← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 175

Sashe 22

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Koda Malam Liman yaje ma Committee na masallaci da wannan batu suma sun tausaya ma Sadiya da mahaifiyarta dukda a baya basa k’aunar kasancewarsu a Layin.. Amma saidai kaf kud’ad’en dake asusun masallaci bai kai ko kwatan kud’ad’en da ake bin Umma da Sadiya ba.. Bazasu isa ba balle a biya masu dashi Sabida falalar dake cikin biyan bashi ga musulmi.. Haka Liman ya tara jama’a ya masu wa’azi kan falala da ladar da mutum zai samu idan har ya cire d’anuwansa musulmi daga k’unci na bashin da ake binsa ya biya masa wannan bashi.. Saidai ba’a samu wanda yace zai iya biyan bashin ba..

Ana haka saiga Alhaji Isyaku Dancanji mahaifin Sabeera Aminiyar Sadiya ya shigo, ya nemi ganawa da Malam Liman.. Bayan sun keb’e ne ya dubi Malam Liman yace “Malam naji sanarwan da kake na neman kud’i da yarinyar nan Sadiya da mahaifiyarta suke.. Zan biya masu bashin amma fah da sharad’i..

Liman ya fad’ad’a murmushi yana fad’in “Alhamdulillah.. Masha Allah.. Allah dai ya biyaka da gidan Aljannah Alhaji.. Taimakon da kake a layin nan Allah ya dad’a bud’e maka k’ofofin arziki.. Inaji mecece sharad’in naka..?”

Alhaji Isyaku yace “Zan biya masu bashin da ake binsu amma fah saidai idan za’a bani auren ita yarinyar Sadiya..”

Liman yai shiru yana dubansa “Alhaji kana nufi Sai za’a baka auren yarinyar ka biya masu bashin..?”

“K’warai kuwa Malam Liman yanda dai kaji haka ne.. Ai dama bashin na shagulgulan Bikin yarinyar ne.. Kaga Shagali bai tashi a banza ba Malam Liman shikenan sai a d’aura aure dani..”

SameenaAleeyou📚

*GIDAN ARO*

*14*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Da tsananin mamaki Umma take duban Malam Liman “Malam Alhaji Isyaku fah kace.. Shine yace zai biya bashin idan za’a basa auren Sadiya.? Malam Sadiya fah k’awar d’iyarsa ce Aminiyarta ce Wanda sam baya k’aunar tarayyarsu shine zai zago yace yana sonta da aure.. Allah mai iko..”

Malam ya nusa kad’an yace “Ni kaina banji dad’in cewa da yayi har sai idan za’a basa auren Sadiya ne zai biya bashin, domin kuwa naso ya biya dan Allah Allah ya basa ladansa toh amma ya kawo sharad’i sharad’i kuma shine a basa auren Sadiya..”

Umma ta katse Malam Liman da fad’in “A’a Malam wannan ma bazai tab’a yuwa ba, Ko lokacin da nake ganiyan son kud’ina da abin duniya bazan tab’a bari Sadiya ta auri mutumin nan ba balle yanzu da duniyar da abindake cikinta suka fita kaina.. Yajesa mun gode da niyyan taimako Allah zai kawo mana wani hanyar amma banda auren Alhaji Isyaku..”

Liman ya nusa yace “Toh shikenan dama ni ga abinda na Fad’i idan na tuntub’eku zaiji ba’asi.. Allah Ubangiji ya huwace ya kawo wani hanyar..”

Umma ta amsa da Ameen Malam Liman yai mata sallama...

Ta rapka uban tagumi tana mamakin halin mutanen duniya.. Lallai kaga d’an mutum ka barsa, yanzu dik kushe Sadiya da hanata k’awance da mutumin nan keyi da d’iyarsa ashe idonsa nakan Sadiyar ce.. Ashe zai zago bayan ya rabata da d’iyarsa yace zai aureta.. Oh Lallai duniyar yau Ta zama abinda Ta zama.. Wai mutum bazaiyi taimako dan Allah ba sai idan zai sami wani abu in return.. Taimako dan Allah yayi k’arancin har sai idan kaima zaka sami wani abu. Ta yaya kuwa Allah Bazai barmu da halinmu ba idan har na sama bazai tallafi na k’asa ba.. Kai Allah ka kawo mana sauk’i a wannan duniyar tamu.. Ta k’arashe tinanin nata tana mai sauk’e nannauyan ajiyan zuciya.

