← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 175

Sashe 87

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aunty Larai tasa Farida tai mata light makeup a fuskarta. Dik yanda Sadiya bataso ba haka dole akai mata mai sauk’i dama ita ba gwanar kwalliya ma fuska bace tin tana amsa sunan Sady pretty.. Kaidai barta da gayu ma jiki sai ka rantse d’iyar wata hamshak’i ne.. Dama bata faye fente fuska ba.. Yau d’in Sai abin ya zama na musamman abinka da wacce bata saba ba. Tayi kyau har ta gaji, Farida ta d’aura mata d’ankwalin daidai da kanta. Sai santin kyaun da ta k’ara suke.. Ita dai batace komai ba sai fad’uwa da gabanta keyi dan ko Aunty larai bata sanar da ita ba tanaji a jikinta Inspector ne zaizo, ga Umma ta kauda kai abinta bama ta saka masu baki cikin al’amaransu.. Toh kodai baiyi tafiyar bane.? Ta tambayi kanta tana duban kanta a mirror bayan an ida shiryata. Tabarakallah Masha Allah shine kawai abinda taji zuciyarta na ambata. Ta fito tsaf da ita kaman wata sabuwar Amarya.

Tana tsaka da tinanin wayar ya soma ruri. Ta juya tana duban wayar kan gado gabanta na kuma fad’uwa. Tasan idan bashi d’in ba babu mai kiran wayar Dikda cewa ba da lambar da ya sanya mata ba yake kiran.

Ta k’arasa a hankali hannunsa sai k’aran awarwaro yake kafin ta d’auki wayar.

Bata furta komai ba daga d’aya b’angaren ta sinkayo muryarsa cikin sallama.

Ta lumshe idanunta a hankali tana tinanin yaushe rabon da taji Muryarsa. Sallamar tasa ma a zuciya Ta iya amsawa.

Shiru kaman babu mai kuma cewa komai. Nan ta sinkayo muryarsa yana fad’in “Are you ready for your next mission..?”

Murmushi ne taji yazo mata wann karon.. Sai ta d’an murmusa tana rufe fuskarta da hannu guda.

Mu’azzam yaji sautin murmushin nata ta cikin waya. Shima murmushin yai kafin yace “Ki fito ina jiranki a parlor.”
Daga haka k’it ya katse kiran.

Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali tana kuma duban kanta. Mayafinta kalan kayan dake aje saman gado ta d’auka ta yafa kaman mai tsoron ganinsa ko kuma wacce basu tab’a had’uwa ba haka nan taji.. Ta kasa fita saima komawa da baya da tai tana sauk’e ajiyan zuciya a hankali.

Kusan minti biyar ta kwashe kafin ta daure ta fito cikin taku a tsanake.

Tin daga nesa yake dubanta dan musulmin k’amshin da take ne ma ya soma yima k’ofofin hancinsa sallama.

Cak ya daina shafa wayar da yake ya mik’e tsaye yana dubanta sanda take k’arasowa.

K’afafunsa ta fara hangowa itama nan ta fahimci yau d’in shigar manyan kaya yayi.. Ta d’ago idanunta a hankali tana dubansa. Jampa ce jikinsa kalan ruwan k’asa sai hularsa Wanda ya dace da shigar tasa.. zata iya cewa wann shine karo na farko da ta gansa da idonta cikin manyan kaya tin bayan hoton aurensu da ta gani shida Safeenah a gidansu. Sosai shigar ya amshesa ita zata iya cewa irin wann shigar ma yafi amsar Sa. Ko kuma dan ta kwana biyu bata gansa bane shiyasa taga hakan bata dai sani ba. Kaman wacce aka tsunkula Ta kuma maida kanta k’asa tana jin kaman bazata iya ci gaba da tafiya ba sabida irin kallon da yake mata.

