← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 175

Sashe 59

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ki ajiye bayananki har sai munje ofishinmu.!” Ya fad’i cikin kad’uwa kafin ya dubi Maleeka yace “Take her.!”

Wane irin k’ara Safeenah ta saki wanda saida ya firgita kowa dake cikin gidan. Su Kiki da dake d’aki basusan wainar da ake toyawa ba ihun Safeenah ne ya fiddo dasu gaba d’aya.

Tashin hankali bisa tashin hankali. A fujajan Mommy tabi bayansu Safeenah tana fad’in Mu’azzam bai isa yakai mata ‘ya ofishin ‘yansanda ba. Dik abinda ake bama tai zaton Daddy na gidan ba. Ta zaci ya fice.. Ta dubi Meema hanaki tashe tace “Call your Dad right now..!” Ta kuma duban Aunty Shemau da tuni ta d’auko mata mayafi tana rufa mata. “Muje Shemau..!” Ta fad’i suna ficewa cikin sauri.

Wani irin wawan birki Mommy tai ganin Wai da sanin Daddy Mu’azzam yazo d’aukan Safeenah. Kuka Mommy Ta fashe dashi sanda Safeenah ke sanar da Daddy cewa batada laifi cikin kuka.

Daddy ya girgiza kai yace “‘Yansanda zasuyi aikinsu.. And if you are proven guilty.. Ki mance kinada mahaifi Marwan Gamji. I do not have a daughter for a criminal.!” Yana ida fad’in haka ya juya cikin gida yana matsan k’walla.

Mommy Ta bisa da kallo baki sake. Lokaci guda ta isa tana janyo Daddy “She’s your daughter.. You should believe her.. Kasan Safeenah bazata tab’a aikata abinda ake zargin Ta ba.. Wllhi our daughter is not a killer.. She can be anything.. But not a murderer.. You can’t neglect your daughter.. She needs you now.. Kai tunanin sunan ahalinmu.. Wannan zai b’ata maka sunanka da sunan ahalinmu ne.. Mu’azzam ba d’an halak bane tinda har ya shigo da ‘yansanda cikin gidan nan akai arresting Safeenah.”

Sai lokacin Daddy ya juyo ya katseta da fad’in “Ina jin kin mance cewa kafin Mu’azzam ya tsaya akan case d’in nan ni ne mutum na farko da yai failing case d’in mutuwar Ikram ma ‘Yansanda.. Kin mance cewa ni ne nan nai k’udirin za’a bincike mutuwar nata dukda cewa ga sakamon da ya bayyana cewa mutumin da ya kasheta ya riga ya kashe kansa.”

Mommy cikin kuka Ta katsesa da fad’in “Amma ai duk mun amince mutumin da ya kashe Ikram ya kashe kansa.. Mu’azzam neman wanda zai d’aura ma Alhaki kawai yake..” Ta k’arashe cikin kuka.

Daddy ya jinjina kai yace “Ki k’yale ‘Yansanda suyi aikinsu Hajara.” Daga haka Sa kai yai ya shige.

Mommy ta soma kururuwa ta nufi mota tana fad’in driver yazo ya tuk’asu itada Aunty Shemau, dole subi bayan ‘yansandan idan Daddy bazaije ba.

Meema da Kiki kaw kuka suka dingayi suna ganin Bak’on al’amaren dake faruwa cikin ahalin nasu. Wai Ya Mu’azzam yai arresting Addah Feenah kuma wai da kisan Ikram ake tuhumarta. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.

Cikin sauri Meema ta shiga neman layin Musaddiq dan Ta sanar dashi abindake faruwa dashike baya gida.

**

Mu’azzam ya k’ura mata idanu sanda aka barsu su biyu a interrogation room saiko d’an mindow mai kaman glass wanda abokan aikinsa zasu iya hangosu daga nan.

Idanunsa jazir yake duban Safeenah sanda ya nuna mata lambar wayarta da time da date da komai da komai na lokacin da aka tura mata sak’on.

Safeenah taci gaba da girgiza kai tana furta “Na rantse da Allah bansan komai ba Mu’azzam..”

