← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 175

Sashe 61

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wai yau Safeenah Marwan Gamji ce a cikin cell, ‘yansanda na tsare da ita.. Abunda ko a mafarki bata tab’a hasasho kanta a irin wannan yanayi ba.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un. Tabbas idan Bawa bai mutu ba bai gama ganin jarabawar rayuwa ba.. Sai masifa Safeenah take tana fad’in azo a fiddata daga cikin cell d’in nan ita bazata iya ba. Sergeant ta darara mata tsawa “Ke Malama Ki mana shiru.. I know you live in a mansion, you better get used to staying jail.. Kin zaci a 5star hotel kike da zaki ishe mutane.. And don’t expect any VIP treatment Dan kina matar Inspector Gamji.. Yanda ake ma criminals d’in dake cikin cell d’in nan haka za’a miki.. Idan kina san samun rangwame shine ki bud’e bakinki ki fad’i Iyakacin abinda kika sani idan kuma ba haka ba. Yanzu kika fara zama behind bars har ki dangana ga Prison that is idan ba’a yanke miki hukuncin kisa ba.”

Safeenah ta zaro ido waje tana girgiza kai “No.. Bazai tab’a yuwa ba wllhi.. Nayi imani da Allah ban aikata ba babu kuma wanda ya isa ya hukuntani akan laifin da ban aikata ba ban kuma San wa ya aikata ba.. Ameer do everything you can to get me out of this place.” Ta k’arashe tana duban Barr Ameer kaman zatai kuka.

Ameer yace “Ki kwantar da hankalinki Safeenah. Zaki fita daga wajen nan.. I promise you.!” Ya k’arashe yana mai jinjina kai alamun tabbatar da kalamansa.

**

A b’angaren Mu’azzam gaba d’aya zuciyarsa a jagule take. Ji yai kaman k’irjin ya masa mugun nauyi. Tamkar dai ya gaza d’aukan abubuwan dake cikin k’irjin nasa.. Gaba d’aya baisan meke masa dad’i ba daga jikinsa har duniyar Tasa ga kansa dake wani irin sara masa tamkar dai kan nasa zai rabe gida biyu.

Sun jima suna tareda Assad har dare, Assad na kuma shawartansa da ya d’auki abubuwa da sauk’i kafin daga bisani yai ma Assad d’in sallama. Bayan rabuwarsu da Assad Tsayawa yai a wani chemist ya sai maganin ciwon kai kafin ya nufo gida.

Yana shigowa gidan ya zube a nan parlor had’ida lumshe idanunsa yana tinanin abubuwan da suka faru a ranar. Rana ce data kasance mai tsawo a garesa.. Kiraye kirayen sallar isha da aka soma ya sanyasa mik’ewa ya nufi d’akinsa. Saida ya tsaya ya dubi k’ofar d’akin Sadiya na d’an lokaci kafin ya maidoda dubansa zuwaga katafaren hoton aurensu shida Safeenah dake aje wajen. Take yaji zuciyarsa na kuma masa zafi kansa naci gaba da sarawa. Lumshe idanunsa yai a hankali kafin ya nufi nasa d’akin.

Tana jin tab’a k’ofa ta mik’e daga zaunen da take tana aikin abu d’aya Wato kuka. Ba kukan abinda matar Mu’azzam da ‘yanuwanta sukai mata a ranan take ba. Kukan rashin sanin halinda ahalinta ke ciki take. Yinin ranan kuka take ga tsananin ciwon kai da ya addabeta itama. Ta fito da sauri tana lek’en ta ina zata gansa ta tambayesa ko an samu su Umma amma bata gansa ba. Baya kitchen sannan baya parlor.. Ta dubi k’ofan d’akin da take tinanin nasa ne. A hankali ta lumshe idanun nata wasu hawayen suka kuma gangarowa.. Bata shiga d’akin ba ta koma da baya ta nufi nata d’akin ta gudanar da sallar isha da tuni aka kira har wasu masallatan sun shiga.

