← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 175

Sashe 83

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kauda zancen Mu’azzam yai da fad’in “Wai ina Shaheed ne..?”

“Ya fice d’azu amma yace ba jimawa zai ba..”

Ya jinjina kai kad’an kafin yace “Maleeka tazo ta dubaka..?”

Assad ya d’anyi jim kafin ya girgiza kai yace “Yusuf dai yace min jiya Sun shigo ina bacci.. Why.. Maiyasa ka tambaya.?”

Mu’azzam ya k’urama waje guda idanu kafin ya d’ago ya dubi Assad yace “Haven’t you noticed anything suspicious tareda Ita..?”

Assad ya girgiza kai yace “Ban fahimta ba..?”

Mu’azzam ya tako kad’an kafin yaci gaba da fad’in “Randa muka fita operation d’in nan.. Something was off with her.. She looked quite disturbed.. Kaman tana b’oye wani abu..?”

Assad ya murmusa yana mai d’an girgiza kai kafin yace “Wacce Ta ceci rayuwarka ne zaka mata wannan zargin.. You owe her a huge debt of gratitude.. She saved your life Mu’azzam..”

K’ura masa idanu Mu’azzam yai kafin yace “Da alama har yanzu baka fahimci abinda na gano ba.. Naji she saved my life.. But Maiyasa babu wanda yaga mai harbin cikin kai da Yusuf sai ita..? Sannan muna isa wajen aka soma attacking namu alamun informant d’insu ya sanar dasu muna hanya..”

Assad yai shiru yana nazari kafin ya dubi Mu’azzam yace “Kana tunanin tana aiki dasu Danger.. And she could be the mole in our group..?”

Ya jinjina kai a hankali kafin yace “Possibly..” Ya gyara tsayuwarsa kad’an kafin yace “Kawai ban yarda da ita ba Assad.. Inaji a jikina itace mai mana zagon k’asa..”

Assad ya d’an sauk’e ajiyan zuciya kad’an kafin yace “Ban tab’a kawowa koda tunanin Maleeka zatai abu mai kama da haka ba..”

Mu’azzam ya jinjina kai yace “We are still not sure.. But they say mugu baida kama..”

Assad yace “Haka ne..Kace wani abu..” Ya k’arada yaushe ne DNA result d’in B.A.T zai fito.?”

“In three days time.. Nan zuwa gobe kenan..”

Assad ya d’an gyara daga yanda yake kishingid’e yana fad’in “Nima dai bazan wuce kwana biyu a nan ba.. Na riga na warke.”

“Hey don’t rush Detective.. Ka bari ka ida samun lafia babu abin hanzari.. Duk da cewa yau a meeting d’inmu da DIG mutuminka neman duk wata hanya da za’ai watsi da case d’in nan yake.. Amma babu abinda zai achieving bazan bashi wann satisfaction d’in ba..”

Assad yace “Jaja will never backdown.”

Mu’azzam ya jinjina kai yace “Ka barshi idan b’era na Yawo mage na Yawo zasu had’e wata rana..”

Assad yace “Kenan idan Jaja na kare ‘yanta’addan nan zai iya yuwa yana aiki tareda Maleeka.”

Mu’azzam ya jinjina kai yace “Exactly.. Nasan kamasu redhanded zai matuk’ar wuya but believe me, we will play myth games.” Ya k’arashe yana jinjina kai a hankali lokaci guda Ya duba agogon dake d’aure hannunsa na hagu “I’ve to go now na maka hira da yawa ai..”

Assad ya murmusa yace “Mai iyalai.. Aima kayi k’ok’ari.. Thank you very much..”

Girgiza kai kurum Mu’azzam yai kafin yace “Don’t let me punch your wound.”

Assad ya darara kad’an daidai lokacin Shaheed k’anin Assad ya shigo suka gaisa yana takama Mu’azzam d’in.

**

Babu yanda Meema batai ba Patrick ya barta Ta shiga wajen Safeenah amma fir ya hana yace Safeenar ce tace ita bata San da zuwan wata Meema ba, bama ta da k’anwa mai wann sunan.

K’arshe Safeenar da kanta Ta fito tana yatsina fuska take duban Meemar daga gate yanda Patrick ya hanata shiga.

