← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 175

Sashe 108

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokaci guda tasa kai ta fice, bata samu sunyi sallama da Ajidde ba dan fitar sassafe sukai, harda Musaddiq suka komo hakan yasa Inne bata sama mata ‘yar rakiyar ba dan Musaddiq yace yana so yaje ya duba gida shima.. Alhali kaw zaman nasa ne a garin sam baya masa dad’i dan tinda ya dawo ya kula Ajidde ta janye masa jiki sann Ta daina duk wad’ann barkwancin nata da yake sanyasa nishad’i a zaman sa a garin.. Sam sai yaji garin bata masa dad’i gwara ya koma ya taka ma Safeenah birki kan haukar da take dan sosai abin da Ta tassama Yi wa matar Mu’azzam ya d’aga masa hankali.

**
Yamma lis suka iso birnin tarayya. Sadiya data sha baccinta a mota, ta bud’e idanu ta gansu a cikin Abuja. Adnan da Musaddiq Sai labarinsu suke, tana ganin an d’auki hanyar foundation zuciyarta ya cika da annashuwa, kenan wajen Su Umma za’a fara kaita. Ko ya akai Adnan yai tunanin hakan bata sani ba.. zuciyarta ya bata amsa da fad’in k’ila Mu’azzam ne yace su fara kaita nan tinda itakam baccinta tasha a mota.

Suna isowa Farin ciki ya cika Sadiya. A farfajiyan apartment d’in ta hangi su Habeeb sai wasa suke.. Suna ida parking kaw Habeeb da Ashir sukai tsaye suna duban motar. Aiko suna ganin Sadiya ta fito ciki suka nufeta a guje suna kiran sunanta suna mata oyoyo.. Musaddiq yai tsaye yana dubansu murmushi saman fuskarsa. Nan Aunty larai da ta jiyo hayaniyarsu ta fito itama.. Aka soma Sabon oyoyo. Musaddiq ya k’araso ya gaida Aunty Larai tana masa tsiyan shine ya girma ya zank’ale haka.. Sai murmushi yake yana Shafa kai.. Aunty Larai ta shigar dashi ta masa iso Suka gaisa da Umman Sadiya. Adnan yaita sauk’e masu tsaraba wanda takeda tabbacin Mu’azzam ne ya umarcesa yai hakan dan lokacin da suka tsaya a Jos yin sallah taga sanda Adnan d’in ke sayen tsaraban.

Aunty Larai sukai masu godiya kafin sukai sallama Sadiyar ma na masu godiya da fatan sauk’a lafia.

Aunty Larai ta kamo hannunta tana tsareta da idanu “Iyye irin wann haske da shek’i da kike.. Aah lallai mission yayi kyau. Tubarkallah Masha Allah.”

Sadiya ta murmusa cikeda kunya tana rufe fuskarta da mayafi.

Sosai taji dad’in ganin ahalinta cikin k’oshin lafiya da kwanciyar hankali. Idan ka gansu duk sun canza ba kaman lokacin da suke cikin tashin hankali ba, Sai godiyar Allah.

Tana ida sallar magrib Aunty Larai ta tarbeta da wasu had’e had’en ta tasa ta gaba sai ta cinye ta shanye. Sadiya kaman zatai kuka babu yanda ta iya haka Aunty Larai ta tasa gaba da had’en had’en nan. Harda wasu turaruka na musamman ta had’a mata da shike gidanta zata tafi.

Kafin isha Aunty Larai ta sakata ta tsala wanka ta shirya tsaf cikin doguwar riga bak’ar abaya mai kyaun gaske wanda ya kuma bayyana kyaun fatarta. Sai zuba k’amshi take.

Ta tada sallar isha kenan ta sinkayo muryarsa da Umma suna gaisawa daga parlor.

SameenaAleeyou📚

*GIDAN ARO*

*54*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Habeeb ya k’araso sukai handshake ya zaunar dashi gefensa saman kujeran kafin yace “Hello little Cop.. Kaje lesson d’in kuwa..? Fad’a mun mai aka koya maku..” Yai maganar yana duban Habeeb d’in dake wasa da wani silver metal shatin kwabo.

