← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 175

Sashe 43

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dubansa tai zuciyarta naci gaba da yankewa sai kuma taga ashe shid’in ta rik’e tsananin firgicin haushin karnukan wanda bama tasan tayi hakan ba. Cikin tsananin huci da zafin nama ta turasa da iya k’arfinta wanda saida ta kusan kaisa k’asa “Idan kana tsoron na shafa maka cutan zamani Maiyasa ka sato ni daga gidanmu ka kawo ni nan.. Bari kaji na fad’a maka Allah bazai tab’a baka nasara akaina ba.. Nafi k’arfinka nafi k’arfin wulak’ancinka..!” Ta k’arashe tana mai kuma janye hijabinta tana sauk’ar sa sosai tana mai kuma rufe jikinta.

Dubanta yake daga sama zuwa k’asa cikeda mamaki kafin yace “Ke.! Cut this nonsense. No one wants a trash like you..!” Yana ida fad’in haka yaci gaba da janyota.

Ga tsananin mamakinta wani d’an d’aki mai kaman store taga ya k’arasa ya bud’e gefen na Karnukan nan daketa faman haushi. Tsoro ya soma cikata sosai, kardai da gaske ya kawota ne ma karnuka su cinyeta. Jikinta yaci gaba da rawa.

Yana ida bud’e d’akin ya turata ciki. Sadiya na hawaye ta d’ago hannu tana rok’onsa “Please don’t.. Don’t leave me here please.. Na rok’eka.. If you have any good in your heart dan Allah kar ka barni a nan.. Dan Allah ka maidani wajen Ummata..Wllhi tsoro nake..”

“Ina tsaurin idon naki da courage d’in suka tafi.? Maima kika ce..?” Ya kannare idanu yana dubanta kafin ya jinjina kai yace “Yauwa kika ce A cheap low life police Officer wanda baida komai bai dogara da komai ba face karb’an bribe baida kud’ad’en da zai sauk’e miki bashinki..? Ko ba haka kika fad’a ba..”

Ta shiga girgiza kai still tana hawaye.

Jinjina kai ya kuma kafin yace “Dama na fad’a miki Zaki maimaita. Well, wannan Matsiyacin D’ansanda ya biya bashin kuma harda sadakinki.. And yau zan tabbatar miki cewa ke d’in Low life ce. Wannan d’akin shi ya kamaci low life irinki.. You’ll spend the night here, tareda Karnukan nan dan na tabbata kema d’in Kariyace.!” Yana ida fad’in haka ya janyo k’ofar ya rufe yai ficewarsa.

Daskarewa Sadiya tai cikin rashin yarda da abinda Mu’azzam ya mata. Rufeta yayi a wannan k’aramin d’akin dake jikin d’akin Karnuka wanda motsi kad’an sukai zataji balle suyi haushi. A hankali taji k’afafunta suna silalewa. Ta tak’ure waje guda tana duban d’akin mai tsananin duhuwa.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un kawai take iya ambata.. Bata tab’a jin ta tsani wani mutum a rayuwarta irin Mu’azzam ba. Ta rintse idanunta tana fad’in “Allah na tuba.. Na tuba ka yafe mun.. Abba ka yafe min.. Umma kizo ki cecen.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.. Na shiga uku ni Sadiya..!” Tana jin sanda Mu’azzam ya fice daga gidan ya rufe gate. Da gaske barinta yai a gidan Ta kwana tareda Karnuka.. Wani wawan haushin da karnukan suka saki saida taji har tsakiyar k’wak’walwarta.. Ta saki k’ara dan tsoro tana mai duk’awa had’ida toshe kunnuwanta da duka hannayenta biyu, ta rintse idanunta dikda tsananin duhuwa dake cikin d’akin wanda ko tafin hannu baka iya gani.

**

A can Fufore kaw anyi carko carko akan Safeenah wacce mai gyaran k’afa yazo ya yana d’aure mata k’afar tata. Sai kuka take tana fad’in ta shiga uku gashi sam batasan yanda Mu’azzam yake ba tin jiya basu had’u ba sannan bata isa ta tink’ari Inne ta tambayeta Ina Mu’azzam yake ba. Ga wayarsa sam ta kasa samu.. Safeenah sai kuka take tana fad’in zafi k’afar take mata.

