Sashe 157
Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hajara Ta shiga jinjina kai tana ayyanawa cikin zuciyarta, kenan akwai wata mace kwance a Zuciyar mijinta.. Toh wacece wann Hasken da Marwan yake magana akai..? Lallai ya zama dole ta nemo wann matar..
A haka akaci gaba da rayuwa Hajara da mijinta babu abinda ya canza. Yayinda a b’angaren Nuratu da nata mijin zallan soyayya da k’auna mai tsafta suke nunama juna.
Marwan baya zuwa Fufore sai sallah ko wani hidima idan ya taso. Hajara duk na hankalce dashi, Ta kula dik kula da take ganin yana bawa yaransu a bayan wanda yake Bawa D’an Hamma mai suna Mu’azzam ne. Muddin sukazo garin Yaron na wajen Marwan ne. Wane irin soyayya maras misaltuwa yake yima yaron. Abin ya soma damun Hajara nan ma.. Sann ta kula indai Nuratu tana waje toh Marwan bai faye zama ba. Sosai Hajara ta saka idanu kan duk wani movement d’in mijin nata tana karantarsa.
A b’angaren su Nuratu kuwa ma iya cewa damuwarsu bai wuce wani hoto da sisin kobo da suka tsinta tattareda ita ba ita da mijin nata. Gashi bata iya tuna komai balle ta tuna a yanda Ta samesu, saidai daga ita har Abubakar sunfi alak’anta hoton da mai yuwa itada mutumin cikin hoton sunada alak’a. Haka Nuratu take zama ta saka hoton a gaba tana kallo, taita juya sisin kobon ko zata tuna wani abu amma shiru bata iya tunawa. Sosai ganinta cikin damuwan yake d’aga hankalin Abubakar dan idan ka cire wann shida matarsa basuda wata matsala, sai matsalar D’anuwansa Salman da ya addabesa da cewa ya cinye masu dukiya yayi k’ak’a gida akan komai tinda mahaifinsu ya rasu.
Abubakar ya dubi Nuratu dake rik’e da hoton tana juyawa had’ida sisin kobon. Lokaci guda ya kamo hannayenta yace “Zan nemo shi da izinin Allah.. Zan nemo wann mutumin da kike kyautata zaton zai iya zama D’anuwanki ko dai yanada masaniya gameda ahalinki da kuma yanda kika fito.. Amma wann sisin kobon shine key d’inmu.. Shine mabud’in Sirrin dake b’oye na sanin asalinki da yanda kika fito.” Ya k’ura ma sisin kobon idanu yanda yaga an rubuta Black African Team. Sai ya furta “BAT.” A fili.. Lokaci guda yaci gaba da jinjina kai yana fad’in “Zan nemo Bawan Allahn nan da duka abinda na mallaka domin Farin cikinki masoyiyata.”
SameenaAleeyou📚
*GIDAN ARO*
*78*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Wani rana Abubakar zai shiga d’akin mahaifiyarsu ya sinkayo muryarta tana sallah tana kuka tana tuba had’ida rok’on gafarar Ubangijinta. Jikinsa yai sanyi dan a lokacin mahaifinsu bai wani jima da rasuwa ba.. Yasan dik cikin kuka ne da alhinin rashin mahaifinsu, yai tsaye yana sauraronta saidai kalaman da ya soma ji tana fad’i daga k’arshe sune suka tayar mai da hankali.
Fad’I take “Allah na tuba.. Allah ka yafe mun.. Mijina ya mutu baisan yanda Iyalinsa da cikin jikinta suka tafi ba.. Shin suna raye ko sun mace..? Ta haife abinda ke cikinta ko bata haife ba.. Hak’ik’a na zalunci kaina kuma na aikata babban zunubi.. Ya Allah na tuba ka yafeni.!” Kuka yaci k’arfin Inne.
A hankali Abubakar ke takowa kusanta yana dubanta, Sai ya duk’a gefenta hawaye na gangaro masa kaman yanda yake gangaro mata.
Bakinsa ne yaji yana furta “Inne.. Mai kika aikata..?”