A d’aki ta iske Sadiya ta gama lallashin Habib yayi bacci dan yaron tinda yaga yanda aka kad’e mahaifinsa akan idonsa Sai ya dinga wani irin firgita idan yana bacci yaita surutai, har sai sunyita masa addu’o’i kafin su samu ya d’anyi baccin..

Umma ta k’ura ma yaran nata idanu cikeda tausayinsu da k’aunarsu, ta k’udiri niyyan da zaran ta gama iddarta zata nemi Sana’a domin ta rufa ma kanta da iyalanta asiri.. Har kullum hannun da yake bayawar yafi hannun da yake karb’a, tayi kuskuren fahimtar rayuwa a baya da tayi tinanin Lallai sai ta hanyar namiji mace zata sami kud’i, yau da ace tanada sana’arta da zai rufa mata asiri da ba sai ta tsaya hangen abin hannun namiji ba balle har taje ta jefa rayuwar d’iyarta a tsaka mai wuya.. Juyowan da Sadiya zatai suka had’a idanu.. Murmushi suka sakar ma juna kafin Sadiya ta gyara ma Habib abin rufuwarsa ta mik’e ta nufo bayan Umma.

Yanayin da taga Umman ciki ya tabbatar abubuwa sunci gaba da tafiya babu dad’i, Ta taimaka ma Umman ta zauna da k’yar saman tabarma sakamakon ciwon dake k’afarta wanda Safeenah ta kuskureta da mota..

“Umma lafiya na ganki haka..? Umma ko wani abin ne ya faru..?” Sadiya Ta tambaya cikeda kulawa tana mai duban mahaifiyar tata..

Umma ta nusa tace “Sadiya wani magana zan fad’a miki amma bana so ki d’aga hankalinki, sannan Inaso ki sani dik abinda kike so, dik abinda zai faranta miki rai nima shi nake so kuma ki sani muddin Ina numfashi Ina tareda ke a Ko menene a matsayina na mahaifiyarki kinji koh...”

K’ak’aro murmushin da yafi kama da yak’e Sadiya tai “Haba Umma ki daina magana haka dik sai kina sa naji wani iri haka nan.. Bazamu sake rasa kowa ba da yardar Allah kinji koh.. Sannan Tabawa Allah zai kawo mana yanda zamuyi da ita...”

Umma Ta kuma nusawa tace “Haka ne Sadiya.. Toh yanzu idan nace miki an samu hanyar rabuwa da tashin hankalin Tabawa amma bisa sharad’i shin zaki amince da sharad’i..?”

Wani irin Farin ciki ne ya mamaye zuciyar Sadiya.. Ta fad’ad’a fari’ar ta tana jinjina kai take fad’in “Umma nasan sharad’in nan bazai tab’a mutuncinki ba sannan bazai tab’a nawa ba, nasan da ace zai shafi mutuncinmu ko sab’on Allah da baki Zo mun dashi ba, da kin watsar tin a inda kikaji.. Umma mecece sharad’in.? Aikatau ne zan masu babu biya ko kuwa wani aikin k’arfi zanyi.. Umma ki sanar dani ko menene zan k’ok’arta na aikata muddin Tabawa zata daina d’aga miki hankali..”

Sauk’e ajiyan zuciya Umma tai cikeda tausayin d’iyar tata, saida ta nusa kafin ta kirawo sunan Sadiya cikin wane irin siga da yanayi..

Sadiya ta d’ago fuska Jiki a sanyaye wann karon ta amsa “Na’am Umma..”

“Zaki iya auren mahaifin Aminiyarki..?”