Inne na zaune saman kujera mai gyara na kuma jan k’afar Safeenah na ihu. Inne tace “Ki rufe mana baki.. Uban da yasa kika zuba ma yarinyar tsantsi a hanya.. Gashi nan da yake batada hakkinki ta tafi gida lafiya ke kuma kin taka abinda kika zuba mata kinji ciwo.”

Safeenah tace “Inne amma ke Wai bakiga abinda yarinyar nan tayi bane.. Wllhi na tabbata akan abinda tayi Mu’azzam zai iya b’ace mana b’att a dena ganinsa a gidan nan.. Ai dai Kinsan halinsa Kinsan yanda yake abubuwa.. Wllhi Allah na tabbata kan abinda yarinyar nan tai zai iya barin gidan nan without informing anyone... Wayyo Allah Malam mai d’auri Kaja a hankali..!” Ta kuma fad’a tana k’ok’arin janye k’afarta.

“Ki rufe wa mutane baki.. Allah k’ara. Gobe ma dan Allah ki k’ara..!”

Musaddiq ya tina sanda Ajidde zata tafi tace masa anyi babu shi bayi kallon birgiman bijimi a k’asa ba.. Dik a tinaninsa D’aya daga cikin shanun gidan ne ya fad’i k’asa yana birgima ashe fad’uwar da Safeenah tai ne take son sanar dashi kenan.. Ya girgiza kai kurum yana ba tareda ya ce komai ba. Sai kuma ya dubi Safeenah dake ture turen baki tana motsa k’afar da k’yar yace “Next time sai a kiyaye.. Allah ya kara sauk’i..”

Bata amsa ba ta rakasa da harara ga hawaye saman fuskarta.

Bayan kowa ya mata sannu an watse Meema ta matso kusanta tace “Sannu Adda Feenah..”

Harara Safeenah Ta aika mata kafin tace “This is all your fault you know.. Saida nace miki kar mu saka mata ruwan tsantsi ba lallai ta taka ba Kikace mahaukaciya ce bata tafiya a natse dole zata taka gashi nan ita bata taka ba ni na taka..”

Meema Ta tab’e baki tace “Addah Feenah ni fa da nace ki zuba mata ai bance kibi bayanta ki duba ko ta taka ko bata taka ba, ke da kanki kiyi wannan shawarin naki.. Toh ki fad’a mun how am I at fault..?”

D’an gyara zama Meema tai tana kuma fito da idanu waje had’i da kwantar da murya tace “Addah Feenah.. What if this is your Karma..! Kin tuna matar nan da kika taka mata k’afa da Mota ranan a k’ofan Police Headquarters.. Karma is backfiring you Addah Feenah..” Tai maganar tana mai d’aga gira sama had’ida jinjina kai alamun tabbatarwa.

Safeenah ta aika mata harara tace “Don’t even start Meema..”

Meema ta murmusa tace “Wllhi Addah Feenah it’s possible hakkin matar nan ne ya kamaki.. Gashi irin abinda kika mata ya sameki.. Now we have no option dole mu k’ara kwanaki a garin nan har ki warke.. Who knows mai rikiceccen mijin nan naki zai tareda budurwarsa yanzu da kika gurgunce a nan..”

Pillow dake gefenta ta d’auka ta jifawa Meema tana fad’in “Get out before I kill you Meema..!” Tai maganar tana huci zuciyata na tafarfasa. Fuskar Maleeka kurum take hangowa tareda mijinta. Lokaci guda Ta saki k’ara tana mai jifa da pillow d’in. Dik shegiyar Ajidden nan ne ta jawo mata.. Wllhi babu abinda zai hanata cin uwar yarinyar nan..

Meema Ta k’unshe bakinta ta fice tana dariya.

**

Misalin k’arfe 11:00pm ya shigo gidan, Kai tsaye sashen Daddy ya wuce dan ya hango wutan parlor a kunne alamun Daddyn bai kwanta ba kenan.

Da sallama ya shigo saman bakinsa.
Daddy dake zaune daga center d’aukeda wasu documents yana sorting. A hankali ya soma zame k’aramar gilashin dake mak’ale idanunsa yana mai amsa sallamar Mu’azzam d’in. Nan fari’arsa ta k’aru.

“A’a Officer sauk’ar yaushe.” Daddy ya fad’I yana mai fad’ad’a murmushinsa.

