← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 160 OF 175

Sashe 160

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mommy ta murmusa kafin tace “Lallai baka abu da lissafi.. Ka mance Ya’yanta Police Officer ne a detective for that matter.. Kasheta har cikin gida yana nufin tonuwar asirina ne domin kuwa duk wani trace sai wann shegen yaron Mu’azzam yabi ya gane.. I’ve already come up with an idea.. Abun shine na saka yarinyar Ta bibiya mun Safeenah kasan yarinyar shegiyar bin k’wak’waf ne da ita.. Zan turo maka lambar Safeenah, ka bawa wann yaron Sagir ya mata proposing business. Abun yayi kaman dai zai k’ulla kasuwanci da Companynsu, kasan Safeenah itace head of marketing department a companyn nasu dake nan birnin tarayya.”

Danger ya katseta da fad’in “Ba satin sama ake d’aura auren Safeenah ba.. Ta yaya zata amince da wani business proposal.”

Mommy Ta murmusa tace “Baka San Safeenah da San neman suna ba.. Nasanta da son birge mutane biyun nan mahaifinta da Mu’azzam.. Na tabbata idan kuka kira mata mahaukatan kud’ad’e kukace zakuyi investing ku saya products d’insu da gudu zata amsa tayin ko dan Ta birge Mahaifinta ta kuma d’aga darajarki Kampaninsu. Idan Sagir ya turo mata adireshi Ikram itace zata karance kuma ita zata Zo wann location d’in.. Sai mu gama da ita once and for all..”

Danger ya jinina kai yace “An gama mai BAT.. Ina yarana da basusan uncle d’insu ba.. Kin hana na masu introducing kaina ne.. Da yanzu Sun sanni na sansu..”

Murmushi Mommy tai kafin tace “In due time zasu sanka bayan mun gama da duk wanda suka sha gabanmu.. Yanzu kasan yanda za’ai aikin nan yayi kyau.. Bana so a sami wani mishkila..”

Danger ya jinina kai yace “Ban tab’a failing d’inki ba kin sani.. Sann abubuwan da kika mun a rayuwa babu abinda bazan miki ba.. Ki saka a ranki anyi an gama..”

Ta murmusa kafin tace “Shikenan bara na turo maka lambar Safeenah.”

Suna ida wayar ta tura masa lambar Safeenah. Nan kuwa Sagir da Danger sukai ma Safeenah proposing business Ikram na kula da hidimanta kaman yanda Mommy ta umarceta. Safeenah na son amsar tayin kasuwancin ko dan ta birge Daddy sann clients d’in ta kula manyan Kamu ne wanda companynsu zasu amfan dasu sosai, bazataso tai masu asara su rasa clients ba. Matsalan mutanen sun saka date din had’uwarsu bayan aurensu da kwanaki k’alilan hasalima cikin week d’in Bikin ne.. Ikram na hankalce da ita idan zatai waya sai ta tashi ko cikin taron mutane ne sabida bata so wani ya fahimci kasuwanci take k’ullawa kar a dakatar da ita ace Amarya ce Ita, gashi mutanen sunce da ita kawai zasu tattauna kasuwancin idan ba haka ba kuma su janye. Ikram duk bata fahimci kasuwanci Safeenah ke k’ok’arin k’ullawa ba sabida abinda Mommy ta sanar da ita. Ga waya da Safeenar take akai akai kuma ba da Yayanta Mu’azzam ba, dik abinda ake ciki Tana sanar da Mommy.. Mommy tace taci gaba da saka ido har su gano mugayen da suka d’auke hankalin Safeenah wanda har lokacin aurenta bata rabu dasu ba.

Safeenah ta bar wayarta saman mirror Ta shiga bathroom nan sak’on adireshi na yanda zasu had’u ya shigo wayar.

Ikram ta d’aga wayar tana karanta sak’on wanda notification ya bayyana sa a saman screen d’in wayar. Cikin sauri Tai snapping notification da nata wayar ta d’auki hoton adireshin taje Ta nunawa Mommy.

Mommy ta jinjina kai tana murmushi had’ida duban Ikram tace “You see, kinga magana ta ta fito fili ko.. kinga abinda nake fad’a miki ko.. Safeenah tana nema Ta tona mana asiri.. Yanzu zaki sake min taimako na gaba Ikram..”

