← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 175

Sashe 18

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokaci guda ya soma tafiya cikin tsanaki.. Bai zarce ko Ina ba Sai gidansa.. Saida ya iso gidan ya tina ashe su Safeenah na gidan ya kwance masu karnuka..

Ya ida shigo da motarsa yai parking a gefe Karnukan har sun koma gefe, suna ganinsa suka taso suna shinshina k’afarsa.. Yakai dubansa ga motar Safeenah, a hankali ya janyo chain d’in dake d’aure wuyan karnukan ya maidasu d’akinsu.. Lokaci guda ya isa jikin motar Safeenah..

Ta cikin glass yake dubansu yanda sukai laushi, d’an kad’an suka zube glass d’in ta d’an sama kad’an yanda iska zaike d’an shigo masu kad’an..Safeenah kam kamar ma bacci tai dan azaba, tana tak’ure jikin seat ga bushesshen hawaye kwance saman fuskarta..

Meema ce batai bacci ba amma har lokacin hawaye ne cikin idanunta.. Tana ganinsa ta mik’e wani kukan na zuwa mata.. Saman gwiwoyinta ta duk’a nan kan seat d’in, Ta had’e hannayenta biyu waje guda tana fad’in “Ya Mu’azzam dan Allah kayi hak’uri.. Wllhi na tuba bazan sake ba.. Dan Allah ka k’yaleni na tafi gida na rok’eka...” Ta k’arashe tana mai kuma fashewa da sabon kuka..

Cikin ransa yace ashe k’aryar rashin kunya kike.. A fili kuwa bai furta komai ba.. Kukan Meema ya tada Safeenah.. Tana ganin Mu’azzam ta wani zabura ta mik’e zaune.. Take ta fashe masa da wani irin kuka ba tareda tace komai ba.. Saida tai mai isarta kafin ta tsagaita, cikin rawar murya take fad’in “please take us home..”. Ta fad’i tamkar zata kuma kurma wani ihun..

Basu baya yai kafin ya ciro wayarsa cikin aljihu.. Dialing layin driver d’in gidan yai ya sanar dashi ya shigo Cab yazo ya samesa..

Jim kad’an kuwa driver d’in ya iso da shike gidan nasu babu wani tafiya sosai tsakani..

Car keys d’in motar Safeenah ya mik’a masa bayan ya iso yace ya kaisu gida. Driver d’in ya amsa cikeda girmamawa kafin ya bud’e motar ya shige mazaunin driver.

Abin sosai ya sosa ran Safeenah watau bazai kaisu gida ba dikda yanda ya basu azaban nan sukai Laushi saidai ya kirawo driver ya kaisu.. Tana fama da kanta bazata iya tanka masa sannan wani sabon shakkarsa ne ya d’arsu a zuciyarta hakan yasa batace komai ba Sai mutsuke ragowar hawayen idanunta da take.. Ita dai Meema bata damu ko uban waye zai maidasu gida ba. Burinta kawai ta fice daga gidan ta ganta a gidan mahaifinta..

Suna isowa gida kai tsaye upstairs suka haye a jikace dan dama gidan ba kowa daga ma’aikata sai Mommy da Kiki. Su Daddy da Musaddiq da Inne harmada Aunty Nurah sun tafi Fufore a jiya.. Mommy ce kawai ma a gidan Sai ma’aikata dan Kiki tana WAEC Lesson zatayi trial a SS2.. Meema kuma dama jiran admission d’inta take ya fito a UK amma bayan Mommy taji yanda Safeenah ta watse da mazan turawa ta fara shakkun Barin Meema ta fita karatu waje.

Ummati Dattijuwa cikin ma’aikatan gidan ne ta had’u dasu zasu haura sama a jigace. Tana tambayansu lafiya suke ko iya amsata basayi Meema kam ma da rarrafe take k’ok’arin shigewa d’aki..

Ummati ta girgiza kai kad’an ta shige sanar da mahaifiyarsu.. Domin kuwa babu lafiya tinda har Meema da Safeenah ne zata masu magana basu darara mata tsawa ba.

Koda Mommy ta taddasu Safeenah ke labarta mata duk abinda ya faru.. Tamkar ta rufe Safeenan da duka dan takaici haka Mommy taji.. Ta rasa wace irin wauta ne kan Safeenah.. Wai har Meema ce zata bata shawari ta d’auka.

