← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 135 OF 175

Sashe 135

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yanzu kam Daddy ya kuma shiga duhu “Mu’azzam ban San mai kake fad’a ba..”

A hankali Mu’azzam ke jinjina kai yana duban Daddy sai kuma yace “Daddy no more secrets please.. Ka sanar dani abinda ka sani gameda wann takardan..”

Daddy ya girgiza kai yace “Mai Hajara ta sanar dakai Mu’azzam.. Ni ban gane mai kake fad’i ba fah..”

“Daddy ka sanar dani gaskiya dan Allah.. Na gaji da wann b’oye b’oyen.. Shin wann takardan shine dalilin da yasa bama shan inuwa guda nida Uncle Salman.. Shin Uncle Salman dukiyar mahaifina da position d’insa a company yake farauta.. Just answer me Daddy..!”

Daga bayansu suka sinkayo muryar Musaddiq yana fad’in “Yes it is true Mu’azzam..!” Yana maganar yana huci dan ya jiyo muryar mahaifiyarsa daga cikin store tana neman d’auki yanda Mu’azzam ya kulleta.

Daddy da Mu’azzam suka juyo suna duban Muassadiq dake ci gaba da takowa kusansu. Lokaci guda yaci gaba da jinina kai yana hawaye “Daddy tell him.. Ka sanar dashi tattaunawar da na sinkaya kunayi kaida Uncle Salman.. Tattaunawar da ka hana na sanar da Mu’azzam..!”

Bugun Zuciyar Mu’azzam ya k’aru sanda ya kaikaito yana duban Daddy dake hawaye.

Musaddiq wanda shima hawaye ne ya wanke masa fuskar ci gaba da jinina kai yai yana fad’in “It is not only Mommy.. Kaima ka b’oye hakan wa Mu’azzam.”

Cikin zuban hawaye Daddy ke furta “I didn’t say anything sabida banga dalilin da zaisa na sanar da Mu’azzam wani abu ba.. Nayi shiru ne To protect our Family.. Sannan banga amfanin sanar da Mu’azzam wani abu ba..”

K’arasowa gaban Daddy sosai Mu’azzam yai yana dubansa yake fad’in “Daddy mai Musaddiq yake fad’i.. Menene abinda ka gaza sanar dani..?”

Musaddiq ya tari zancen da fad’in “Mafarkin Uncle d’inka Salman shine mahaifinka ya mutu domin ya d’ale muk’aminsa a company sann ya mallaki komai nasa... A ranar da Dad d’inka zai bar duniya Uncle Salman da Dad d’inka sunyi sa’insa kuma Uncle Salman ya sanar dashi sai ya d’ale kujeransa by all means..” Musaddiq yaci gaba da jinjina kai yana hawaye “That same day, Your Dad died in a cold room which’s somehow suspicious.. A wann ranan aka tsinci gawarsa ya daskare a d’akin k’ank’ara bayan sun gama wann sa’insan da mahaifinka.. Daddy ya b’oye maka wann labarin ne don kar ya tarwatsa zuciyarka..! Ya b’oye maka hakan ne dan kar ka binciki D’anuwansa Salman sanin cewa kai d’in Jami’in bincike ne.. Ya b’oye maka hakan ne to protect our family..!” Ya k’arashe maganar yana zira hannu cikin aljihun Mu’azzam d’in ya zaro keys d’in store d’in. Murya a hankali yaci gaba da furta “If there’s someone you should investigate here.. that person should be your Uncle Salman, and not my Mother..!” Yana ida fad’in haka yasa kai ya shige.

Mu’azzam dake ganin duniyar na juya masa da k’yar ya iya zama saman kujeran dake aje gefensa yana jin kaman gwiwoyinsa sun kwab’e. Maganganun Musaddiq harma da na Mommy na zarya a dodon kunnuwansa.

