← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 175

Sashe 118

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mommy Ta girgiza kai tace “Haba ke kaw Safeenah. Yanzu fah Mu’azzam a tafin hannnunki yake sai yanda kikaga damar juyasa. Yanzu lokaci ne da zaki d’aga darajarki a idanunsa ba wai kiyita lik’e masa kaman wata ‘yar anace ba. Ai idan kinaso ya yarda ya amince ciki gareki ba ke ya kamata ki kirasa ba. Ni ce nan zan kirasa na kuma sanar dashi halinda kike ciki.. Na tabbata idan yaga kirana bazai tsallake ba zai d’aga.”

Safeenah tai shiru tana duban Mommy kafin Mommyn ta jinjina kai a hankali, tai kiran mai aiki ta d’auko mata wayarta a uwar d’aki.

Ana kawo wayar Mommy Ta danna kiran Mu’azzam yayinda Safeenah Ta kafeta da idanu.

**

Mu’azzam kaw suna tafe saman kwalta shida Assad wayar Mommy ya kuma shigo masa bayan kiran Safeenah ya k’araci ruri bai d’aga ba.

Assad ya dubesa ya girgiza kai kad’an yace “Wai bazaka d’aga kiran nan ba.. Zai iya zama wani abu ne mai mahimmanci.”

Ba tareda ya dubi Assad d’in ba, idanunsa da hankalinsa naga tuk’in mota da yake yace “Mommy ce mai kira nasan duk bazai wuce kan fitinar Safeenah bane.”

“Haba Mu’azzam Mommy Ta wuce kaga kiranta kai biris da ita.. Ka daure ka d’aga kaji ko menene.. Tinda har kaga Safeenah ta kira sann ga Mommy na kira na tabbata it might be something serious.. Ko ba komai Mommy uwa ce ka d’aga wayarta dan Allah.”

Gajeren fuci ya fuzar kafin ya d’aga wayar ba tareda yace uffan ba tinda yasan shidai a idanun Mommy Sarkin laifi ne.

Daga d’aya b’angaren Mommy na jijjiga kaman wani Mu’azzam d’in na ganinta take fad’in “Ka rik’e gaisuwar ka dama bana so..” Saida tai fasali kafin tace “Mu’azzam, kazo ka d’auki matarka Safeenah ko dan ajiyan da kayi cikin cikinta.”

Out of the blue yaji maganar wanda har saida yasa ya kusan gwaran motar gabansa dan baima kula traffic light ya tsaida su ba.

SameenaAleeyou📚

*GIDAN ARO*

*60*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

D’if yaji Mommy Ta katse kiran ba tareda Ta saurari abinda zaice ba.

Ya dinga nanata maganar Mommy a kwanyarsa yana ji kaman sautin maganar cikin kunnensa. Dik maganan da Assad ke masa yana fad’in an basu koren wuta baiji mai Assad d’in ke fad’i ba har saida ya soma jiyo horn daga motocin dake bayansa sahu sahu.

A hankali ya soma jan motar yana kuma jin maganar Mommy har wann lokacin.

“Are you alright..?” Assad ya tambaya daga yanda yake zaune gefensa.

Bai amsa Assad ba sai canza hanya da yai ya d’auki hanyar gidan Daddy dan dama kusan layin gidan suke. Assad ya zuba masa idanu dan yasan tinda Yai shiru bai amsa ba idan zai kwana a wajen yana tambayarsa ba lallai ya amsa d’in ba.

Suna isowa Assad ya dubesa kad’an yace “Daddy fah yana ciki ne..? Naga kusan duka motocinsa gasu nan a gida.”

Girgiza kai Mu’azzam d’in yai jikinsa duk ba kuzari “No yana Adamawa..”

Gyara zamansa cikin kujera Assad yai yana fad’in “Tinda baya nan no need na shiga ka shiga kai Bikon matarka kai kad’ai dama da Daddy na nan ne da Sai na shiga na tayaka biko.. A fito lafiya.” Ya fad’I yana mai tura kai cikin kujera cikeda zolaya.

Mu’azzam bai ce masa komai ba sai dubansa da yai kad’an kafin yasa kai ya nufi cikin gidan.

