Sashe 67
Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
“Hajaraa!” Daddy ya darara mata tsawa yana mai d’ago hannu kaman zai kai mata mari.. Lokaci guda yake nunata da ‘yar yatsa “Ki iya bakinki kuma kar ki sake zagar mun mata, a yanda take a nakashe tafimun ke sau babu adadi.. Kuma da sannu zaki gani Allah zai bata lafiya ta dawo cikin gidan nan.. Tamkar bata tab’a jinya ba..!”
Ya dubi Safeenah yace “Shige muje..”
Babu musu Safeenah ta janyo suitcases d’inta tabi bayan Daddy. Aka bar Mommy baki sake tana duban bayansu har suka fice.. Yau itace Marwan yake cewa nakasasshiyar can ta fi masa ita, matar da ma cushe aka masa ba cewa yai yana sonta ba tun fil azal.. Lallai tun kafin ta makara gwara ta tura Shemau ta koma ta duba mata wanne hali Nuratu ke ciki.. Da wannan tunanin Mommy ta haura sama tana kiran Shemau.
Shemau tana jin Mommy na kiranta tai rounding up wayar da suke da mijinta Salman.
Ta dubi Mommy dake sakin huci ta tambayeta ya akai. Mommy ta sanar da ita komai cewa Daddy yakai Safeenah gidan Mu’azzam dukda irin cin kashin da Mu’azzam d’in yai masu, harda cewa da Daddy yai Nuratu tafi masa Ita.
Tab’e baki kad’an Shemau tai tace “Ai kuwa gwara ki tabbata Nuratu bata sami lafiya ba dan da alama mijinki ya fara sonta tin kafin ta warke daga jinya.. Ina ji miki tsoro kar ta dawo Gidanki a kan k’afafunta bayan an fitar da ita a kwance.”
Mommy ta sauk’e fuci tace “Kin mance cewa gidan mijina tamkar dai GIDAN ARO yake a wajenta.. Ai yanda aka fitar da ita a kwance Saidai a turata rami a haka.. Gidana ya haramta a gareta.. Yanda idan aka mutu ba’a sake dawowa Gidan Duniya haka itama yanda Ta fice daga gidan nan bata kuma dawowa.. Shemau ya kamata ki koma gida tinda dai Safeenar ta tare ki duba mana halin da nakasasshiyar cen ke ciki.”
Shemau ta jinjina kai tace “Gawa zakice dan kullum jikinta dad’a gaba yake yanzu haka wayar da nayi da Salman abinda ya sanar dani kenan cewa jikin Nuratu yak’i dad’i har Inne ta fara tinanin ko mai magani za’a canza..”
Mommy ta zaro ido dafe da k’irji tace “Shemau kar ki bari a canza mai magani.. Asirinmu zai tonu.!”
Shemau ta murmusa kafin tace “Baki da damuwa hakan bazai tab’a yuwa ba.. Bazan bar hakan ta kasance ba. Yanzu Salman yace zai taho Abujan gobe Ina tsammanin Business trip ne, zai kwana biyu sai mu koma tare. Kinsan nace miki Su Husna sunata shirin waec ga twins ma na barsu wajen mai aiki gwara na koma sai naci gaba da saka mana idanu kan Nuratu.”
Mommy ta jinjina kai tace “Hakan yayi.. Allah yasa kafin gobe muji Labarin nakasasshiyar nan ta mirgina..”
Suka saki shewa suna masu tafe hannaye.
**
Assad yana k’arasowa yai masa knocking da yatsar saman glass, lokaci guda Mu’azzam d’in ya danna unlock Assad ya ya bud’e ya shiga.. Kallo d’aya yaiwa Mu’azzam d’in ya basa tausayi.. Kai da gani Kasan abubuwa sun taru sun masa yawa k’arfin hali kurum yake.
Assad yace “Ya jikin Mamy..?”
Lumshe idanunsa kad’an Mu’azzam yai a hankali kafin yace “Munyi waya da Inne da safe tace mun jikin nata da sauki an gode Allah..”
Assad ya jinjina kai yace “Allah ya bata alfiya yasa kaffara ne.. Allah ya tashi kafad’unta..”
Mu’azzam ya amsa da “Ameen ya Allah..”
“Safeenah fah..? Wanne kake ciki da nata batun..?”
Ya d’an tab’e bakinsa kad’an kafin yace “I still don’t know.. Ban Sani ba Assad..”
Assad ya fuzar da fuci kad’an cikeda tausayin Mu’azzam d’in kafin yace “Kar ka damu Mu’azzam Ubangiji yana jarabtar bayinsa ta ko wacce hanya.. Ba wai yak’ika bane yake aiko maka da jarabawa daki daki, daga wannan sai wancan.. Kai hak’uri sannan kai addu’a Allah ya baka ikon cin jarabawarka Brother..”
Mu’azzam ya d’an kaikaito ya dubi Assad d’in kafin ya jinjina kai a hankali ba tareda ya iya furta koda kalma ba.
Assad yace “Ta ina zamu fara yanzu..?”
Mu’azzam ya d’ago yana dubansa kafin yakai ga basa amsa wayar Daddy ya shigo masa.
“I’ll take this call, Daddy ne mai kira.”
Assad ya jinjina masa kai ba tareda yace komai ba.
Mu’azzam ya d’aga da sallama yana mai gaida Daddyn.
