Sashe 98
Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
K’ok’arin saita kansa yai kafin yace “Bazaki fahimci komai ba Ajidde koda zan miki bayani.. Amma abinda nake so ki sani shine ban b’oye miki kaina dan rashin yarda dake ba ko wani abu makamancin haka.. Ki yarda dani bana nufinki da sharri face alkhairi..”
Shiru tai tana juya kalamansa cikin zuciyarta kafin ta d’ago ta dubesa kad’an. Sai kuma ta goge hawayenta ta murmusa kad’an tace “Banida hurumin jin haushi dan baka sanar dani asalinka ba.. Saidai naji zafi sosai bayan na aminta da kai, na sanar dakai sirrin maganin Innata.. Wanda Sirri ne Babba na zab’i sanar dakai.. Amma kai ka b’oye mun wani abu, dukda cewa munyi tarayya wajen watsar da maganin Inna Kyallu da kuma amsar maganin Malama Hafsah..” Fasali tai tana kuma maida kukan dake k’ok’arin zuwa mata.. Kafin Ta murmusa tace “Tabbas ka taimakeni kuma na gode.. Watak’ila badon kai ba da yanzu nayi abinda Inna Kyallu ke umartana na aikata a cikin gidan nan.. Ina nufin sata.. Na gode maka matuk’a.. Ubangiji ya biyaka..” Tana ida fad’in haka tasa kai ta shige.
Musaddiq yabi bayanta da kallo yana jin wani abu can k’asar zuciyarsa. A haka Jume da k’arasowarsa kenan ya hangesa.
Har ya iso wajen Musaddiq baisan ya iso ba. Jume ya dubesa ya kuma duban yanda Musaddiq d’in ke kallo kafin ya k’ara sautin muryarsa yace “Wai lafiya kake..? Bakina na uku fah kenan Ina maka sallama..”
D’an sauk’e ajiyan zuciya Musaddiq yai had’ida jan gajeren tsaki yace “Kar ka raina mun wayo mana, mai ka d’aukeni da zakata buga sallama banji ba..”
Jume ya murmusa yace “Malam naga yanda idanunka ke Kallo.. Fad’a mun mai ya faru.. Ka riga ka sanar da ita yanda kake ji ne tinda har ka sanar da Inne ko so kake taji batun daga cikin gida..?”
A d’an karkace ya dubi Jume kafin ya girgiza kansa kad’an ya k’arasa saman karyayyen bishiya ya zauna.
Jume ya k’araso ya zauna gefensa. Yai gyaran murya kad’an kafin yace “Wai bazaka iya fad’a mata bane..?”
A dak’ile ya dubesa kafin yace “Mai zan fad’a mata..?”
“Kace mata kana sonta..” Jume ya basa amsa kai tsaye.
Gimtsewa yai kad’an kafin yace “Ni nace maka ina sonta..?”
Jume ya saki baki yana kallonsa “Ikon Allah.. Jiya jiya ka d’aga jijiyan wuya cikin gidan nan cewa kana sonta zaka aureta.. Toh ina courage d’in ya tafi..?”
“Kai yanzu idan nace maka ina son Ajidde sai ka yarda..?” Ya tambaya yana duban Jemen.
Jume ya girgiza kai yace “Ban gane ba.. Mai zai hanani yarda. K’warai ma kuwa da gaske zan yarda.. Maiyasa bazaka sota ba.. Sabida wayewarku ba iri d’aya bane kokuwa status d’inku ba d’aya ba..?”
A dak’ile yake dubansa kafin yace “Kaima kasan bazan tab’a fifita kaina sama da wani sabida wani ni’ima da Allah ya bani wanda bai bama wancan d’in ba.. Kawai ni ba sonta nake ba.. Na fad’i haka ne to save her.. But I don’t love her.. In fact ban tab’a kawo Ajidde a irin jerin matan da nake son aura ba.. Kawai dai nasan tana saka ni nishad’i.”