Tsawa ya daka mata yana mai buga table d’in da ya raba tsakaninsu “Don’t you dare lie to my face.! You received this text message a ranan d’aurin aurenmu.. Admit it Safeenah.!” Yai maganar idanunsa tar akanta wayar Sagir rik’e cikin hannunsa yana mata nuni da sak’on.

Safeenah taci gaba da girgiza kai tana hawaye ba tareda tace komai ba.

Mu’azzam yaci gaba da furta “You were not yourself that day Idan ban mance ba. You were acting very strange.. I even asked you meke damunki, but what did you say..? Ce min kikai nervousness ne na barin gida sabida zakiyi aure.. Washe garin wannan ranan aka tsinci gawar Ikram... Haka ne..?!”

Ta kuma girgiza kai tana hawaye “Na rantse da Allah ban San komai ba..”

Wani Farin takarda Mu’azzam ya ajiye gabanta nan saman table d’in wannan karon cikin rawar murya yake magana “This is the autopsy result of Ikram’s death Safeenah..!” Muryarsa yaci gaba da rawa yana furta “Take a look Safeenah.. Ki duba autopsy result d’in.. Binciken da likita ta gudanar akan gawan Ikram.. She was raped Safeenah..!” Izuwa lokacin hawaye ne ke gangaro masa haka ma Safeenar wacce take girgiza kai tana duban takardan.

Mu’azzam yaci gaba da furta “My sister was raped and then shot.. An mata fyad’e sannan aka harbeta da bindiga.. An kasheta a wulak’ance. Wulak’ancin da ko dabba baza’a masa ba.. Idan kinada zuciya cikin k’irjinki Safeenah zaki sanar dani gaskiyan al’amarin.. Zaki sanar dani gaskiyar da kika sani..!” Ya k’arashe gumi na gangarowa daga cikin sumarsa zuwa goshinsa.

Safeenah taci gaba da girgiza kai tana hawaye “Wllhi ni bansan komai ba Mu’azzam.. Ka yarda dani.!”

Buga table d’in ya kuma da k’arfin gaske wanda saida ya storata Safeenah “Isn’t it enough that you’ve been fooling me for almost a month now.. You insulted my intelligence and my profession as a police officer.. Safeenah let’s not make this difficult anymore.. Ki sanar dani mai kika sani..”

Safeenah ta d’ago tana dubansa cikin huci wannan karon “Banfa mance abinda ka min ba Mu’azzam.. Dan Mommy tace zata maka ka a Kotu shine bari ka b’ullo ta nan.. Bazaka tsere ma laifinka ba.. Ka cuceni ka kai min mace cikin gidana.. Kana kwanciya da ita a saman gado na kai ko kunya bakaji ba.. Tell me mata nawa ka kai min gida ka kwanta dasu saman gadona.”

“Feenahh..!!” Ya daka mata tsawa yana mai d’ago hannunsa kaman zai mareta. Sai kuma ya sauk’e hannun nasa a hankali..

Safeenah taci gaba da kuka tana fad’in “Kai mugu ne Mu’azzam.. Azzalumi ne kai.. Ka cuceni Ka cuceni.!” Tai maganar tana k’ok’arin turasa tana kuka sosai tana bige bige.

Mu’azzam ya shiga k’ok’arin kame hannayenta dole Maleeka ta shigo tana taimaka masa da rik’e Safeenah dake Ta faman buge buge kaman sabuwar kamun hauka.

Ficewa yai daga interrogation d’in to get some fresh air, saida Safeenah ta daina bige bigen da take kafin ya dawo cikin tsananin tsimewa. Tai zaune saman kujeran tana sakin huci.

“Shall we continue.”ya fad’i yana dubanta.

Kauda Kai gefe tai kafin tace “Ina son magana da lawyer na. Ko shima banida dama.?”

Yai mata K’uri yana dubanta “Daddy yace lauyansa bazai tsaya miki ba. Kinada wanda kike so a kira miki in mind.”

Ta d’ago da mamaki tana dubansa jin abinda ya fad’i. Kafin Safeenah takai ga magana sukaji an turo k’ofa an shigo.

“I need to speak to my client. Mr Inspector.” Abinda ya fad’i kenan daga nan yanda yake tsaye cikin bak’ar suit d’insa.

