mai minding business d’inka.. Hadisi ne guda manzon Allah (S.A.W) yace yana daga kyaun musuluncin mutum ya bar shiga abinda bai shafesa ba.. Toh matsala ta kenan ni Meema kuma na tuba na daina daga yanzu.. Babu horo mai tsananin da zan samu a duniyar nan kaman gaba da ‘yaruwata wacce muka fito ciki guda wacce nake matuk’ar k’auna irin Adda Feenah.. Da ace shawari masu kyau nake bawa Addah Feenah duk da hakan bata kasance ba.. In sha Allah zan gyara alak’armu Addah Feenah.. Kuma zan wanke sunana a wajenki ki fahimci cewa ni Meema ba ni na turawa mijinki sak’o ba sannan banida buri tamkar naga Kun zauna lafiya da Ya Mu’azzam..” Tana ida fad’in haka tasa kai ta shige gida tana tinanin abinyi..
Wani tunani ne ya d’arsu mata hakan yasa ta nufi d’akin Mommy ta d’au wayarta ta kofe lambar Barr Ameer dan lokacin da aka tsare Safeenah Barr Ameer d’in ya kira Mommy a matsayinsa na lauya da zai kare Safeenah a kotu.
Meema tana kira ta sanar dashi itace Meema k’anwar Safeenah.. Tana so su had’u.
Babu musu Barr ya bata lokaci da wajen da zasu had’u. Meema ta jinjina kai tace Babu damuwa zatazo wajen.. Sai Sun had’u.. Daga haka sallama tai masa tana kuma tabbatar ma kanta zata wanke kanta da sunanta da izinin Allah.. Sann sai ta gano wacece wacce ta tura wa Ya Mu’azzam wannan sak’on. Itama aikin Detectives zatai wannan karon (Wayaga Detective Meema.. Lol)
**
A b’angaren Mu’azzam kaw yana ficewa shopping mall ya biya yai mata sayayya kafin ya nufi asibitin.
Maleeka tana mak’ale wani b’angare cikin asibitin dan tasan dole zai dawo tinda Sadiya tana asibtin.
Nan Ta hangesa sai jidan kaya yake cikin shopping bags ya shige ward d’in da Sadiyar take..
Maleeka ta rakasa da mugun kallo tana jin zafin yanda yaketa rawar k’afa kan wata alhali Ita ta ceci rayuwarsa baiko ga hakan ba. Tai k’wafa a hankali daga nan yanda take zaune Ta rufe fuskarta da nose mask tayi shiga irinta ‘yan asibiti harda Lab cot da hular da Malaman jinya ke rufe kawunansu dashi.. Sam bazaka fahimci Maleeka ba.
A fili Maleeka take furta “Let’s see idan na shiga d’akin na dannawa matar taka Allurar mutuwa ya zakai.. Inspector Gamji..” Ta k’arashe tana sakin murmushi
D’akin Sadiyar ya nufa yayinda suka had’u da likitan nata a hanya. Suka gaisa da Mu’azzam yana basa update kan jikin Sadiyar. Likita yace da sauk’i sosai dan yanzu haka ma ruwan da aka saka mata ya k’are kuma ya cire mata, yanayin fargaba kuma da take ciki sai a hankali traumatic experience d’in zai rabu da ita.. Sannan tanata nanata abu guda cewa a kaita wajen Ummanta da ‘yanuwanta.
Mu’azzam ya jinjina kai yace “Yanzu za’a iya sallamarta kenan..?”
Dr yace “Of course Inspector.. Amma da son samu ne a kaita wajen mutanen da take ta nanata sunayensu hakan sai ya zamto tamkar therapy ne a gareta..”
Mu’azzam ya jinjina kai yace “Shikenan Dr.. Na gode sosai.. Zan iya shiga na ganta yanzu.?”
Dr ya jinjina masa kai yana mai fad’in zai bada takardan sallamar nata in a bit.. Daga haka musabaha suka kumayi Mu’azzam na masa godiya kafin ya nufi d’akin Sadiyar.
‘Yansandan dake tsaye k’ofar d’akin suka sara masa kafin ya shige ciki.
Tana zaune saman gadon ta nad’e k’afafunta, har lokacin ga alamun hawaye saman fuskarta.
Kallo guda tai masa ta d’auke kai fuskarta a tamke saima kukan da taji na kuma zuwa mata.
Ya k’arasa saman drawer dake gefen gadon ya aje shopping bags d’in dake hannunsa. Sai karantar yake ta wutsiyar idanu.. Yasan bazata masa magana ba dan baima saka ma ransa zata amsa gaisuwarsa ba hakan yasa bai mata sannu da jikin ba dukda cewa abinda zuciyarsa ta soma fad’i kenan sanda ya turo k’ofar d’akin.
Ya soma fito da kayayyakin, toothpaste da toothbrush da set d’in shower ya soma fitarwa. Ya nufi bathroom d’in dasu a hannunsa ya duba komai need harta water heater akwai sannan akwai ruwan yin wankan.