SameenaAleeyou📚

*GIDAN ARO*

*45*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Kasa k’arasowa tai saima tsayuwa da tai daga can nesa kanta a k’asa. Gabanta na wani irin fad’uwa musamman da ta jiyo sautin footsteps d’insa alamun yana k’arasowa.

Saida ya tako kusanta kafin yaja ya tsaya yana kuma k’are mata kallo lokaci guda yana tsarkake mahaliccinta.. Cikin ransa yake fad’in Maiyasa suke kiranta Pretty...? Beauty ta cancanci su kirata ba Pretty ba domin kuwa she’s truly beautiful.. Ya k’arashe zancen zucin nasa yana mai kuma k’arasowa kusanta, dab kusanta ya tsaya yana duban tsakiyar kanta sabida ratan tsawo dake tsakaninsu.

K’amshin dake jikinta na kuma tasowa yana bugan k’ofofin hancinsa, hannayensa ya bud’e had’ida rungumeta cikin jikinsa idanunsa a lumshe. Itama d’in lumshe idanunta tai tana jin wani irin salama had’ida nastuwa na ratsa zuciyarta.

Sun d’an jima a haka kafin ya rik’o hannunta suka zauna saman kujera. Ta d’an duk’a ta gaishesa kanta a k’asa.

Ya tsareta da idanu yana duban Bak’on Al’amari a wajenta. Gaba d’aya shi gani yake ma kaman an canzata.

Ya amsa ba tareda ya janye idanunsa daga kanta ba. Suka d’auki lokaci a haka Sai k’are mata kallo yake, har ta soma gundura tana tinanin bazai kuma cewa komai ba, dan tasan mai hali baya fasawa. Nan kuma ta sinkayo muryarsa yana fad’in “It seems to me you’re ready.. For your next mission.. Kin shirya komawa GIDAN ARO..”

Sai sann ta d’an dubesa kafin ta maida kanta wani b’angaren, d’an juyowa tai tana dubansa murmushi saman fuskarta kafin ta jinjina kai tace “Of course Inspector.. I’m super ready to carry out my next mission.. But only for Inne..” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta.

D’an tsimewa yai kafin yace “Aw sabida Inne zaki yarda ki bini ba wai dan kina son bina ba.. Didn’t you miss me at all..?”

Sunkuyar da kanta tai tana murmushi. Sai kuma ta girgiza kai alamun a’a.

Kafeta da idanu yai sai kuma yace “Idan bakiyi kewata ba bazaki min Duka wad’ann kwalliyan ba..”

Dubansa ta kumayi, sai ta murmusa kad’an itama tace “Unfortunately ba sabida kai nai ba Inspector.”

“Toh sabida wa kikayi.?” Ya tambaya yana dubanta.

“Inne of course..” Ta basa amsa kai tsaye.

Mamaki ya cikasa ganin bataji haushi ba, yasan da da ne da yanzu hiran ya k’are yana sako mata zancen mission.

Ya jinjina kai kad’an kafin yace “Ki shiga ki masu sallama we are leaving now.. Akwai yanda zamu biya.”

Ta d’an d’ago tana dubansa a d’an tsorace wann karon “Da gaske kake yanzu zamu tafi..? To.. To.. Bakaci komai ba.. Should I bring something for you..?” Duk sai ta wani daburce lokaci guda.

“Calm down.. I’m not hungry.. I’m ok..” Ya fad’i yana mai kamo hannayenta da zanen k’unshi ya k’ara masu kyau.

Jiki a sanyaye take duban yanda ya sakale yatsun hannunta cikin nasa “I thought you said Kin shirya ma mission d’inki na gaba.. Why are you panicking then..?” Ya k’arashe yana mata wani salo cikin tafin hannunta.

So take ta cire yatsun hannun nata daga nasa amma ta kasa, ga tsareta da idanunsa da yai. Saida ya tabbata ya kashe mata jiki lak’was kafin ya d’anyi gyaran murya yace “Jeki masu sallama na k’agu a fara wann mission d’in..”