Mommy tai k’wafa tana duban Safeenar cikeda takaici “Ya miki kyau ai.. Ki godema Allah da bai baki takardanki tin a titi kafin ki tare gidansa ba.. Banda shashanci da dolanci irin naki ta yaya zaki bisa har wajen aikinsa kici masa mutunci kici ma abokiyar aikinsa mutunci without any solid evidence..”

Cikin kuka Safeenah ta katseta da fad’in “Mommy I’ve proof... Sanitary pad d’in is enough evidence.. And Mommy you should have seen her face sanda nake cin mutuncinta ita karuwar.. Wllhi Ko kaffara bazanyi ba cin amanata yake da Ita...”

Dak’uwa Mommy ta dunk’ula mata tana fad’in “Kimin shiru kafin na tashi na tattakaki a wajen nan.. Banda ke shashasha ce sokuwa, idan ma da gaske cin amanar naki yake ta haka ne zaki samu gaskiyan lamarin..? Ta haka ne zaki kare auren naki..? Wannan dolancin da kikayi bashi zai hana ya fasa abinda yake ba idan ma yanayi d’in..Kusanci ma zaki K’ara masa da ita.. Yanzu haka zaije ya lalasheta bayan ya gama cin k’aniyarki.. Kinga wa gari ta waya..”

Safeenah tai shiru tana duban mahaifiyarta tana jin zuciyarta na mata k’una. “Mommy yanzu ya zanyi..?”

“Ya kuwa zakiyi banda ki k’yaleshi har ya sauk’o kafin ki basa hak’uri kan abinda kikai..”

A zabure take duban Mommy “Mommy shi fa ya mun laifi amma kike cewa na basa hak’uri..” Ta shiga bubbuga k’afafu tana turo baki tana kuka take fad’in “Wllhi dama an jima ana nuna wariya gidan nan.. Daga ke har Daddy bakwa tab’a ganin laifin Mu’azzam, dik abinda yayi daidai ne wajenku.. Wllhi Mommy this is not fair..!” Tana maganganun tana kuka ta shige bathroom..

Tsaki Mommy tai cikeda takaicin ‘yar nata.. Ita batasan ba dan komai take so Ta auri Mu’azzam ba sai dan watarana Fortune d’in Mu’azzam d’in wanda Mahaifinsa ya mutu ya bar masu ya dawo hannunsu.. Mahaifin Mu’azzam shike Babba cikin yaran mahaifinsa.. Su Uku ne yaran Jauro Gamji, Abubakar wanda shine Babba kuma shine mahaifin Mu’azzam da marigayiya Ikram, sai Marwan Wanda shine mahaifin Safeenah Musaddiq Maryam(Meema) da kuma Karimatu (Kiki). Sai Salman wanda shine autan Inne kuma shine cikon na ukunsu.. Shi yana zaune ne a can Fufore dan kula da gidan gonar su dake Fufore d’in da kuma Kampaninsu na GAMJI MEAT FACTORY dake Adamawa.. Kaman yanda Daddy ke kula da Kampaninsu na GAMJI DIARY DISTRIBUTION FACTORY dake a birnin tarayya Abuja.. Gidan Gonar da kakansu Jauro Gamji ya mutu ya bar masu shine yake samar da nama da kuma madaran da companies d’insu ke producing.. A halin yanzu Uncle Salman shike kulada Gamji Meat Factory dake Adamawa wanda a baya mahaifin Mu’azzam shike kula dashi. Sannan shi Uncle Salman d’in shi ke kula da Babban gidan gonar nasu dake garin Fufore. A can gidan gonar suke zaune gaba d’aya dan mahaifinsu saida ya k’era gini maiji da lafiya a cikin gidan Gonar wanda tafiya mai d’an nisa zakai kafin ka isa ginin sabida tsaban girman da gidan gonar kedashi bama zakai tunanin a gidan gona kake ba idan ka shige cikin Mansion d’in.. Shuka da shanu suna cen gefe yanda ake kula dasu..