Murmushin ne saman fuskar Mu’azzam d’inma sanda ya k’araso saman carpet d’in. Gaban kujeran da Daddy ke zaune ya duk’a ya zauna yana mai gaida Daddyn.

Da sauri Daddy ya mik’a masa hannu sukai musabaha kafin yace “Yanzu ne zuwan Naka kokuwa ka jima da shigowa garin..”

Mu’azzam ya d’an girgiza kai yace “No Daddy tin da yamma na shigo na biya na kula da wasu al’amran ne..”

“Oh toh toh Allah sarki.. Kun taho tareda iyalin taka ce...?”

Tambayan da Daddy yai masa saida ya sanya k’irjinsa bugawa sannan sosai yaji nauyin Daddyn dan har cikin ransa ji yake abinda yake yima Safeenah bai kyautawa. Iyayenta sunada mutunci musamman Daddy. Gaba d’aya sai yaji bai kyauta ba. K’ok’arin saita kansa ya d’anyi yana mai girgiza kai “No Daddy.. Fitowar gaggawa nayi shiyasa na taho ni kad’ai..”

Daddy yace “Allah sarki.. Toh yayi kyau Allah dai ya taimaka yai maka jagora..”

Muazzma ya amsa da “Ameen Daddy.”

“Ya ka baro mutan gidan Inne da ‘yanuwanka.. Ya jikin Mamyn naka kuma.. Ana samun progress..?”

“Kowa lafiya Daddy.. Jikin Mamy Alhamdulillah da sauk’i sosai.. Mun sameku kafiya..”

Daddy yace “Toh Alhamdulillahi... Lafiya lou an gode Allah.. Gashi ka shigo ka samu ina duba takardu..”

Mu’azzam ya soma k’ok’arin mik’ewa yana fad’in “Barin Barka kayi aikinka Daddy..”

Daddy yace “No zauna abinka.. dama akwai maganar da nake so muyi amma yanzu naga dare yayi so zamuyi maganar gobe idan Allah ya kaimu.. And akwai yanda nake so muje dani dakai..”

Mu’azzam ya jinjina kai cikeda risinawa yace “Okay Daddy Allah ya kaimu.. Mommy ta kwanta koh..”

Daddy yace “Eh kasan Mamar taku kaman kasa ce nan da nan tayi bacci..” Ya k’arashe cikeda barkwanci irin tasu ta manya kafin Muazzma ya mik’e yana d’an Murmusawa. Saida safe yaima Daddyn kafin ya fice ya nufi side d’insa. Saidai tinda ya shiga d’akin tinanin yarinyar ya addabesa. K’ok’arin kauda tinanin yai kafin ya fad’a shower.

SameenaAleeyou📚

*GIDAN ARO*

*25*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

A hankali take k’ok’arin bud’e idanunta da suka mata nauyi, tas ta Ware idanun nata tana duban yanda take. Wani had’add’en d’aki ne da ya tsaru iyaka tsaruwa. Tsoro ya kuma bayyana saman fuskarta, itadai tasan a wani d’aki mai kaman store ya barta wanda Tim wani haushin kare dataji bata kuma sanin meke wakana ba. Zumbur Sadiya ta mik’e tana duban d’akin.. Kallo guda zakai ma d’akin ka fahimci cewa d’akin Amarya ce. Ta saka hannayenta biyu tana kuma mutsuke idanunta ganinta da tai kwance saman gado har an rufeta da duvet. Kalle kalle ta soma tana kuma Shafa gadon dan dai ta tabbatar da gaske ne.. Toh ya akai tabar wancan d’akin yaushe aka kawota nan..? Tambayoyi ne da batada amsoshin su.. Gefen bedside ta hango hoton wata mata kyakkyawa an aje cikin k’aramar frame. Ta matso tana duban Matar.. Gani tai kaman ta tab’a ganin fuskar matar amma saidai sabida heavy makeup dake fuskar matar bata iya ganeta ba.. Bata kuma gane ina tasanta ba. Hasken rana data hango ya tabbatar mata gari ya waye. Tsalle tai ta diro daga saman gadon tana kuma juye juye zuciyarta naci gaba da yankewa “A ina nake..?!” Ta tambayi kanta cikeda firgici.
Chapter 43 · 0% Book details