Ikram ta jinjina kai a hankali cikin sanyin jiki da rashin jin dad’in abinda ke faruwa.

Mommy Ta dafata tace “Kar ki damu zamu taimaki Safeenah kinji koh.. Yanzu zakije wann location d’in da time d’in da suka saka da date da komai dan mu gano wanene wann mutumin mai neman lalata rayuwar auren Safeenah.”

Ikram tai shiru kaman mai nazari.. Maiyasa Mommy zatace taje wann location d’in.?

Mommy kaw kaman tasan tunanin mai take. Ta dafata tana rau rau da idanu “You promised me Ikram... Help a mother please.”

Yanda Mommy tai maganar duk sai jikinta yai sanyi. A hankali Ikram Ta jinjina kanta “Zanjeni Mommy.”

Mommy Ta murmusa tana goge k’wallan da suka ciwo idanunta tace “Na gode K’warai Ikram.. Allah shi miki albarka.”

Shiru Ikram tai jikinta dik a sanyaye ba tareda Ta iya cewa komai ba. Ko da zataje wnn location d’in gaba d’aya hankalinta bai kwanta. Bataso tai disappointing Mommy dan sosai take ganin k’imarta da girmanta, dole ta aikata abinda Mommy ta umarceta koda bata so.. Da wann tunani ta tsaida zuciyarta kuma Mommy tace kar ta tafi da driver ta shiga cab tinda abin nasu ‘yar sirri ne. Hakan yasa tai kiran Musaddiq dan Allah ya gani tsoro take.

Mommy na hankalce da Ita, Ta kula hankalin yarinyar bai kwanta ba.

Aiko Musaddiq na isa da kad’an Sagir ya k’araso, sanda Sagir ya k’araso Musaddiq ya fad’i wajen tamkar sumamme Ikram nata kiran sunansa tana fad’in ya tashi su gudu dan Ta fara tsoron wajen. Amma inaa Musaddiq baima San duniyar da yake ba tamkar sumamme tamkar mai bacci.

Sagir ya k’araso yana Washe baki “What do we have here..” Ya fad’i yana wani shafe baki.

Ikram taci gaba da jijjiga Musaddiq tana fad’in ya tashi.

Sagir yaci gaba da matsowa Ikram na hawaye ta shiga jada baya tana girgiza kai “Please don’t hurt me.. Just stay back.. Don’t come near me..!”

Bai fasa matsowa yana sakin muguwar murmushi ba.

Cikin kuka take waige waige tana furta “Mommy please help me.. Mommy..Mommy..!” Daidai lokacin Sagir ya cimmata.. Ta soma kiciniya tana kiran sunan Musaddiq dake kwance kan ya tashi ya taimaketa.. Inaa babu abinda ya canza.. Tai k’arfin halin gantsara masa cizo a hannu take ya d’auketa da jahilar mari wanda saida yasa Ta zube k’asa.. Kuka take tana rarrafawa alamun neman hanyar tsira.. Sagir ya shiga janyota a k’asa yana kuma kai mata wasu marin.. Abin tausayi abin tashin hankali.. Babu imani ya rabata da mutuncinta ya mata wulak’anci mafi muni..

Daidai lokacin Danger ya k’araso ya tadda Musaddiq kwance gefe ga Ikram tamkar maras numfashi ga Sagir tsaye gefe yana wani Washe baki.

Danger ya k’arasa ya shiga kai masa duka yana fad’in “That’s not the plan you Bastard.. Mai ka aikata..?”

Sagir na dariya yake fad’in “She’s going to die anyway.. So kafin ta mutu gwara na rage zafi da ita.. She’s beautiful, after all.”

Danger ya ciro bindiga ya saita Sagir dashi kan kace mai ya d’ana masa harsashi.

Daidai nan Mommy ta k’araso dan dama jikinta ya bata Ikram zata iya kiran wani ta nemi taimako musamman Musaddiq.

Nan ta tarar da abinda ke faruwa. Sanda taga Ikram dafe k’irjinta tai tace “Muttaqa ba haka mukai ba.. Maiyasa ka mata fyade.?”