Meema da Ta hango Safeenah ta kuma saurin matsowa jikin gate d’in tana fad’in “Addah Feenah please let us talk.. I have something important to tell you..”

Patrick ya dubi Safeenah yace “Ma’am, should I let her in..?”

A yatsine Safeenah ke duban Meema kafin ta dawo da dubanta ya Patrick tace “Don’t you dare.. Kai ko mai kamanninta ce tazo kar ka barta Ta shigar mun gida.. I don’t know her.”

Meema baki sake take duban Safeenah kafin tace “Addah Feenah ni kike kora haka daga gidanki har kina cewa ko mai kamanni na kar a bari ta shiga..? Addah Feenah ni ce Meema fah.. Your sister..”

Safeenah ta juyo tana aika mata mugun kallo “I don’t remember having a sister like you..”

Ta maidoda dubanta ga Patrick tace “Kai kuma idan ka barta ta shigo a bakin aikin ka.. Idan ta matsa sai ta shigo ka kwance mata karnukan nan..” Daga haka Safeenah sa kai tai ta shige cikin gida abinta.

Aka bar Meema baki sake tana duban Safeenah har ta b’acewa ganinta.

Fuzar da fuci kad’an Meema tai kafin Ta wuce ta shiga mota ta bar wajen.

Tana isowa gida ta tadda Kiki tana jiran k’arasowarta. Jiki babu laka Meema ta zauna cikin kujera tana kwance belt d’in takalmin dake k’afarta.

Kiki Ta dubeta tace “Ehen, ya kukayi da Adda Feenah..?”

Meema ta tab’e baki kad’an tace “She wouldn’t listen to me.. Tama hanani shiga Gidanta.. Tayi instructing security man d’insu cewa idan na shiga ya kwance min karnuka..”

Baki sake Kiki ke dubanta “Addah Feenah ce ta miki haka.. Anya kuwa Meema..?”

Meema ta kuma tab’e baki tace “Kinsan dai na daina tsara zance.. Wllhi gaskiya nake fad’a miki.. Addah Feenah shut me off..”

Kiki ta jinjina kai cikeda Mamaki “Yanzu kece Wai Addah Feenah ta kora daga gidanta..”

Meema bata kai ga bada amsa ba suka sinkayo muryar Mommy tana fad’in “Wacece Safeenah ta kora..?”

Kiki Ta dubi Mommy tace “Mommy Wai fah Meema ce Addah Feenah ta hana shiga gidanta.. Can you imagine..”

Mommy ta jinjina kai tace “Ai Safeenah ta zama sallamammiya.. Ku k’yaleta bata cikin hayyacinta.. Gata ga namiji idan ya gurza mata guda d’aya k’wakk’wara zata dawo cikin hankalinta.. Sannan ne zata nemi ahalinta..” Mommy tana ida fad’in haka tai k’wafa kafin tai shigewarta zuciyarta fam takaicin Safeenah.

Meema da Kiki suka dubi juna kawai ba tareda sunce komai ba.

**

Tana jin shigowar motar Mu’azzam Ta mik’e tana gyara kwalliyarta. Abincin da tai googling Ta girka Ta shiga jerawa saman dining table.. Tayi kyau kam dan kyau dan Safeenah akwai iya gayu ma jiki da kwalliya. Saidai fah kana iya hango kwantattun k’ura cikin gidan Dikda kuwa ta daure tayi picking wanda idanu ke iya gani.

Mu’azzam na shigowa Ta tafi Ta D’ale jikinsa tana masa sannu da zuwa.

Ya sakar mata gajeren murmushi yana mai amsa gaisuwarta.

“My Halal.. Nayi kewarka da yawa.. I thought zaka dawo da wuri.” Ta k’arashe tana turo baki.

Murmushi ya sakar mata a d’an gajiyye kafin ya kai dubansa ga dining table yaga komai a shirye.

Da mamaki ya juyo yana dubanta “You cooked all this..?”

Ta jinjina masa kai tana juya idanu “Of course..”

Ya d’an rage girman idanunsa yana dubanta “For real..?”

Ta d’an turo baki tana juya idanu “Haba my Halal na maka girki instead kaji dad’i shine kake doubting d’ina..”

