← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 175

Sashe 57

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mik’ewa Mu’azzam yai yana fad’in “You’re not the one who’s being fooled by the woman you call her wife..! You are not the one who lost a sister in the most painful way.. So don’t.. even.. ask me to Calm down..!” Yai maganar jijiyar goshinsa na kuma fitowa sosai gumi na kuma tsartsafo masa.

Kafin Assad yace wani abu Mu’azzam ya nufi k’ofa. Assad yai saurin take masa baya yana ambaton sunansa amma inaa ko sauraronsa baiba.

Karo suka kusan yi da Chief Jaja wanda ya nufo Office d’in.

Mu’azzam ya tsaya Cak yana duban Chief da idanunsa da suka gama kad’uwa.

Chief yana murmushi yake shafa hab’arsa lokaci guda yana duban Mu’azzam d’in “Inspector Gamji, I hope you learned your lesson.. You should know there’s no right way to do wrong things.. Next time sai a kiyaye..!” Ya k’arashe yana bubbuga kafad’an Mu’azzam d’in guda.

Maleeka dake tsaye gefe itada Yusuf sai aika ma Chief mugun kallo take musamman da taga yanayin Mu’azzam d’in.

Mu’azzam baice da Chief komai ba har ya gama maganganunsa sai dubansa da rinannun idanunsa da yake.

Lokaci guda Chief ya gyara tsayuwarsa had’ida gyaran murya “Any update regarding your case, Inspector Gamji..?” Ya tambaya yana tsare Mu’azzam d’in da idanu wanda ko motsi mai kyau ya kasa Sai dad’a damk’e wayar Sagir dake cikin hannunsa yake.

Chief ya gyara tsayuwarsa yana karantar Mu’azzam d’in.. Lokaci guda Maleeka da Yusuf suka k’araso yayinda Assad ma gaba d’aya za’a iya cewa ya shiga missed call. Yama rasa mai zai yi sai duban Chief yake yana kuma duban Mu’azzam.

Chief ya dubi Assad ya kuma duban sauran team members d’in Wato Yusuf da Maleeka. Nan yaga gaba d’ayansu kaman an cire masu laka.

“Detectives..!” Chief ya fad’i yana dubansu d’aya bayan d’aya kafin ya tsaida idanunsa kan Assad.

“Shattima.!” Ya kira surname d’in Assad.

Assad ya sara masa “Sir.!”

Chief yaci gaba da fad’in “Any progress..?”

Duban Mu’azzam Assad yai cikin rasa mai zai fad’i.

Yanzu kam ran Chief ya soma kad’uwa wajen b’aci. Cikin tsananin zafin nama yake furta “Why are you all mute.?”

Ya girgiza kai yana ci gaba da furta “It seems we assigned this case to bunch of incompetent Detectives.. Am I right.?” Ya k’arashe cikin daka tsawa. Yayinda suka duk’ar da kawunansu k’asa idan ka cire Mu’azzam wanda har lokacin duban Chief yake bai daina murza hannunsa ba.

“Give me updates now. Detectives.!” Ya k’arashe cikin tsananin daka tsawa.

Zuciyar Chief fari k’al ganin basu ce komai ba, yanzu ya tabbata dole a gaji ai closing case d’in kaman dai yanda suka tsara. Ya wani gyara tsayuwa yasha mur sosai kafin ya soma jinjina kai cikin tsananin b’acin rai yana duban Mu’azzam d’in “I am going to warn you for that last time Inspector Gamji..! Bring all your team together to collaborate more effectively on this case.. Unless kana so ai maka retire before your retirement period.!”

Lokaci guda Mu’azzam ya d’ago wayar daketa faman dunk’ulewa cikin hannunsa yana nunawa saitin fuskar Chief.

“Meye wannan..?” Chief ya tambaya.

“It’s Sagir’s cell phone.. Sir.!” Mu’azzam ya basa amsa kai tsaye.

Dukda cewa zuciyar Chief ya yanke, ya kuma razana da ganin wayar Sagir d’in amma Sai ya wayance yace “Good.. At last something good came out of your investigation.! Good Inspector Gamji.. You’re one of our best agents. Nasan bazaka bamu kunya ba.. Let’s see what you found inside..” Ya k’arashe yana mai kad’a kafin ya nufi office yana fad’in su biyosa.. Babu musu suka bi bayan Chief.