Dettol d’in dake hannunsa ya k’ara zubawa a bathroom d’in tai disinfecting dukda cewa ko Ina a gyare yake.
Ya fito ya taddata har lokacin tana nan yanda ya barta.
“Tashi kije kiyi wanka zamu tafi yanzu..”
Kuka ne taji ya kuma zuwa mata gadan gadan.. Ya d’an shafi sumarsa yana mai kauda Kai kad’an..
Batace komai ba sai kukan da take tana ambato Umma dasu Habeeb.
D’an duk’awa yai yana dubanta yanda ta kifa kanta tana kuka.
“Kina son ganin su Umma..?” Ya tambaya idanunsa akanta.
Batace komai ba sai dubansa da take.
“Come here..” Ya furta yana mai janyo hannunta.. Ya nufi bathroom d’in da ita still bata iya furta komai sai dubansa da take tamke dai an canzata..
Hular da sumarta ke rufe ciki ya soma zame mata.. Yana k’ok’arin zame tufafinta tai saurin turasa tana girgiza kai take kare jikinta da hannayenta “Don’t touch me..” Ta fad’i jikinta har rawa yake tana kuka.
Yanzu kuma tausayi take basa sosai domin kaw ka kasance hannun ‘yantadda abu ne mai matuk’ar tashin hankali.
Zuciyarta ta shiga bugawa kardai Danger ya mata wani abu ne.. Ya matsa baya a hankali yana mai d’ago hannayensa alamun bazai tab’ata ba.
“Did he do something to you..?” Ya tambaya yana dubanta.. Still tana duk’a wajen tana hawaye.
Saurin girgiza kai tai alamun a’a kafin Ta d’ago idanunta masu zuban ruwa tana dubansa “He didn’t.. But you did.. I hate you.. And I’ll never forgive you for what you did.. Kaima bakada banbanci dashi.. Kaima D’antadda ne.. Harma ka fi shi.. Sabida shi bai mun abinda ka tasamma min ba..!”
Wannan karon sosai bugun zuciyarsa ke k’aruwa, yana jin kalamanta suna masa zafi a kunnuwarsa da zuciyarsa.
Cikin huci ya k’araso ya kamo arms d’inta, ya shiga jijjigata yana furta “Kar ki sake had’ani da wanann D’aniskan.. I’m your husband in case you forgot.!” Ya kuma jinjina kai yana mai ci gaba da furta “And I’ll touch you, not just once... As many times as I want.. Because you are my wife..” Ya k’arashe rik’e da ita har lokacin hawaye take.
D’an saita kansa yai yana mai fuzar da huci kad’an kafin yace “Get ready now.. We are leaving.. That is idan kinaso ki sake ganin ahalinki..” Daga haka ficewa yai daga bathroom d’in tabi bayansa da kallo jin abinda ya fad’i mata.. Mai yake nufi ko ya samo yanda Su Umma suke ne.. Abinda zuciyarta ya dinga raya mata kenan.
Tai saurin mik’ewa tana addu’an Allah yasa zata dake ganin Su Umma.
Mu’azzam kaw yana fitowa ya fice gaba d’aya daga d’akin abubuwa fal zuciyarsa.
D’akin hutu da aka kwantar da Assad ya nufa. Yanda ya tadda Assad d’in bacci yake bai tashi ba.. Likita ya basa update akan jikin Assad d’in. Ya jima kan Assad yana masa fatan samun sauk’i kafin ya nufo motarsa ya d’auki samples d’in sumar Musaddiq da ya d’auka da kuma hular da suka tsinta a wajen alk’allar Danger.
Maleeka tana reception acting like a Staff ta hangosa rik’eda samples d’in ya nufi Lab.
Shiru tai ta soma tinanin mai zai a Lab.. Lokaci guda ta soma binsa cikin yananyi na b’adda kama.
Da shike asibitin is more of glass nan ta hangesa yana magana da ma’aikacin lab d’in Mu’azzam na mik’o masa samples guda biyu cikin leda.. D’aya hular B.A.T ne d’aya kuma bata iya hango menene a ciki ba.
Tai saurin mak’alewa gefe sanda taga Mu’azzam da Mutumin sun fito yana jaddada masa cewa yana so komai ya tafi perfect.
Mutumin yace baida matsala zai k’ok’ari result d’in ya fito da wuri..
Maleeka ta lab’ab’a ta shige burut cikin Lab d’in ta mak’ale a bayan k’ofa ba tareda sun kula da ita ba.
Daidai sanda Mu’azzam sukai sallama da mutumin ta shige store d’in dake cikin Lab d’in.
Ta ramin k’ofa take hango mutumin yanda ya d’auki Samples d’in da Mu’azzam ya basa da alama aiki yake so ya fara gudanawar kansu..
Maleeka Ta girgiza kai tace “Bazan bari ka samu result mai kyau ba Mu’azzam... Lokaci guda ta janyo wasu takardu nan cikin store d’in suka zubo k’asa wanda hakan yaja hankalin mutumin..