Jiki a matuk’ar sanyaye Daddy ya k’araso gaban Mu’azzam d’in, kujeran dake gefe dashi ya janyo kafin ya zauna had’ida dafa kafad’an Mu’azzam d’in, suka d’an d’ibi lokaci a haka kafin Daddy ya soma fad’in “Mu’azzam, my son.. I believe your Uncle didn’t kill your father.. I believe Salman bazai tab’a aikata abu makamancin haka ba.. Salman zai iya zama mai son abin duniya amma bazata kaisa har haka ba.. Bazai je da nisa har haka ba.. Nasan kaima zaka iya yarda da hakan. Right..!” Ya k’arashe hawaye guda na gangaro masa.

Har Mu’azzam bai iya d’agowa ya dubi Daddy ba.

“Why did you keep this from me..?” Mu’azzam ya tambaya murya a hankali.

Daddy ya girgiza kai yace “Menene amfanin sanar dakai sa’insan da ‘Yanuwana sukai.. Menene amfanin tarwatsa kan ahali.. Sanar dakai Baida wani amfani idan har hakan na nufin tarwatsewar ahalinmu ne..”

Wann karon hawaye ne ke gangarowa daga idanun Mu’azzam sanda ya d’ago yana duban Daddy cikin wane irin yanayi “Koda hakan yana nufin Uncle Salman shi ya kulle mahaifina a cold room.. Koda hakan yana nufin Uncle Salman shi ne ya kashe mahaifina..? Koda hakan yana nufin Uncle Salman shi ya causing accident d’in da Mamy ta tsinci kanta ciki dan ya tabbata ya kauda dik wani Magajin mahaifina.. Koda hakan yana nufin Uncle Salman shi ya kashe Ikram dan ya tabbatar ya mallaki dukiyar mahaifina.. Daddy koda hakan yana nufin Uncle Salman shine mutumin da naketa nema naketa bincike akansa.. Answer me Daddy..!” Ya k’arashe cikin wane irin yanayi kuka na kufce masa..”

Girgiza kai Daddy yake sanda suka mik’e tsaye dukansu biyun.

“No Mu’azzam.. D’an uwana bazai tab’a zama mugu irin haka ba.” Yana maganar yana kuka sosai hannunsa guda dafe da fuskarsa. Baya fata hakan ta tabbata.

Mu’azzam yaci gaba da jinjina kai yana duban Daddy, cikin wane irin raunanniyar murya yake furta “Who am I investigating Daddy.. My Uncle, or a criminal.?” Yanda Yai maganar dole ya baka tausayi. Cikin sanyi jiki yaji k’afafunsa na k’ok’arin gaza d’aukansa. Duk’awa yai a wajen saman gwiwoyinsa had’ida rufe fuskarsa da Ta koma jazir da duka tafukan hannayensa.

Daddy ma ya duk’a a wajen, shikam kuka yake sosai sanda ya duk’a a wajen.

A can store kuwa Musaddiq na bud’ewa Mommy Ta k’araso ta rungumesa tana kuka.

“Musaddiq you need to help your Mom.. Zaka sake taimakona kaman yanda ka taimakeni a baya..!”

Cikin zafin nama ya b’amb’are hannun Mommy daga rik’on da tai masa “You killed Safeena’s child Mommy.. You killed your own grandson.. Ta yaya zaki aikata abu makamancin haka.. Mommy ko kinsan kin kashe rayuwar Safeenah da abinda kika aikata..?!”

Cikin zuban hawaye take girgiza masa kai.

Cikin kuka take furta “Mommy ke ‘yar ta’adda ce shin Kinsan da hakan.. I thought bayan asirin Aunty Shemau ya tonu zaki nastu ki tuba.. But what did you do.. Kin kashe D’an Safeenah sann kin haukatar da Safeenar.. Mommy wace irin uwa ce zatama d’iyarta haka..?!”

Cikin zuban hawaye Mommy ke girgiza kai “Ka yafe mun Musaddiq burin d’aukan fansa ne.”

Girgiza kai yake shima yana fad’in “Kin tafi da nisa wann karon Mommy.. Ya kamata ki biya abinda kika aikata..”

Daga haka Sa kai yai zai fice, Mommy na kuka na k’ok’arin dakatar dashi. Ganin bai tsaya ba ya sanya Mommy fad’in “Bani kad’ai bace ‘Yarta’adda a nan Musaddiq.. Harda kai..!”