Zuciyar Chief sai yankewa take. Ya kula Mu’azzam bazai tab’a dakatawa ba har Sai ya tono komai. Ya tsani Mu’azzam.. Sannan zai komai in his power ya tabbata Mu’azzam ya bar aikin D’ansanda for good.

**

Su Safeenah suna komawa guda suka tadda Daddy zaune harabar gidan saman kujeru na shak’atawa. Sai kallon kallo suke ma juna ganin Daddy ras kaman ba shine Aunty Shemau ta kira ta sanar dasu Baida lafiya sosai ba. Dan har kaman kuka sukaji tanayi cikin wayar.

Gaba d’aya suka fito suka nufi mahaifinsu wanda Mommy ke zaune gefensa ta cika tayi fam sai girgiza take.

A guje Meema da Kiki suka k’arasa suka rungumesa “Daddy wai bakada lafiya..? Daddy munji tsoro sosai.?”

Murmushi ya sakar masu ya shafi fuskokinsu kafin yace “I’m fine now.. Ku kwantar da hankalinku Kunji koh...”

Kiki ta kuma rungumarsa tana fad’in “Daddy banso mu rasaka.. I can’t even bear the thought of it..”

Ya shafi kanta kad’an yana murmushi kafin yace “Ku shige ciki zamuyi magana da Addarku..”

Babu musu suka shige dan Mommy kam basu ma ga fuskar mata magana ba tsaban tafarfasa da take.

Safeenah dake tsaye daga baya tana hawaye suna shigewa ta k’araso ta zube kanta saman cinyar Daddy dake zaune kan kujera. Kuka take sosai tana fad’in “Daddy it is true..! Daddy Mu’azzam mace yakai cikin gidana.. Daddy zan mutu.. Mutuwa zanyi Daddy.. I can’t take this anymore..!”

Bai hanata kukan har saida tai mai isanta kafin ya dubi Mommy yace “Can I have a moment with my daughter, Please.”

Mommy Ta dubesa da mamaki kafin Ta soma magana cikin huci “Wllhi wllhi kaji na rantse maka da Allah sai na maka Mu’azzam a kotu.. Ko ka shawo kan Safeenah ka danneta wllhi sai nayi k’aran Mu’azzam kan abinda yayima Safeenah. Har ofishin nasu zan tafi na kai masa sammaci wllhi.. Babu ruwana da cewa shi D’ansanda ne.. Idan shi bakin bindiga ne k’arewar tsaro wllhi Sai na maka k’ararsa ehe..!” Ta k’arashe tana mai mik’ewa tsaye.

Daddy ya d’ago yana dubanta “Kin gama.?”

Bata basa amsa ba sai ci gaba da jijjiga da take.

“Idan kin gama leave us alone with my Daughter.. Please..”

Mugun kallo ta watsa masu daga shi har Safeenar kafin Ta wuce fuu kaman zata tashi sama.

Aunty Shemau dake tsaye saman Balcony d’in Mommy akan idonta komai ya faru. Tana ganin Mommy ta nufo cikin gidan ta nufo k’asa itama.

Daddy ya d’ago Safeenah ya zaunarta saman kujerar gefensa yanda Mommy ta tashi. Har lokacin Safeenah bata daina jan zuciya ba alamun taci kuka.

Daddy yai gyaran murya a hankali kafin ya soma fad’in “I know you’re hurt.. And you’ve the right be angry.. Dole kiji zafi dan jin zafi.. Amma abinda nake so ki sani shine tashin hankali bai tab’a kawo solution wa matsala ba, saidai ma ya k’ara b’ata komai.”
Ya d’anyi fasali kafin yaci gaba da fad’in “Safeenah my Daughter, don’t allow your anger to consume you.. Kiyi hak’uri mubi komai a sannu.. Give your husband a chance to explain himself.. Bamusan dalilinsa na yin auren ba.. And yace zaiyi bayani, I’m sure Mu’azzam yanada bayanin da zaiyi.. You and I both know Mu’azzam is a good person.. He might have his faults as a human being, but he’s not a bad person.. Ba ina fad’in haka dan nafi sonsa ne ko nafi sonki ba.. No, I’m not taking sides here.. I love you both.. Kai gaba d’ayanku yarana ina k’aunarku kuma bazanso naga abinda zai cutar da d’ayanku ba.. Kiyi hak’uri Safeenah.. Da zafi na sani. Amma ki daure ki saurari mijinki kiji dalilinsa.. Allah ya miki albarka tashi ki shige..”