Jume ya girgiza kai kad’an had’ida murmusawa kafin yace “Idan kace haka ni bazan ce komai ba.. Allah ya ara mana kwana muga k’arshen taimako.. Ni zan wuce kafin Sarkin gida yace nayi latti..” Daga haka shigewa yai ya bar Musaddiq zaune nan wajen yana tinanin rayuwa.
**
A b’angaren Ajidde kaw tana shiga gidan ta tadda Mama Hindu na had’a breakfast.
Mama Hindu ta dubeta tace “A’a mutuniyar yau babu shigowa da wak’en da kika saba ne..?” Tana maganar tana murmushi.
Ajidde ta turo baki gaba kad’an tace “Ai wllhi Mama Hindu da k’yar ma na shigo saida nayita jero addu’a cikin zuciyata Ina fad’in Allah Sa kar naga Kofur Zalimu a hanya..”
Mama Hindu ta saki baki tana dubanta kafin tace “Waye kuma Kofur Zalimu a gidan nan ni Hindatu..”
Ajidde ta aje Jakarta tana fad’in “Ahtoh.. Yanzu baki San Kofur Zalimu ba.. Chaabb ga gidansa ta can..!” Tai nuni da section d’in su Mu’azzam.
Dariya ce ta kufcewa Mama Hindu kafin tace “Kice shi ya saita mun ke kika shigo a natse salin alin Babu hayaniya.. Fad’a min wace kalan wa’azi ya miki da ya shiga kanki tinda nidai babu kalan wacce ban jaraba ba..”
Ajidde ta kuma k’wafa tana danna harara ma rufin kwanon b’angaren Mu’azzam kafin tace “Muguntarsu ta ‘yansanda mana.. Dama ance sunfi Soja iya makirci.. Yanda tufafinsu yake bak’i haka zuciyarsu ma.. Kai shiyasa ma duk suke bak’ak’e da k’yar kaga fari.”
Mama Hindu tace “Toh ai shi Baban Inne nada haske idan baki saka sa layin farare ba ai bazaki saka sa layin bak’ak’e ba..”
Har yanzu bakinta a ture yake “Ahap ai Farin fata ne kawai amma Zuciyar babu annuri.. Shiyasa kullum fuskarsa kaman an masa mutuwa..”
Mama Hindu ta kuma murmusawa kafin tace “Aiko kinzo a daidai dan yanzu nake cewa bara na kirawo Ummilo tazo Ta kai masu abin kari kinga shikenan sai ki kai masu..”
Ajidde ta zaro idanu tana aza hannaye saman k’irji “Ni wa..! Mama Hindu ki rufa mun asiri.. Ni wllhi kinga hanyar can ko cikin maye nake bazan yi gigin bi ba.. Bana fata wani abu ya had’ani da Kohur Zalimu.. Ko a k’iyama bana fata mu had’u..” Tai maganar tana nuna hanyar sashen Mu’azzam tana tofi da bakinta.
Mama Hindu tace “Haba Ajidde Musulmi d’anuwanki kice baki fata ku had’u a k’iyama.. Kika sani ko ku shiga Aljannah lokaci guda..” Tai maganar cikeda barkwanci.
Ajidde tace “Wa Tabb. Ai wllhi dan dai Malama Hafsah tace Babu kyau kai wa d’anuwanka musulmi mummunan addu’a bane da na masa addu’a..”
Mama Hindu ta katseta da fad’in “Da kin masa addu’a kar ya shiga aljannah.. Haba Ajidde ko mai ya miki ai dai yaci albarkacin makusantarsa dake k’aunarki.”
Ajidde ta jinjina kai tace “Ai sabida su ne ban masa addu’a ba.. Kinga matarsa ai Tanada kirki ni bansan mai ta gani wajen mugun nan ba k’ila tsawon da fankam fankam d’in ta gani dan dai naga itama farar ce tas kyakkyawa tama fisa kyau.. Sai Inne sai Mamy.. Sai...” Musaddiq tai niyyan ambata sai kuma bata ambata ba tai shiru.
Mama Hindu ta girgiza kai tace “Banida lokacin shirirtarki Ajidde lek’a baya ki kira mun Ummilo..”
