Sashe 8
Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiru tai tana dubansa cikeda tausyawa, ta jinjina kanta a hankali kafin tace “Idan kace haka zan iya fahimtarka Modibbo.. Nasan har yanzu alhinin rashin ‘yaruwarka na tareda kai.. Amma idan kana tareda Matarka sai ta d’ebe maka wani kewan ka fahimta..”
D’an shafe fuskarsa yai kad’an kafin yace “Inne ai akwai abubuwan da nake so su daidaita kafin nan.. Kinga yanzu babu Ikram dama itace take taimaka wa Aunty Hajara da jinyar Mamy na.. Aunty Hajara bazata iya kulada Mamy ita kad’ai ba dukda dai dama akwai ma’aikatan jinya da ake hayansu masu taimakawa.. Inaso idan al’amarin suka daidaita Sai mu tare mu koma cen gidan..”
Katsesa tai da fad’in “Ni nan zanyi jinyar Nuratu.. Dama wannan karon nace zan d’auketa mu koma gida a jarabba jinyar gargajiya tinda na asibitin Allah bai nufa za’a dace ba.. Nayi magana da Baban naku dikda shima naga yafi son zamanta a nan amma haka dole zaku hak’ura a jarabba na gargajiyan.. Sannan zatafi samun kulawa a wajena sama da nan d’in..Watak’ila maganinta na gida bamu sani ba..”
Shiru yai kaman mai nazari, harga Allah baison mahaifiyarsa tayi nesa dashi musamman duba da yanayin jinyar da take ciki.. Amma baida wani zab’i idan hakan shine Alkhairi.. Zaifi kowa son mahaifiyarsa ta sami lafiya.. Kaman kuma yanda Inne tace zatafi samun kulawa wajen Kakar tasa dukda kuwa cewa bai tab’a ganin gazawar Mommy ba sannan har kullum fatan alkhairi ne tsakaninsa da ita.. Ko dan mutuncin iyayen Safeenah Daddy da Mommy da yanda suka rik’esu amana shida ‘yaruwarsa da kuma mahaifiyarsu dake cikin tsananin jinya baiji zai iya wulak’anta Safeenah, koda ace baya sonta zaiyi hak’urin zama da Ita.. Mommy da Daddy sun cancanci ya rik’e masu d’iya da amana..Alk’awari ne da ya d’aukar ma kansa..
Muryar Inne ya sinkayo tana ci gaba da fad’in “Jinya yak’i ci yak’i cinyewa.. Idan ban b’ata lissafi ba yau a k’alla kusan shekaru shabiyar kenan Nuratu na fama da jinyar nan, ni ban tab’a gani ko jin had’arin mota irin nasu ba..”
Mu’azzam ya d’ago yana dubanta “.. Ina makarantar Kwana a lokacin, aka sanar dani Mamy ta auri Uncle Marwan saidai a hanyarsu Ta tafiya Abuja daga Adamawa sunyi accident.. She survived the accident amma tana cikin critical condition.. Condition d’in da bata fice daga ciki ba har rana mai kaman Ta yau.. Ance motar da Mamy na take ciki kowa ya mutu ita kad’aice tayi rai a ciki..”
Ya k’arashe cikin yanayi na ban tausayi.
Sauk’e ajiyan zuciya Inne tai tana mai d’an goge hawayen da ya mak’ale mata cikeda tausayin Mu’azzam d’in..
“Modibbo ina k’aunar Mahaifiyarka tamkar d’iyar dana haifa a cikina wannan dalili yasa na umarce d’anuwan mahaifinka da ya aureta bayan da muka rasa mahaifinka... Ina tsananin k’aunarta kuma bana so ta bar cikin ahalinmu.. Nuratu yarinyar kirki ce mai tsananin biyayya.. Da ita da Baffanka Marwan sunyi min biyayya kuma Sun cika min burina sun amince da auren juna.. Saidai bansan wannan aure haka zai kasance ba.. Bansan a hanyar zuwa GIDAN Baffanka Nuratu zata had’u da wannan mummunan tsautsayi ba.. Ance had’arin motar bama irin wacce aka saba gani bane.. A samar bishiya aka tsinci motar da mahaifiyarka ciki... Mu’azzam inaji kaman alhakin ciwon mahaifiyarka a kaina yake.. Watak’ila da banyi masu umarni da su auri juna ba itada Marwan da yanzu lafiyarta lau.. Bazan daina jin zafin abun nan ba har na koma ga mahaliccina..” Ta k’arashe tana mai fashewa da kuka.