Ta d’ago tana dubansa tana hawaye, taci gaba da girgiza kai tana fad’in “Mummunan laifi.. Mai girma wanda ban Sani ba idan Ubangijina zai yafe mun.. Magaifinku ya rasu ba tareda na nemi yafiyarsa ba..” Ta d’anyi fasali kafin taci gaba da fad’in “Dik matar da mahaifinku ya auro ya kawo gidan nan.. Masifana da tashin hankalina bai barinta ta zauna.. Nakanyi furucin cewa gidana GIDAN ARO ne sai ta fice ta bar mun gida.. Toh matar da Baffanku ya aura daga k’ashe A lokacin kuna can tsangayar Malam Sallau da kaida d’an uwanka Marwan Itace tai k’argo a gidan nan har Allah ya nufa akwai RABO tsakaninta da mahaifinku.. Ta samu juna biyu har Ta kusa haihuwa masifana da tashin hankalina bai koreta ba.. Na k’asa jurewa na Kasa hak’ura.. Sai na tafi wajen Malamin tsubbu nace dik yanda za’ai a fitar da Ita daga gidana, da ita da abinda ke cikinta.. Ayi mata Kurciya ta tafi kuma kar ta sake waiwayo gidana balle mijina sann a rufe Bakin mijina kar ya sake tunaninta balle ya tambayi Ina take..!” Inne hawaye Abubakar hawaye.
Inne taci gaba da fad’in “Tanada juna biyu Ta fita Ta tafi.. Har mahaifinku ya koma ga Ubangiji ban sanar dashi ga abinda nai wa matarsa da D’an cikinta ba.. Bamu sake ji daga gareta ba.. Ta haihu bata haihu ba Allah masani.. Kaico na Kaicon son zuciya..!”
Cikin zuban hawaye Abubakar ke dubanta yana girgiza kai “Inne kece kika aikata irin mugun abun.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.. Matar ta tafi tana d’auke da D’an mahaifina.. Mahaifina ya rasu bai sani ba ko ta haihu ko bata haihu ba.. Inne kan wane dalili.. Dukiya.? Wann gadon da mahaifina zai bari.. Kan haka ne kika cutar da wata kika hanata zaman gidanki..?!” Kuka yaci k’arfin Sa yayinda Inne ma ke kuka..
Kuka take tana girgiza masa kai tana fad’in “Sharrin zuciya ne.. Ka yafe mun D’ana wllhi nayi nadama kuma nayi danasani mai tarin yawa.. Kuma nayi alk’awarin sadaukar da sauran rayuwana ga tuba da bautan Allah had’ida hidimta ma Al’umma... Bansan yanda zan samu Harira ba wllhi da na bita na rok’i yafiyarta..”
Girgiza kai yake yana duban Inne hawaye na gangaro masa “Kin aikata mugun abu Inne.. Idan akan dukiyar mahaifina kika aikata haka ki sani bana buk’atar wann dukiyar.. Zanyi sadaukarwa da wann dukiyar... Sann zan d’auki iyalaina muyi nesa da nan Inne.. Bazan iya ba.. Bazan iya ci gaba da zama a nan ba..!” Yana maganan hawaye na gangaro masa yana girgiza kai.
Inne na hawaye Ta kamo hannayensa “Kai hak’uri d’ana kar ka tafi ka barni.. Dan Allah ka zauna.”
Ya girgiza mata kai kad’an kafin yace “Na riga na tsara hakan Inne.. Zanyita rok’ar miki Ubangiji ya yafe miki.. Kinsan Maiyasa..? Sabida ke mahaifiyata ce.. Amma zan d’auke iyalaina daga nan zamu tafi da nisa.. Allah ya yafe miki Inne..!” Yana mik’ewa ya fice ya bar Inne wajen tana kuka had’ida nadaman abinda Ta aikata a baya.
Zai wuce company ya had’uda Marwan, suka jera suna tattaunawa. Marwan ya kula da yanda jikin D’anuwan nasa yake a mace, kaman dai wani abu na damunsa. Ya tsaresa da tambayar meke damunsa.
