← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 139 OF 175

Sashe 139

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A can gidan Daddy kaw a babban parlorn Daddy suka hallara bayan da suka tabbata Inne ta shiga ta kwanta dan bazasuyi komai a gabanta ba gudun kar hankalinta ya tashi da abubuwan da zataji. Daddy Uncle Salman Mommy sai ko Mu’azzam.

Uncle Salman ya girgiza kai a karo na biyu yana duban D’anuwansa Marwan wanda shi ne ya gayyatosa gidan nasa “Marwan Wai meke faruwa ne.. Ka kirani kace na taho cikin gaggawa zamu tattauna matsala da ya shafi companies d’inmu.. Mene kuma nake gani haka.. Idan Mu’azzam nada shares a company naji zai iya tsayuwa a nan a tattauna dashi toh amma mai matarka take a nan..?”

Daddy yai gyaran murya kad’an yace “Munada buk’atansu a nan ne Salman shiyasa ka gansu..” Ya d’an gyara zamansa kafin yaci gaba da fad’in “Salman wace takarda ce kake nema wajena wanda har kukayi amfani da Hajara kaida matarka dan kun cimma burinku na mallakar wann takardan.?”

Dummm! K’irjin Uncle Salman ya bada wann sautin. Bakinsa ya soma rawa yana furta “Ta..Takarda kuma.. Wace irin takarda..?”

“Yarjejeniyar da kace kinyi kaida mahaifina cewa ya mallaka maka Kaso na dukiyarsa.. Shin Ka tuna Uncle..?” Mu’azzam ya k’arashe yana duban Uncle Salman cikin ido.

Uncle Salman ya shiga girgiza kai yana furta “Ban.. Ban fahimta.. Wace takarda kenan..?”

Mommy tai caraf tace “K’warai kuwa ka sani Salman domin kuwa Shemau ta sanar dani cewa dan na samo maku wann takardan daga hannun Marwan shiyasa ka turo Shemau ta shiga jikina.. A cewarka Marwan shi ya d’auke wann document d’in domin ya cinye dukiyar D’anuwanku Abubakar.. Tabbas anyi haka kuma kaima kasan anyi haka.. Ni bansan da wata takarda ba na yarjejeniya har saida Shemau ta sanar dani cewa wann takardan kuke farauta hannun Marwan kaida matarka Shemau..” Ta k’arashe cikeda k’warin gwiwa irinta mai gaskiya.

Daddy ya girgiza kai yana duban Uncle Salman da gaba d’aya ya daburce kafin yace “Salman wace takarda ne wann..? Sannan Maiyasa kace takardan na hannuna bayan ni bansan da wata takarda ba..?”

Mu’azzam ya k’araso gaban Uncle Salman sosai wanda gaba d’aya gumi ne ke karyo masa dukda sanyin AC dake busawa cikin parlorn. Lokaci guda yake furta “Sabida ka cimma burinka na mallakan takardan yasa kukai tarayya kaida matarka harma da Mommy kuka d’auko wa mahaifiyata mai magani na bogi..? Sabida ka mallaki wann dukiyar ne da kake hari Uncle..?” Yaci gaba da jinjina kai yana furta “Akan dukiyar ne kai ruining ahalina..? Akan dukiyar ne ka kashe mahaifina..? Akan dukiyar ne ka jefa mahaifiyata cikin halinda ta tsinci kanta ciki..?! Akan dukiyar ne kasa aka kashe ‘Yaruwata..?! Answer me Uncle Salman.! Ka amsa min..!” Cikin wane irin yanayi da basu tab’a ganinsa ciki ba yake maganar gumi Sai karyowa yake daga tsakiyar sumarsa zuwa goshinsa.

Yayinda Uncle Salman ya saki baki yana duban D’an D’anuwan nasa da tsananin mamaki yana mai girgiza kai daga nan yanda yake zaune.

A fusace Uncle Salman ya mik’e yayo kan Mu’azzam d’in kaman zai shak’o wuyarsa yana furta “Kai har ka isa ka jefeni da irin wann k’azafi..? Kai har ka isa kace ni na kashe D’anuwana kuma na tarwatsa masa ahali.. Bakai wann girman ba Mu’azzam kuma k’aryar uniform d’inka na D’ansanda kake.!”

Daga shi har Mu’azzam d’in banda sakin huci basa komai, Daddy ya taso a fujajan ya janye Uncle Salman wanda bai daina sakin huci yana aikawa Mu’azzam mugun kallo ba.

Mommy kaw sai dukan hannunta take a hankali, cikin zuciyarta tana furta ‘Yauwa ku daku.. Ku bawa hammata iska wanda yafi k’arfin wani ya kashe.!’

Daddy ya dubi Uncle Salman cikin b’acin rai yana furta “Kana cikin hankalinka Salman, ka nufosa a haka dukansa zakayi ne ko me..?”

Mommy tai caraf tace “Shak’esa zai k’ilan kaman yanda ya kashe mahaifinsa da ‘Yaruwarsa.. Ni nayi d’an danasanin bin turban da Shemau taso d’aurani akai, Allah ya gani ba halina bane Shemau ce tazo da wann shawarin yace mijinta ya tsara mata yanda za’ayi..” Sai kuma Ta fashe da kuka tana fad’in “Lafiya lou muke zaune da Nuratu suka kaw wann gurb’ataccen shawari dan kawai a kawar da Baiwar Allah su samu su cimma burinsu.. Kaico na ni Hajara amfani dani sukai da raunin zuciya irinta d’iya mace.!”

