← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 171 OF 175

Sashe 171

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwanci tashi babu wuya wajen mai duka anyi auren Umman Sadiya da Uncle Ramadan yanda suke zaune a nan Abuja dan yanzu kusan ragamar Gamji Dairy Company dake Abuja Daddy ya sakar masa.
Su Habeeb da Asheer suka samu sabon Abba dukda cewa basu mance da Abbansu ba kuma kullum suna masa addu’a. Allah sarki rayuwa komai yai farko zai k’arshe. Tsanani na tareda sauk’i. Family ya cika da albarka.. Yayinda su Mommy suke can gidan kasu suna biyan abubuwan da suka aikata.. Mommy tsaban bala’in dake tattare da ita.. Inmates d’in da suke tare da ita ma basu tsira ba idan Shedaninta ya tasamma bugunta. hakan yasa dole ake kulleta Ita kad’ai a nata d’akin yaita kilanta yan prison d’in su kasa kunne suna sauraron yanda ake Lapkar Mommy ba tareda sunga mai bugun nata ba.

Jaja da Danger ma kullum sai Inmates Sun lakad’a masu na jaki harda su stabbing da makami.. Iyaka jigata da jin jiki harma da wulak’anci suna ganinsa.

**

Masha Allah cikin Sadiya ya shiga watan haihuwarta.. A lokacin kuma ake bukin Karrama Mu’azzam harma dasu Assad d wasu abokan aikinsu had’ida basu lambobin yabo bisa jajircewarsu akan aikinsu. Musamman cin nasaran kawo k’arshen gurb’atattun Yansanda wanda cin Hanci da rashawa ya masu Katutu irinsu Jaja.. Ga kuma Gasunkumin D’antaddan nan da Mu’azzam ya kawo k’arshensa Wato Muttaqa Danger.

Sadiya na zaune parlorn Mamy dan tinda Ta shiga watan haihuwarta sai ta dawo gidan. Yayinda su Mamy da Daddy suka tafi taron, itakam bata samu taje ba sabida nauyi da tai haihuwa zai iya zuwa any moment.

A b’angaren Mu’azzam kaw gaba d’aya sai yaji wani abu is missing a taron.. Babu Stubborn Head d’insa kuma Beautiful wife d’insa, taron kawai ake gudanarwa amma jikinsa duk mace musamman idan ya tuna mafarkin da yai a daren da ya gabata cewa ana tsaka da gudanar da bukin k’arin girman aka harbesa a k’irjinsa sanda ya fita zai amshi awards and medals nan kuwa ya fad’i k’asa matacce..
Kawar da tunanin yai ta hanyar ciro wayarsa ya kirata video call.

Tana zaune shame shame da zungureren cikinta a gaba tana shan grapes wayar tasa ta shigo. Ta d’aga da murmushi saman fuskarta ganin fuskar mijin nata ya bayyana saman screen dashike video call ne.

“Hello Chop chop.” Abinda kawai ya fara fad’I kenan daga d’aya wayar nata.

Ta saki murmushi tana dubansa cikin ceremonial Kakinsa, lokaci guda take furta “Congratulations, Chief Inspector Mu’azzam Abubakar Gamji.. Wai har ka samu sararin kirana..?” Ta fad’i tana duban fuskarsa da ya bayyana fuskar wayar kyakkyawan murmushi saman fuskar nasa. Tana iya hango anini da aka mak’ala masa jikin Uniform d’insa na Nigeria Police Force alamun karin girma, kansa babu hula da alama ya cire hular ne.

Murmushi yake yana dubanta shima kafin yace “Of course my beautiful wife has to be with me on this momentous occasion.. After all, k’arin girman da awards d’in duka nata ne.. Congratulations Beautiful..” Ya k’arashe murmushin bai gushe saman fuskarsa ba.

Sai murmushi take tana dubansa, lokaci guda yace “So ya kuke.. How’s my jewel doing.?” Yai tambayar yana kai dubansa zuwa zungureren cikinta.

Ta kuma murmusawa tana dubansa ba tareda ta iya cewa komai ba, Sai k’ura ma fuskarsa idanu da tai ko k’yafta idanun batayi kai kace kallon k’arshe take masa.

Jikinsa ya d’anyi sanyi da ganin yanayin da Ta shiga, bata amsa sa sai k’ura masa idanu da tai tana sakin murmushi.