Habeeb ya girgiza kai yace “Nace masu ni Cop ne.. Chasing bad guys nake so na koya..”

Ya murmusa yana duban Metal d’in wanda ya mugun d’aukan hankalinsa. Take yaji zuciyarsa yai wani irin yankewa sanda ya soma tuna Ina yasan irin wann metal d’in.. Take yarintarsa ya soma dawo masa yana wasa da irin wann metal yana mannasa da magnet. Karb’an metal d’in yai yana juyawa, exactly babu abinda ya raba da irin wanda yake wasa dashi yana yaro.

Ya dubi Habeeb yace “Where did you get this from.?”

Habeeb dake ‘yan tsalle tsallensa yace “I don’t know.. Kawai nima na samu ne a gidanmu kafin mu dawo wann gidan..”

Mu’azzam yaci gaba da juya metal d’in.. Sai wann lokacin yake karanta abun da aka rubuta tsakiyan shatin kwabon cikin yanayin rubutu mai tsananin k’ank’anta wanda sai ka saka idanunka sosai kafin ka iya karantawa _Balck African Team_. Shine abin da aka rubuta tsakiyar metal d’in cikin rubutu mai style. Zuciyarsa ya yanke sanda ya karanta rubutun. Ya nanata a fili Black African Team...!” Ya nanata a hankali yana mai kuma juya coin d’in cikin hannunsa.

Hayaniyar Habeeb dake kallon cartoon d’in spider man yana kwaikwayonsa shi ya dawo da hankalin Mu’azzam ya d’an dubesa yace “Hey little Cop.. Can you borrow me this.” Ya k’arashe yana nuna masa Coin d’in.

“Sure Mr Cop. Na baka kyauta idan kana so.”

Murmusawa yai kad’an kafin yace “Kar ka damu aro zaka bani.. Idan na gama amfani dashi zan dawo maka dashi kaji.”

Habeeb ya jinjina kansa daidai lokacin da Aunty Larai ta kirasa ciki.

Mu’azzam yaci gaba da juya coin d’in yana nanata word d’in dake jiki wanda a yarintarsa bai kula da wann word d’in ba sai yanzu.. Balck African Team” Ya kuma fad’i yana juya coin d’in.

K’amshinta ne ya soma masa sallama, Cak ya tsaya da abinda yake ya soma janye idanuns daga duban coin d’in.

Tin daga k’asa ya soma dubanta har zuwa kyakkyawan fuskarta da yai kewa.

Ya mik’e yana mai jefa coin d’in cikin aljihunsa. A hankali yake takowa har zuwa kusanta.

Suka jima a haka suna duban juna cikeda shauk’i. Hannayensa ya d’ago duka biyu ya tallafi fuskarta, kafin ya matso da nasa fuskar kusan nata. Ya manne goshinsu waje guda su duka biyun idanunsu a lumshe “I’ve missed you.. I’ve missed you so much Beautiful.!” Ya fad’i cikin murya mai tsananin sanyi.

Bata iya furta komai ba Sai wane irin sanyi da illahirin jikinta yai. Tana jin sanda ya rungumeta cikin jikinsa. Ta lumshe idanunta a hankali tana shak’an k’amshinsa da tai kewa.

Hannunta ya kamo suka zauna saman kujera ya tsareta da idanu kaman ranan ya soma ganinta.

Ta d’an muskuta tace “Ina yini..”

Bai amsa ba saima ci gaba da kallonta da yake harda yin tagumi still idanunsa akanta. Gaba d’aya sai ta jita a tsarge. Ta sadda kanta kad’an ko zai daina duban nata ya amsa mata gaisuwarta amma inaa kaman ma ba dashi take ba.

D’agowa Ta kumayi suka dubi juna still bai daina kallonta ba bai kuma canza position d’in taguminsa ba.

Ta d’an tsime kad’an tace “What.. Why are you staring at me like that.. Wait is there something on my face..?” Ta shiga shafe fuskarta tana turo baki gaba.

Jinjina mata kai yai yace “Umhum.”