Cak Musaddiq ya tsaya zuciyarsa na bugawa.

Mommy taci gaba da jinina kai tana fad’in “Ko ka mance cewa kai ne kayi ma Ikram Fyad’e..!”

Mommy taci gaba da jinjina kai tana fad’in “You raped Ikram Musaddiq.. Kaine ka aikatawa k’anwar Mu’azzam fyad’e.. Ikram died because of you Musaddiq.. You are a criminal just like your Mother.!”

Taci gaba da takowa kusansa a hankali tana furta “Ko ka mance Ni ce nan nayi destroying evidence da ka bari a wajen, hularka da ya fad’i a wajen.. Ka tuna Musaddiq..? Wann hular dai taka Wanda ke d’auke da wasu harrufa..” Ta d’an sassauta murya kafin taci gaba da fad’in “Meye ma haruffan..? Wait barin tuna..” Ta d’anyi fasali kaman mai nazari sai kuma tace “Oh! Yauwa Na tuna..” Ta jinjina kai tana sakin murmushi a hankali kafin taci gaba da furta “B.A.T.. Wad’ann haruffan ne rubuce a gaban hular.. Kai ka aikatawa k’anwar Mu’azzam fyad’e Musaddiq.. Kai d’an ta’Adda ne just like me.. Kaman dai yanda na zamto silar mutuwar D’an Safeenah haka kaima ka zamto silan mutuwar Ikram Yarinyar da bata nuna maka komai ba face zallan k’auna..! Kai d’antadda ne Musaddiq..!” Ta k’arashe tana bud’e murya.

Duk’awa Musaddiq yai wajen yana toshe kunnuwarsa da k’arfin gaske kuka mai zafi na kufce masa.

SameenaAleeyou📚

*GIDAN ARO*

*69*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Cikin kuka yana nan duk’e wajen yaci gaba da girgiza kansa, har lokacin kunnuwansa a toshe suke da hannayensa “That’s enough.. That’s enough Mommy.. Kiyi shiru haka nan..!” Ya k’arashe cikin tsananin kuka.

Mommy taci gaba da jinjina kai “Kai D’anta’adda ne Musaddiq.. Idan Mu’azzam yaji abinda ka aikatama ‘Yaruwarsa zai tsaneka tsana na har abada kuma Sai ya rufe ka shafe shekaru da dama gidan yari..!”

Cikin kuka Musaddiq ya d’ago yana dubanta lokaci guda yake furta “Do you think I’m afraid of going to jail Mommy..? Kina tunanin Ina tsoron na biya abinda na aikata ne..?” Ya girgiza kai yana mai ci gaba da hawaye “No Mommy.. Bana tsoron na tafi gidan yari dan na biya abinda na aikata.. Abinda nake tsoro d’aya ne shine rasa Mu’azzam.. Rasa D’anuwana Mommy.. Zan rasa Mu’azzam bayan na rasa Ikram.. I’m nothing but a monster.. I feel like I’m the worst person in this world Mommy.. Ni azzalumi ne wanda bai cancanci rayuwa ba..!” Yana maganar yana dukan kansa da hannunsa guda had’ida duk’awa nan wajen.

Mommy tai saurin k’arasowa ta rungumesa tana fad’in “Abinda ya riga ya faru ya faru Musaddiq.. We can’t erase the past saidai muyi abinda ya dace kawai a gaba.. And abinda ya dace shine kayi shiru da bakinka and do not say a word to anyone and especially to Mu’azzam, idan ba haka ba zaka tarwatsa Mu’azzam ne bayan abinda Uncle Salman ya aikata wa Mahaifinsa idan yaji kai ka aikata ma Ikram Fyad’e heart attack ne zai ajalin Mu’azzam and na tabbata baka so ka zama silan mutuwar Mu’azzam, right..!” Ta k’arashe cikin kwantar da murya tana goge ma Musaddiq d’in hawaye.
Chapter 135 · 0% Book details