Zaune ya hango Safeenah a parlor fruit salad bowl ajiye gabanta. Aiko Safeenah tana jin alamun shigowarsa tai saurin ture kwanon fruit salad d’in ta soma yunk’urin amai kai kace da gaske aman ne ke taso mata.

Cikin sauri ya k’araso parlorn yana ambato sunanta “Feenah are you alright.? Do you need help..?” Yana maganan yana k’ok’arin duk’awa kanta.

Safeenah bata amsa sa ba sai k’ok’arin k’wak’ulo amai take tana rik’e cikinta tana kiran Mommy.

Babu shiri Mommy ta k’araso tana raba tsakanin Mu’azzam da Safeenah take fad’in “Safeenah sannu koh.. Cikin ne.. Tashi muje na rakaki bathroom.. K’ok’arta ki tashi..”

Kuka Safeenah ta fashe dashi tana kuma narkewa take fad’in “Mommy cikina it hurts.. Mommy bazan iya tashi ba.. Wayyo Mommy..”

Mu’azzam ya d’an kuma matsowa kaman mai son taimaka wa Safeenar.

“Kar ka kuskura ka tab’a mun ‘ya kauce ka bamu waje..” Mommy tace tana rik’o Safeenah, Mu’azzam ya d’an matsa gefe kad’an ya zuba masu idanu har suka nufi toilet.

Furzar da huci yai kad’an yana mai daidaita tsayuwarsa, nan idanunsa suka sauk’a kan takarda dake gefen Safeenah. Ya k’arasa ya d’auki takardan yana karantawa. Sakamakon gwajin cikin da aka mata ne wanda yai daidai da lokacin data sha poison har aka bata gado a asibiti.. Safeenah nada ciki har poison take sha duk a sabida shi.. What if wani abu yaje ya sami d’an.. Koma cikin ya fice gaba d’aya.. Baya fata rashin hankalin Safeenah yasa ya rasa D’ansa ko ‘yarsa dake cikinta.

Yaita juya takardan yana kuma nanatawa cikin zuciyarsa, Wai shi Mu’azzam zaiyi D’ah.. Allah mai iko.. Sai kuma yaji murmushi from no where na zuwa masa.

Yana nan zaune saman kujera har su Mommy da Safeenah suka fito, Mommy na tallafe da ita. Yanda Mommy ke riritata Kai kace kanta aka soma yin ciki.

“Sannu ko.. Kina buk’atan wani abu ne..?”

Idanunta a lumshe tace “No Mommy.. I just need to rest.” Ta fad’i daga nan yanda take kishingid’e.

Mommy ta dubi Mu’azzam da ya tsare Safeenar da idanu, har lokacin takardan na nan cikin hannunsa “Toh likita yace kar a dinga d’aga mata hankali.. High risk pregnancy ne da ita.. Matuk’a tana shiga damuwa komai ka iya faruwa..” Daga haka bata saurari mai zaice ba ta juya ta fice.

Mu’azzam baice komai ba, kansa na duk’e har Mommy ta gama maganganunta.

Tana ficewa ya taso daga kujeran da yake ya dawo kusan na Safeenah.

Safeenah tana jin alamun dawowarsa kusan kujeranta, tsaban kewarsa da tai sai taji kaman ta rungumosa ta sanar dashi irin missing d’insa da tai.. Amma sai Tai k’ok’arin rik’e kanta sabida ta d’auki shawarin Mommy na cewa Ta nuna masa itama mace ce kuma tanada aji da matsayi musamman yanzu da zata bashi abunda babu wata mace da Ta tab’a basa wato D’an cikinta. Muryarsa ta sinkayo Wanda Ta jima bataji ba, muryar da duk duniya babu muryar da take jin dad’in sauraro sama dashi.

“Why didn’t you tell me.. Maiyasa baki sanar dani tuntuni ba.?”