“Hey Beautiful..You there..?” Ya tambaya a d’an dame wann karon.. Har lokacin murmushi take tana duban fuskarsa.

Sai ya soma tunanin k’ila network ne, ya soma k’ok’arin katse kiran da zummar ya sake kira, nan ya sinkayo muryarta tana fad’in “You are the most handsome and Honorable police Officer I’ve ever seen.. Congratulations once again Handsome.”

Saida ya sauk’e deep breath kafin yaci gaba da kallon kyakkyawan fuskarta shima yana sakin murmushi. Nan ya sinkayo Muryar Assad alamun ana nemansa.

Lokaci guda yake furta “I love you Beautiful.. You take care okay..”

“I love you too Handsome.. Please enjoy your day..” Ta fad’i tana murmushi.

Saida d’aga mata wayar yana nuna mata environment d’in kafin yai ma fuskokinsu hoto shida ita ya katse kiran. Kaman kar Su rabu da juna.

Suna ida wayar taji kaman abu na mintsillinta a mararta da bayanta kad’an, ta d’an gyara zamanta tana aje bowl d’in grapes d’in a gefe. Can taji ciwon ya kafa haka yasa Ta d’an kishingid’a kadan.

**
A b’angaren Mu’azzam carko carko sukai gaban DIG da wasu manyan Yansandan yanda DIG Ke ci gaba da fad’in “Mun samu rahoto na gaggawa daga prison cewa ‘Yanfashin daji sun fasa prison domin fitar da ‘Yanuwansu dake tsare.. And cikin escapees d’in da suka gudu an tabbatar harda Danger da ‘Yarwarsa Hajara.. A sabida haka aiki ne ja a gabanmu na ganin mun capko ‘Yantaddan nan da suka gudu gaba d’aya.”

Mu’azzam ya soma girgiza kai yana fad’in “No.. no this is not happening..!” Lokaci guda yasa kai a fice hankali tashe. Yayinda Hukumar NPF ta soma yunk’urin baza dakarunta a fad’in garin da kewaye.

Kan kace mai taro ya watse dan dole ma taro ya watse gari babu lafiya.
Hankalin Mamy da Daddy duk a tashe Musamman da Mu’azzam ya k’araso yana basu tsaro na musamman ya had’a Adnan da wasu cops yace aima su Mamy da Daddy rakiya zuwa gida sabida su Danger da Hajara da sukai escape yasan dole family d’insa su zama target.

**
A can asibiti wajen Safeenah ranan ake sallamarta. Musaddiq shi ne yaje d’aukanta.

Tana ganinsa ta sakar masa murmushi tana girgiza kai “I thought kana can UK.. When did you come back.?”

Ya murmusa yana d’aukan jakan kayanta “Kwana biyu da suka shige.. Ya jikinki..? I can see kin samu lafiya Masha Allah..”

Ta murmusa tana dungurinsa kad’an “Ina Daddy why isn’t he here..?”

Musaddiq ya kuma murmusawa yace “Kinsan Allah na yarda kin samu lafiya Sister, da ace da ne Your Halal zaki fara tambaya amma gashi Daddy kike tambaya.?”

Murmushi kurum Safeenah tai kafin tace “Af na mance yace mun yau ake bukin k’arin girman Mu’azzam, yace zai Zo ya d’aukeni nace masa kar ya damu he should be with his wife.. Kar ya bar Aunty Nuratu ita kad’ai a wajen taron Mu’azzam..”

Musaddiq ya kuma murmusawa cikeda jin dad’i yace “I’m so happy kin samu lafiya Feenah.” Ta murmusa itama tana fad’in “Hey, do not exaggerate.. Ina bak’auyar matarka.?” Ta k’arashe tana d’an yatsina fuska, sai ta koma asalin Safeenarta.

Ya d’an tsuke fuska “Haka dai nake son kayana..”

Safeenah ta murmusa kad’an had’ida dungurinsa “Just kidding.. Allah ya kaimu lokaci musha biki..” Musaddiq ya saki murmushi yana mai amsawa da Ameen. Safeenah ta dubesa tana murmushi kafin ta d’an janyosa jikinta “Hey.. I love you.” Ta fad’i murmushi saman fuskarta. Shima murmushin yai yana duban abokiyar fad’an tasa Safeenah kafin yace “I love you too.” Fuskokinsu cikeda annuri suka shige mota suka nufo gida.
**

A b’angaren Sadiya kaw ciwo sai k’aruwa yake, sai juyi take tana dafe bayanta tana tamke idanu tana ambaton Allah. A haka Mama Hindu tazo ta taddata, babu shiri Tai kiran Driver yazo ya kaisu asibiti.

