← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 174 OF 175

Sashe 174

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ka kwantar da hankalinka Alhaji. We are currently operating on her..kuma..” Bai k’arasa fad’in abinda yake cewa ba suka soma jiyo sautin alarm daga cikin ER d’in ga wasu nurses sun fito gudu gudu.. Babu shiri Likitan ya nufi Emergency Room d’in Bakin Daddy na karanto Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.

SameenaAleeyou📚
*GIDAN ARO*

_(2022)_

*85*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Tashin hankali wanda ba’a saka masa rana, gidan duniya ake ma taken GIDAN ARO wanda duk ya shigo cikinta toh kuwa ko shakka babu akwai ranan da zai barta da shiri ne kokuwa babu shiri. Hankula sun kuma tashi musamman da ya kasance likitocin sun d’auki tsawon lokaci a d’akin operation d’in, babu wanda ya fito babu wanda gifta balle suyi tunanin jin ba’asi.. Sallah ne kawai yake fitar dasu amma haka suka yini zubur suna jira suji daga likitocin.

Zaune yai cikin masallaci bayan sun ida sallah yana tunanin rayuwar da sukai da Sadiya da kuma Safeenah. Yaita kwararo masu addu’an samun sauk’i domin kaw baya fata ya rasa guda daga cikin su Fatansa shine su sami lafiya gaba d’ayansu.

Saman wasu kujeru suka zauna shida Assad bayan sun fito daga masallacin Assad na kuma tausansa da basa baki kan cewa shi musulmi ne kuma ansan musulmi da d’aukan k’addara a duk yanda tazo masa.
Fuskarsa na duban wani b’angaren yake tuna victims d’in Mommy da Danger. A hankali yake furta “First it was my Dad.. Then Ikram, sann mahaifin Sadiya.. Sann D’an cikin Safeenah.. Yanzu kuma.. Yanzu kuma Sadiya da abin cikinta harma da Safeenah.. Kana tunanin zuciyata zata iya d’aukan duka wad’ann abubuwan kuwa Assad.. Assad banida wann jarumtar.. I’m not that strong..!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya mai cikeda rauni.

Assad ya Dafasa kad’an yace “Kai hak’uri Mu’azzam.. Sann Ka tuna Allah baya d’aurawa rai abinda bazata iya ba. Sann ita duniyar nan ba’a barin wani dan wani yaji dad’i.. Kowa lokacinsa k’ayaddade yake jira.. Dukanninmu kuwa.”
Ya k’ura ma Assad Idanu kafin ya jinina kai a hankali.
Da kalaman Assad masu kwantar da hankali ya d’an samu nastuwa kafin suka mik’e suka koma cikin asibitin.

Ana a haka Umma da Uncle Ramadan suka k’araso. Allah sarki Mamyn Mu’azzam sai ta tafi ta rungume ‘Yaruwarta yayinda Uncle Ramadan ya k’araso ga D’anuwansa Daddy shima yana k’ok’arin tausarsa da fad’a masa kalamai na kwantar da hankali.

Haka Umman Sadiya ma gaba d’aya sai ta shiga tuna rashin mahaifin Sadiyar da sukai.. sai tana ganin kaman zata rasa Sadiyar ce ma. Tsananin tashin hankali ta shigesa, Mamy taita tausanta tana bata baki. Mu’azzam ma Musaddiq ne mai k’arfin halin basa baki saiko Assad. Gaba d’aya hankulansu ba’a kwance yake ba kana ganinsu.

Can wasu likitoci guda biyu suka fito suna rage nose masks d’in dake rufe fuskokinsu.

Mu’azzam dake zaune Assad na dafe dashi saurin mik’ewa yai ya nufi likitocin yayinda su Daddy suka tako masa baya.

Daddy ya sami zarafin tambayarsu “Dr how are they.. What’s the situation..?” Yai maganar cikin rawar murya

Likitan ya dubesu Sai ya d’an furzar da huci kad’an “Da farko ina mai baku hak’uri..”

Ai bai kai aya ba Mu’azzam ya soma girgiza kai yana fad’in “No.. No.. Dan Allah kar ka bamu hak’uri Dr.. Just tell us sun samu lafiya dukansu.. Zamu iya ganinsu Ko Dr..?” Ya k’arashe yana k’ok’arin nufan ER saidai tuni Assad ya rik’osa.