Daga Safeenah har Mu’azzam juyawa sukai suna duban Ameer dake tsaye kansu.

Mu’azzam ya mik’e shaye da mamaki yana duban Brr Ameer dan tsaf ya ganesa tsohon saurayin Safeenah ne.

SameenaAleeyou📚

*GIDAN ARO*

*32*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Mu’azzam ya girgiza kai yana duban Barr Ameer disbelievingly kafin ya kuma duban Safeenah wacce itama Ameer d’in take duba.

Lokaci guda Ameer ke takowa gaban Mu’azzam d’in muguwar murmushi saman fuskarsa. Ba tareda wani b’ata lokaci ba ya mik’awa Mu’azzam dake tsaye gaban yana dubansa hannu alamun musabaha “Inspector, long time no see.” Ameer ya fad’i still murmushin saman fuskarsa yana mai mik’a right hand d’insa ga Mu’azzam d’in.

Ganin Mu’azzam bai mik’o masa hannun ba ya sanyasa sakin wata k’asaitacciyar murmushin kafin yace “Nasan ka sanni by name so need na maimaita abinda ka riga ka sani. After all, your wife and I used to be very good friends.”

Izuwa lokacin zuciyar Mu’azzam takai k’ololuwa wajen b’acin, hannayensa kaw sai faman dunk’ulesu yake jijiyon jikinsa na kuma fitowa sosai.

Ameer ya kuma gyaran murya yana d’an gyara tsayuwarsa kafin yace “Aff ashe fa na mance ban maka murnan aure ba, everything happens so fast.. I couldn’t get the chance to congratulate you.. But wait.. Shin ka cancanci nai maka murna..? Wanne irin miji ne zai arresting matarsa..? What kind of a husband does that to his wife .? Aren’t you ashamed of yourself Inspector.? Kana tuhumar matarka da kisan k’anwarka..” Ya d’anyi fasali yana mai girgiza kai kafin yace “Don’t you have anything to say to me, Mr Inspector..?” Ya d’an tab’e baki kad’an kafin yace “Koda shike ba Kai bane abokin karawan nawa wannan karon. I rather speak with your Lawyer in court.. Sai muga waye kuma zai sha k’asa yanzu.!” Baikai aya ba yaji sauk’an naushi a hancinsa wanda saida ya kaisa k’asa.

Safeenah ta mik’e da sauri tana k’ok’arin tare Mu’azzam yayinda Maleeka da Assad dake dubansu ta cikin glass sukai saurin shigowa.

Assad ya k’arasa ya rik’e Mu’azzam d’in yayinda Maleeka ta duk’a tana tambayan Barr Ameer if he’s okay.

Barr ya mik’e yana kame bakinsa da Mu’azzam ya basa naushi wajen.. Yana fad’ida Maleeka “I’m alright.. Kar ki damu Officer.”

Assad yaci gaba da k’ok’arin janye Mu’azzam yana fad’in “That’s enough Mu’azzam..”

“You Stay out of this Assad.. Let me teach this moron some manners.” Yana maganar yana fincika Assad na kuma rik’esa.

Ameer yai wata k’asaitacciyar murmushi kafin yace “Can I speak to my client now..?” Yai maganar yana duban Mu’azzam dake aika masa razannan kallo. Ya kuma murmusawa kafin yace “In private.”

Mu’azzam ya kuma yowa kansa Assad yai saurin janyesa ya fice dashi.

Suna ficewa Mu’azzam ya finciki hannunsa daga rik’onda Assad yai masa yana mai shafe fuskarsa da tafukan hannayensa.

Assad ya jinjina kai yana dubansa “Just what do you think you are doing..? What has gotten into you.?” Assad cikin fad’a fad’a yake maganar. Ya shafi kansa kad’an yana duban Mu’azzam da ya dafe benci ya kifa kansa kurum ba tareda yace komai ba Sai zuciyarsa dake tafarfasa.

Assad yaci gaba da fad’in “You attacked her lawyer Mu’azzam.. What if wani yaga hakan.? Ka godewa Allah babu kowa wajen...”
Chapter 59 · 0% Book details