Daga d’aya b’angaren Daddy ya amsa cikin sakin fuska kafin yace “Baka gida ne, gashi munzo bamu taddaka ba sai gateman.”
Ya d’an dubi Assad kafin ya girgiza kai cikeda mamakin jin Daddy yana gidansa “No bana gida Daddy. Ai na fice..”
Daddy ya jinjina kai yace “Toooh da kuwa gashi na taho da Safeenah ce zan had’aku gaba d’aya harda d’aya matar taka nai maku nasiha.”
Jin abinda Daddy yace ya sanya Mu’azzam ware idanu babu shiri yana jin wani abu na neman toshe masa mak’oshi.. D’an girgiza kai yai kafin yace “Daddy you mean, ka kawo Safeenah yanzu haka..?”
Daddy yace “K’warai kuwa Mu’azzam, na kawo maka matarka dan zaman nata a gida can baida wani alfanu.. Kyaun mace mai aure ta kasance a d’akinta shine cikan mutuncinta.. Sannan kaima shine cikan Kamalarka..”
Mu’azzam ya jinjina kai a hankali kafin yace “Haka ne Daddy..Amma yanzu bana gida and.. Bazan dawo gida nan kusa ba..” Yai maganar cikeda jin nauyin Daddy.
Daddy ya d’anyi jim kafin yace “Tooh lafiya dai koh..?”
Mu’azzam ya jinjina kai kaman Daddy na ganinsa “Eh.. Eh wani aiki ne ya taso mun shisa zan d’an makara.”
Daddy yace “Af Toh ai babu komai, nan gaba sai na had’aku na maku nasiha.. Ina ita matar taka take..?”
Mu’azzam ya dubi Assad dan baisan mai zai sanar da Daddy ba.. Baisan ta yanda zai soma fad’a masa cewa Sadiya ta gudu daga gidan ba. Ya d’an shafi fuskarsa kad’an kafin yace “Bata gida inaga taje can wajen mahaifiyarta..”
Daddy yace “Allah sarki toh shikenan.. Allah Ubangiji ya zaunar daku lafiya ya had’e maka kan iyalanka.. Allah shi maku albarka gaba d’ayanku..”
Mu’azzam yanata amsa masa da Ameen kafin Daddy yai masa sallama yana mai sanar dashi ya bar Safeenah a gidan shi kuma ya koma gida.
Suna ida wayar Mu’azzam ya dubi Assad yana mai kuma tura yatsun hannunsa cikin sumarsa.
Assad ya d’an girgiza masa kai alamun meke faruwa.
Mu’azzam ya d’aura duka hannayensa saman steering yana mai kuma fuzar da huci, idanunsa naga glass na gaban motar yake furta “Daddy yakai Safeenah gidana..”
Assad ya murmusa yace “Kaga mai tagwayen mata.. Baka Farin ciki da hakan ne..?”
Da wutsiyar idanu ya dubesa kafin yace “If she’s still my wife it’s because of Daddy..”
Assad ya d’an girgiza kai kad’an yace “Mu’azzam, Safeenah batada wani laifi.. Kawai dai she got trapped ne.. Gashi Allah ya wanketa. Su Danger sunso saceta ne suka sace Ikram. At least ka godewa Allah da ya wanke Safeenah.. Ko Babu komai ‘yaruwarka ce kuma matarka ce
Still da wutsiyar idanu yake dubansa kafin yace “Ka mance text d’in BAD ne.. I’m pretty sure D’aniskan Lauyan nan shine BAD.. Ban kuma yarda da sak’on BAD ba har Sai na isa k’arshen binkicen nan.”
Assad ya jinjina kai a hankali kafin yace “Ta ina zamu fara yanzu.?”
“Suleja..” Mu’azzam ya basa amsa kafin yaci gaba da fad’in “Babu yanda zatai tunanin zuwa sai nan, na tabbata can zata tafi ta nemi mahaifiyarta da ‘yanuwanta.”
Assad ya jinjina kai kafin yace “Let me drive..”
Mu’azzam ya murmusa yace “Kai haba rangwancin nawa ai bai kai nan ba.” Yana maganar yana tada motar had’ida d’aukan hanya.
**
Daddy yana tafiya Safeenah ta dinga zagaya gidanta tana imagining kalan cin amanarta da Mu’azzam yai a cikin gidan da wannan ‘yariskan yarinyar. Tai tsaye tana duban Parlorn sai taga kaman tana hangosu saman kujera Mu’azzam na zaune yarinyar tayi matashi da cinyarsa. Tai saurin rintse idanunta tana jin zuciyarta na mata wane irin zogi da k’una. Can taga kaman ta soma hangosu yana mata cakulkulkuli tana dariya tana zillewa.. Har kaman shewarsu takeji cikin kunnuwarta suna wasanni irinta masoya a parlorn gidan dikda kuwa tasan mislkilanci irin na Mu’azzam.. Ta sak’i k’ara tana mai toshe kunnuwarta “Enough Feenah..!” Ta daka ma kanta tsawa da fad’in haka “This is just your imagination.. Mu’azzam would never do something like this musamman da k’aramar yarinya irin wannan.. Asiri tai masa kawai shiyasa ya aurota ba tareda sanin kowa ba..!” Ta k’arashe zancen nata tana sakin huci kafin ta haura upstairs.