Abubakar ya murmusa kafin ya dafa kafad’an Marwan yace “D’anuwana nasan dik cikinmu ka fimu zuciya mai taushi.. Zanso na bar maka amanan ahalinmu a bayana.. Ka kular mana da ahalinmu kar ka bari ahalinmu ya rushe..”
Marwan ya murmusa kad’an yana duban D’anuwan nasa kafin ya girgiza kai yace “Kana nan Hamma kuma zamu kula da bayan Baffah tare.. Ka tuna kullum wasiyan Baffah a garemu shine mu so junanmu mu zama tsintsiya mad’auri d’aya sann mu kula da kasuwancin Ahalinmu..”
Abubakar ya murmusa yana hango Musaddiq takwaransa da kuma Mu’azzam da suketa shawagi suna wasan Cop and bad guys a cikin fad’in Gidan gonan.. Lokaci guda ya saki murmushi kafin yace “Mu’azzam D’ansanda yake mafarkin zama Ina fata Takwarana ya gaji mahaifinsa wajen aiki tuk’uru kaman dai yanda kake Marwan ya k’arashe yana duban Musaddiq murmushi saman fuskarsa. Lokaci guda ya k’arada “Allah ya masu albarka”
Marwan ya murmusa kad’an kafin yace “Ameen Hamma..” Sai karantar D’anuwan nasa yake yana ganin kaman wani abu ke d’awainiya dashi.
Abubakar ya d’an murmusa kafin yace “Zanje Factory yanzu.. Akwai abubuwa da dama da nake so mu tattauna Marwan.. Allah yasa lokaci ya ara mana kansa.”
Marwan ya murmusa kafin ya jinjina masa kai kad’an yace “Allah ya kaimu Hamma.. A dawo lafiya..”
Har Abubakar yasa kai zai tafi sai kuma ya juyo ya dubi Marwan yace “Idan baka komai anjima ka sameni a company sai mu tattauna..”
Marwan ya jinjina kai kad’an yace “Ba matsala zan sameka anjima a company in sha Allah..”
Suka sakar ma juna murmushi kafin Abubakar ya dawo da baya ya d’an rungumi D’anuwan nasa.. Su duka biyu suna duban juna cikeda k’auna. Abubuwan da Abubakar yake yanda kasan mai sallama da D’anuwan nasa. Koda yake yai k’udirin zai tattara iyalansa su tafi bayan abinda yaji Inne Ta aikata wa matan mahaifinsu. Bazai iya sanar da D’anuwansa ga abinda ya faru ba sann bazai iya sanar dashi kai tsaye cewa zai tafi da nisa ba sabida yasan irin k’aunan dake tsakaninsa da D’anuwansa.
Salman dake tsaye daga can yana hangensu jinjina kai yai yana sakin huci.. Ya jima da sanin ‘Yanuwan basa wani sonsa, waresa suke kansu su biyu a had’e.. Yai k’wafa cikin zuciyarsa kafin ya shige Mota yabi bayan Abubakar da ya nufi Factory.
Marwan ciki Gida ya nufa.. A hanyarsa na komawa cikin gida ya hangota.. Zuciyarsa yai wani irin tsinkewa.. Yai tsaye yana hangeta ba tareda yasan ya aikata hakan ba. Tana tsaye kusan wani saniya tana rik’e da d’iyarta Ikram tana shafasa hannun d’iyar nata jikin saniyar murmushi saman fuskarta sai wasa ma Ikram d’in take sunata murmushi gwanin ban sha’awa.
Kasa janye idanunsa yai ga wane irin rauni da ya cika idanun nasa.. Ya dinga tina sanda suka tsinceta da yanda ya kwashe sauran kwanakinsa a makaranta yana lissafin yanda zai dawo ya gina soyayyarsa mai tsafta cikin zuciyarta. Tinawa da haramcin abinda yake aikatawa ya sanyasa saurin janye idanunsa ya janye jikinsa ya nufi cikin gida yana istigfar.