Gabanta ya fad’i tai saurin d’agowa tana dubansa, sai gani tai yankashe mata idanu guda “Go now.” Ya fad’i murya a hankali yana mai mata alama da idanu.

Jiki a sanyaye ta mik’e ta nufi ciki yayinda Mu’azzam ya d’au wayar salulansa

Tana shiga ciki maimakon ta sanar dasu d’aukanta yazo, sai ta soma masu kuka. Ta duk’a saman cinyar Umma tana kuka.. Aunty Larai ta duk’a tana lallashinta had’ida bata baki “Haba Sadiya saikace tafiyar da bazaku dawo ba, dukda duka bazaku shige sati biyu ba.. Tashi abinki kayayyakinki ma an fitar miki tintini.. Tashi kar ki b’atawa mijinki lokaci kinji koh.”

Ta d’ago tana duban Umma, kwantattun hawaye ta hango cikin idanun Umman. Basu iya furta komai ba Sai rungume juna da sukai.

“Allah shi maku albarka.. Allah ya tsareku daga dukkanin abin k’i ya azurtaku da zuri’a d’ayyiba.. Tashi kije Sadiya na yafeki duniya da lahira.. Allah yajik’an mahaifinki ya miki albarka..” Ta k’arashe suna masu kuma rungume juna cikin hawaye.

Haka su Aunty Larai dasu Habeeb suka rakota har waje kaman kar su rabu da juna.

Mu’azzam ya bud’e mata front seat ya kuma musu sallama kafin Sadiya ta shige kanta a k’asa.

Nan suka d’auki hanya sun Aunty Larai dasu Habeeb suna masu waving.

Tana hangosu ta mirror tana jin wasu hawayen na kuma zuwa mata.

Yana hankalce da ita saidai bai furta komai ba har sukai nisa da tafiya.

Hannunta dake aje saman cinyarta taji masa hannun guda akai d’aya kuma yayi amfani dashi wajen rik’e steering wheel. Zata janye taji ya d’an rik’e da k’arfi still idanunsa naga kwalta ba tareda ya dubeta ba.

Babu yanda Ta iya dole haka hannunta guda ya kasance cikin na Mu’azzam dake driving da hannu guda.
**

Da k’yar ta iya tashi tana murtsuke idanu, alarm d’in da Ta saka ne ma ya tada Ita dan a ranar take shirin komawa Office.

Bathroom ta fad’a Tai wanka kafin ta tana drying kanta, sai lokacin ta zira Doguwar riga da hijab tai sallar asuba. Dan dama tin da Mu’azzam ya tasheta tai Sallah sai ta gudo nata d’akin tai kwanciyarta. Harda kulle k’ofa tai dan karma idan ya dawo ya shigo ya tada ita ya tambaya ko tayi sallan. Ta d’an tsuke baki tace “Haka kawai ba gashi yanzu nayi sallar ba, da ace ina can d’akinsa na tabbata da yanzu ya katse min bacci na yace lallai Lallai dole dole Sai na tashi sallah. Dik San bacci na kusanka my Halal zan iya yafe baccin safe a jikinka..” Ta k’arashe tana mai ci gaba da shirin fitarta. Nan ta duba time taga har 9:30am.

A gurguje ta ida shirinta ta nufi nasa d’akin Dikda tasan by then ya tafi office. Kaman yanda tai tunani d’akin nasa tas tas kaman basu kwanta saman gadon ba.. Har Ta juya zata fice Ta dawo da baya tana duban side lamp dake kunne.. K’arasawa tai zata kashe lamp d’in nan taga drawer d’in kaman a bud’e ga wani abu kaman picture ya sako kai. Zuciyar Safeenah yai wani irin yankewa.. A hankali ta ida bud’e drawer d’in zuciyarta naci gaba da bugu.. Bata ida jin tashin hankali ba saida ta ciro hoton gaba d’aya.
Chapter 87 · 0% Book details