Uncle Salman da iyalansa harma da Inne a nan gidan Gonar suke zaune.. Uncle Salman yanada mata guda d’aya mai suna Shema’u tareda yaransu guda uku duka mata. Babbar zatai tsara da Meema sai sauran k’annenta guda biyu wanda Twins ne...
A lokacin da mahaifinsu Mu’azzam ya rasu Uncle Salman yaso a cire kason Su Mu’azzam da k’anwarsa Ikram a basu tinda dole sunada kaso a both companies d’in.. Kason mahaifinsu.. Ya zaman babu sauran kason mahaifinsu cikin dukiyar.. Babu yanda Uncle Salman baiba Daddy yak’i amincewa da hakan.. Yace wannan kasuwanci ta ahalinsu bazai tab’a yuwa a cire kason Su Mu’azzam a basu ba dole za’a ci gaba da juya musu dukiyarsu ba tareda an bari dukiyar ta salwanta ba, idan shi Salman bazai iya kulada dukiyar ‘ya’yan d’anuwansu ba Wato Mu’azzam da Ikram shi Daddy zai kular masu dashi zaici gaba da juya masu har lokacin da zasu buk’ata.. Koda Mu’azzam ya girma Uncle Salman baisan Ina Daddy ke kai kud’ad’en Mu’azzam d’in ba amma yasan duk budget da za’ai sai an cire nasu.. Yasan har wannan lokacin Mu’azzam da ‘yaruwarsa harma da mahaifiyarsu sunada kaso cikin dukiyarsu.. Wannan kenan..

**
A b’angaren Mu’azzam kusan kwana yai yana tinanin Abinda ya samu mahaifin Sadiya. Baisan dalili ba amma tinanin nasa mahaifin ne ya fad’o masa..Mahaifinsa da ya rasa a Meat cold Room wanda ya shiga inspecting freezer d’in tsautsayi da ajali ya ritsa dashi a can Meat Distribution Factory d’insu dake Adamawa.. Mahaifinsa yayi stucking a cikin meat cold room wanda har yayi ahalinsa sai gawarsa aka cire.. Mu’azzam ya lumshe idanunsa a hankali yana tuna irin mutuwar da mahaifinsa yayi, lokaci guda ya tina jarabawa na cuta da mahaifiyarsa ta had’u dashi ya kuma tuna rasa ‘yaruwarsa Ikram da yayi... A hankali ya shafi fuskarsa da tafukan hannayensa biyu.. Babu abinda yake so a halin yanzu kaman ya kasance da mahaifiyarsa.. Sosai yaji yana so ya tafi Fufore.
Bazai mance sanda aka ciro gawan mahaifinsa da ya sandare da k’ank’ara ba, kwanciya yai saman gawan mahaifin nasa yana kuka kaman dai yanda Sadiya ta kwanta bisa gawan mahaifin nata itama tana kuka..

Bazai tab’a mance kalaman lallashi da mahaifiyarsa ta fara furta masa ba ‘Kai hak’uri Mu’azzam, Duniya GIDAN ARO ce yanda mukazo cikinta kaman bak’i haka wataran zamu tafi mu barta.. Kayi hak’uri kayima Daddynka addu’a muma duka ma tafiya ne idan lokaci yayi’

A hankali ya sauk’e ajiyan zuciya kafin ya mik’e ya nufi motarsa..

Wajajen k’arfe shabiyu da rabi na dare ya shigo gidan. Baibi takan kowa ba ya nufi side d’insa ya soma shirya kayansa jirgin Washe gari yake so yabi zuwa Adamawa.

SameenaAleeyou📚

*GIDAN ARO*

*12*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

A hankali yake takowa yana kuma k’arema wajen kallo, memories d’in baya suna dawo masa.. Daidai jikin wata bishiyar mangoro ya tsaya ya d’aga kai yana duban bishiyar, lokaci guda yake tuna zamanin yarintarsa, sukanyi wasa da mahaifinsa wasan Corps da Bad guys, dama tin yana k’arami yake mafarkin zama D’ansanda domin ya kama masu laifi.. Ya tina wasu lokutan yakan d’ale bishiyar yayi kwanton b’auna Babansa na k’asa yana nemansa.. Sai ya bari Babansa yazo daidai jikin bishiyar Sai ya d’ago bindigar robarsa ta wasa yana pointing Baban nasa dashi yana fad’in ‘Na kamaka.. Freeze or I’ll shoot..’ Ya saki murmushi yana tuna moments masu dad’i da suka kasance ciki shida mahaifinsa.. A hankali ya aje jakarsa jikin bishiyar kafin ya dafa bishiyar ya d’ale.. Sai yana ganin hoton abubuwan cikin idanunsa kaman yanzu suke faruwa, komai yana nan yanda yake babu abinda ya canza Sai rayuwarsu data canza..
Chapter 18 · 0% Book details