Ta jima tana addu’o’inta tana sauraron ko zataji bud’e k’ofan d’akinsa amma shiru bataji ba.. Ta soma tinanin kodai ya fice daga gidan ne bataji fitarsa ba.? Ai kuwa bataci ta zama ba, bazata bari ya fice ba tareda ya sanar da ita komai gameda neman mahaifiyarta da ‘yanuwanta da yai mata alk’awarin zai ba.. Bazai yuwu ya kulleta a wannan kurkukun ba ya hanata fita neman ahalinta sannan shi ya gaza yin komai.. Ta mik’e da sauri ta fito tana dubasa cikin gidan. Bai ko ina sannan ga motarsa a haraban gidan. Definitely yana cikin gidan kenan. D’akinsa ne kawai yai saura bata duba ba, yau kam zata shiga domin tasan wani hali Umma dasu Habeeb suke ciki.. Ta isa jikin k’ofar d’akin ta murd’a handle d’in a hankali nan taga k’ofar ya bud’e.

D’ago idon da zatai ta hangesa kwance saman sallaya yana sanye da jallabiya mai ruwan sararin samaniya.. Take ta shiga sakin huci, Wato ma kwanciyarsa yazo yayi mahaifiyarta da ‘yanuwanta suna can ba’asan duniyar da suke ba. A zuciye ta shigo cikin d’akin tana fad’in “Mr Inspector ka tashi ka sanar dani Ina ahalina suke.. Bazai yuwu ka ajiyeni a wannan kurkukun da kake kira gida ba sannan kazo kai kwanciyar ka ba tareda sanin ina ahalina suke ba..!”

Shiru taji bai amsa ta ba sannan ko motsawa daga yanda yake kwance bai ba.. Nan Ta soma rau rau da idanu cikin rawar murya take fad’in “Nasan tsiwa bazai saka ka kai abu ba.. But please na rok’eka ka k’yaleni na fice na nemosu da kaina.. Please Mr Inspector.. Just put yourself in my place.. Dan Allah please..!” Ta k’arashe kuka na zuwa mata.

Har lokacin yana nan kwance bai ko motsa ba.. Abun ya soma k’ular da Sadiya ganin ya bata baya ko juyowa baiba balle ya amsata. Ta k’araso ta yanda fuskarsa ke kallo nan taga idanunsa a lumshe suke. Takaici ya kuma cikata.

“Mr Inspector..!” Ta fad’i daidai saitin fuskarsa.

Shiru bai amsata ba.. Ta shiga bubbuga gefen sallayar tana ambato sunansa, nan ma dai shiru bai amsata ba har lokacin idanunsa a lumshe suke.

Nan ne fah tsoro ya soma kamata, gani tai tamkar ma bai numfashi.. Taci gaba da buga gefensa tana ambaton sunansa.. Ganin da gaske dai k’ila numfashi ne baiyi ya sanyata matso da kunnenta guda saitin hancinsa taji kodai numfashin ne baiyi.. Aiko nan taji tamkar dai bai numfashi.. Girgiza kai ta soma tana fad’in “Oh no.. He’s not breathing..! What do I do now..? Na shiga uku ni Sadiya ya zanyi..? Who do I call..?” Ta soma girgiza kai cikin birkicewa da tinanin mai zata aiwatar.

“The gateman.. Shi zan kira.. Bara nai sauri na kirasa..!” Ta k’arashe tana mai k’ok’arin mik’ewa saidai kafin ta ida mik’ewa taji Mu’azzam ya kamo hannunta ya janyota ta fad’o jikinsa.

Zaro ido tai tana duban fuskarsa wanda har lokacin idanunsa a lumshe suke yana sakin murmushi a hankali. Still idanun nasa a lumshe yana shak’an k’amshin jikinta yake furta “Your perfume is nice.!”

Takaici ya cika Sadiya, Wato dama duk yana jinta yai banza da ita, tana maganar neman ahalinta shi ta perfume ma yake, wai your perfume is nice.. Ita da ko turare bata saka ba bayan kayan wanka masu k’amshi da ya tara mata a toilet.. Inama taga wani nastuwan fesa perfume..Ta shiga kokawan cire jikinta daga nasa tana fad’in “You.. You scared me.. Let me go now.. Inspector.”