Ta kuma rataya Jakarta kafin ta amsa ma Mama Hindu ta fice kiran Ummilo, tana tafe tana sand’a tana addu’an Allah Sa kar tayi mugun gani.
**
Aunty Shemau ta mik’e tana fad’in “Toh Amarya.. Bara na barki ki huta dan nasan kina buk’atar hutun.. Kindai ji abinda na fad’a miki.. Ki d’aukeni tamkar uwa.. Dik abinda ya shige miki duhu a gidan nan ki sameni ki sanar dani.. Ni babu wata surkunta kinji koh..”
Sadiya dai kanta a k’asa kurum take murmushi har Shemau ta ida bayanan ta. Saida takai k’ofa kafin Ta juyo tace “Allah ya kawo mana k’azantar d’aki da wuri..” Tai maganar tana duban Sadiyar kafin ta fice.
Wulk’awarta Mu’azzam ya hango dan fitowarta kenan daga sashen Inne ya tsaya wajen Mamynsa.
Ya k’araso ya tadda Sadiya na k’ok’arin mik’ewa. Tana ganinsa kaman wata marar gaskiya ta koma ta zauna da d’an k’arfi wanda har cikin kanta saida taji zafin zaman.
Ta tamke idanunta tana sakin k’ara a hankali. Lokaci guda ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta.
K’arasowa yai ya zauna gefenta kad’an. Ya d’an shigar da ita jikinsa ba tareda yace mata komai ba.
“Kin mance ke patient ce zakiyi irin wann zaman..?” Ya fad’i mata cikin sigan rad’a saitin kunnenta.
Ta kuma danne fuskarta da tafukan hannayenta cikeda kunya.
Murmusawa yai kafin yace “Wai yaushe kika fara kunyata har haka ne.?”
Ya d’anyi fasali kafin yace “Oya toh bud’e idon mu gaisa..”
Ta mak’e masa kafad’a alamun a’a.
Ya kuma sakin miskilin murmushi kafin ya sakalo hannayensa daga bayanta zuwa cikinta ya manneta jikinsa kad’an yace “Idan baza’a gaisheni ba Na yafe gaisuwan amma a bud’e mun kwalliyata na gani..” Ya k’arashe yana mata wasu salon da hannayensa wanda ya soma birkitata gaba d’aya. A tsorace ta sake masa kuka cikeda shagwab’a tana fad’in yai hak’uri ya k’yaleta.
“Toh a bud’e mun kwalliyata a zauna lafiya..” Ya fad’i yana d’ago hab’arta kad’an. Ya jima yana dubanta kafin yace “Kin san wani abu..?”
Ta girgiza masa kai a hankali.
Yaci gaba da fad’in “At times sai yana mun kaman na tab’a sanin ki can da dad’ewa.. Like mun tab’a had’uwa a wani waje.. But I can’t remember when and where.”
Tai masa tsuru tana dubansa itama yanda ya tsareta da idanu.
Sai kuma ya murmusa yace “Kema kinji haka koh..?”
Ta girgiza masa kai a hankali tana kuma duban kyakkyawan fuskarsa. Su duka biyun duban juna suke cikeda shauk’i.
Murmushi taga ya saki mata kafin ya kashe mata idanu guda yace “See.. Nasa kin bud’e idanunki.. I worn..” Ya k’arashe yana sakin murmushi mai bayyana hak’wara.
Pillow dake gefenta ta d’auka ta kai masa dukan wasa tana fad’in “That was cheating Inspector..”
Ya kuma murmusawa kafin ya janyota jikinsa yace “Inada tactics da dama da zansa kiyi abinda baki shirya ba yarinya..”
Ta kuma nitsar da kanta cikin k’irjinsa tana shak’an ni’imtaccen k’amahinsa, ta lumshe idanunta a hankali kafin tace “Because you are a detective right..?”
Murmusawa yai tana nan cikin k’irjinsa, ya fashi gefen fuskarta kad’an kafin yace “Because you are my wife and I can read your mind..”
Murmusawa tai wanda saida jikkunansu suka d’an motsa ba tareda tace komai ba.