Cikin sauri Mu’azzam ya taso ya duk’a gabanta, ya kamo hannayenta ya dunk’ule cikin nasa “Inne none of this is your fault.. Ki daina d’aura ma kanki alhakin ciwon Mamy, wannan wani abu ne da Allah ya K’addara.. Mutum baya shige k’addarar Sa a rayuwa.. Wani baya iya yi ma wani abin cutarwa ko na amfanarwa face Allah ya k’addari faruwar hakan,.. Baki nufi Mamy da komai ba face Alkhairi. Had’ari kuma ko ta auri Uncle ko bata auresa ba tuni Allah ya rubuta hakan zai faru.. Ki daina d’aura laifi ma kanki kinji Inne..” Ya k’arashe yana mai goge hawayen fuskar Kakar tasa da ‘yan yatsunsa..
Ta Shafa sumarsa murmushi saman fuskart “Allah shi maka albarka Modibbo na.. Ubangiji ya maka jagora a duk abinda kasa gabanka.. Allah tsare mun kai ya kareka daga sharrin mai sharri..”
Sumbatar hannayenta dake rik’e cikin nasa yai yana furta “Ameen Inne na.. Allah ya bar mun ke..” Ya k’arashe yana mai d’aura kansa saman cinyarta..
Dik zafin da zuciyarsa Ke ciki idan yana tareda Kakar tasa Sai ya dinga jin wani sanyi can k’asar zuciyarsa, har wani shagwab’a yake mata, ga wanda yasan zafin sa a waje idan ya gansa da Innensa sosai zaiji mamaki..
Daga wajen Inne Kai tsaye wajen mahaifiyarsa ya nufa...
SameenaAleeyou📚
*GIDAN ARO*
*05*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Ya jima tsaye bakin k’ofa yana dubanta, yana mai tina tattaunawarsu da Inne. A hankali ya soma takowa cikin d’akin har ya k’araso bakin gadon da take kwance.. B’angaren da fuskarta yake duba ya k’arasa, ga duk’a kad’an yana mai k’ura mata idanu.. Su kuma kalan tasu k’addarar kenan.. Da fari mahaifinsa ya rasa sannan mahaifiyarsa ta had’u da tsautsayi na jinya yanzu ga tilon k’anwarsa itama ta tafi.. Tinani yake lokacin ahalinsu ke cike, Daddynsa Mamynsa da kuma ‘yar k’aramar k’anwarsa Ikram.. Ahali mai cikeda Farin ciki da k’aunar juna.. Inama wad’ancan lokutan zasu iya dawowa.. Inama zai bud’e idanunsa yaga mafarki ne duk abubuwan da suke faruwa.. Amma saidai wannan itace gaskiyar, littafin k’addararka a kullum bud’e maka Sabon shafin rayuwa takeyi.. Rayuwar duniyar kenan, duk yanda ka kaiga ganin cewa dad’i kakeji a duniyar nan toh wannan dad’in k’ayadadde ne, aronsa aka baka akwai ranan da zaka wayi gari ka rasa wannan jin dad’in.. Sannan duk yanda ka kaiga ganin wahala kake sha toh wannan wahalan yanada wa’adi akwai ranan da zai k’are.. Duniya ba gidan zama bace gida ce ta jarabawa, dik yanayin daka tsinci kanka ciki a gidan duniya toh kuwa ko shakka babu jarabawa ce kake cikinta.. Gidan duniya gidace da aka baka aronta domin a jarabceka a cikinta, ba gidan Sharholiya bace sannan ba gidan baje koli bane.. Kai d’in tamkar matafiyi ne da aka baka Aron Gida domin ka yada zango na wani d’an lokaci k’ayadadde.. Babu komai a GIDAN ARO face tarin jarabawa da kuma k’alubale na rayuwa..
Mu’azzam ya lumshe idanunsa yana mai kamo hannayen mahaifiyarsa wacce ga dai idanunta a bud’e tarau amma wani b’angaren take duba.. Bata um bata um um.. A hankali ya soma furta “Mamy inada babban albishir da zan miki.. A yau d’in na soma gano wani abu gameda mutuwar Ikram.. Kuma na miki alk’awari in sha Allah bazan gajiya ba har sai na samo bakin zaren.. Mamy na Sani addu’arki da albarkanki suna tare dani.. Fatana shine Allah ya baki lafiya ya tashi kafad’unki.. Inada yak’inin cewa wata rana komai zai wuce ya zamto labari.. Wanda sukaci zarafin d’iyarki suka kuma kasheta zasu biya.. Zasu biya abinda suka aikata Mamy.. I won’t rest until I get to the bottom of everything..” Ya k’arashe yana mai sumbatar hannayen nata dake rik’e cikin nasa had’ida lumshe idanunsa siririyar hawaye ta gangaro daga cikin idanunsa guda...