Dr ya d’an girgiza kai kad’an yana mai sadda kansa k’asa “I’m sorry.. We did everything we possibly could.. But harsashi ya riga yayi damaging da yawa daga cikin organs d’inta..”

Mu’azzam kam bai tsaya sauraron Likitan ba ya nufi ER a guje ba tareda ya bari wani ya sami zarafin taresa ba.. Saidai yana shiga ya hango mutum kwance saman gado an rufe ta da Farin mayafi.. Sai ya soma tuno sanda aka kawo Dad d’insa a lokacin da ya daskare cikin d’akin K’ank’ara.. An rufesa da Farin k’yalle irin haka, ya k’arasa saman gawan mahaifin nasa ya kifa kansa yana ambaton sunansa yana fad’in ya tashi ya tashi..! Saidai bai tashi d’in ba Mahaifiyarsa ta k’araso ta d’agosa tana kwantar masa da hankali had’ida basa hak’uri. Kalman Mamynsa ya dinga tunowa ‘Mu’azzam kai hak’uri.. Ita gidan duniya ba gidan tabbata bane GIDAN ARO ne wanda kowa zai tafi ya barta, babu wanda zai wuce wa’adin da Allah ya d’ibar masa.. Kai hak’uri kaiwa mahaifinka add’ua..’ Ya lumshe idanunsa hawaye suka gangaro masa yana mai ci gaba da takowa yana tuna sanda ya tsinci gawan Ikram.. Lumshe idanunsa ya kuma yi hawaye naci gaba da gangaro masa. A haka har ya iso jikin gadon. Ya soma k’ok’arin kai hannunsa dake tsananin rawa yana k’ok’arin yaye k’yallen. Kuka ne yaji gadan gadan na zuwa masa sanda yai karo da fuskar Safeenah wanda har kaman ya k’ara Haske na musamman da annuri, zai iya cewa bai tab’a ganin tsananin hasken fuskar Safeenah irin na wann ranan ba, kaman ka kirata ta amsa sabida annuri na musamman da fuskar nata tai... Idanunta a lumshe wanda Ko ba’a fad’a maka ba kasan ta amsa kiran mahaliccinta ne.. Take ya soma tuna abubuwan da suka faru tsakaninsu, Tun tasowarsu har zuwa aurenta da yai da rabuwarsu da cire mata ciki da Mommy tai har kawo yau da ta amsa masa harsashi bayan Danger yayi niyyan kashesa. Hawaye sukaci gaba da gangaro masa yana girgiza kai “Why Safeenah..?. Please get up.. Get up.. Dan Allah ki tashi.. Kinji.. ki tashi.. Ki tashi haka nan..!” Yana maganar hawaye na gangaro masa yana duban fuskar Safeenah. Kifa kansa yai yana kuka sosai daidai lokacin da yaji hannun mutum saman kafad’arsa. D’agowa yai yana duban mutumin wanda ba kowa bane face Daddy.

Cikin zuban hawaye Mu’azzam Ke girgiza kai yana duban Daddy “She saved my life.. Safeenah saved my life Daddy.. She took a bullet for me.. Safeenah ta mutu sabida ni Daddy..!” Ya k’ura mata idanu yana ci gaba da fad’in “Yau ce rananta na farko da ta fito daga asibiti da burin fara sabuwar rayuwar dake jiranta.. Sai gashi ya kasance rananta na k’arshe a duniya.. Daddy Maiyasa Safeenah zata mutu yanzu da rayuwa mai inganci Ke jiranta..!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya yayinda Daddy ya janyosa jikinsa suka rungume juna hawaye na fito masa yake fad’in “Kar ka fad’i haka Mu’azzam.. Safeenah bazata shige lokacin da Allah ya d’ibar mata ba.. Allah ya k’addari lokacin tafiyarta da kuma sanadinta.. Addu’armu shi tafi buk’ata a halin yanzu.. Allah ya gafarta mata yasa k’arahen wahalarta kenan.”
Daddy ya k’arashe yana mai lumshe idanunsa had’ida shafe goshin Safeenah. Hawaye suka d’igo daga idanunsa suka sauk’a saman goshin Safeenah. A hankali Daddy ya furta “Na yafeki Safeenah.. Na yafeki duniya da lahira.. Allah ya baki Aljannah a gidanki na gaskiya.”
**