Danger da Mommy cikin b’adda kama suka shige gidan bayan Danger ya sumar da securities masu tsaron gate d’in gidan.

Koda driver ya k’araso yana horn mamaki ne ya cikasa ganin babu security ko guda da yai attempting bud’e masu gate ga Sadiya a bayan mota tana labour Mama Hindu Sai mata sannu take.

Driver yana sauk’owa da zummar bud’e gate yaji sauk’an itace a k’eyarsa. Tuni shima ya fad’i sumamme.

Mommy ta fito daga mab’oyarta yayinda Danger ya k’arasa ya bud’e marfin mota b’angaren da Mama Hindu Ke zaune wacce sam bata fahimci meke faruwa ba sabida hankalinta kacaukam naga Sadiya dake cikin yanayi na nak’uda.

Tuni Danger ya rabzawa Mama Hindu abu aka itama ta fad’i sumammiya kafin ya janyota ya fiddata daga cikin motar ya shige mazaunin driver.

Sadiya ta Ware idanu a galabaice tana girgiza kai ganin Mommy ta shigo cikin motar tana sakar mata muguwar murmushi.

SameenaAleeyou📚
*GIDAN ARO*

*84*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Sadiya taci gaba da girgiza kai da k’yar gumi da hawaye suna gangaro mata dan tsaf Ta gane Mommy itace matar da Ta kashe mahaifinta Ta kuma kashe Dad d’in Mu’azzam da Ikram “Dan Allah kar ku cutar.. Dani.. Wayyo Bayana.. Cikina... Bayana ciwo yake mun.. Wai Allah na.. Ina kike Mama Hindu..? Zan mutu..!” Cikin tsananin pain take sumbatun.

Mommy da ta kafeta da idanu dariya ta shek’e dashi tana jinjina kai “Shegiya ciwon Haihuwa kikeji..! Lallai munyi babban kamu, wann ciki shine Zuciyar ahalin nan.. Zuciyar Nuratu da Marwan harma da tantirin maras kunyar uban cikin da ya dage Sai yaga bayana.. Dama na fad’a maka Mu’azzam saina k’arar da gudan jininka a doron k’asa yanzu dai ga matarka masoyiyarka da D’anka under my mercy.. Gashi kuma Banida imanin balle na masu rangwame.!” Ta k’arashe tana mai kuma fashe da muguwar dariya.

“Kai Danger ja mota muje..”

Jin Ta ambaci sunan Danger ya kuma rikita Sadiya.. Taci gaba da girgiza kai gumi da hawaye suna ci gaba da wanke mata fuska “Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un Dan Allah kuji tausayina kar ku cutar dani.. kar ku cutar da abin cikina.. Na rok’eku..”

Daidai lokacin suka fito daga gidan Musaddiq kuma k’arasowarsu kenan. Nan suka bi motar da kallo.

Sadiya tai azama ta turo kanta ta tagar motar tana fad’in “Help.! Please help me..!” Bata k’arashe ba Mommy ta funcukota ta kifa mata mari had’ida matse cikinta da k’arfin gaske.

Wani irin gigitaccen k’aran azaba Sadiya ta saki wanda har jijiyoyin dake kwance cikin goshinta saida suka fito waje.

Musaddiq ya taka uban birki yana duban motar da ta wuce gashi kaman Sun hango mutum ciki na ihu dukda da nisa tsakaninsu.

Safeenah ta shiga girgiza kai tana fad’in “Kaman matar Mu’azzam ce.. Meke faruwa toh.. Mubi bayansu Musaddiq.. Yi sauri mubi bayansu..” Ta k’arashe tana bubbuga hannun Musaddiq dake dafe da steering wheel.

Cikin sauri yake jinjina kai kafin ya taka motar suka d’auki hanyar da suka bi.

Suna tafe wayar Mu’azzam ya shigowa Musaddiq.

Mu’azzam tambayarsa ya fara suna ina sabida ahalin gaba d’aya suna cikin had’ari ne.
Chapter 171 · 0% Book details