Taci gaba da Shafa Fuskar nata tana neman mai yake kallo tana yi tana fad’in “Where ina yake..?”

“There.” Ya bata amsa yana d’aga mata gira da idanu alamun yana mata nuni da abinda ke bisa fuskar nata.

Ta marairaice fuska tana fad’in “Inspector Nidai banji komai ba.”

“Come here.. Zo na nuna miki..” Ya k’arashe yana janyota kusansa kad’an.

Dik ta sakankance zai cire mata abinda ke fuskar nata ne saiji tai ya manne bakinsa da nata. Daskarewa tai tanajin yanda yake sarrafa harshenta cikin bakinsa. Tai ta maza ganin yana neman fice mata daga giya ta turasa da iyaka k’arfinta.

Tallafo fuskarta yai yana dubanta da idanunsa da tuni sun k’ank’ance “Didn’t you miss me..?” Ya tambaya cikin kasaliyar murya.

Kaman zata fashe masa da kuka take fad’in “Of course I did miss you.. But.. Ba irin wann kewar ba.. And besides baka San yanda muke bane.. What if..What if..”

Bai bari Takai aya ba ya katse Ta da fad’in “Fine.. Tashi mu tafi gidanmu.. Ince kin masu sallama..”

Ta mak’e masa kafad’a tace “Ni dai dan Allah ka barni na Kwana..”

D’an shan mur yai had’ida matsawa baya kad’an “Shiga ki masu sallama ki fito mu tafi..” Ya fad’i yana duba writs watching d’insa ba tareda ya dubeta ba fuskar nan babu walwala.

Ta kuma yin narai narai da idanu tana dubansa yanda ya canza lokaci guda. Tasan tinda ya fad’i haka bazai canza ba. Jiki babu laka Ta mik’e ta nufi ciki.

Daga yanda Aunty Larai ta ganta tasan akwai wani abu “Ya na ganki haka.. Har zaku wuce ne..?”

Sadiya ta d’an turo baki gaba kad’an tace “Aunty Cewa yai Wai bazan kwana ba.”

Aunty Larai ta saki baki had’ida kame hab’a tace “Au Wai dama saida kika ce masa kwana kike son yi.. Ai ban zanci zaki fad’i haka ba da tun kafin ya zauna na koraki Kun tafi.. Au ashe da yace a fara kawoki nan bai maki ba saida kikace masa kwana kike son yi.. Toh bazaki kwanan ba.. Ko ya k’yaleki ma mu dai kam bamuda masauk’inki a nan.. Kar ma kiyi Umma taji wann batun dan Kinsan Sauran. Ungo amshi nan..” Ta k’arashe tana bata sauran had’e had’en kayan gyaran da ta mata.. Saura idan kinje kar kisha kiyi flushing nasu a toilet nida ke ne.. Natural Herbs ne duka a nan masu kyau ga lafiyar d’anadam da honey ake sha kaman tea zaki had’a maku instead of sugar ki zuba honey har shima idan yana so zai sha kinji koh.. Ta d’an turo bakinta gaba kad’an tana jinjina kai. Tana iya jiyo k’amshin cloves daga cikin jakan da yake da tabbacin dangin itace ne masu inganci da kuma kyau ga lafiya.

Jiki a sanyaye ta isa taima Umma sallama ta fito ta taddashi. Sanda ta iso waya ne manne kunnensa yana amsa kira. Yana mik’ewa taga bayan navy blue polo d’in dake jikinsa an rubuta FCID da manyan haruffa.. Ko ba’a ce ba kasan rigar Office ne. Ta d’an tab’e baki kad’an a ranta tace k’ila daga Office ko gida baije ba kenan.. Watak’la ya tsaya wani wajen ne.

Har suka shige Mota waya yake, ita har mamaki take shin kunnensa bai gajiya ne. Har suka kusan isa gida waya yake wanda zata ce bata fahimci komai ba dan aikinsa ya shafa.. Yo itakam ma window take ta duba abinta tana kallon tangama tangaman titunan birnin tarayya da aka k’awatasu da security lights ta ko Ina.
Chapter 108 · 0% Book details