Yana duk’e wajen yaji hannun mutum a kafad’arsa, sanin ko wanene tsaye Kansan ya sanyasa k’ok’arin saita kansa kafin ya mik’e yana goge fuskarsa da duka tafukan hannayensa..
“Sorry Daddy banji shigowarka..” Ya fad’i yana mai k’ok’arin mik’ewa tsaye.
K’ak’aro murmushi Alhaji Marwan yai kafin ya girgiza kai kad’an yace “Babu komai Mu’azzam..”
Ya kuma duban Mu’azzam d’un cikeda kulawa kafin ya maidoda dubansan ga mahaifiyar Mu’azzam d’in.. Idanunsu Su duka biyu naga mahaifiyar Mu’azzam d’in Daddy Ke fad’in “D’azu muke magana da Inne cewa tana so Nuratu ta koma Fufore.. Za’a gwada yi mata maganin gida ko Allah zaisa a dace.. Hajara ta fara mun maganar sai kuma Inne ma tazo da batun.. Toh amma a zahirin gaskiya Mu’azzam ni banyi Na’am da maganin gargajiyan nan ba.. Tinda ga abinda likitoci daga manyan asibitoci na duniya suka fad’i.. Zai matuk’ar wahala ta warke a bisa iya binciken da sukayi..So ina tunani kar aje a shiga bata wasu magunguna da babu dosage ba likita bane yayi prescribing aje a k’ara rikita jikin nata.. Toh amma kuma sai nayi tunanin likitocin nan ba sanin gaibi sukayi ba.. Cuta Allah Ke sakashi kuma shi Ke yayewa, saidai yakan bama wasu daga cikinmu ilimin sanin magani domin kuwa bai halicci cutan ba har saida ya sauk’ar da maganinta.. Ba Lallai sai ta hanyar likitoci wanda sukayi karatun ilimin zamani ba.. Wani dake rayuwa cikin daji ma sai Allah ya basa ilimin sanin magunguna a kumayi amfani dashi idan Allah ya nufa sai a dace...Amma Kai mai kake gani..”
Shiru Mu’azzam ya d’anyi kaman mai nazari kafin yace “Haka ne Daddy..Abinda ka fad’a gaskiya ne.. And duk hukuncin da ka yanke zanyi na’am dashi.. Kaine mijin Mamy, and you’ve every right ka Kai Matarka jinya yanda kakeda tinanin za’a iya dacewa da magani.. Inne ta min maganar d’azu dana shiga wajenta.. Daddy duk hukuncin da kuka yanke yayi.. Fatanmu shine Allah ya Bawa Mamy lafia..”
Murmusawa yai kafin ya d’an bubbuga kafad’ar Mu’azzam yace “Ka kasance d’a mai biyayya a wajena.. Ko Hamma ne yake raye yanzu iyakacin biyayyar da zaka masa a matsayinsa na mahaifinka irinsa kake min Mu’azzam.. Allah Ubangiji ya maka albarka ya dafa maka cikin duk abinda ka saka gabanka...”
Kansa a k’asa kad’an yace “Ameen Daddy..”
“Ya maganar binciken case d’in Ikram.. Ba wani abu da aka samu har yanzu..?”
Mu’azzam ya d’an shafi sumarsa yace “Muna nan Muna bincike Daddy.. And da zaran mun sami wani haske zamu maka k’aran a Kotu..”
Jinjina kai Daddy yai yace “Allah ya mana jagora, Allah kuma ya tona asirin duk wanda sukai mana wannan aika aikan..Zan kira Adnan yaje yai mana booking flight zuwa Adamawan within the week.. Zaka samu zuwa kuwa..?”
“Idan Mamy zata tafi ya kamata nima ina wajen.. But I’m not sure idan zan samu damar hakan..”
Daddy ya jinjina kai yace “Hakan yayi, kar ka samu damuwa zamuyi duk abinda ya dace in sha Allah.. Just concentrate on your job kaji koh..Allah ya shige mana gaba..”