Idanunta a lumshe still tana nan kishingid’e take fad’in “Ka damu ka sani ne.. Yanzu ma ba don ina cikin mawuyacin hali ba da bazan bari Mommy ta kiraka ba..” Muryarta ya soma rawa irinta mai kuka “Kayi neglecting d’inmu nida abinda ke cikina.. Baka damu kasan wani hali nake ciki ba.. Yanzu idan aka haifo D’an nan yaji ga abinda Dad d’insa yaiwa Mom d’insa lokacin da nake d’aukeda cikinsa kana tunanin yaron zai tab’a yafe maka ne..?”

Ta bud’e idanunta masu zuban hawaye “Every single night cikin pain nake bacci sabida high risk pregnancy da nake d’auke dashi.. Dr ya bani bed rest ko toilet wasu lokutan bana iya zuwa sai Mommy ta taimaka mun.. Duk baka San wann wahalan da nake sha ba bayan cewa D’an nan ba nawa ni kad’ai bane harda kai.. And idan na haifesa har sai ka fini gadara dashi.. Sabida ku maza haka kuke.. Mace zata d’auki ciki na tsawon watanni tara.. Ta raini kayanta tayi enduring duk wani pain amma sabida son zuciya irin naku na maza ku amshe yaron nan ku rabasa da uwarsa yayi tashin maraici.” Ta gyara zamanta tana ci gaba da fad’in “Irin haka ne kake so ya faru da d’anmu..? Do you really want our child to grow up without a complete family... Do you really think your decision won’t affect our child..?!”

Tinda Ta soma magana yake tattara naman goshinsa yana furzar da iska a hankali. D’agowa yai had’ida dakatar da ita da fad’in “Enough Safeenah.!”

Tai Burki tana dubansa da idanunta masu zuban hawaye.

Daga nan yanda yake zaune ya d’an rank’wafo hannayensa saman gwiwoyinsa yake jinjina kai yana fad’in “My child won’t grow up without a complete family in sha Allah.” Yana maganar yana jinjina kai alamun tabbatarwa.

Wani irin sanyi Safeenah taji ya ratsa zuciyarta tana jira taji yace ya maidata d’akinta sai sinkayo muryarsa tai yana fad’in “Have you forgotten.. Inada mata, and I’m hundred percent sure zata kular mun da d’ah na ina raye ko bana raye..” Yaci gaba da jinjina kai still yana duban Safeenah wacce ta daskare tana dubansa “I’ll be a parent to my child.. Koda ban zama miji ga mahaifiyarsa ba.”

Baikai aya ba ya hango Safeenah tana sauk’owa daga saman kujera cikin hawaye. Lokaci guda ta duk’a gabansa ta had’e hannayenta biyu waje guda alamun rok’o..

Girgiza kai ya shigayi yana furta “What are you doing Safeenah.. Please get up..”

Bata tashin ba, taci gaba da hawaye tana fad’in “Nasan ni mai laifi ce.. Nasan nayi kurakurai da dama a baya.. But please kar ka bari kurakuraina ya shafi innocent soul d’in dake cikina... Ko banci darajan kasancewa ‘yaruwarta ba.. Naci darajan gudan jininka dake cikina.. Dan Allah kar ka bari D’anmu ya fito duniya ya tadda iyayensa basa tare.. Punish me all you want.. But please don’t punish our child..!” Ta k’arashe tana shafe cikinta still tana nan duk’e gabansa tana hawaye.

Tinda yake a rayuwarsa bai tab’a jin tausayin Safeenah irin na yau ba.. Allah ya gani baya sonta matsayin mace face ‘yaruwa.. Allah shine shaidar shi yana ma Sadiya soyayyar da bazai iya had’ata da wata mace ba.. Yana tsoron yai rashin adalci a tsakaninsu Ubangijinsa ya tuhumesa.. Amma yau yaji tausayin Safeenah.. Irin tausayinta da bai tab’a ji ba.. Shin yanzu idan Sadiya ta gujeshi zaiji irin ciwon da Safeenah ke ji cikin zuciyarsa..? Tambayar da ya kuma kashe masa gwiwa lak’was.

Cikin kwantar da murya yake fad’in “Safeenah.. Feenah.. Tashi ki zauna..”

Girgiza masa kai tai still tana duk’e gabansa tana hawaye “No.. Sai kace ka maidani..”
Chapter 118 · 0% Book details