Danger yace “Kinsan a tsarina babu mace.. Bani na aikata ba kuma wanda ya aikata na aikasa barzahu.. Itama yanzu sai mu aikata..” Ya k’arashe yana saitata da bindiga.

Mommy tai saurin dakatar dashi kafin ta isa kan Ikram dake fidda numfashi da k’yar.

Ta dubeta hawaye na fitowa daga idanun Mommy, lokaci guda take shafa sumar Ikram “Watak’ila da baki faye shishigi da San bin diddigin al’amara ba da hakan bai faru dake ba. Zanyi kewarki Ikram... Kuma zan sanar da nakasasshiyar uwarki ga abinda ya sameki..”

Idanun Ikram a lumshe hawaye na fitowa daga idanunta Mommy taci gaba da fad’in “Mahaifiyarki ta k’untata min da yawa Ikram.. Mutuwa kad’ai ya mata sassauci gwara ta cazga bak’in cikin rayuwa.. Zan kasheki da hannuna kaman yanda na kashe mahaifinki..”

Daidai lokacin Ikram ta Ware lumsassun idanunta ta sauk’esu kan Mommy dake rik’e da bindiga tayi pointing d’inta. A hankali ta kuma lumshe idanun nata hawaye suka kuma gangaro mata.. Mommy na cazgan kuka ta d’ana mata harsashi tau! Ta kasheta.

Gefe ta koma tana kuka sosai kafin Danger ya k’aradu yana fad’in “Gawarwaki guda biyu.. How do we get rid of the bodies..?”

Mommy tace “Mu k’onasu ta yanda bazaa gane ba.”

Danger ya girgiza kai yace “Yayanta D’ansanda ne kuma one of their best agents, nayi imani idan mun Had’iye gawarwakin nan ne Sai ya gano mu.. Abun yi kawai mu saka bindigar cikin hannun Sagir.. Kinga shikenan zai zamana Sagir shi ya kasheta bayan ya mata fyad’e sann ya kashe kansa. Babu sauran zargi.”

Mommy tai saurin jinjina kai kafin ta juyo ta dubi Musaddiq dake kwance “Ni zan kula da Musaddiq kai ka k’arasa sauran aikin.”

Danger ya jinjina mata kai sukai duk yanda suka tsara.

Hular Musaddiq da ya fad’i a wajen Danger ya d’auka yana murmushi “Hular nephew d’ina..” Ya kuma murmusawa kafin ya saka hular akansa. Wann shine dalilin da hular Musaddiq ya isa hannun Danger har Mu’azzam ya tsinci hular a business location d’in Danger.

Wad’ann sune abubuwan da suka faru a baya. Tashin hankula da duk wani k’ulle k’ullen da suka wakana. Allah ka rabamu da sharrin son zuciya. Ka shiga tsakanin na gari da mugu a ko Ina...

_CIGABAN LABARI_

Banda sautin fitan kuka babu abinda kake iyaji a parlorn bayan Mommy ta bada labarin duk abubuwan muguntar da Ta aikata. Inne ma na hawaye take furta “Inaji duk laifina ne.. Laifi d’aya ne tak da na aikata Allah ya jarabceni da samun sirka irinki a ahalina Hajara.. Kin tarwatsa min ahali.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.. Hakkin rayuka biyu da na d’auka Harira da abinda ke cikinta kin kashe rayuka biyu a ahalina.. Kin kashe D’ana Habubakar sann kika kashe jikata Ikram.. Kaico na Kaicon son zuciya.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un..! Ku yafe mun ku yafeni laifin duk nawa ne ya shafeku..!” Ta k’arashe tana dafe k’irjinta cikin wane irin yanayi hawaye na kuma gangaro mata..

Uncle Salman ma hawaye yake furta “Ashe kece kika kashe D’anuwanmu kike yunk’urin d’aura laifin akanmu.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.. Ban tab’a danasanin son abin duniya irin yau ba.. Ban tab’a ji duniya da abinda ke cikinta Sun fita akaina irin yau ba.. Ashe ni da Shemau shashashai kika d’aukemu.. Hasbunallahu wa ni’imal wakil.. Allah mun tuba.. Allah kad’ai shi zai maganin azzaluma irinki Hajara.!” Ya k’arashe cikin rawar murya irinta mai kuka.
Chapter 160 · 0% Book details