Da tsananin mamaki Safeenah ke duban Daddy, lokaci guda take girgiza kai still hawaye na zubo mata.

“Seriously Daddy.. This is all you can say..?!” Tai maganar cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka kafin taci gaba da fad’in “I can’t believe you are asking me to give him a chance to explain.. “ Ta girgiza kai kafin taci gaba da fad’in “Daddy what explanation kuma. Bayan abinda na gani da idanuna Daddy you still ask me to wait for his explanation..?”
Taci gaba da hawaye tana girgiza kai “Daddy Mu’azzam fooled me.. He fooled us all. All this while wata ya aje gidana shiyasa yak’i amincewa na tare.. And yet you’re asking me to give him a chance to explain how he cheated on me with that prostitute he called wife..!”

“Safeenahhh!!” Daddy ya daka mata tsawa yana mai d’auketa da mari mai ji da lafiya wanda ya haifar mata da gani giftawan walk’ila harda taurari.

Ta d’ago a gigice tana duban Daddy dake tsaye kanta rik’eda k’uncinta.

Yaci gaba da nunata da yatsa “Ban haifi ‘yarda zatafi k’arfina ba. Idanma mahaifiyarki ce mai zugaki.. kije.. Go ahead, ku shigar da Mu’azzam Kotu.. Ni kuma na rantse sai na tsaya masa tinda duk kayan jeren naki da kud’ina aka saya.. Shashasha kawai maras hankali..! Get out of my sight now..! B’ace min da gani.. Stupid kawai..!”

Da d’ingishi Safeenah ta wuce rik’eda k’uncinta ko takan crutches d’inta batabi ba.. Tana tafe tana kuka tana k’wallawa Mommy kira.

**

Mota guda suka d’auka ta ‘yan sanda irin yanda ake idan za’ayi arresting mai laifi, bayan Maleeka harda wata ‘yar sanda mace mai sanye da uniform d’in police.
Lokaci guda Mu’azzam ya nufi nasa motar yana jin zuciyarsa na masa wane irin k’una.

Assad ya biyosa dan bazai barsa yai driving a yanayin da yake ciki ba.

Wayar Mu’azzam d’in ne Ta soma ringing, nan ya duba yaga Mommy ce mai kira.

Ya d’aga without saying a word.

Daga d’aya b’angaren Mommy ke fad’i cikin tsananin huci “Ka gama gudunka Mu’azzam wllhi wllhi kaji na rantse maka sai ka biya abinda ka aikata ma Safeenah.. Bazan dubi zumunci ba Mu’azzam ba kuma zan dubi alak’a Ta jini dake tsakaninku da Safeenah ba balle na duba matsayinka na kasancewa miji a wajenta.. Sai na maka ka a kotu saidai duk abinda za’a fad’I a fad’I.. Ka riga da ka ruguza ahalin da Kakarku tai k’ok’arin ginawa tsawon shekaru. Wllhi you will pay dearly for what you did to my daughter.. I don’t give a damn about your police uniform..!” Tana ida fad’in haka ta katse kiran ba tareda ta tsaya ta saurara daga nasa b’angaren ba.

Tana katse kiran ya cire wayar daga kunnensa yana jinjina kai idanunsa na duban waje guda. A hankali yake furta “You’re right Mommy.. Ahalin ya tarwatse.! Kuma zamu tafi Kotu kaman dai yanda kikace.!”

Suna shigewa Maleeka Ta silale Ta ciro wayarta Ta soma dialing layin Barr Amir.

Bugu d’aya a na biyu Amir ya d’aga kaman wanda yake jira.
Chapter 57 · 0% Book details