Dummm! Haka k’irjin Sadiya ya buga, taji batun wani irin gantsagarau wanda zatace ba don daga bakin Umma ya fito ba zasu hau sama Su fad’o da dik wanda yazo mata da wannan batu.. Mahaifin Aminiyarta.. Wacece ma Aminiyarta ai ita tama mance tanada wata Aminiya.. Kai Aminiya fah k’awa mafi kusanci ake nufi.. Wacce kuka d’auki yarda kuka aza ma junanku.. Ita ko lokacin da take Sady pretty d’inta mai son dukiya da abin duniya Ai bazataso ta auri Baban Aminiyarta ba dan idan akwai abinda tafi tsana shine cin amana.. Ita bazata tab’a cin amanan K’awarta irin haka ba..

Muryar Umma ne ya katse mata tinanin nata.. Ta d’ago tana duban Umma tamkar mutum mutumi..

“Umma wacece Aminiyata.. Umma mai kike fad’i... Ban gane komai ba Umma..?” Ta k’arashe gaba d’aya a daburce take.

Umma ta jinjina kai tace “K’warai dole ki shiga rud’u amma ya zama dole na fayyace miki komai yanda mukai da Malam Liman..”

Cikin tsanaki tiryan tiryan Umma ta karanto mata dik yanda sukai da Liman.

Da tsananin mamaki Sadiya ke duban mahaifiyarta “Umma Abban Sabeera fah kikace, Sabeera dai Sabeera aminiyata.. Haba haba Umma.. Wllhi ni koda ace ban tsani mutumin nan ba bazan auresa ba Ko dan Sabeera.. Bana k’aunar ko ganin mutumin nan balle ace aure ya shiga tsakaninmu...Haba Umma ai akan bar halal dan kunya.. Balle ma mutumin nan Umma wllhi ayarsa yake shek’ewa cikin Abuja shisa yake tak’urawa ‘yarsa yake kaffa kaffa da ita dan kar a lalata masa ita kaman dai yanda yake lalata yaran mutane.. Saidai ya mance abinda yakeyi bashi ne kuma adashi ne da dik daren dad’ewa sai ya d’iba.. Ai dik Wanda ya faye kushe da aibata wasu shima d’in na aikatawa ne.. Bayan dik cin mutuncin da ya mana shine yanzu zai wani zago ko kunya babu yace ni zai aura.. Wllhi Allah ya sawak’e min Allah ya tsari gatari da saran shuka..”

Umma ta katseta da fad’in “Nima abinda na fad’iwa Malam Liman kenan, yaje can da taimakonsa bama so Allah zai kawo mana wani hanyar.. Allah yana jin addu’an bayinsa kuma bai mance damu ba, da sannu zai yassare mana kinji koh.. Kar ma Ki saka wannan abu a ranki balle ya dameki.. Kuma kar ki nunawa Sabeera komai dan yarinyar da mahaifiyarta sunada mutunci.”

A hankali Sadiya ta jinjina kai ba tareda ta iya furta komai ba dan har lokacin cikin Shock take, Wai Baban Sabeera Alhaji Isyaku Chanji ke sonta.. Ikon Allah kenan.. Kai jam’a sai kaga mutum ka barsa.. D’an Mutum sai Allah.

**

Ita kad’ai sai zagaya d’akin take tana kuma duban wayarta ta rasa yama akai Barr Ameer ya kuma samun sabon layinta, layin data canza tin lokacin mutuwar Ikram.. Ta masa kashedi ya daina kiranta it’s over between them amma yak’i daina kiranta, ta kula so yake ya kashe mata aure tako ta halin k’ak’a bacin haka mai yasa zai damu da kiranta a waya har yana ce mata yasan bata tare a gidan Mu’azzam ba.. What if Barr Ameer yanada masaniya kan sak’on da aka turo mata a daren da ya gabata kafin safiyar da aka tsinci gawan Ikram.. K’irjin Safeenah yai wani irin yankewa ya fad’i.. Idan kuwa Barr Ameer yasan wani abu tabbas tasan zai dik yanda zai ya tabbata aurenta ya k’are kafin tariyarta da Mu’azzam.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.. Ya zama dole ta tabbata Barr baisan wani abu akan wannan sak’on da ya shigo wayarta ba.. A fili ta furta “Enough Feenah.! You can’t get convicted.. After all, you’re innocent.. You didn’t kill her.. Shegen san sanin k’wak’waf d’inta shi yayi ajalinta..” Ta k’arashe tana mai cusa yatsu cikin sumarta..
Chapter 22 · 0% Book details