Allahu Akbar Kabiran.! Idan lokaci yai ba’a jinkirta ma bawa, haka nan Mutuwa bata shawartan waye ya kamata ta d’auka waye ya kamata Ta bari. kowa a GIDAN ARO yake kuma kowa lokaci yake jira. Safeenah ta amsa kiran mahaliccinta, Zuciyar kowa ya cika da alhini na rashin Safeenah. Tayi sadaukarwa mai girma yanda ta ceci rayuwar Mu’azzam, matarsa Sadiya da kuma d’iyarsa dake ciki. Safeenah ta bada nata rayuwar daga k’arshe domin ta ceci Mu’azzam ta kuma dasa aya wa muguntar Mommy da kashe kashen da take na son zuciya.. Tabbas sadaukarwar Safeenah bai tafi a banza ba, domin kuwa Mommy bata sake yin nasara a karo na babu adadi ba wajen ganin bayan matar Mu’azzam da cikin jikinta.. cikin ikon Allah da k’udurarsa anyi nasara ceto ran Sadiya harmada abinda Ke cikinta. Tabbas Allah shine mai raya wanda yaso ya kuma kashe wanda yaso.. Dik yanda Hajara taci burin taga bayan Mu’azzam da sauran Farin cikin da ya rage masa na wutin gadi a GIDAN ARO bata sami wann nasaran ba, Allah ya nuna mata iyakarta kuma yayi ikonsa akan Sadiya da abinda Ke cikinta. Ranan da wani Ke barin GIDAN ARO ranan wani ke zuwa. A ranan da Safeenah Ta amsa kiran mahaliccinta a ranan aka ciro wa Sadiya d’iyarta. Dikda cewa Likitoci Sun sha wahala matuk’a kafin su cire harsashin da jariryarta hakan baisa an rasa ko guda daga cikinsu biyun ba domin kuwa Allah shine mai yin yanda yaso ba tareda shawari, yarda ko amincewar wani ba.. Saidai Sadiyar tana a coma ne har na tsawon kwanaki bakwai . A ranan kuma akai bakwai d’in Safeenah. Koda Sadiya ta farka batasan sun rasa Safeenah ba. Abinda ta farka dashi shine sunan Safeenah, sabida kafin ta fad’i sumammiya sanda Mommy ta tanad’a mata harsashi taga sanda Safeenar ta amshe bindigar hannun Mommy tai pointing kanta da bindigar.

Mu’azzam kaw a asibti yake yini wajen matarsa. Yau d’in na zaune gefe rik’e da Babynsu yana d’an jijjigata yana mata wasa nan ya soma hango hannun Sadiya na motsawa a hankali. Cikin sauri ya mik’e ya isa jikin gadon yana kuma dubanta. A hankali taci gaba da motsa yatsarta guda idanunta na lumshe. Nan ta soma motsa baki tana k’ok’arin ambato sunan Safeenah.

Cikin sauri Mu’azzam ya tab’a k’ararrawar dake mak’ale saman gadon aiko nan take wata nurse ta shigo, nan ya sanar da ita abinda ke faruwa. Sauri sauri tace bara ta kirawo Dr.

Fitanta da kad’an Sadiya ta bud’e idanunta. Fuskar mijinta abin k’aunarta ta soma tozali dashi Wanda ta yanke k’aunar bazasu kuma ganawa ba tun sanda Mommy da Danger suka d'auketa, yana rik’e da wata kyakkyawar jaririya gwanin ban sha’awa.

Murmushi yake sakar mata yana ambato sunanta “Alhamdulillah.! Beautiful you are awake..!” Ya fad’i yana d’aura hannunsa guda saman fuskarta murmushin bai gushe daga saman nasa fuskar ba.

“Safeenah.. Where’s she.. Ina take.. Mommy zata kasheta.. You need to save her.. You.. need to arrest Mommy...” Ta fad’i murya da k’yar.

Saurin dafa hannunta yai yana girgiza mata kai “Calm down Beautiful.. its over now..!”

Dubansa take tana duban jaririyar dake rungume cikin hannunsa tana tsotson yatsun hannunta.

Sai Tai k’ok’arin kai hannunta saman cikinta tana shafawa a hankali tana duban jaririyar hawaye na k’ok’arin ciko idanunta.

Jinjina mata kai Mu’azzam yake murmushi saman fuskarsa alamun eh ga dniyarsu nan cikin hannunsa.

Hawaye suka gangaro ma Sadiya.. Murmushi saman fuskarta take duban jaririyar “Is she..?”
Chapter 174 · 0% Book details