Ya jinjina kai yace “Naji dad’i.. I’ll take a shower first Sai na sauk’o muci abincin..” Ya k’arashe yana mik’a mata k’aramar shopping bag irin wacce ya bawa Sadiya.

Safeenah ta Ware idanu tana amsa “Wow.. Menene wann. A surprise gift.?” Ta k’arashe tana ciro kwalin sabuwar wayar.

Mu’azzam yace “Nasan bata kai naki kyau da tsada ba.”

Rungumesa tai tana fad’in “Duk abinda ya fito daga wajenka is priceless a wajena.. Thank you My Halal.”

Ya sakar mata murmushi kafin yace bari yai wanka.

Ta jinjina kai cikeda jin dad’i tana mai take masa baya.

Da k’yar ta barsa yai wanka da kansa. Shiryawa ma ita ta tayasa.. Suka nufo parlor a tare ta mak’alesa tsam cikin jikinta. Safeenah Ita Ta janyo masa kujera ya zauna kafin Ta soma serving nasa.

Kallo d’aya yaima abincin yaji ya k’oshi, bai dai ce komai ba har ta soma serving abincin.

“Do you want me to feed you..?” Ta fad’i tana mai zama kujerar gefensa.

“Kar ki damu I can feed myself.” Ya fad’i yana janyo plate d’in.

Spoon d’aya yai ya dakata..

Safeenah ta tsaresa da idanu tana duban reaction d’insa. Yinin ranan a YouTube ta k’are tana checking recipes d’in da zata girka masa.

Da k’yar ya had’iyi abincin da ya saka bakinsa yai saurin janyo ruwa ya tsiyaya a cup yana kwankwad’a “It’s too spicy.. Wann abincin baza’a iya ci ba Safeenah.. Ga gishiri ga yaji.. Ya kuma janyo ruwa yana sha yana hura iska ma bakinsa.

Safeenah tai saurin matsowa kusansa ta amshe glass cup d’in Ta aje saman dining table tace “Nasan maganin yajin..” kafin yai aune ta rufe masa baki da nata.. Daga nan bata yarda Ta bar jikinsa ba har saida Ta tabbata an isa yanda take so.

K’ara shiryawa yai cikin k’anan kaya kafin ya kuma ficewa.

Safeenah fitowa tai daga bathroom taga baya nan.. K’aran ficewar motarsa kurum taji.. Tai saurin janye labule tana lek’e tana mamakin Toh ina ya kuma ficewa..?

Kodai wajen wancan ‘Yariskar ya tafi ne..? Toh amma ai basa tare yanzu dama auren mission ne sukai ta tabbata Mu’azzam babu abinda zai da wann yarinyar tinda har Ta gama zamanta cikin gidan babu wani abinda ya shiga tsakaninsu.. Bazata saka ma ranta wani damuwa ba yanda Ta samu yanzu suke zaune lafiya tana samun kula da tarairaya daga mijinta.

Sauk’owa k’asa tai tana duban abincin da suka kasa ci. Tai tsaki a hankali tana yatsina fuska “Kai Kai Feenah anya zaki iya wann d’awainiyar..?” Ta tambayi kanta tana duban gidan. Tsaki tai kafin ta isa dining table d’in ta shiga d’iban abincin tana juyewa cikin dustbin. Tanayi tana mitan bazata iya wann wahalar ba. K’arya da ciwo gwara taci gaba da yo masu order idan yaso sai tace ita ta girka.

**

Duba d’aya Sadiya tai masa ta sadda kanta.

Yai gyaran murya kad’an kafin yaci gaba da fad’in “Bazan k’ara tilasta miki komai ba, kuma bazan kuma d’aukan ki bada amincewarki ba.”

Ta d’an girgiza kai kafin tace “Amma ai kai da kanka kace auren mission mukai kuma gidanka tamkar dai GIDAN ARO yake a wajena.. Maiyasa zan koma bayan an gama mission d’in.”

Idanunsa k’ar akanta “Nayi alk’awari ma Inne zan kai mata ke.. Bani d’in bane mai son tafiya dake..”

Murmushin da yafi kama da yak’e tai kafin tace “Maiyasa ka kasa sanar da Inne gaskiya cewa Auren Mission kai dani.. Kuma mission d’in ya k’are.”
Chapter 83 · 0% Book details