Bai sakenta ba har lokacin saima sakin murmushin da yake still idanunsa a lumshe. Saitin kunnenta yake furta “Did I scare you..? Kin zaci kin rasani kenan..? Kar ki damu bazan mutu ba until our mission is finally accomplished..!”

Turasa tai da k’arfi tana fad’in “Toh kama mutu mana. Who cares.. The only thing da na damu dashi shine kar ka mutu baka samo mun Ummata da k’annena ba.. I don’t care idan ka mutu..”

Ya bud’e lumsassun idanunsa wanda da gani zaka fahimci baijin dad’i yana dubanta dasu.

Still murmushin ne saman fuskarsa yana duban yanda take sakin huci “Don’t make the mistake of falling for me, because I’ll never love someone like you.” Ya fad’i idanunsa akanta.

A yatsine ta dubesa kafin tace “I’d rather die than to fall for someone like you. Mr Inspector.! Now you let me out and look for my family.”

Ya kuma murmusawa kafin yace “Kina son sanin ina ahalinki suke.?”

Tai saurin jinjina kai tana dubansa.

Ya jinjina kai kafin yace “I’m sick, and I need someone to take care of me.. Can you stay here in my room and look after me..?”

Galala take dubansa kafin tace “Allah ya sawak’e mun..!”

“Ashe baki son sanin ina suke.. Kin mance cewa yin hakan duk cikin mission d’inki ne..”

Sadiya tai rau rau da idanu tana dubansa, dik wani salon mugunta ya sani, dik abinda zai yi ya k’untata mata shi yakeyi da sunan mission. Tasa bayan hannunta ta goge hawayenta “But you’re not a baby. You can move your hands and legs.. Mai yasa zan tsaya na kula da kai.”

Duban fuskarta yake musamman d’an bakinta da taketa faman turo shi gaba kafin ya soma k’ok’arin mik’ewa zaune, yace Ta mik’o masa pillow.

Baki a ture ta isa ta d’auko pillow d’in, ya d’an matsar da bayansa alamun ta saka masa pillow d’in jikin gadon. Nan ma fuska babu walwala ta k’arasa ta saka masa pillow d’in ya d’an jingina bayansa.

“Sai mai kuma.?” Ta tambaya Cikeda k’osawa.

Juyawa yai gefen bedside yanda magani da ruwan gorar ke ajiye yace ta mik’o masa. Babu musu Ta isa tai yanda yace d’in.

“Saura cup.” Ya fad’i yana dubanta.

Babu musu ta sauk’o downstairs ta haura masa da glass cup. Ya dubeta yace ta zuba masa ruwan ciki. Nan ma babu musu tai yanda yace Ta mik’a masa.

Maganin ya d’auka ya b’alla yasha, lokaci guda ya maida kansa ya jingina jikin pillow d’in had’ida lumshe idanunsa.

“Zan iya tafiya..?” Sadiya ta tambaya tana dubansa.

Still idanunsa a lumshe yake fad’in “I might need something.. You stay here until I fall asleep.. Amma idan baki so na kaiki kuma fine.. Kina iya tafiya..”

Idanunta sukai raurau, ta koma gefe ta zauna ta tak’ure cikin hijab d’inta Dan ji take sanyin AC d’in dake d’akin ya mata yawa ga sanyin damina.. Gaba d’aya sai kan nata yaci gaba da sarawa.

Suka d’ibi lokaci a haka, yana nan kishingid’e idanunsa a lumshe. Sadiya kaw Sai rawan d’ari take tana daga can gefe tak’ure cikin hijabi. Maganin dake gefensa Ta hanga takeda tabbacin na rage rad’ad’in ciwon kai ne. A hankali ta sad’a’d’a ta d’auko maganin da ruwa ta b’alli guda biyu tasha ko zataji sauk’in ciwon kan dake damunta.

Mu’azzam yana jinta saidai bai bud’e idonsa ba baice komai ba har ta dawo da maganin Ta ajiye.
Chapter 61 · 0% Book details