Daddy ya darara mata tsawa da fad’in “Kimin shiru Hajara maslaha ake nema a nan ba tashin hankali ba.. Kema ban gama dake ba..!”

Daddy cikin b’acin rai yaci gaba da duban Uncle Salman yana fad’in “Ka daina wann borin kunyar Salman ka sanar dani wace takarda ce kake so Hajara ta samo maka daga wajena..?!”

Cikin d’aga murya Uncle Salman yace “Takarda BAT..!”

Cikin tsananin shock Mu’azzam ya furta “BAT..!”

Uncle Salman yaci gaba da jinjina kai yana furta “Yes takardan yarjejeniya.. Yarjejeniyar da Yayana Abubakar ya saka hannu cewa ya mallaka min dukiyarsa.. Dukiyar tawa ce, magadansa basu da kaso ciki domin kuwa D’anuwana shi da kansa ya bani.. Kuma inada tabbacin Kaine ka b’oye wann takardan Marwan.. Ka fad’a mun nayi laifi don na nemi hakki na wanda nasan duk runtsi bazaka bani ba.. Watak’ila kaima ka azurta kanka dashi kokuma dai ka ajiye wa masoyiyarka da D’anta har ta samu lafiya ka dank’a masu dukiyar da tuni D’anuwana ya bani a rubuce.!”

Girgiza kai kurum Daddy yake yana duban Uncle Salman cikeda tsananin mamaki. Yayinda kan Mu’azzam ya soma juyawa, kalman BAT da uncle Salman ya fad’I shine kawai ke Yawo a kwanyarsa da dodon kunnuwarsa. Take ya tuna wann Syndicate d’in na Black African Team, wanda ya samu coin d’aya gidansu Sadiya d’aya kuma cikin stuff d’in mahaifinsa.. Yaji jiri na neman kaisa k’asa.. Meke faruwa..? Meke shirin faruwa dashi. Muryar Uncle Salman ya kuma sinkayo yana duban Daddy yana ci gaba da fad’in “Dik son da nake na mallaki dukiyar nan bazan tab’a kashe D’anuwana ba balle na tarwatsa ahalinsa.. Amma kai Marwan Kaine kake da babban dalilin kashe Hamma..!”

Cikin zafin zuciya Daddy ke furta “Ya isheka haka Salman..! Koda wasa kar ka juya wani abu a nan wajen.!”

Uncle Salman ma cikin zafin rai yake ci gaba da furta “K’warai kuwa Marwan Kaine kake da babban dalilin da zaisa ka a kashe Hamma idan ma kashesa d’in akai.. Domin kuwa Hamma ya aure masoyiyarka wacce daidai da rana guda baka tab’a cire soayyarta cikin zuciyarka ba.. Kayi k’ok’arin b’oye soyayyar Nuratu wa mutane amma ni naji komai a ranar da ka dawo daga makaranta..! Ranan da ka tadda ana d’aura wa masoyiyarka Nuratu aure da D’anuwanka Abubakar..! Da kunnuwana naji kana fad’awa Hamma cewa ko ba dad’e ko ba jima Nuratu zata baro gidansa ta dawo Naka domin kuwa ita d’in taka ce sann zata rayu ne a gidan Hamma tamkar dai tana a GIDAN ARO..!”

“Salmaaaan..!” Daddy ya daka masa tsawa da fad’in haka hawaye na gangaro masa yayinda Mu’azzam ya tsaya Cak yana jin kaman zuciyarsa dake cikin k’irjinsa Ta daina bugawa na wasu dak’ik’ai..

SameenaAleeyou📚

*GIDAN ARO*

*71*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Uncle Salman yaci gaba da jinjina kai yana takowa gaban Daddy “So tell me dear Brother.. Between the two of us waye yakeda motive na kashe Hamma.. D’an uwansa da yake son ya mallaki dukiyarsa da position d’insa kokuwa D’anuwansa da yake tsananin son kasancewa da matarsa.. Ka fad’a mun wanene yake da babban dalilin kashesa.!”

“Ya isheka..! Ya isheka haka Salman.!” Daddy ya fad’i cikin tsananin daka tsawa hawaye na gangaro masa. Yayinda Mu’azzam ya kasa gasgata abindake faruwa kan idanunsa.

Uncle Salman ya tako gaban Mu’azzam dake tsaye wajen cikin wane irin yanayi da ko ba’a ce zaka fahimci kaman gangar jikinsa ne ke dashe wajen, kai kace ruhinsa bai tare dashi.

Uncle Salman yaci gaba da nuna Daddy yana fad’in “Your Mother is the love of his life.. He loved her and never stopped loving her... Yayi furuncin rabata da mahaifinka ko ta halin k’ak’a.. A ranan da mukai sa’insa da mahaifinka he was at the company, yayi amfani da wann damar bayan mun gama sa’insa da Hamma sai ya rufesa a cold room dan ya cimma burinsa na mallakar masoyiyarsa Nuratu.!”

Jiri ne yake neman kai Mu’azzam k’asa, ya soma kame kansa da kunnuwarsa yana girgiza kai yake furta “That’s enough... That’s enough please..!” Yana maganar ne tamkar zai kifa k’asa sabida tsananin tashin hankali.
Chapter 139 · 0% Book details